49

  ❄️❄️❄️❄️❄️
     *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
       ❄️❄️❄️❄️❄️

      *°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*

*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*

    *MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*

*WATTPAD:HAFNANCY*

https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/

*•°ѕadaυĸarwa ga Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*

*ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

____________________________________
                        💥

   _*Kuyi breakfast da wannan,lunch nanan tafe anjima insha Allah*_

   *NOT EDITED❌*

 

       *PAGE 49*

  Sai bayan Hayat ya samu nutsuwarsa sosai,toh asannan ne tunanin wanda yayi musu lab'e ah dazu ya dawo mai,sosai ya soma zurfafa tunani akansa,yaga dai gaggawa banasa bane yafara bibiya da kuma binciken wani Mahalukin ne yayi mishi lab'e?gwara kawai yabi komai asannu.

  Duk wani kokarin Hayat na sanin ko waye wannan tantirin acewarsa kenan amma ya kasa gane ko waye Saboda bai gansa ba inuwarsa kawai yagani.Ganin xuciyarsa ta soma tafasa tamk'ar d'anyar ganda ya sashi kulle babin wannan d'an talikin kana ya shiga duniyar tunanin mak'iyinsa domin shi kaf aduniyan nan mak'iyinsa guda d'aya ne Wato *MAI MARTABA FARUQ* Sai kuma Najmiyyah wanda laifin Faruq dinne ya shafeta,shi fa ko kadan baya son ne Faruq yaji dadin Rayuwarsa so yake gaba daya rayuwarsa takare a useless babu wani amfani..

   Labarin Da Awwalu yabasa shi yakara sakashi cikin matukar Farinciki da murna domin yasan Fitowar labrin kamar wani bangarene na tarwatsa shi Faruq din,domin mutumcinsa da martabarsa zata zub'e ne ah idon talakawansa wa inda suke yabonsa uwa uba Najmiyyah ya tabbatar zamansu zai lalace harma Kila auren nasu ya rab'e..Kunga shikenan komai yazo mai Da sauki,tunanin Hakan ne ya sashi mikewa cikin tsantsar farinciki tare da Furta.

  "Yes...Yes...komai na tafiya daidai yadda nakeso..Am sorry Yah King duk laifinka ne dakayi tarrayya dani cikin abinda nake so kuma kayi sanadin nesanta ni da abin da xuciyata take matuk'ar so da kuma qauna,kasa akamin iyaka da Najmiy Gaddafi sannan kayi sanadin fad'awata cikin rough life da kuma kuncin rayuwa don haka inason ka sani kamar dai yadda na fad'a afarko cewa tsakanina dakai babu yafiya saina dauki fansa akanku duka har ita Najmiy din,saina tarwatsa duk wani farin cikinku,Saina mai daku kananun mahaukata,kuma abinda yasa nayi amfani da danku kenan donna tabbata idan kuna ganinsa acikin wannan halin kullum tofa kuda farin ciki kunyi bankwana dashi,haka zalika kuma watarana heart attack ko kuma hauka tana iya kamaku........."

    Ya fashe da wata muguwar dariya kana yace"Ana kan wata sai kuma ga wata sabuwa inji 'yan caca,labarin wata wai *'AISHA FULANI'* ,ashe har akwai lokacin da zaizo da har zaka iya b'oye min wani sirri naka irin wannan king Faruq?Sai kuma kayi rashin dace cewa d'aya daga cikin abokanan cin mushen naka beda amana tunda har ya fallasa min komai ba tare dana sha wani wahala ba kuma wai akan 'yan kalilan kudi,kai kud'ad'e sunyi ne arayuwa......"

  Jan wani gwauron numfashi yayi kana ya cigaba"Am so sorry Son Aryaan,duk abinda nake maka bada Son raina bane,iyayenka da kuma kakanninka sune suka ja maka hakan,don da'ace sun faranta min toh da kuwa wannan kiyayyar bata shiga tsakanina dasu har takai ni ga aikata munanan laifuka irin wannan ba....."

    Ya fad'a cikin Sad face kamar mutumin kwarai kafin lokaci daya yakece dawata mahaukaciyar dariya.

  Kai Tsaye yatafi ga mamaken wardrope din dake dakin yabude kofar tsakiya wani dan akwati naga yafito dashi kai tsaye kan gado yanufa dashi yadaddana wasu lambobi sai gashi tabude hannu yasa yazaro wani bebin roba wanda aka mamayesa da Allurai,cikin azama yafara ciccire alluran jiki bayan yagama yafara kwakwance Bebin roban lokaci daya yana cewa.

   ""My Son any moment from Now nasan zaka tashi..Domin bani son Abubuwa sutaru suyima dan"uwana yawa domin bawai hakan na nufin nabarka bane,No zan dawo gareka amma sai bayan nagama cusawa Ubanka bakin cikin da nake shirya masa na wannan matar daya tsinta tukun,zan dawo gareka amma for now ka huta, kasha shagalin rayuwarka dak'yau,kana bani tausayi don haka watakila na had'a da 'yat k'anwarka Zaituna...... Son ka yafeni bada son raina nake maka abubuwan da nake maka ba laifin abbanka ne......"

Ya kareshe fad'a yana kuka harda hawaye kamar wani karamin yaro Sai da yagama kukansa kana ya tattara komai ya maida cikin sanda ya fito don yasan any moment from now Maryam matarsa kuma 'yarsa Ilham na iya shigowa dakin nemansa,kan gado ya koma ya kwanta yana sakin wani d'an banzar  murmushi wanda ni kaina *HAFNAN* nakasa gane abinda yake kullawa aransa agame da *'AISHA FULANI DA KUMA MAI MARTABA FARUQ'*

*****   ******    *****    ******

  *INDIA*

*6:15pm*

     *Ummii.......Umiiiiiiii..*

  Shine abinda Aryan yaketa Fada kenan Lokacin daya farfad'o ya komo cikin duniyarmu kamar wanda aka tasa..Gimbiya Najmiyyah Dake gefe zaune tayi zumbur tamike tana rarraba idanuwa,abinda yabata mamaki shine na ganin Aryan zaune kan gadon marasa lafiya yana ambaton sunanta Saboda rud'ewa tama rasa ina zata nufa cikin rawar jiki takwashi gudu zata fita sai ta tuna da Na'urar kiran office din DR Bature..cikin azama ta isa ta danna kararrawan kafin ta isa ga Aryan lokaci daya tana Rumgumesa tana Fadin"Am here my Son,my son welcome back to our world,I can't juz express my happiness,Aryaan speak again,talk to ur ummi,inason na sake jin muryarka,kace Ummiiii da k'arfi......."

   Ai kuwa yayi kamar yadda ta buk'ata,da karfin gaske yace"Ummiiiiiiiiiiiiiiiii...." Wanda hakan ce tayi sanadin farkawar Jakadiya agigice da kuma Zaituna wacce ta fasa ihu don gigicewar da tayi.Adaidai lokacin shima Dr.Bature ya shigo dakin,atare shida Jakadiya suka karasa wajen gadon da sauri ganin sabon al'amari kuma dadda'dar al'amari wato farfadowar Aryaan.

  Can Aryaan ya cikata kowa na binsa da kallo yace"Abbii..Abbii."Kara rikesa tayi tana Fadin"Abbinka zaizo nan bada dadewa ba Son...."

  Dr Bature Shima wit face full of Suprise ya kurama Aryan ido,kan yayi magana Najmiy ta k'arbe tace"Doctor Kagani ko?Aryaan dinmu ya farfad'o,he's awake ka kira abbinsa ka gaya masa good news"Tafada tana share hawaye,itama Jakadiya matsowa tayi tana share hawaye tana mai shasshafa jikin Aryaan murna fal cikin xuciyarta.

 Cike da farin ciki Dr bature ya rungumo Aryaan yana fad'in"Aryaan son welcom back,ina ke maka ciwo yanxu gaya min?"

   Daga kai Aryan yayi yana kallonsa bakinsa na motsi,ahankali ya furta"Babu....."

  Hannu Dr bature ya daga yana godiya ga Allah kafin yacema Najmiy ta matsa ya sake duba Aryaan din dak'yau.Yana gama dubashi ya zaro waya cikin aljihu ya latso layin mai martaba kamar yadda Najmiy ke gefe tana kokarin kiran Maimartaba don bashi good news din,amma bata San cewa shi din Doctor ke kokarin k'ira ba.

       *NIGERIA*

    *2:35pm na dare*

  Mai martaba Faruq bahago yana zaune bisa sallaya bayan ya idar da Sallolinsa ya zauna yana zuba addu'o'i,ana haka sai wayarsa ta hau kuka alaman ana kiransa baiyi hanzarin tashi ba sai da ya kammala  kana yamike ya ninke sallayyah ya ijiye sannan ya nufi kan Side drower ya dauki wayar

  Abinda yabashi mamaki shine na ganin missed call din Dr.Bature har guda uku,sannan gana Najmiy har guda uku..Abun yabashi mamaki cikin rawar jiki yabi na bayan Dr Bature amma abin takaichi busy komawa yayi yana kiran Gimbiya Najmiy itama Busy yakasa samunsu rudewansa yasa yakasa fahimtar yabari suma Suna Nemansane.

    Cikin ikon Allah Saiga Dr Bature yasake kira,cikin Hanzari yadaga call din yana Fadin"Dr meke Faruwa ne? naga kiranka kaida Najmiyyah alokaci daya,hop ba mutuwa Son yayi ba dai ko?" Ya fad'a cikin Rauni.

Cikin farin ciki da murna Dr Bature yace"Good News ne yasamu Abokina..Am very hppy to be the first person to break the good news to u dat our son is back to life,ma'ana Aryaan ya farfad'o...

  "Yafada cikin nuna murnansa lokaci daya kuma Faruq yanajin muryan Najmiy cikin farin ciki..

  Cikin Abinda baifi sakwan ba mai martaba yazube kasa yakalli gabas yayi sujadar godiya ga Allah..Dr Bature nata hello hello..Ina Maimartaba ya gurfana gaban Allah yana zuba godiya garesa wanda sai da yasa ya fitar da kwallah,bayan yadago ne yasake kiran Dr Bature yana bayyana godiyansa da murnansa lokaci daya Shima Dr Baturen yana cikin murnan.

    Gimbiya Najmiyyah takasa hakuri yana waya Da Dr Bature yaga call dinta bai katseba sai da yaga yakirata Fashewa da kukan murna tayi tafadin"Aryan Yah Hayati...Aryan Yah Hayati.."

  Katseta yayi cikin farinciki yana fadin"Alhamdulillah zaki ce Habib Albi sannan ki kuma godewa Allah Stop crying kinji..i will be there soon insha Allah,sundade Suna mgana harta bashi Aryaan din sukayi magana kafin daga bisani su kayi sallama suna masu farin cikin wannan al'amarin.

Adaren Maimartaba ya isa bangaren Hayat ya tasheshi yana Fad'a mai wayar daya samu daga india cikin murna Hayat ya rumgume Mai martaba yana kukan munafunci amma akasan Ransa yana fadin _" Daba don ni ba ai da bazai Taba tashi ba"_

   Kafin kace kwabo labrin Farkawan Aryan ya yad'u awannan masarautar da kuma dangi da abokan arziki acikin wannan  daren,duk wanda ya dace yasani an buga an sanar masa..Kowa sai taya mai martaba murna yake saboda Sanin halin Da suke ciki na ciwon dansu kwara daya tak aduniya.












_*Guys how was this page?Interesting or not?*_

_*Anya Hayat zai ga annabi kuwa?mudai cigaba da taya Mai martaba da kuma iyalansa addu'ar tsira daga mugun nufin Hayat*_

_*Ina labarin Jabir?Labarin Yarinya fa?*_

_*Zaku ga update da yamma insha Allah ko kuma kafin nan*_




*Comment*
*Share*
*VOTE*

*#Intelligent Writer's #*
*#Hibbatullah#*
*#_Official_Hafnancy#*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top