52
️❄️❄️❄️❄️
*Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*•°ѕadaυĸarwa ga Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*
*ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
____________________________________
💥
*°PAGE 52•*
*NOT EDITED❌*
Misalin sha d'aya da rabi na dare aka sauke captain Sumayyah da Fulani ah army barrack na garin Kaduna,kallo d'aya zakayiwa fulani kasan cewa cike take da tsoro tamk'ar kace mata arrr! ta arce ah guje.
Captain Sumayyah ta dubi sojan dake hakimce ah kujerar mai zaman banza bayan ta sakko daga cikin motar tace"Corporal Aliyu inason ku tursasa wa'ennan samarin har sai sun gaya muku wanda sukewa aiki,idan kuma suka ki toh ku tabbatar da cewa kun azabtar dasu yadda ya kamata,ita kuma yarinyar gobe insha Allahu zan taho da ita,yanxu ma don dai ina da buqatar hutu ne if not ai dana biku,haba haba tun shekaranjiya dana zo Kaduna ban fa runtsa ba ina kan aiki don haka kaji nace wallahi goben bazan musu da sauki ba don haka gara dai ku basu shawarar su gaya muku gaskiya tun wuri if not nawa hukuncin zaifi muni......"
Corporal Aliyu ya d'an duk'ar da kai yace"An gama ranki shi dad'e,zamuyi yadda kikace da yardan Allah ba za'a samu wata matsala ba..."
"Good...oya maza yi sauri kubi bayansu seargent Bangis,Goodnite...."
Ah 360 suka bar wajen.Ta juya ga Fulani wacce take b'oye abayanta don ita harga Allah tsoron had'a idanuwa da Captain Sumayyar take.Ita kanta ta lura da yadda Fulani ta kame jiki tamk'ar mai jin sanyi,sai ta saddar da kai kasa don kada ta had'a ido da Captain.
Fesar da iska Captain Sumayyah tayi tare da watsa hannayenta cikin aljihun wandonta tace"Yarinya ki saki jikinki don kin fad'o hannu mai k'yau, babu cutarwar da zamu miki face tseratar dake daga hannun azzalumai......"
Babu zato babu tsammani sai kawai Fulani ta fidda hannunta ta kamo hannayen Captain Sumayyah, wannan karon babu alamun tsoro atattare da ita tace cikin k'aryewar murya"Don Allah mama! na rokeki ki taimakeni ki rikeni awajenki zuwa wani d'an lokaci,wlhy bazan iya komawa ba......"
Gaban Captain Sumayyah ne ya bada rasss!! Axuciyarta tace"Mama kuma? _bazan iya komawa ba_ ...toh ina ne bazata iya komawa ba?inda ta fiton ne bata son ta koma ko menene?kai lamarin yarinyar nan yana buqatar bincike......"
Ahankali tace"Mu shiga daga ciki sai muyi magana kinji?"
"Toh...." Ta fad'a cikin sanyin murya kana tabi bayan Captain Sumayyah da sauri saurinta.
Babban barrack ne wanda ya tara manya da kuma kananan sojoji,b'angaren manyan daban haka zalika na kananan ma daban yake,toh kasancewar Captain Sumayyah babbar soja ce shiyasa aka tsara mata nata gidan mai dan banzar k'yau madaidaici sannan aka zuba mata sojoji masu hidima maza da matansu.Ainihin location dinta Abuja ne amma wasu lokutan akan turata wasu garuruwa don aiwatar da aiki,wani sa'in tayi kwanaki,sati infact har watanni.Yanxu haka aikin ne ya kawota Kaduna kuma dama aikin sati daya ne sai gashi Allah yasa taci nasara kansu Prosper.
Suna shiga ciki tayiwa Fulani tayin zama kana tasa aka kawo mata abinci.Dama gashi Fulanin yunwa takeji sosai tamk'ar hanjinta zai tsinke,rabonta da abinci tunda tabar asibiti.Sakkowa tayi kasa ta shiga cin abincin ayunwace,farar shinkafa ce da jar miya wanda yasha zok'o-zokon naman kaji.
Captain Sumayyah ta d'an murmusa cike da tausayinta tace"Bari na d'an watsa ruwa na fito,kema idan kin gama saiki watsa kinji ko?"
"Toh abincin fa Mama ai da kema kin zauna kinci tukun...." Ta fad'a da fuskar tausayi.Sosai Captain Sumayyah kejin dadin mamar da Fulanin ke k'iranta dashi kasancewar bata da 'ya mace sai d'a tilo daya mai suna *'AMAAN'*.
"karki damu naci abinci kafin na fita sannan kuma bani cin abinci mai nauyi late at night,kema din don naga alamun yunwa ne atattare dake if not bazan bari kici abu mai nauyi ba yanxu....."
Tana gama fad'ar hakan tayi gaba ayayin da Fulani tabi bayanta da kallo.
"Ashe haka take da saukin kai?afarko idan baka fahimceta ba sai kayi tunanin Kamar zatayi mugunta,gashi komanta da tsari take yinsa...." zantukan da Fulani tayi kenan acikin zuciyarta.
Ba'a wani dau tsawon lokaci ba sai ga Captain Sumayyah ta fito cikin kayan baccinta pyjamas wanda ba karamin k'yau yai mata ba har yasa ta koma tamk'ar 'yar 25 alhalin she's clicking almost 40.
Fulani kasa dauke idonta daga gareta tayi don sosai tai mata k'yau,sai taji inama ace itace.Bata gama tunaninta ba taji tace"Oya baby maza tashi kije kema ki watsa an had'a miki ruwan,Rose pls direct her to the bathroom sannan ki zab'a mata kayan baccin da zata saka,ki kuma dauro alwala ki rama sallolinki don nasan ana binki bashinta....."
Daga ita har Fulanin suka murmusa.Atakaice dai sai misalin karfe d'aya saura suka samu lokacin ganawa.Awannan lokacin duk wani mutumin arziki yana kwance yana hutawarsa sai wanda matsalolin rayuwa suka sanyashi agaba ya kasa baccin,sai kuma azzalumai wanda suka maida dare lokacin ayyukansu.
Captain Sumayyah ta buqaci da Fulani ta bata labarinta,kuka Fulanin ta fashe dashi
Da sauri Captain tace"Shhhhhh! ba kuka nace kimin ba amsa nakeson ki bani idan ba haka ba zan zaneki kina jina ko?kuma wallahi i mean it bawai da wasa nake ba....."
Da sauri Fulani ta gumtse kukanta tace"Naji Mama zan fad'a miki....."
Captain tayi calming nerves nata down tace"Good....yanxu gayamin *WACECE KE?* sannan kuma ah ina wa'ennan samarin suka ganki har suka satoki?
Fulani ta matse kwalla kan ta durkusa ta kamo hannun Captain tace"Mama na rokeki idan kina yiwa Allah da annabinsa kibar wannan zancen tukunna donni dai ahalin yanxu bazan iya tuna komai ba,amma nai miki alqawari insha Allahu nan gaba zan gaya miki duk wani abinda ya dace ki sani agame da *'AISHATU FULANI'* ,nidai abinda nakeso dake shine inason ki rikeni tamk'ar 'yar da kika haifa sannan kita min addu'a Allah yasa komai ya dawo min aka,idan kuma lokacin tafiyata tayi zan sanar miki,mama don Allah ki taimaka don ......."
"Aisha ya isa hakanan,zan taimakeki ko don yadda kika daukeni mahaifiya agareki,amma ina mai tabbatar miki da cewa bazan miki da sauki ba idan har na samu wani labari sab'anin abinda kika gayen,don haka so nake kice mama abinda na gaya miki tsakanina da Allah gaskiya ne,kuma kar ayi wani bincike har sai na tuna komai da kaina...."
Da sauri Fulani tace"Mama wallahi ki yadda dani bazan ma iya tuna inda suka dakkoni ba don alokacin ba'a cikin hayyacina nake ba amma kina iya tambayarsu,saidai don Allah mama karki maidani....." Ta sake barkewa da kuka.
Lokaci daya kan Captain ya daure,itafa ta kasa gane lamarin yarinyar nan don haka ya zamar mata dole tayi bincike akanta ab'oye,sannan kuma zancen ijjeta awajenta bai taso ba don dole yanxu haka iyayenta nacan na nemanta,she has to do something about Aisha Fulani.Abangaren Fulanin kuwa bawai ta manta da Yarinya bane amma bata son ta koma gareta ne.Ko zata manta da komai toh bokam Mariya baya da ikon sanyata ta manta da gud'an jininta.
Wannan kenan!!
***
Bayan sun zazzauna akan kujeru ah ofishin Dr.Philips,Dr.Philips ya shiga binsu da mugun kallo d'aya bayan d'aya ayayin da tsanar Awwalu ke dad'a ratsa bargon xuciyarsa.
Cike da tsana yace"Yarima Hayatu ina jinka meke tafe daku?"
"Basai mun tsaya wani dogon turanci ko larabci ba ina wannan matar da kuma 'yarta suke wanda dan'uwana ya kawo jinya nan asibitin?
Wayamcewa Dr.Philips yayi yace" Ban fahimci inda zancenka ya dosa ba?wani dan'uwan naka?wata matar?sannan kuma wacce 'yar kake nufi?
Axuciye Hayat yace"Kai Malam banison rainin sense kana jina ko?maza ka tashi kaje ka fito mana dasu right now...."
Dr.Philips shima din axuciye amike yace"Malam get out don bansan meh kake nufi ba...."
Hayat ya dubi Awwal,tun kan yayi magana Awwal yace atsorace"Wallahiiii Yallabai gaskia na fad'a maka nan asibitin muka kawota,karya yake maka yasan komai munafinci ne suka kulla...."
Hayat ya maido kallonsa kan Dr.Philips wanda ya cika da tsananin mamakin Awwalu,Hayat yace dashi"Tunda bazaka gaya min gaskia ba toh ina da buqatar ganin cctv cameras naku duka,inason ganin duk abinda ya faru ah asibitin nan daga on 25th har zuwa yau dinann...."
"Excuse me sir! U don't have the right to come into my office and be giving me commands,baka da right din da zaka zo kana bani directives kan aikina,ka tsaya kan matsayinka nima na tsaya akan nawa....."
Wasa wasa fad'a ta kaure tsakaninsu,Dr.Philips ya k'ira securities suka tasa k'eyarsu waje.Hayat sai fadi yake yana dad'a nanatawa"Zakasan ka tab'a Hayatudden Bahago wallahi,ka shiga list...." Toh babu wanda ya baiwa maganarsa muhimmanci ballantana ayi tunanin da akwai wata akasa.
Bayan sun bar asibitin Hayat yace "Yanxu Jabir shine next target dina,dole ne ya gayan inda suka b'oye matar nan dashi da dan iskan likitan nan....."
Ya zaro wayarsa ya latso Jabir,shi kuwa Jabir awannan lokacin yana kan hanya don ya yanke shawarar kai Yarinya gidan gajeyu(orphanage home) dake cikin garin minna,don haka Minna ya koma.
Yana ganin k'iran Hayat jikinsa ya dauki rawa,dakyar ya natsu ya dauka.
Yana daukawa Hayat bai bari yayi magana ba yace"Ina kake?"
Cikin in-ina yace"Am...Am... Nadan fita ne,lafiya dai ko?"
"Ganinka nakeson yi nan da awa d'aya kacal....." Ya bashi amsa atakaice.
Jabir yace "Toh an gama yallabai...."
Alokacin kuma Yarinya ta d'an tsala ihu,da sauri Jabir ya tsohe mata baki.
Cike da zarginsa Hayat yace"Ya nake jin kukan Yarinya ne sannan kuma Kamar kana cikin abin hawa don ina jin karar iska......"
Da sauri Jabir ya datse call din tare da kashe wayar gabaki daya atsorace.
Hayat ya dubi Awwal yace "Zargina akan Jabir ya tabbata gaskiya,ina ganin yanxu haka ma yana tare da Matar ne don naji ihun jinjira,yanxu ina mafita?
Awwalu yace" Kawai muje gida sai ka jira zuwansa sannan ka tursasashi ya gaya maka inda suka b'oyeta...."
"An gama......"
**
Jabir na sauka amotar haya ya tari adaidaita wanda ya kaishi har kofar gidan marayu.Ya nemi wani tsohon abokinsa dake aiki agidan.Bayan sun gaisa Mal.Ahmadu yace"Kai Jabiru ina ka samo Jinjira ne kuma?"
Toh dayake akwai aminci na gaskiya atsakaninsu sai Jabir ya warware masa komai,Babu abinda Mal.Ahmadu ya iya cewa sai "Ikon Allah" shine abinda yake ta fad'a yana kuma nanatawa.
Jabir yace"Yanxu so nake na baka amanar wannan yarinyar Ahmadu donna yadda dakai akwaika amana,nasan zaka rufawa mai girma sarkin Minna asiri,bazaka so ace sunansa ya b'ace ba ko don kirkinsa ga al'umma,don Allah ka taimaki martabarsa...."
Da sauri Ahmadu yace"Haba! Jabiru har sai ka rokeni?karka damu ni kaina bazan so ace sunan mai martaba ya b'ace ba,don haka insha Allahu yanxu zan samo mata uwar rik'onta mama sameera wacce itace mai kula da jira-jirai,shi kuma Yarima Hayat Allah ya shiryeshi don kiyayyar da yakewa dan'uwansa ya wuce misali,gashi dan'uwan na daukarsa tamk'ar mutumin kirki alhalin makashinsa kenan,Allah ya k'yauta,ya sunan yarinyar?"
Sai alokacin Jabir ya tuna cewa ba'a sa mata suna ba kuma idan har lissafinsa daidai ne toh kuwa yau ne kwanakinta bakwai aduniya,yayiwa Mal.Ahmadu bayanin hakan kuma yace ashirye yake asiyo ragon sunanta.
Cikin awa daya kacal aka siyo rago aka yankawa Yarinya,Jabir ya tuna lokacin da za'a shigar da Fulani tiyata tace masa _*"Don Allah Babban Yayah idan ban tashi ba na rokeka ka kaiwa Yallabai *'YARINYATA'* ,na bashi ita halak-malak don nasan zai dorata kan ingantacciyar rayuwa,asanya mata suna *'HIBBATULLAH'* ,ma'ana k'yauta daga Allah....*_
Hawaye yad'an cicciko masa,yace"Aishatu ayau na iya cika miki burinki guda wato sanyawa 'yarki suna *'HIBBATULLAHI'* (KYAUTA DAGA ALLAH) amma na kasa cika miki dayar burinki wato baiwa Yallabai 'yar sabida wasu dalilai amma na tabbata komai zai lafa nan bada jimawa ba insha Allah,kuma kema na rokeki aduk inda kike ki dawo garemu....."
Ji yayi an dafashi daga bayansa,da sauri ya juya sukai ido hudu da Mal.Ahmadu,ya saukar da ajiyar xuciya mai nauyin gaske don na karamin tsorata yayi ba,Mal.Ahmadu yace"Muje ciki ka sake damka amanar *HIBBATULLAH* ga iyayen rikonta abokina....."
Sai kusan karfe hudu ta yamma Jabir ya baro gidan marayu cike da dacin rai na rabuwarsa da Hibbatullah wanda har hawaye sai da yayi,ya cika iyayen rikonta da makud'en kudad'e da za'ana kula da buqatun 'yar,kai infact hadda sauran 'ya'yan ma zasu sha inuwar *HIBBATULLAH*
Ya dauki alqawarin zuwa yana dubata lokaci zuwa lokaci har lamuran su daidaita.
Sai awannan lokacin Jabir ya kunna wayarsa kuma ayanxu ne ya yanke shawarar xuwa ga Yarima Hayat tunda dai yasan ya riga ya gama komai
_*Yanxu muma sai mubi bayansa muga wainar da za'a Toya*_
_*Masha Allah!yanxu sunan littafi ya fito,welcome *'HIBBATULLAH'*_
_*Yanxu labarin rayuwar Hibbah zaya soma,fasten ur seat belt 💯*_
*#Intelligent_Writers#*
*#HIBBATULLAH*#
*#OFFICIAL_HAFNANCY*#
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top