40-42
❄️❄️❄️❄️❄️
*Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*°•ѕadaυĸarwa ga Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє,мιииα•°*
*°•ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍•°*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
____________________________________
💥
_*°•ѕíѕ ѕαfíччαh ínα tαчαkí murnαr kαmmαlα líttαfínkí mαí ѕunα 'вα jínѕínmu вαcє' hαqíqα kín вαzα вαѕírα dα kumα fαѕαhα αwαnnαn líttαfín,ídαn вαku kαrαntα вα ku nєmα ku kαrαntα kαrku ѕαkє αвαku lαвαrí,í wíll ѕtíll rєpєαt thє nαmє,'BA JINSINMU BACE'°*_
*NOT EDITED🔨*
*Թɑցҽ 4⃣0⃣ Եօ 4⃣2⃣*
Agame da rashin lafiyar Aryaan kuwa babu labari meh dadi akansa don har yanxu yana cikin coma dinne,Gimbiya Najmiy ta rasa inda zata saka kanta taji dadi,ga rashin lafiyar mafi soyuwar danta sannan kuma ga mutuwar Haj.Babba dake dukanta sosai,Sam Najmiy bata da wannan k'yan da aka santa dashi don ta kode ta kuma lalace.Ko kadan bata son ace yau an wayi gari babu Aryaan don ji zatayi tamk'ar dan'uwanta ne ya sake tafiya ya barta.
Anty Nabila wato matar Dr.Bature ce tazo tare da twins dinta Nadeem da Nadeema (idan zaku tuna awani page nace Dr.Bature aminin Mai martaba Umar Faruq ne,kuma agidansa suka sauka).Toh bayan twins ko b'arin wata Nabila bata sake yi ba.Shekara daya kacal Aryaan ya basu,kenan su suna da 6years ayayin da shi kuma yake 7years.
Gimbiya Najmiy ta dubi Nabila tace"Kai Nabila kedai wallahi bakya gajiya,ke kenan kullum idan zaki zo baki rasa abin kawowa?don Allah ki dan dunga hutawa...."
Murmushi Nabila tayi kana tace"Gimbiya ance fa idan kana dashi ka taimaka,sai kaga Allah ya sake bud'a maka,don haka ki dena wannan maganar...."
Gimbiya tace"Hakane kuma fa,toh Allah ya dad'a rufa mana asiri,angode Allah ya saka da alheri...." ta fada tare da mika hannu ta karbi basket din dake hannunta ta baiwa Jakadiya.
Nabila tace"Amin amin,addu'armu dai akullum shine Allah ya bashi lafiya...."
"Ameen maman twinx..." Gimbiya ta fada cikin raunin murya.
Ta dubi twinx wa'enda ke rungume da kafafuwan mamansu tace"Haba my twinx yau babu gaisuwa ne?Nadeema u look paled,zoki gayan abinda ke damunki....."
Da sauri ta saki kafar uwar ta isa ga Gimbiya rungumeta tare da fashewa da kuka,hakan yasa hankalin Gimbiya Najmiy dagawa,arud'e ta dago fuskarta tace"Subhanallah! babyna wat happen?Nadeema waya tab'a min ke?Momy ce ko dady ko kuwa Nadeem?gaya min nayi maganinsu yanxun nan kuwa agabanki...."
"Aryaan ne..." ta fad'a tana mai kokarin tsai da kukanta.
Cike da mamaki Gimbiya tace"Aryaan kuma?meya miki shida yake kwance rai ahannun Allah?huh my Nadeema?"
Nadeema ta sake fashewa da kuka tace"Momy kice masa ya tashi,kullum idan na masa magana baya tankani saidai ya rufe idanuwansa,ku rokeshi idan wani laifi na masa shine yaki kulani kuce masa yayi haquri baran kuma ba...."
Ta zube akasa ta hau shure shure da kafafuwanta tana sambatu,axuciye Nabila ta taso ta hau jibgarta tana fadin"Don qaniyarki tashi ko kuma inci ubanki yanxun nan don na lura so kike ki tara mana jama'a anan dakin kuma gashi lalularsa baya son hayaniya,bazaki tashi ba?"
Da sauri Gimbiya ta taso tana fadin"Haba Nabila meye haka ne kikeyi kamar wata zautacciya?karamar yarinya kamar Nadeema ce kike bugu haka don ta nuna tsantsar damuwa da kuma kulawa akan Aryaan?haba wallahi ni kin bani kunya wallahi,sakarta don Allah ni...." dakyar ta kwaci Nadeema ahannunta.
Cikin daga murya Nabila tace"Gimbiya wallahi karki ga laifina don tun jiya yarinyar nan ta saka mana rigima akan Aryaan,har tara mana jama'a tayi agida amma bamu damu ba sai haquri muketa bata akan zai tashi insha Allahu,amma don iskanci shine zatazo nan asibitin ta bud'e mana filin bori salon ta janyo masa wata matsalar?"
Ta dubi Nadeemar wacce sai ajiyar xuciya take saukewa boye abayan Gimbiya,tace"Don ubanki dena kallona awurin kafin na ciccire miki idanuwan nan naki masu kama dana mujiya...." da sauri Nadeema ta runtse idanuwanta,Gimbiya tace"Agaskia Nabila ko kadan banji dadin actions dinki akan Nadeema ba,bai kamata ace kina hukunta karamin yaro haka ba tamkar kina hukunta babban mutum ba,don Allah ki dena banaso,yarinyar ta damu ne da dan'uwanta dake kwance shiyasa take hakan,pls try to control ur anger incase of next time...."
Ta dubi Nadeema tace"Sorry babyna,ki yafewa mommanki kinji koh?"
Daga kai tayi alamun ta yafe matan,ta dubi uwar hadi da kama kunnuwanta tace"Am very sorry my love,bazan sake ba...." haka suke yiwa iyayensu akodayaushe idan har zasu nemi yafiya, *'MY LOVE'* , shine sunan da suke kiran mamansu dashi ayayin da suke kiran dadynsu da *'HEARTBEAT'* ,lol su Dr.Bature rayuwar turawa suke tsantsa kuwa.
Cike da sha'awarta Gimbiya tace"Good,oya yanxu maza jekiyi wa Aryaan dinki wishing quick recovery,oya Nadeem kaima bi bayanta,miskilin mutum kawai...." aka murmusa da maganarta.
Nadeema tana isa kusa da gadon ta kamo hannun Aryaan ta hadashi da nata,hawaye na gangaro mata tace"Aryaan my best friend pls get well soon,Nadeema and Nadeem are all missing you,ka tashi mu koma sabon School tare wanda heartbeat (dady) ya maidamu,sunan school din *'BOMBAY SCOTTISH SCHOOL'* ,akwai liluna da kayan wasanni sosai,sannan kuma ana karatu dakyau,I know u will love the school so pls Aryaan ka tashi mu dunga xuwa Bombay tare....."
Kuka yaci k'arfinta,can ta soma numfashi sama sama tana lumlumshe idanuwa,can ta dauke wuta,ta tafi zata fadi,Gimbiya da Nabila suka fasa ihu atare tare da nufar inda take.
*"NADEEMAAA..... "*
Nadeem ne yayi dabaran tarota ta fad'o jikinsa,Nabila tace"Gimbiya kin gani ko abinda naketa jiye mata kenan,idan har Nadeema tayi kukan fitar hankali toh kuwa next thing suma ne zai biyo bayan kukan,haka ita dai Allah yayi ta.
"Ikon Allah..." shine abinda Jakadiya da kuma Gimbiya keta nanatawa,Jakadiya ta yayyarfa mata ruwa,sai gashi ta farfad'o tana saukar da numfashi da k'arfi.
Koda ta farfad'o cigaba tayi da ambaton sunan Aryaan,saida uwar ta tsawatar mata kafin tayi shiru.Gimbiya ta dubi Nabila tace"Nabila akaita gida ta huta,I think idan tabar ganin Aryaan din acikin wannan halin na tabbata hankalinta zai dena tashiwa..."
"Toh Gimbiya ina ganin ma zan dena tahowa dasu tunda abin ya zama haka...."
Gimbiya tace"Hakan shine daidai...." daga haka sukayi sallama,saida suka soma biyawa ofishin Dr.Bature Nabila ta labarta masa komai,murmushi yayi kawai cike da mamakin irin chemistry of love dake tsakanin *'ARYAAN'* da *'NADEEMA'* ,zai kuma so ace nan gaba idan har Aryaan ya rayu har suka zamo cikakkun mutane toh kuwa zaiso su kasance ma'aurata.
Itama Gimbiya Najmiy mamakin Nadeema ne ya cikata fam! ta rasa wani irin qaunace haka yaran kewa junansu,don haka Aryaan shima yake yawan damunsu da zancen Nadeema akan lallai sai an kawoshi india wurinta.
"Allah sarki haduwar jini ce kawai...."ta furta ahankali.
**
Akalla an kwashi kusan awanni biyu da rabi sannan aka fito da Fulani wacce idanuwanta ah lumshe suke bata san abinda ma ya faru da ita ba sabida allurar baccin da aka mata kafin asoma aiwatar da aikin.Anyi aiki cikin nasara kuma likitoci sun bada tabbacin nan bada jimawa ba zata farfad'o.Aka gurgura da ita xuwa dakin hutu.
Jabir ya latso Mai martaba wanda tunda aka fada masa cewa ai an shigar da ita dakin aiki,ya kasa zaune haka kuma ya kasa tsaye,sai safa da marwa kawai yake tayi.Yana ganin call din Jabir yayi saurin danna button din receive.
"Yaya dai Jabir ya ake ciki ne?ina fatar ba mutuwa tayi ba dai ko?"
Jabir yace"Ranka shi dade ka kwantar da hankalinka don anyi aiki cikin nasara sannan kuma Aisha bata mutu ba tana raye,yanxun ma haka baccinta take hankali kwance.
Wani wawan ajiyar xuciya ya sakar,alokaci daya kuma wani irin kayataccen murmushi ya sub'uce masa kana yace"Alhamdulillah!Alhamdulillah!!! Allah nagode maka,toh Jabir kuna iya kamo hanya yanxu,idan yaso zan k'ira Dr.Philips na k'ara masa wani aikin...."
"Toh ranka shi dade an gama,sai mun iso..." acewar Jabir.Daga haka ya datse call din.Ya latso Dr.Philips,yana dagawa yace"Ranka shi dade anyi aiki successfully,yanxu haka patient dinka is in a very good condition,bacci ma take ahalin yanxu..."
Cike da farin ciki mai martaba yace"Jabir ya fad'a min komai,yanzu abinda nakeso dakai Doctor shine inason akara bata extra care akan nada,I will pay any amount,burina kawai abata kulawa daga ita har babynta...."
Dr.Philips yace"Alryt sir amma who is she to you?"
Mai martaba bai tankashi ba ya datse call din dauke da murmushi akan fuskarsa.
*
"Yayah King da waye ka gama waya yanxu?sannan kuma wacece kake nemar abata extra care harda cewa ko nawa ne zaka biya?"who could she be?"
Dam! Yaji kawai gabansa ya yanke ya fadi,ahankali ya juyo da kansa xuwa 90° direction din inda maganar ta fito kenan,idanuwansa suka gauraye dana k'anwarsa Abida.
Ta sake cewa"Yayah ka amsani man,wacece wannan kuma?"
Saukar da wata sassanyar ajiyar xuciya yayi kana ya bata labarin Aishatu fulani.kunsan mata akwai mu da raunin xuciya don haka kuka Abida ta fashe dashi sosai tana mai tausayawa Aisha da kuma yarinyarta.
Ta dubeshi tace"Yayah King pls can u take me there to see her?"
Dan Jim! yayi kafin yace"Zan kaiki amma sai bayan anyi sadakar uku gobe,sannan kuma maganar nan ta tsaya iya ni dake,karki kuskura ki bari su Hayat su sani..."
"An gama Yayanah...." acewarta
Yace"Good,oya tashi ki tafi...."
*****
*AFTER FIVE HOURS🕔*
Fulani ta farfad'o tana salati tare da ambaton sunan Allah abaki,Nurse Asmy ce zaune asaman kujerar masu jinya tana baiwa Yarinya madara ah fida don tun sanda za'a shigar da Fulani theatre tasha nonon karshe.Toh tun asannan ne ta dunga bata madararsu ta yara idan ta soma rigimar yunwa.
Da sauri Nurse Asmy ta kwantar da Yarinya akan gadon yara ganin Fulani ta farka.Ta isa gareta tana fadin"Sannu sister kin tashi?ya kike jin jikin naki yanxu?"
Murya kasa kasa tace"Da sauki,wai har an min aikin kenan?ko kuwa da saura?"
Murmushi Nurse Asmy tayi kafin tace"Akalla an sami kusan awanni bakwai kenan dayi miki aikin,kuma anyi nasara,yanxu babu ke babu yoyon fitsari....."
Kabbara tayi tare da daga hannu sama ta shiga yiwa Allah kirari da kuma gogewa mai martaba hadda kukanta,can ta dubi nurse tace"Ina yarinyata?"
Nuna mata Yarinyar tayi da hannu tace"Gata can kwance tana daga kafafuwa sama..."
. Cike da tausayinta ta dubi inda take tare da langwab'ar da kai tace"Allah sarki yarinyata nasan tasha kukan yunwa,don Allah taimaka ki mik'o min ita na bata mama tasha..."
Da sauri Nurse tace"Karki wani damu don tun da aka shigar dake dakin aiki aketa bata madararsu ta yara tana sha,yanxu kedai bari na samo miki abinda zaki saka anaki cikin...."
"Toh nagode sosai yar'uwa da kulawa...."
Bayan awa daya sai ga Dr.Philips ya shigo dubata,yayi 'yan gwaje-gwajensa ya tabbatar da cewa yanxu komanta normal yake.Can saiga Mai martaba ya k'irashi awaya,yace kuma abaiwa Fulani wayar.
Dr.Philips ya mika mata wayar yace"Ungo karbi nan mai martaba ne keson magana dakai...."
Rasss! taji gabanta ya bada,hannu na rawa tasa hannu ta k'arbi wayar tare da doka masa sallama.
Ajiyar xuciya ya saukar kana yace"Amin wa'alaikis salam..."
"Aishaaaaaa....." yajah sunan hadda wani lumshe idanuwa.
Ji tayi kamar ana mata wasar tafiyar tsutsa atafin kafarta don yadda ya k'ira sunan ba karamin tafiyar da imaninta salon nasa yayi ba.
Ahankali ta furta"Naam yallabai?an yiwa Aisha aiki cikin nasara,Yallabai zan fison na ganka agabana donna gode maka da k'yau yadda ya kamata,don Allah zakazo?"
Ajiyar xuciya ya sauke kana yace"Fine,gobe ina nan tafe insha Allah,ki shafa min kan yarinyarmu,take care....." ya datse call din,ita kuwa xuciyarta ce ta hau bugawa da sauri da sauri,kafin ta ankara taga kawai hawaye ya kwaranyo mata.
Axuciyarta tace"Meyasa yake nuna tsantsar damuwa da kuma kulawa akaina ne haka?meyasa bazai iya ce min bazai zo ba don yana cikin zaman makokin rasuwar mahaifiyarsa?"
Wata xuciyarta ta bata amsa"Sabida shi din mai taimako ne,kuma komansa tsakaninsa da Allah yake yinshi ba wai don ayabeshi ba...."
"Yah! salam!!!...." ta furta ayayin da wasu sabbin hawaye ya ziraro mata.
Dr.philips wanda keta lure da ita yace"meya faru kuma?ko kina jin ciwo awani wurin ne kuma?"
"A'ah babu...." ta fad'a tare da mik'a masa wayarsa,ya sanya hannu ya karba,adaidai lokacin ne kuma Nurse Asmy ta fito daga bandaki bayan ta gama yiwa yarinya wanka.......
*VOTE*
*COMMENT &*
*REBROADCAST*
*mσm híввαh*
,
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top