46-48
❄️❄️❄️❄️❄️
*Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*•°ѕadaυĸarwa ga Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*
*ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
____________________________________
💥
*Թɑցҽ 4⃣6⃣ Եօ 4⃣8⃣*
*NOT EDITED⚠*
*•MAI KUMA YA FARU BAYAN TAFIYARSU MAI MARTABA FMC BIDA?°*
Bayan tafiyarsu Mai martaba,Jabir bai koma gida ba,sai yace da Awwalu zashi dubo jikin uwargidansa don ya barota agida ba lafiya.
Awwalu ya amsa masa da "Toh agaisheta Allah ya sauwak'e. "Ameen ameen" Jabir ya amsa masa kana ya juya yayi gaba ayayin da Awwalu kuma ya nufi gida.Yana kusta kai ciki sai kawai suka ci karo da Hayat wanda ashe ya jima yana musu lab'e anan,duk yaga abinda ya gudana tsakaninsu da mai martaba amma ko kadan beji tattaunawarsu ba sabida long distance dake tsakani.
Gaban Awwalu ne ya yanke ya fadi don ya tabbata Hayat yaga komai abinda kuma suke ta gudunma faruwarsa kenan,had'e girar sama data k'asa Hayat yayi kana yace"Biyo ni....."
Yana gama fad'ar hakan ya juya yayi gaba,jiki ah sab'ule Awwalu yabi bayansa ayayin da k'irjinsa ya cigaba da dukan uku-uku.
"Shikenan ta faru ta k'are,mun shiga ukunmu...."haka Awwalu ya fad'a acikin xuciyarsa.
Wani apartment Hayat ya nufa wanda ya kasance b'angaren saukar baki na gidan,amma ahalin yanxu babu kowa aciki,duk an watse hatta zugar masautar katsina(mutanan Haj.Babba kenan) sun tafi,ana gama addu'ar ukun suka kama hanya.Ah falo Hayat ya zauna saman wani one seater,sai karkad'a kafafuwa yake yana mai cije leb'ensa na k'asa.
Awwalu ya doka sallama ya shigo,yanayin Hayat ya sake hargitsa masa hanjin ciki.
"Gani ranka shi dade...."
"Zauna man,kuma ka saki jikinka I mean no harm,kawai magana muhimmiya ce zamuyi....." Hayat ya fad'a in a serious tone.
"Toh" shine kawai abinda Awwalu ya furta sannan ya nemi waje ya zauna opposite Hayat,sai ya zamana suna facing juna ne.
Hayat ya tallafe both cheeks dinsa da hannayensa tare da k'urawa Awwalun too eyes.With full seriousness yace"Awwalu tun ba yau ba nake ta lura da take-takenku kuda dan'uwana Faruq,amma sai dai ban san meh kuka sa agaba ba,nadai san duk yadda akai akwai zurƙillon da kuke kullawa wanda ko kadan baku son wani ya jita ciki kuwa hadda ni,abin mamaki hadda Abida k'anwarmu acikin lamarin nan,nadai batsar ne nayi kamar ban sani ba don inason ta ruwan sanyi na gano wannan takun sakar naku,sannan kuma na zabi naji ta bakinka ne don nasan kai zaka fi sauk'in kai,zaka fi bani cikakkiyar bayanin abinda nakeson ji,shi kuwa Jabir ko kasheshi zanyi wallahi bazai tab'a gayan komai ba,kai infact ko siyen bakinsa bazan iyayi ba sabida Jabir nada wayau sosai,kayi haquri ni bance kai baka da wayau ba,nufina kai zaka fi taimaka min kamar yadda nima zan taimaka maka ayanxu........."
Da sauri Awwalu yace"Yallabai don Allah kayi haquri ni bansan komai dangane da abinda kake fad'a ba,abinda kawai na sani shine ita Abidar ne bata da lafiya shine Mai martaba shida kansa yace bari ya kaita asibiti ganin likita......"
Saurin taran numfashinsa Hayat yayi,xuciye yace"Look Mallam karka maidani yaro d'an shekaru goma mana,ko an gaya maka cewa na soma shan ƙwaya ne da har zaka nemi ka raina min hankali?ko kuwa an gaya maka cewa ni wani Jahilin ne da har zaka nemi kamin dabara?toh bari kaji duk wani moves da kuma tactics na Mai martaba Umar Faruq toh ni Hayatudden ina saka ido akai,idan moves dinsa ya canza,ma'ana idan ya koma yin abubuwa kamar munafiki mara gaskiya nasan tabbas akwai wani abu ak'asa,idan wani abin na damun Faruq na sani,don haka kai baka isa ka canza min tunanina akan dan'uwana ba acikin kwana daya tak! ba,ita kuma Abidar da kake magana akanta toh bari na maka wata 'yar kamar k'arya,ba psycology na karanta ba amma ni daka ganni nan,ina iya studying halayyar mutum acikin kwana daya idan har na zauna dashi,balle mutanen da muka taso tare tun muna yara,taya za'ai kuwa kayi tunanin cewa bansan komai akansu ba?idan har Abida tazo nan gidan sannan amisali ace bata da lafiya koda mijinta baya kusa ne,tofa k'iransa take aduk inda yake kan yazo ya kaita asibiti,Sam bata yadda wani acikinmu ya kaita saishi mijin nata sabida sanin da tayi masa na kishin bala'i,duk da cewa yasan babu aure atsakaninmu da ita amma still yana tsananin kishinmu,nasan zakace taya akai nasan hakan?toh ka sani ita da bakinta ta tab'a gaya mana cewa mijinta na kishin ya ganta ta fita tare da wani koda ace kuwa dan'uwanta ne,sannan kuma babban mutum dai kamar Faruq mai mulki wanda kodayaushe yana cikin jama'arsa bana tsammanin har yana da time din kai Abida asibiti balle acikin irin wannan lokacin na zaman makokin rasuwar mahaifiyarsa,Sam beda lokaci sai dai ya aiki wani ya kaita,kai to make it Short mallam am sorry to say Abida lafiyarta qalau,ka gayan nawa kake son na baka sannan ka fayyace min komai?dubu hamsin,dubu dari,dubu dari biyar,name it zan baka don akwai kudin,kudi ba matsalata bace idan har zaka gayan abinda nakeson ji yanxun nan kuwa zan baka check ko kuma na damk'a maka kudin,don haka wanne kakeso aciki.......?"
Jikin Awwalu ne ya dauki rawa sosai jin anyi masa zancen makuden kudad'e,lura da yanayin da ya shiga yasanya wani killer smile sub'ucewa Hayat,yasan tabbas tunda an sako zancen kudi acikin lamarin,tofa bazai sha wahalar samin hadin kan Awwalun ba.
Axuciyarsa yace _*"Money can buy anything except life"*_
Sanya hannu cikin aljihu Hayat yayi,ya zaro bandir din kudi ya cillawa Awwalu,dududu dubu ashirin ce,da sauri Awwalun ya cafe yana mai washe haqora,Hayat yace"Somin tab'i kenan,nasan wannan zai baka kwarin gwiwar fayyace min komai kafin ciko ya biyo baya."
Awwalu tamkar babyn robar da aka jonawa batir,haka ya shiga fayyace masa komai yana masa bayani da kuma kwatance da hannu,kamawa daga farkon soma haduwarsu da Fulani awajen Bahago roundabout,tausaya mata da mai martaba yayi da kuma kaita FMC Bida daya sanya akai,da operation da kuma zuwa gunta da zasuyi ayau shida Abida wanda har ya hana musu binsa.
Tunda Awwalu ya soma bada labarinsa Hayat keta aikin k'yak'yata dariya hadda rike cikinsa wanda hakan kuwa ba karamin baiwa Awwalun mamaki yayi ba.Bayan ya kare tatsuniyar gizonsa,dakyar Hayat ya tsagaitar da dariyarsa kana ya dubi Awwalu yace"kasan meyasa nake tsananin farin ciki da wannan xancen?"
Cike da rashin fahimta Awwalu ya girgiza kai alamun "a'ah"
Wani d'an tunani kuma Hayat yayi,can yace"Koda yake ba dole saika san dalili ba,yanzu dai Abunda nakeso dakai Tashi zakayi muje ka kaini har asibitin Da Shi Yayah king din yake zuwa ab'oye."
Awwalu ya Rausayar Dakai zai yi mgana kenan Hayat yakara jefamai wani bandir din kudin ya chab'e yana washe baki kamar wani shashashan Madina yake Fadin"Ranka yadade Ko yanzu kake bukata ai sai na kai Ka"Yafada yana juya kudin Ahannunsa.
Wata muguwar Dariya Hayat ya saki yanayi yana k'yatatawa kamar wanda yazare kafin ya tsagaita yana fadin "*UMAR FARUQ BAHAGO*" Yafad'a yana wani killer Smile,ya sake furtawa ahankali"ka sake fad'awa cikin tarkona akaro na biyu,nan da d'an k'ank'anin lokaci zan gama had'a maka duk wani makirci agame da wannan lamarin....I promise to scatter ur life,zan maidaka tamk'ar mahaukaci.... ".
Adaidai lokacin kuma ya dago kai yaga kamar inuwar mutum ta tagan window alamun dai lab'e ake musu,lokaci d'aya Fara'ar ta dauke,sai ya koma tamk'ar mayunwacin zaki sabida yadda yayi tsananin fusata da hakan.
Cikin Tsawa ya furta"Waye Anan?Nace waye? yake fada cikin zafi yana kuma tunkaran wajen.
Cikin Azama da rawan Jiki *JABIR* yabi ta kofar dake bayan dakin dasu Hayatun ke ciki dama akwai wata kofa wacce zata bulla da mutum waje,Wanda bakowa bane ya sanda da ita ba,Tanan yabi yafice jikinsa na Rawa lokaci daya yana Furta kalmar *Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un*
Dama tun bayan rabuwansu Da Awwalu har yamika hanyan Gida sai jikinsa bai bashi ba,shiyasa yadawo dawowarsa keda wuya yaga Sanda Hayat Da Awwalu suka Nufa cikin Dakin shiyasa cikin sanda ya bisu abaya ya lab'e ajikin tagar windon dakin,kakaf! yaji duk wani tattaunawarsu.
Jabir ya rud'e iya rudewa yashiga tashin hankali matsananci kuwa najin Abunda Hayat ke fada yasani tunda mai martaba yace kada abari kowa yasani to yana da dalili,Kuma shi gaba daya Hayat din ne baiyarda dashi ba..Abun ban Haushi Da takaichin shine akan kudi kalilan Awwalu ya zubar da yarda Da maimatarba yayi musu.Yanxu idan magana ta fito ana iya rasa wanda ya tona asirin atsakaninsu don ya tabbata Awwalu bazai tab'a fitowa yace shi bane.Sannan kuma ya tabbata burin Hayat shine ya b'atawa mai martaba suna agari.
"Ya salam!" Shine kawai abinda Jabir ya iya furtawa cike da mutuwar jiki ya kara sauri yabar cikin masarautar xuwa gidansa.Gashi layunkan mai martaba duka basa xuwa balle ya fad'a masa abinda ke faruwa,Dr.Philips kuwa bugun duniyar nan ya masa amma bey daga ba(Alokacin yana kan aiki ne).
Ab'angaren Hayat kuwa bayan yafito yagama duba ko'ina bai ga kowa ba sai yadawo dakin yana kallon Awwalu wanda sai faman juya kudad'ensa yake,kudad'en sun matuk'ar dauke masa hankali
wani irin k'ask'astanccen kallo Hayat ke jifansa dashi kan ya doka masa tsawa yace "Inna kuskura naji lbrin Abunda muka tattauna dakai I swear sai na lahira yafika jin Dadi,da fatar kana jina ko?"
Jikin Awwalu na Rawa yace"Bama wanda zaiji Ranka yadade Insha Allahu."Yafada muryansa na rawa, Hayat yayi nuni da kofar fita tare da sake doka masa tsawa yace"Oya! get out idan ina da bukatarka kuma zan nemeka..."
Murya na rawa yace"Yallabai zancen fitar fa?"
"Kaje ba yau ba idan na shirya zan fad'a maka.." ya bashi amsa atakaice.
"Toh shikenan ranka ya dade,ahuta lafiya..." Ya fice sum-sum tamk'ar wani munafikin daya laftawa sarki k'arya(lol).
**********************
Cikin Sauri Da azama maimartaba ya biyo Abida abaya har haraban Asibitin yana kwalamata kira ammh ko waigenshi bata yi ba burinta kawai ta ganta agida
kokarin ficewa take daga asibitin gashi har hankalun jama"a yafara zuwa kansu,akunyace kuma da sauri mai martaba Sha gabanta lokaci daya tare da rik'o hannunta,cikin wani yanayi yafara cewa.
"Haba Abida yazakimin Haka? Kinfi kowa sanin Halin Dan"uwanki kinsan Abunda zan aikata haka kuma kinsan wanda bazan iya aikatawa ba..Na dauka ko a ina ne zaki iya dukan k'irji ki kareni ko agaban waye,amma sai gashi kuma kin shayar dani madaran mamaki ayau dinnan."Yafada cikin wata murya mai bayyana tashin hankali karara.
Kallonsa Abida tayi lokaci daya tare kuma dajin tausayinsa ya tsiro mata..Ba shakka Yayah king halinsa Daban ne,shine ya kwaso halayen mahaifinsu sak,tasani Abunda zuciyarta ke kokarin kitsamata game da dan'uwanta ba alheri bane kuma ba Halinsa bane..
Maimartaba Yabi Abida da kallo, ganin kwakwalwarta tashiga tunani yasa yakara gyara tsayuwa yana Fadin"Wlh ki yarda Dani bani da alak'a da * AISHATU FULANI* balle har nazama wanda yayi sanadiyar zuwan
*'YARTA* duniya,har ga Allah taimakonta nayi,Abida pls ki fahimceni....."Yafada yanajan Hannunta zuwa cikin asibitin.
Turjewa tayi tana kallonsa cikin karyewan murya tace"Yah king yanxu wai so kake na yadda dakai?.."Ta
fada cikin Rawan murya,wani tunani tayi kuma sai kawai naga ta juyo ta zube ak'asa tare da fashewa da kuka tace"Am Srry Ya king Wlh sharrin Shedan ne ammh i already know that bazaka taba aikata abu makamancin hakan ba..Kayafemin don Allah"Tafada hawaye na zuba bisa kuncinta.
Cikin Azama yasaka hannu ya dagata yana Fadin"Bari Abida stop it plz..Babu komai wlh am so hppy dakika Fahimci cewa *FARUQ BAHAGO* bai chanza ba"Yafada yana sharemata hawaye lokaci daya yana riko hannunta suka Nufi mota kai tsaye babu maganar komawa cikin Asibitin.
*INA LABARIN AISHA FULANI?*
Lokacin Data Fito Hijabin jikinta ta sanya tarufe gefen Fuskarta Ruf saboda bataso wani ya ganta Aharaban Asibitin Taci karo Da maimartaba Da kanwarsa Abida suna mgana daga nesa tasamu wani waje ta lab'e,duk da bata jin mesuke cewa ammh Yadda yake magana kadai ya tabbatarmata da cewa haryanzu yana cikin tashin hankali.
Lokaci Daya Fulani taji hawaye sun zubo mata ta sanya hannu ta share tana Fadin"Allah sarki *YALLABAI* Ubangiji Allah yadubi lamarinka Alkhairin Dakayimin Allah yayi maka shi...Gashi Nasake barin maka wani Nauyi,Ya Allah don Darajan Sunayenka madaukaka ka sanya Yarinya tazamo haske ga Rayuwan Wannan Bawan naka"Tana gama fadar hakan ta shafa addu'arta
Adaidai lokacin kuma taga Maimartaba Ya jawo Hannun Abida yana sharemata hawaye ya nufi gun mota da ita,agaban idonta suka Fice daga Cikin Asibitin.
Ganin Haka yasa ta fito cikin Sanda Tana waige waige Tadunfari get din Asibiti sai taci Sa"a Securities din sunje sallah dake har ankira sallar Magrib shiyasa tasamu daman Ficewa ba wanda ya ankara da ita.
*Comment*
*Vote*
Share*
*MOM HIBBA*💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top