51

❄️❄️❄️❄️❄️
     *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
       ❄️❄️❄️❄️❄️

      *°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*

*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*

    *MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*

*WATTPAD:HAFNANCY*

https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/

*•°ѕadaυĸarwa ga Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*

*ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

____________________________________
                        💥
*°PAGE 51•*
 
    *NOT EDITED❌*

   _*√My wattpadian's and my watsap fan's I know how much u all love diz book and I will try my possible best to complete it insha Allah,nidai hadin kawunanku kawai nakeso,comment line by line and touch dat star hakan shine zai bani kwarin gwiwa,Good morning all and have a nyc day ahead,Hafnancy cares°*_

                 💥
    

..........Kafin su karasa garin kaduna tuni Kunnama da kuma Dragon da suka sanyata atsakiya sun bubbuge da bacci sabida barasar da suka tuttulawa cikinsu,sai ya rage prosper dake tuk'i wanda shima din idanuwansa cike suke da baccin dauriya kurum yake tayi.

  Ganin kowannensu yayi nisa da baccin ya sanya Fulani soma warware igiyar da suka daure mata hannu dashi,dake ba wani kwakkwaran dauri sukai mata ba shiyasa nan da nan ta kwanceshi,tana gamawa tayi saurin kai hannu ta zare plaster din da suka rufe mata baki,duk abinnan da take tayi ko kadan prosper beda masaniya don gabaki daya hankalinsa na kan hanya ne,yanxu akalla za'a ga sha daya ta dare ta kusa don sun daya awani wajen suka karbi abu.

   Bindigar dake atsakanin kafafuwar Dragon ta daga dakyar,cikin dauriya tayi shahada ta tsaitashi adaidai keyar prosper tace da iya k'arfinta"Koka tsaya na sauka ko kuma na fasa maka kai da alburushi yanxun nan kuwa...."

Jikin prosper ne ya hau rawa,gashi yana son ya juyo da kansa gareta amma yana tsoron karta danna kunnamar bindigar ta harbeshi har lahira kuwa,ya rasa meh zaiyi da har zai iya tada sokwayen abokanan cin mushen nasu.

     "Baby drop the gun first...." Ya fad'a ayayin da muryarsa take rawa sosai.Toh ita dai Fulani ba jin yaren tayi ba don haka sai tace"malam karka raina min hankali nace ka tsaida motar ko?idan kaki toh kuwa ina mai shaida maka cewa yanxun nan kuwa lahira zatayi baki don nima dinnan da kuka ganni na fiku bushesshiyar xuciya,don banga wani abin da yayi saura ga mace mara imani ba wacce ta gudu tabar 'yar jinjirarta mai kwana shidda aduniya ba,tunda har kuwa na iya aikata hakan,toh nasan kun kwana da sanin cewa babu makawa zan iya aikata abinda na fad'a......."

   "Wai su waye ke mana hayaniya ne haka mutum na morar baccinsa mai dadi?meke faruwa ne......?

Cak! ya tsaya yana kallonta baki wangale sabida tsananin mamakin ganin hannunta rike da bindiga adaidai saitin k'eyar prosper.

     " Bindiga kuma?ke waye ce ki daukata ko an gaya miki abar wasa ce?" Dragon yakai hannu zai karbe bindigar,da sauri ta mayar da saitinsa kan goshinsa wanda hakance ta sanya cikinsa durar ruwa.

  Atsiwace tace"Ahir! dinka karma ka soma don wallahi ina iya kashe kowa acikin motan nan hatta dani kaina idan lamuran suka cakud'e suka kuma lalace,watakila bamu da rabo don babu tantama gabaki dayanmu anan nasan mu din 'yan wuta ne,don haka ina ga gara din mu mutu duka muje mu tarar da azabar Allah acan,wallahi kunji dai nace wallahi bazan tab'a bari Ku kashe ni ba saidai mu tafi tare,idan kuma baku son ku mutu toh ashe rayuwa tana da dadi shine ni kukeson ku hallakani?kamar yadda kuke da masoya haka nima nake dasu wanda bazan so ace an rabani dasu ta k'arfi da yaji ba sai dai idan wa'adina ne ya cika,haba bayin Allah meyasa kuka dauki duniya da zafi ne?ku tuna fa akwai mutuwa,akwai hisabi sannan kuma akwai tsayuwa agaban Allah gobe kiyama,Allah zai fa bimin haqqina dana masoyana akan kashenin da kukai,har nawa ne za'a baku da har zai iya kareku daga azabar Allah gobe kiyama?ku gayamin nawa ne?amma shikenan idan kunfi son kudin akan hisabinmu aranar da zamu tsaya akotun Allah shikenan ku hanzarta aiwatar da kudirinku akaina........."

   "guys mu mayar da ita kawai wallahi maganganunta sun matukar kashe min jiki...." Acewar Dragon wanda har ya soma hawaye don dama can beyi nisa sosai ba acikin wannan harkan.

Da sauri Kunnama ya tari numfashinsa"Kan babban bura uba......10million fa oga Nabalaska ya bamu ya kuma ce zai mana cikon miliyan biyar shine kake cewa mu saketa?amma wallahi Dragon ban San cewa kai wawa bane sai yau..."

  Wasa wasa fa fad'a sosai ya kaure tsakanin samarin,prosper da Kunnama sunki bada hadin kai,sai ya zamana Dragon ne kurum ke bayanta,motarsu ta soma karkacewa tana zuwa gefa sabida mai tukin ya sanya hannu cikin fadar,sai ji kake kiiiiiiiiii!kiiiiiiiiiiiiii! Sautin da motar ke badawa kenan,Aisha fulani kuwa sai ihu da salati take ta sakewa don kam tasha unexpected blows sosai ayayin da mazan ke gwabzawa.

  Adaidai wannan lokacin kuma motar *'CAPTAIN SUMAYYAH'* na tafe abayansu.Captain Sumayyah tace da yaranta"Boys I said it,tun dazu naketa gaya muku cewa nidai ban yadda da waccan motar ba amma kunce everything is cool,yanxu da fatar kunji ihun mace sannan kuma da yadda motar ke kokarin somalsaulting?"

  Gaba dayansu sukace"Yes! Captain da gaskiyarki bari muyi saurin shan gabansu,kai seargent Musa k'ara gudun motar" acewar babban cikinsu.

Ai kuwa neatly suka sha gabansu suka tare hanya,wani irin wawan birki Prosper yajah wanda kadan ya rage ya bugesu amma ko ajikinsu don zakuna kuke gani awajen,cikin prosper ne ya bada kuuuuuuuut! ganin zugar sojoji agaban motarsu wanda wutar motarsa ce ta taimaka masa wajen ganinsu,dama night duty Captain Sumayyah suka fito yi don ana zargin akwai masu garkuwa da mutane agarin Kaduna don ana dama labarin hakan.

   Cike da tsoro yace"Guys kubar shirme ku kalli gabanku...." Sai alokacin suka lura cewar motar ta tsaya,suka kalli inda yake kallo suka gan sojoji,habawa nan da nan suka birkice,ita kuwa Fulani babu abinda take yi sai hamdala acikin zuciyarta na ganin ta samu masu taimakonta.

   Gani sukai an bud'ewa wata classic army woman kofa ta fito tana takowa sannu ahankali xuwa ga motarsu,da sauri Prosper ya rike sitiyari yana kokarin juyawa zuwa 180,sai dai kuma ya makaro don ta bayan nasa ma akwai wasu sojojin don dama motoci biyu ne keta bibiyar motarsa.

   Sauran sojojin suka rufawa Captain Sumayyah baya,tana isa tasa hannu ta bubbude murfa yen motocin.

   '"Don Allah ku ceceni kasheni sukeson suyi...." Haka sukaji an fad'a tare da barkewa da matsanancin kuka.

  Sai asannan ne kallonta ya sauka kan Fulani kuma ta tabbata satota din sukayi,ai bata San lokacin da tayi wani kukan kura ba ta shak'o kunnama wanda shine yafi kusanci da ita,tace"Wato kune masu sace mutane kuna garkuwa dasu ko?toh yau kwanakinku sun Kare aduniya,maza boys afito dasu ayi gaba dasu,kuma ahorasu da shock da ruwan kankara har safe kafin sauran hukuncin ya biyo baya......"

   Kuka dukansu suka shiga yi hadda majina suna roko amma haka suna ji suna gani aka tasa keyarsu zuwa daya daga cikin motar,amma kam sun daku ba kadan ba har suka baiwa Fulani tausayi.

  Captain Sumayyah ta mayar da kallonta ga Fulani wacce ke kaduwar sanyi tace"Daga ina ne suka satoki?"

   Gabanta ya yanke ya fadi,amma sai ta fashe mata da kuka,juyin duniyar nan tayi da ita ta fad'a mata amma sai kuka take tayi,can captain tace"Wuce muje don akwai case dake acikin wannan al'amarin kafin mu sakeki......."

Gaban Fulani ya sake tsinkewa,azuciyarta tace"Kuma dai?" Haka tana ji tana kuma gani akai gaba da ita amma tare da captain ta zauna abayan mota,wani acikin sojojin ne ya tuk'a motarsu Prosper da akayi condemning dinsa can gefe.

   Wannan kenan!

***
     Bakwai da rabi tayiwa Jabir ah Bida,dama Dr.Philips yasan da batun zuwansa don haka ba tare da wani b'ata lokaci ba suka had'e.Tafe suke suna hira ayayin da suka nufi dakin da aka kwantar da Fulani.

    Dr.Philips yace"Yauwa mutumina kana jina ko?wallahi jiya ni banma San da tafiyar Yallabai ba don bemin sallama ba (alokacin da shida su Abida suka wuce kenan),sai can ga Nurse Asmy wai ba'a ga Aisha ba,nace baa ganta ba fa kikace?tace eh kuma tabar yarinya akan gado,hankali tace na biyo bayanta don tabbatar da zancenta,har waje muka fito don azatona tana tare dasu Yallabai ne ashe dai da gasken guduwa tayi tunda kace Yallabai ma beda labari,yanxu bani son ya sani har sai ya dawo daga tafiyarsa amma yanxu meye shawararka agame da wannan al'amarin?ta ina zamu soma?"

   Jabir beso fallasa masa shirin Hayat ba amma ya zama dole tunda har yana son taimakon megidansa ne,kakaf! ya warware masa komai wanda yayi tsananin cika da mamakin Hayat.

Jabir ya karashe da"Yanzu zancen da nake maka yana nan tafe zuwa karfe takwas shiyasa nayi saurin daka sammako,zan dauke jinjirar daga nan asibitin don kar asiri ya tonu,kaga idan har yaga 'yar babban matsala ce,ita kuma uwar saimu cigaba da nemanta asirance har agano inda take."

  Cike da mamakinsa Dr.Philips yace "Idan ka dauketa anan toh ina kuma zaka kaita bayan nurse Asmy tana kula da ita?ka barta man ahannunta ko gidanta ne ai sai ta tafi da ita ai nadan wani gajeran lokaci ne......"

   Jabir yace axuciyarsa"Bazan taba bin shawararka ba don ko kai kanka ban yadda dakai ba,dauke wannan yarinyar daga nan asibitin itace rufin asirin shugabana......"

Azahiri kuma yace"Karka damu na riga na shirya komai tun adaren jiya..." Ya fadi hakan tare da bubbuga kafadar Dr.Philips.Idanuwan Jabir ne ya sauka akasa sai ganin Hayat yayi tare da Awwal suna fitowa cikin mota,wani irin tsananin faduwar gaba ne yaji yakai masa mugun duka ak'irji,yaushe takwas tayi?ai k'arfe takwas dinma Hayat yace zasu taso daga minna kuma tafiyar awa daya da rabi ce don haka beci ace sun iso ba,k'ara murza idanuwansa yayi yaga ko shine bey dai gani dakyau,ai kuwa Haytun ne ba wani mai kama dashi ba(Kai Hayat anyi dan tashar mutum anan,duk wayonka da dabarunka ya fika,yana zargin Jabir amma beda masaniyar nan Jabir din ya taho shiyasa ya dako sammako,ya fasa zuwa takwas din kamar yadda ya fad'a).

   "Ya naga kaja ka tsaya kuma mutumina?meya faru kake kallon kasa kuma?" Dr.Philips ya fadi hakan tare da kai kallonsa kasa inda Jabir din ke kallon abin mamaki na Hayat.Shima din arikice ya maida kallonsa kan Jabir yace"Wai ba kace sai takwas zai kamo hanya ba?toh ko takwas dinma bai gama cika ba ai?kai wannan mutumin akwai ilimin makirci,maza hanzarta muje saika dauki 'yar sannan musan kofar daya kamata ka fita da ita......"

Da sauri-sauri gudu-gudu suka isa dakin da yarinya take,banko k'ofar sukai wanda hakan ba karamin firgita Nurse Asmy yayi ba wacce take sanyawa 'yar pampas bayan ta gama yi mata wanka.

   "lafiya kuke kuwa?Doctor meya faru?ko anga Aishar ne?" Ta jero musu tambayoyi alokaci gud'a.

     "nurse wannan ba lokacin questions and answers bane,taimako zaki mana yanxun nan,tashiwa zakiyi ki tsaya mana abakin kofa kita duba idan kinga wani mai navy blue kaftan tazarce da kuma mai kodadd'iyar koren t-shirt da jeans suna zuwa sai ki gaya mana,ni zan cigaba da shiryata da sauri,oya maza nace......" Acewar Dr.Philips.

Da sauri ta nufi kofar kamar yadda ya umarceta hankalinta tashe,ayayin da Dr.Philips ya dakko riga zai sanyawa yarinya,Jabir beyi wata-wata ba ya kwashi zanin da yake tsammanin na goyonta ne kana ya fizge yarinya daga hannun Dr.Philips ya azata abaya ya daura,daga ita sai pampas babu kaya,kuka ta canyara don sosai fizgar ya shigeta.

   "Kai meye haka Jabir kabi komai ahankali mana,meyesa kake tsananin tsoronsa sai kace wani mala'ikan mutuwa ne....?" Acewar Dr.Philips cike da takaicinsa.

   "Bak'ar makircinsa da salon muguntarsa itace abinda nake tsoro ba shi ba......" Acewar Jabir

"Ga....gasuuu...nan...zuwa...fa...." Suka tsinkayo maganar Nurse Asmy cikin sarkewar murya.

   Ba tare da wani dogon tunani ba Jabir ya nufi wani window ya lek'ata yaga dai bata da wani nisa da kasa kuma sannan akwai wuraren ajje kafafuwa,habawa ai tuni ya haye windon ya sauka kuma adaidai lokacin Hayat ya banko k'ofar dakin ya shigo....................





   *_Fulani Allah yasa kin kubuta kenan,Allah yasa shigowar Captain Sumayyah cikin rayuwarki ya zamo haske (Ameen),army woman kuma oga da kanta,Hahaha ni kaina abin ya burgeni,toh shin wacece ita wannan Captain Sumayyar?,sai nan gaba zamu sani*_

_*Weldon! Jabir agaskiya kayi namijin kokari,wayyo yarinya yaushe ne zakiyi dariya tun sanda aka haifeki sai b'acin rai kike ta kunsa*_

_*Mtsssss! Hayat makirin k'arshe ne wallahi,dan air kawai*_

     _kuyi haquri jiya baku jini ba wallahi rashin chargy awaya ne_

   _Sai kunga next page_

*VOTE*
*COMMENT*
*SHARE*

*#intelligentWriter's#*
*#Hibbatullah*#
*#_Official_Hafnancy#*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top