50
❄️❄️❄️❄️❄️
*Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*•°ѕadaυĸarwa ga Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*
*ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
____________________________________
💥
*PAGE 50*
*NOT EDITED❌*
*°TUKUNNA DAI INA LABARIN FULANI?*•
Bayan tayi nasarar ficewa daga cikin asibitin ba tare da kowa ya ankara da ita ba,taci tafiyar mintuna talatin wanda har ta soma d'an fita daga cikin mutane.Adaidai bakin titi ta tsaya,akalla ta sake kwasar kusan mintuna goma kafin can sai taga wani mota na tahowa da gudunsa,ba tare da tayi wani dogon tunani da kuma nazari ba ta sanya hannu tana kokarin tsaidashi,har motar tayi gaba sai kuma tayi slow down,ahankali matuk'in ya soma dawowa da baya,adaidai gefenta akayi parking.
matuk'in ne ya saukar da gilashin window tare da lek'o da kansa waje,wani irin mayataccen kallo ya soma wulla mata kafin yace"Yan mata yaneh?wani taimako kikeson ayi miki ne?" yayi mata wannan tambayar tare da lashe kasan lips dinsa.
Burin Fulani shine taga ta nisanci Yarinya ayanxu,shiyasa ba tare da dogon nazari ba ta zab'i neman taimakon samarin dake cikin wannan motar,bata damu da abinda zaije yazo ba kawai tace"So nake nidai kawai ku fitar dani daga cikin wannan garin......"
kallon junansu sukai atare cike da mamakin jin irin furucin daya fito daga bakinta,na bayan ne yace musu"ku wai tunanin meh kuma zamu tsaya yi bayan abinda muke ta nema kenan kuma gashi mun samu asaukake?kawai ku gaya mata ta shigo....." ya fad'i hakan ahankali yadda Fulanin bazata ji ba.
kan suyi wata magana tuni na bayan ya bud'e mata gidan baya inda yake zaune yace"Ke! shigo zamu taimaka miki.."
cike da farin ciki kawai ta afka ciki sukayi gaba,sai asannan ne tasan ta tafka babban kuskuren bin wa'ennan samarin sabida lura da tayi da kayan maye ahannun kowannensu,k'irjinta ne ya soma dokawa da k'arfin tsiya alokacin data ga wanda ke zaune agidan gaba ya komo baya,sai suka sanyata atsakiya tare da matseta.
Atsorace ta dubeshi tace "malam meh hakan ke nufi kuma?ya zaka dawo kusa dani kana shisshige min jiki tamk'ar wani mage ?daga taimako?shin dama haka akeyi?
hayak'in sigarin daya zuga ya fesa mata kan fuska kana yace"Ai yarinya mu kika taimakawa bawai ke muka taimaka ba,munan da kika ganmu 'yan garkuwa da mutane ne,tun dazu muke ta farautar wacce zamu sace don 'ya mace budurwa akace mu samo sai gashi cikin ruwan sanyi kin kawo mana kanki,kai prosper garin *KADUNA* muka nufa adaren nan don mu cika wa oga alqawari......."
"Toh k'aramin oga...." haka wanda aka kira da prosper ya fada wanda kuma shine matuk'in.
salati AISHA FULANI ta shiga jerowa ayayin da hawaye ya shiga kwaranyo mata,can ta saki wani razanannen ihu tana fadin"Don Allah na rokeku kumin rai karku kasheni wallahi ina da 'ya bani son ta rasani,bata da kowa sai ni,wallahi bani son taimakon kuma ku saukeni zan koma gareta don tana tsananin buqatata........."
"ihu bayan hari kenan,ji nan yarinya ai kin riga kin kawo kanki garemu don haka babu wani sassaucin da zamu iya maki don mu nan da kika ganmu xuciyar kafirai ce garemu bamu da tausayi ko kadan....." acewar wanda ake kira da kunnama wanda tun asali shine ke zaune agidan baya.kan ta sake yin wani magana tuni suka rufe mata baki da plaster tare da daure mata hannaye,ta shiga shure shure tare da zazzare idanuwa,alokaci daya nadamar abubuwan data aikata ya dawo mata,don tasan hakkin mijinta ne ke bibiyarta ayanxu,komai dake faruwa da ita arayuwa itace silar faruwarsa.
***
Achan Asibitin Bida kuwa,Dr Aisha ta dawo night duty,ta shiga dakin da'aka Kwantar da Aisha Fulani,ta iske *YARINYA* kwance kan gado tanata tsala kuka murmushi tayi kan takarisa tadauketa tana jijjigata tace "Oh Srry Yarinya..mamanki ce ko? tabarki ke kadai ko? sai mun mata bulala"
Tafada tana mata wasa harda dariya..Zuru yarinyar tamata kan takara barkewa da kuka,Dr Aisha tace"Oh ni Aisha kina toilet ne? kiyi maza fa tagaji babyna tana son tasha mama" Shuru Shuru Dr Aisha bataji duriyar Aisha Fulani ba,Dole tasa tasa ta ijje 'yar ta lek'a tiolet din abinda yabata tsoro shine na ganin band'akin wayam babu fulani aciki kuma babu dalilinta.
Hankali amatuk'ar tashe ta fito kai tsaye office din Dr Philips taje ta kirasa shima cikin mamaki ya shigo dakin suka kara bincika ko"ina babu Aisha Fulani ba dalilinta.Har wajen asibitin an duba bata.hakan tasa hankali tashe Dr Philips ya zaro wayarsa yahau laluban maimartaba, amma ina bata shiga shiga yayi iya bakin kokarinsa yakasa samunsa..Hakura yayi kawai saiya k'ira Jabir don dama can ya iske missed calls dinsa toh sai ayanxu ne dai zai tuntubeshi tunda yana mai son Isar da muhimmiyar sak'o don wannan irin labarin bazai iya gayawa mai martaba kai tsaye ba,sai ayanxu ne yaga wautarsa na son gayawa mai martaban afarko.
Bayanin Da Dr Philips ke jerama Jabir shiya kara tadamai hankali..Aisha Fulani ta gudu bata ako'ina,an nemeta an rasa? Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un.." Shine abinda Jabir keta maimaitawa har Dr yakashe waya baisani ba,wannan wani irin iftila"i ne lokaci daya?duk kuma akan Aisha Fulani?
kara neman maimartaba Jabir ya cigaba dayi ammh sharrin Network yaki bari..Gashi dare ya lula babu halin yaje masarauta awannan lokacin...Cikin damuwa da jimami jabir ya kareshe wannan Daren.
Ada can kafin daren ya lula yaso binsu Bidar sabida rashin samunsa da beyi ba awaya amma sai kuma ya samu jikin uwargidan nasa ba dadi,adolensa ya haqura don ya bata kulawarsa wacce take matukar buqata ayanxu.Da abin ya kwana axuciya,shi kuwa mai martaba alokacin koda ya dawo gida bai nemi Jabir ba don akodayaushe suna tare bayan sallar isha'i su d'an tab'a fira ah fada kafin Jabir ya tafi gida,amma ayau da bai gansa ba sai yayi tunanin kila gajiya ce ta hana masa dawowa.
ckin ikon Allah misalin Uku na dare sai ga kiran Mai martaba jabir jikinsa na rawa yadaga kiran..Amma sai meh?kan yayi magana mai martaba ya fesa masa good news din farfad'owar Aryaan,cike da farin ciki mara misaltuwa Jabir ya tayashi murna amma kuma sai ya samu kansa da kasa labartawa mai martaba
zancensu Hayat da kuma labarin guduwar fulani,har suka gama waya zancen fulani bey shiga tsakaninsu ba don shi mai marataba ta d'ansa yake ayanxu bata wani ba.
***
"Acikin wannan daren mai martaba yasamu kira daga mai girma gwamnan jahar Niger a inda yake tayasa murna na farfadowar tilon dansa Aryan(Dama abokai ne sosai dashi da mai martaba) cikin Nuna tsantsan Farincikinsa yace ma mai martaba ya shirya bayan sallar Asubahi su wuce india ta private jet dinsa..murna fal aran maimartaba Wanda har yama kasa b'oyuwa, godiya yayi ta zubama Mai girma gwamna wanda ya kashe waya yana ma maimartaba dariyansu dai na tsofaffun abokai.Ab'angaren Hayat kuwa addu'a yake tayi kan Allah yasa wannan tafiyar ba tare dashi za'ayi ba don ya samu damar aiwatar da kudirin dake ransa kafin mai martaban ya dawo.Ai kuwa addu'arsa ta karbu don yayan nasa ce masa yayi da yayi zamansa ya kula da buqatun jama'a don bazai yuwu ace dukansu su bar gari hakanan ba.Hayat tamk'ar ya zuba ruwa ak'asa yasha don murna.
*WASHEGARI*
*Misalin 5:15*
Harsu mai martaba sun shirya tafiya,dashi da kuma wani kanin babansu zasu sai kuma mai girma gwamna,kafin su tafi mai martaba yajah Jabir ah gefe tare da zaro bandir din makud'en kud'ade ya mikawa Jabir yace"Jabir karbi nan akula da buqatun Aisha Fulani,na rokeka don Allah Ku rike min amana kaida Awwal,kar abari kowa yasan da labarinta,idan na dawo zamu san yadda zamuyi da ita insha Allah,amma for now Dr.Philips ya cigaba da tsare mana ita,ya naga kayi shiru Jabir karbi man....."
Hannu na rawa Jabir ya karbi kud'aden,kamar yace masa ai asiri ya tonu sannan ma kuma ai Aisha fulanin ta gudu amma yasan yana fadin hakan zai batawa shugaban nasa komai.Ahaka su mai martaba suka nufi airport don acan private jet din gwamna take.
*
Misalin Shidda da rabi Jabir ya kama hanyar Bida don ya sake jin tattaunawarsu Hayat,Hayat din ya buqaci Awwalu ya kaishi asibitin da Fulanin take da karfe takwas na safe,shiyasa Jabir yayi saurin daka sammako kafin su rigashi.
_*Tofa!Fulani ta sake fadawa cikin wani mugun hannun,Allah sarki Allah ya kawo miki dauki*_
_*Bari muga ya zata k'aya tsakanin Jabir da Hayat?*_
_*Insha Allahu zanta kokari naga na baku two pages arana amma fa banyi alqawari na*_
*VOTE*
*COMMENT*
*SHARE*
*#IntelligentWriter's#*
*#Hibbatullah#*
*#_Official_Hafnancy#*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top