43-45

     ❄️❄️❄️❄️❄️
      *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
         ❄️❄️❄️❄️❄️

    *°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*

*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*

  *MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*

     *WATTPAD:HAFNANCY*

https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/

*°•ѕadaυĸarwa ga Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα•°*

    *°•ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍•°*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
____________________________________
                              💥

*Թɑցҽ 4⃣3⃣ Եօ 4⃣5⃣*

     ^^^^misalin qarfe hudu da rabi ta yammancin washeqarin ranar sad'akar uku,bayan mutane sun soma dan watsewa,Mai martaba yaje ya sauya kaya don tafiya wajen Fulani.Simple dressing yayi sannan kuma mutanen da zashi dasu daga Jabir sai Awwalu direba don baya son mutane susan da fitarsa musamman ma Hayat.

  Gama sanya kayansa kenan,ya hau feshe jikinsa da tsadadden turarensa,wayarsa dake kan gado ya shiga ruri yana mai neman agajinsa.Duk azatonsa k'irace daga Najmiy dinsa.

   Ahankali ya furta"I know it's you my Habib albi......"

Ya saukar da numfashi kana yace"Allah dai yasa naji alheri daga gareki akan Aryaan....." ya maida kwalbar turaren ya ijje asaman dressing mirror,kana ya juya ya soma takawa sannu ahankali xuwa direction din wayar cike da k'asaita,salon yadda yake moving jikinsa kadai ma mai jan hankali ne,uwa-uba nazarinshi ah mutum dinsa might even seize ur breathe😉.

    Instead of yaga *'Habib Albi'* yana yawo akan screen,sai kuma yaga akasin hakan, *'DR.BATURE'* shine sunan daya gani.Wani dan siririn tsaki ya sakar don harga Allah ba call dinsa yaso gani ba,tun jiya yake ta damunsa da magana daya daya amma yaki saurarensa da batun.

Afari yi yayi kamar bazai dauka ba,can wata xuciyar tace"Ka dauka don bakasan alherin dake ciki ba..."

    Da hanzari ya danna wajen receive don kiris! ya rage call din ya yanke.

Saukar da ajiyar xuciya Dr.Bature yayi don ada ya fidda rai da cewa Mai martaba zai dauki k'iransa idan akayi duba da yadda suka rabu jiya awaya bata dadi ba.

Yauma saukar masa da sunan saurautar Dr.Bature yayi kamar dai yadda ya saba yi idan har zaiyi magana mai muhimmanci.

   Yace"Umar wai wats wrong with you ne?yanxu aduniyar nan kai kana ganin har akwai wani abokinka wanda zai iya tsayawa yana gaya maka gaskiya bayan ni ne?sannan kuma kana ganin akwai wani abokin da zai iya shanye irin wannan wulaqancin da ni kake min ne?No,am very pretty sure dat am d only friend of urx dat can endure all diz ur stupidity,kayi haquri idan har na b'ata maka rai ne da hasashena akan d'anka,amma I will never stop saying d fact,ina tunanin akwai aikin sihiri acikin lamarin Aryaan cuz babu yadda za'ayi ace kamfutoci su kasa detecting sickness dinsa,shawarata agareka shine kafin ka taho inason ka Sanya malamai su saukar masa da alqur'ani,kai if possible zanso azo adaukeshi amaidashi gida don ayi masa aikin da k'yau yadda ya kamata,wannan itace shawarar da naketa son na baka tun ranar da zaka taho Nigeria amma kaki saurarata,Umar kabi shawarata if not ko zamu shekara dubu ne muna zaga asibitocin duniyar nan,then believe me the answer will always and forever remain *'SICKNESS NOT DETECTED'*......."

   Cikin hargowa Mai martaba ya tari numfashinsa"Taya akai kasan hakan?ko kai din Allah ne?"

Murmushi mai ciwo Dr.Bature yayi kana yace"Ni din ba Allah bane amma Ina kokarin tunatar dakai cewa babu abinda yafi k'arfin ubangiji ne,so dear friend juz do as I said,na barka lafiya ranka shi dade......"

Yana gama fadin hakan ya datse call din,Mai martaba ne ya shiga hura hancinsa don sosai jikinsa yayi sanyi da kalaman Dr.Bature,can ya fesar da iska daga bakinsa yace"Kai da k'amshin gaskiya acikin xancen Bature amma kafin nayi yadda ya bukata zan soma ganawa da Hayat...."

    Dakatawa yayi,ya dan fada wani tunani,can ya shiga girgiza kansa yana fadin"Yes zantawa da Hayat din shine daidai kafin komai sabida muna nemar shawarar juna before going ahead to do something...."

Duba agogon dake makale ah tsintsiyar hannunsa yayi,yaga 4:35pm,da sauri ya mike yace"Kai lokaci dai ba wuyan yi,yanxu har hudu da rabi tayi?watakila ma yarinyar nan ta fidda rai da xuwana..."

Ya fice bayan ya latso Abida yace mata ta sameshi awaje acikin mota sabida bayason kowa yasan da batun fitarsa.bata wani dau tsawon lokaci ba sai gata ta fito,can nesa da gidan aka parker motar.

    Mai martaba dake hakimce abayan seat ya bude kofa ya fito bayan Abida ta karaso,ya zaga xuwa bangaren direba yace"Kai Awwalu maza fito nama fasa xuwa daku,zan tuk'a kaina...."

Sake baki sukai suna kallonsa don this is the first time da Mai martaba Umar Faruq zai tuk'a kansa.

   Jabir baki na rawa yace"Yallabai...kai.... da... Kanka zaka tuk'a mota?gaskiya bazamu yadda ba kawai ka bari mu kaiku...."

Cikin daga murya yace"My friend I said get down!!I will drive the car myself...."

Tofa! anzo gun😀don Awwalu ba jin turanci yayi ba,arud'e ya dubi Jabir yace"Master meh yace ne?"

Jabir da yake danne dariyarsa yace"Cewa yayi ka sauka ka bashi gu ya tuk'a kansa...."

    "Kuna b'ata min lokaci fa..." ya sake fada cikin tsananin fusata.Da sauri duk suka fito shi kuma ya shige ya zauna tare da rike sitiyari.

Ya dubi Abida wacce take waje tana inda-inda,yace"Ke kuma zaki shigo mu tafi ne ko kuwa in wuce abina kin fasa xuwa?"

Da rawar murya tace"A'ah Yayah King nifa tsoro nake karkaje ka ballo mana wani musifar don rabonka daka tuk'a kanka harna manta...."

   "Good and fyn,toh koma gida...." ya soma kokarin jan motar,da sauri tace"A'ah tsaya wallahi zani...." da hanzari ta bud'e b'angaren mai zaman banza ta zauna.Su Jabir kuwa sai dariya suke musu.

           Mai martaba ya yafito Jabir da hannu,da sauri Jabir din ya isa ga b'angarensa yace"Gani gareka mutumin talakawa..."

Yace"Jabir banison kowa yasan da labarin fitata,idan aka tambayeku inda naje kace baku sani ba,na gaya muku kar wanda ya sake ya labartawa kowa labarin *'AISHATU FULANI'* da kuma *'YARINYA'* ,kuyi kokarin kiyaye harshenku...."

Kan Jabir yace wani abin tuni yaja motar yabar wajen.Jabir ya sake gargadin Awwalu akan karya kuskura ya baiwa kowa labarin Aisha da kuma yarinyarta kamar dai yadda Mai martaba ya masa kashedi.

  *
Akan hanya saida ya tsaya ya siye kayan itatuwa har ledoji biyu kuma kowanne shake yake fam.

     Fulani ce zaune agefen gado tana baiwa Yarinya mama ayayin da take tsotsa tana lumlumshe idanuwa kamar yadda dai ta saba yi akodayaushe.Nurse Asmy ba karamin kokari take wajen kula da ita ba,don har sinadarin da zaiyi saurin kawo ruwan nono saida ta hada mata,kuma ba laifi abin ya karbeta sosai don ayanxu Yarinya tana samin wadataccen ruwan nono.

   Sai wasa takewa Yarinya cike da so da kuma qaunarta.Nurse Asmy tun safe ta tafi gida kuma sai dare zata dawo.Don haka ita kadaice kurum adakin,lokaci xuwa lokaci Dr.Philips ke shigowa dubata da kuma tambayarta ko dakwai abinda take da bukata?

Dan saurarawa tayi da wasar da take mata don jin muryoyi da kuma takun tafiyar mutane.

    Ji tayi ance"Ai ranka shi dade Aishatu ta sami lfy,komai nata is normal ayanxu,don haka I think nan da kwana uku ko hudu zamu bata takaddar sallama...."

Mai martaba yace"Alhamdulillah Allah abin godia,a job weldon to you Dr.Philips,haqiqa ka faranta min don haka ka jira isowar babbar ƙyauta daga gareni..."

   Gabanta ne ya bada rasss!! don harta mutu bazata tab'a manta da wannan muryar ba,wannan zazzaƙar muryar bata kowa bace face ta *'YALLABAI'* kamar dai yadda take k'iransa.

Ji tayi suna kokarin bud'e kofar dakin,da sauri ta kwantar da Yarinya kana ta maida kai ta kwanta tare da rufe idanuwanta kamar mai bacci,kallo daya zaka mata ka rantse harga Allah baccin gaske take,irin nannauyan nan ma kuwa.

     Hadi da sallama Mai martaba ya shigo dakin ayayin da Abida ta take masa baya,idanuwansa fes akanta.

Axuciyarsa yace"Anya wannan din Aisha ce kuwa?" mamaki ne ya kamashi ganin yadda ainihin k'yawunta ya bayyano acikin kwanaki biyun nan,ranar farko daya kanta acikin kazanta ce,amma sai gashi ayau real self dinta ya bayyana sabida gyaran data sha.Shiyasa mallam bahaushe ke cewa _*"Mutum ne ke gyara waje ko kuma wani abin idan har yaso"*_

"Ashe ma bacci take,bari na tada ita..." acewar Dr.Philips wanda yakai hannu yana kokarin tada itan.

Da sauri Mai Martaba ya rik'o hannunsa yace"A'ah batta karka tada ita,muna nan zamu jira tashiwarta..."

      Ya isa ga yarinya wacce take kwance kusa da mamanta,ya dauketa tare da sab'ata akan kafadarsa,sosai yake jin qaunar 'yar na ratsa jinin jikinsa.Dr.Philips yayi taking excuse ya fita,dakin ya rage daga mai martaba,Abida sai kuma mai baccin k'arya😀.

Ahankali ya furta"Yarinyata Ina qaunarki sosai......"

   "Yayah King d'an bani 'yar na ganta..."Haka Abida ta fad'a cikin mutuwar jiki don ita ta fara tsurewa da lamarin yayan nata,infact tana zarginsa akan cewa yana da babban alaƙa da Aishatu Fulani wanda har yake boye musu.

Da sauri ya mik'a mata 'yar kamar dama jira yake tayi magana,ta tsurawa Yarinya ido,cikin dakik'u goma kacal ta gama nazarin 'yar da kuma uwarta dake kwance take baccin k'arya.

   Ahankali ta furta"Ko kadan 'yar bata kama da uwarta,yanayinta ma ni yafi kama da naka,ma'ana jikina na bani cewa wannan 'yar *JININKA* ce....."

Cikin tsananin kid'ima da kuma mamakin furucin daya fito daga bakinta yace"Abida meh kike nufi da hakan ban gane ba,taya akai ta rikid'e ta zamo 'yata kuma bayan na gaya miki komai?Abida meyasa kike neman ki jagula min lissafi ne?"

Murmushin takaici tayi kana tace"Yayah King what are you hiding for Allah's sake?kawai ka fito fili kace wannan 'yar tawa ce,kuma wannan matar aurenta nayi ba tare da sanin kowa ba,ko kuwa ai na soma tarayya ne da matan banza awaje har nayi wa wata ciki........."

   Kan ta karasa maganarta taji saukar wani zazzafar mari asaman kuncinta na dama,cike da zafi ya soma magana ayayin da wasu hawaye masu dumi suka shiga kwaranyo masa,yace"Abida You are very very stupid with your negative thinking on me,ban tab'a sanin cewa ke din dakikiya sakarya bace sai ayau dinnan da kika tabbatar min da hakan,azatona da kuma tunanina kin yadda da dan'uwanki wanda kuka fito ciki daya dashi fiye da kowa,azatona kinsan abinda zan iya aikatawa da kuma wanda bazan iya aikatawa ba,azatona kin riga kin gama karantar halayen *MAI MARTABA UMAR FARUQ BAHAGO* amatsayinsa na dan'uwanki wanda kuka fito daga tsatso daya dashi,ashe abin ba haka bane,Abida yanxu inason ki gaya min,idan har ke da kike yar'uwata ta jini kika iya yi min irin wannan mummunan zargin,toh wani tunani kike ganin Hayat da sauran mutane za suyi akaina agame da wannan al'amarin?"

   Cike da zafi itama tace"Ai shi halaye ba haihuwarsa ake tare da mutum ba,mutum girma yake tare dashi bayan an karantar dashi ya kuma dauka,wasu ana dorasu kan turba meh k'yau ne,ayayin da wasu kuma kan b'atacciyar hanya ce ake dorasu akai,and again halaye can never be permanent sabida wasu mutanen nasu halayyar is juz for the main time(temporary),daga bisani sai kaga sun sauyashi,wasu daga munanan halaye xuwa k'yawawa,ayayin da wasunmu kuma daga k'yayawan halaye xuwa munana wanda ayanxu nake k'yautata zaton cewa hakan ce ta faru dakai,Yayah King wannan 'yar taka ce kuma ni wallahi saina fallasa asirinka gasu Yayah Hayat sabida kana kokarin b'ata mana suna......"

      Wani uban zufa ne ya shiga feso masa kota ina, _*"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un*_ shine abinda ya furta,kan yayi wata magana yaga Abida ta ijje Yarinya agefen uwarta kana tayi hanyar fita da sauri saurinta.

"Abida Ina zaki?" ya fad'a cikin tsananin fusata.

Ba tare da ta juyo ba tace"Zanje ne in taho dasu Yayah Hayat don su gani da idanuwansu abin kunyar da wansu ya aikata...."

    Da sauri yabi bayanta yana fadin"Haba Abida yadda mukai dake kenan?ba cewa kikai babu wanda zaiji wannan maganar ba?meyasa kike neman sab'a alqawari ne?ki yadda dani Aisha ba matata bace ko dadiro ba sannan kuma Yarinya ba 'yata bace,don Allah karki b'ata k'yakkyawar alak'ar dake tsakanina da matata Najmiy......"

  Daga haka suka karasa fita daga dakin,kakaf zantukansu Fulani ta haddacesu,kenan Abida yar'uwarsa ta jini ce?

  k'arfin hali ne kawai take tayi kwance anan,tana jin fitarsu,ta saki wani faint cry,ta bude idanuwanta tace"Allah sarki bawan Allah daga taimako gashi ayanxu na jefaka cikin bala'in da babu wanda zai iya kubutar dakai face Allah,baxan so nayi sanadin b'ata k'yakk'yawar alakar dake tsakaninka da matarka ba don baka cancanci hakan daga gareni ba,sabida haka zanyi nesa daku,duk da cewa idan na fita daga nan bansan inda zan dosa ba don na manta wacece ni,amma duk da hakan na gwammace na fuskanci kalubalen rayuwa dana b'ata maka rigar mutuncinka ah idon duniya,sai dai kuma zan bar muku Yarinya ko dan nan gaba,watakila Yarinya ta zamo hanyar wankeka daga zargin da ake maka,watakila nan gaba ta zamo wani haske ga Zur'iarku,Yallabai don Allah ka yafe min...." kuka ya soma kokarin cin k'arfinta.

  Da sauri takai hannu ta toshe bakinta,ta dubi Yarinya tace"Yarinya don Allah ki yafewa mamarki,xan barki anan ba don komai ba don bani son ki bini ki fuskanci kuncin rayuwar da zan shiga,nasan Yallabai zai gwada miki qauna idan akayi la'akari da yadda yake masifar sonki,kiyi kokarin zamo 'ya ta gari wacce duniya zatayi alfahari da ita,sannan kuma kiyi kokarin shanye duk wani kuncin rayuwar da zaki shiga nan gaba don ba kullum ake jindadi ba,dole watarana ah dandani d'aci,Allah ya kaddara saduwarmu da alheri idan da rabon zamu sake ganawa arayuwa YARINYA....."

    Ta Mike tana kuka,zoben hannunta ta ciro ta zirawa Yarinya ah d'an karamin yatsarta tace"Wannan zoben mahaifina ne ya bani tun Ina 'yar karamata don kariya agareni,kema gashi yau na baki ita amatsayin kariya agareki......"

Da sauri tayi hanyar fita ba tare da ta dauki komai ba,hijab kawai ta zura,tana kaiwa kofa Yarinya ta canyara kuka,Fulani tayi mata duban k'arshe tace"Kiyi haquri yarinya nasan Yallabai nanan dawowa gareki....." ta murda kofa ta fice da sauri tana mai rufe fuskarta da hijabinta,ita sauri take kar Abida tayo mata zugar yan'uwansu kamar dai yadda ta fad'a........."

   _*gαn gαn gαn!!! αnα wαtα gα wαtα,ínjí 'чαn cαcα ѕukαcє"wαtα ѕαвuwα ",tσfα αвídα mєчα ѕhígα cíkín ѕkull dínkí nє?*_

_*ínα kumα αíѕhα fulαní zαtα tαfí tαвαr dαnчαr jínjírα вαчαn kσ ѕunα вα'α ѕαnчα mαtα вα?*_

    _*kuчí hαqurí dα rαѕhín jín mσtѕínα wαllαhí tєѕt mukє,чαnхu mα kσkαrí nαчí nα muku tчpíng*_

    *mσm híввαh💕*

  

    

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top