34-36

❄️❄️❄️❄️❄️  
    *Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
      ❄️❄️❄️❄️❄️

         *°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*

*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*

     *MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*

       *WATTPAD:HAFNANCY*

https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/

*•°ѕadaυĸarwa ga Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*

       *ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
___________________________________
                    💥

_*hαqíqα ruwαn cσmmєntѕ dínku чαnα ѕαnчαní fαrín cíkí dα kumα вαní kwαrín gwíwα mч lσvlч fαnѕ,ku ѕαní hαfnαn tαnα ѕσnku σvєr durlíngѕ*_

      *NOT EDITED🔨*

     *Թɑցҽ 3⃣4⃣ to 3⃣6⃣*

        

       *INA LABARIN SU MARIYA?*

Bayan sun gama tikar rawarsu atsakar gida,Mariya ta zari mayafinta dake saman wata igiya tace da Uwale tana zuwa bayan ta bata directives kan sanwar da zata aza na dare.

   Lungu-lungu,sako-sako shi Mariya ta dunga bi har ta fita can bayan gari,ta soma waige-waige alokacin da take tukaren wani daji,da sauri sauri take tafiya don kada wani ya hangota har ta shige can ciki babu alamun tsoro atattare da wannan baiwar Allahn.

Adaidai wani 'yar bukka dake kusa da wata katuwar bishiya naga ta dakata,ahankali ta furta"Boka na gindin bishiya kana ina?"

 

   Daga ciki ya amsa mata da karfi"Ke!ke!!ke!!! Waye anan wurin?"

"Niche Mariya...." ta bashi amsa ah sa'ilin data sami waje ta zauna.

    Can sai ga boka ya fito saye da wata doguwar riga baka wacce yake yawo acikinta sabida yawar data masa,sai kuma jan hula daya kafa akansa kakkaura irin dai ta sanyi.

Yana had'a idanuwa da Mariya ya washe jajayen haqoransa yace"A'ah Mariya tawa kece tafe da yammancin nan?kodai anzo ah dan latsa min zuman nan mai dadi ne agurguje?"

   Wani uban harara ta watsa masa hadi da jan malalacin tsaki tace"Wane kai?yau hadin zumar nan da nayi ta megidan ne....."

Zai sake magana tayi saurin cewa"Boka ni mubar wannan zancen,nazo ne don kamin wani aiki da gaggawa....."

   Tattaro dukkan nutsuwarsa yayi bayan ya zauna,ahankali yace"Meke tafe dake Mariyata?"

Kamar baza tayi magana ba,can tace"Wato yarinyar nan dai dana baka labarinta wacce nace maka bamu san inda megidanmu ya dakkota ba,haka kuma bamu san gaskiyar alaƙar dake tsakaninsu ba,kawai ya tashi ya kawo mana yarinya dauke da ciki wai kuma taimakonta yayi,toh ni ina zargin cewa wannan yarinyar karuwarsa ce,aganina kila don nida amaryarsa bama haihuwa shiyasa yaje ya dirkawa wata ciki acan waje shine ya kawota don ta haifa masa d'an,kasan nace maka ta haihu shekaranjiya koh?"

    Daga mata kai yayi alamun "Haka ne".

   Ta kada kai kana ta cigaba"Toh yanxu dai munyi nasarar korarta daga gidan amma kuma xuciyata bata kwanta da megidan namu ba,tsoro nake ji karya bi bayanta......"

Boka ya saki dariya irin dariyar kafi mahaukaci ban haushin nan kana yace"Yanxu meh kikeson amata daga ita har 'yar tata?"

     Babu tsoron Allah aranta tace"So nake kasa Mal.ya manta da batunta,karya sake koda ambaton sunanta ne balle takai shi ga zama yana hirarta,ita kuma Aishar inason akashe min ita daga ita har 'yar.........."

Da sauri Boka ya tari numfashinta cikin fushi"Ke Mariya ya kike nema ki b'ata min tsarin aikina ne?nasha fada miki cewa ni ina iya yin komai amma banda kisa,ke kina ganina dinnan ko karamin dabba ban iya kashewa ba balle dan'adam,don haka ki kiyaye....."

     Kallon wutsiyar ido ta masa cike da jin haushinsa kafin tace"Toh kayi haquri......"

"Ya wuce amma dai ki kiyaye,ki sake canza ra'ayi,meh kikeson amasu?"

   Jan gwauron numfashi tayi kana tace"Tunda kace abar batun kisa,toh inason itama Ayshar amantar da ita hanyar Tewi da kuma labarinmu gabaki daya,inason Aisha ta manta ko ita din wacece balle tayi tunanin komawa mahaifarta,inason Aisha da 'yarta su fuskanci kuncin rayuwa gaba da bayanta,kai boka inason su zama abar  tausayi yadda babu wanda zai iya taimakonsu arayuwa,ya zamana ko'ina sukaje hantararsu ake,hakan ne kadai zai iya sanyawa na huce takaici akan cin amanar data min........" (kai wasu matan akwai kishin jahilci,adaidai wannan lokacin ne kuma su Fulani suka iso Begger junction).

   Boka ya shiga tsafe-tsafensa yana bubbuga hannu akasa,can ya dubeta yace"Mai yiwuwa ma Aishar ba mai tsawan rai bace......"

Cikin rashin fahimta tace"Ban fahimci abinda kake nufi ba,wayar min da kai....."

     Yace"Maganar danayi ai abune dake abayyane,ma'ana basai kin wahalar da ita ba don yadda ake nuna min anan kamar bazata wani jima ba aduniya....."

Dariya tayi mai kayatarwa kana tace"Kai boka na gindin bishiya kana sani farin ciki,jinjina gareka,yanxu kana nufin mu k'yaleta kawai basai mun baiwa juna wahala bako?"

Gyad'a kai yayi alamun hakan yake,yace"Amma duk da hakan bara na mantar da ita wasu abubuwan...." yayi 'yan tsafe-tsafensa,can ya dubeta yace"An gama....."

   Tayi murmushi tace"Dak'yau,toh shegiyar 'yar tata fa?"

   Ya sake shiga tsafe-tsafensa akan Yarinya,ya jima yana abu daya daya amma ya kasa gane komai akai,Mariya tace"Boka yaya dai naga kayi shiru lafiya dai koh?"

Sai ayanxu ya sami damar magana"Wallahi na kasa gane komai akan wannan 'yar,duhu kawai ake nuna min agame da lamarinta....."

    Cike da haushi tace"Mene?????sake gwadawa kuma dai....."

Har sau uku yana sake gwadawa amma still ya kasa gane komai akan *'YARINYA'* ,saukar da ajiyar xuciya yayi kana yace"Mariya sai dai kiyi haquri nan da kwana biyu ki sake dawowa sai mu kara gwadawa,amma yanxu idan na matsawa abin toh tabbas ana iya hanani ganin komai akanta,kai ko duhun ma ba gani zanyi ba,don haka kiyi haquri ki sake dawowa ranar asabar ta sama....."

    Dakyar ta iya furta"Toh Boka nagode bari naje,sai mun sake haduwa...."ta Mike tana karkade duwaiwanta sabida kasa daya manne mata kan zani.

Susa kai Boka yayi yace"Haba Maririya baza'a samin koda kadan ne ba?"

  Tsaki tajah tace"Kai Boka wallahi kaidai jarababben mutum ne mtcheew ni muje amma wlhy minti daya na baka......."

"Naji mu shiga daga ciki....." ya fada tare da dube duben wurare don tabbatar da babu kowa awajen,suka nufi cikin bukkarsa.

    *(Wa'iyazubillahi)*

   **
"Yarinya don Allah ki yafemin kinji nasan sanyi kikeji sosai,kiyi haquri da lalurar mamarki watarana sai labari....." kuka yaci k'arfinta.awannan halin sambatun ne Awwalu direba ya iso gareta,yace"Assalamu alaykum malama lafiya kika tsaya abaki titi kika tasa jinjiri gaba kina kuka?meya faru?"

     Dago kai tayi ta zuba masa idanuwa kana ta murmusa tace"Macece ba namiji ba,kuma nima bansan meh aka min ba,abinda kawai na sani shine wannan din 'yata ce...."  (aikin Boka ya soma ci shiyasa har ta soma mantawa da abubuwan da suka faru da ita).

Hannu yasa ya toshen hancinsa don zarni take sosai ba kadan ba,yace"cikin shege kikai kenan shiyasa aka koraki daga gida........?"

     "kai Awwalu aiken dana maka kenan?meh yasa kayi mata irin wannan tambayar ne eyyy?" Mai martaba ne yayi masa wannan tambayar daga bayansa,ya kasa haquri ne shiyasa ya fito ya tako har xuwa inda suke don yaga kamar Awwalun tsareta yayi da tambayoyi masu caza kwakwalwa wanda ko kadan ba haka yaso ba.

Da sauri Awwalu ya zube agabansa yace"Afagarceni mutumin talakawa bazan kuma ba....."

     "Tashi kaban wuri...." Ya fada alokacin daya sauke kallonsa kan Fulani wacce sai ruwan hawaye take ta zubarwa sabida shegenta mata 'ya da Awwalun yayi...."

Da hanzari Awwalu ya mike ya koma gefen Jabir dake tsaye.

      Tun kan mai martaba yayi magana Fulani tayi saurin taran numfashinsa,cikin kuka tace"Ranka shi dade tun randa nayi cikin yarinya aketa shegenta min ita har xuwa sanda na haifeta ba'a dena ba,ni kuma wallahi na rantse da ALLAH yarinyata ba shegiya bace,'yar halak ce......"kuka yaci k'arfinta.

Wani irin mugun tausayinta ne ya tsirgu acikin xuciyar Mai martaba,ahankali yace"Yar budurwa natsu ki bani labarinki....."

Tofa! nan kuma ta rasa ta inda zata fara,idan tayi kamar zata soma bayani sai kuma kaga ta rufe bakin,hawaye ya gangaro mata saman kunci tace"Ranka shi dade wallahi bazan iya tuna komai agame da kaina ba,abinda kawai na sani shine inason na koma ga iyayena amma na manta garin da suke....."

    "Subhanallah...." shine abinda Mai martaba ya furta,tabbas akwai wani boyayyen al'amari agame da wannan yarinyar don haka bazai iya bari ta tafi ba don idan ya bari ta tafi acikin wannan halin bai k'yauta ba kuma Allah bazai yafe masa ba,ya zama dole yayi taimako kamar yadda mahaifinsa yakeyi sanda yake araye.

"meye sunanki?"

    Tace"Sunana *'AISHATU'* wacce aka fi sani da *'FULANI'* ,'yata kuma *'YARINYA'* nake kiranta sabida yau ne kwananta uku da haihuwa,ba'a riga an mata hudub'a ba......"
.

Ahankali yace"Dakyau.....kamar fisari kikai ajiki ko?"

Kunya ya lullubeta tace"Eh amma lalurace,tun randa na haifi yarinya na soma fitsari ajiki,naji wasu sun k'ira hakan da yoyon fitsari,kuma wasu sunce gadon maita ce,wai hakane?" tayi masa tambayar da fuskar tausayi.

   Ga abin tausayi ga abin dariya,ya lura akwai yarinta sosai atattare da ita,don haka yace"Aishatu shekarunki nawa?"

"ina cikin na goma sha tara kenan...."

Jinjina kai kawai yayi,yama rasa ta ina zai soma,can yace"Aisha zan taimaka miki,amma taimakon farko da zan soma yi miki shine zansa akaiki inda ake warkar da masu lalura irin taki,ma'ana zansa akaiki asibiti yanxun nan...."

  Cike da murna tace"Laah da gaske?yanxu kana nufin zan warke?kana nufin zan dena yoyon fitsari?"

Gyad'a mata kai yayi alamun "eh",ta shiga masa godia sosai,shi kuwa wayarsa yasa aka miko masa ya latso wani abokinsa likita dake aiki ah asibitin dake Bida wato *'FEDERAL MEDICAL CENTER,BIDA'* ,Bida wani yanki ne dake cikin garin minna,tafiyar awa biyu kacal zakayi yakaika Bida daga Minna.

Bayan sun gaisa da Dr.Philip,yayi masa bayanin cewa yanxu mutanensa zasu taho masa da wata fistula patient don Allah ya bata kyakkyawar kulawa.Yace babu damuwa sai tazo.

     Ya dubi Jabir yace"Jabir kayi haquri ku dauki mota daya akaita FMC Bida,nayiwa Dr.Philips magana don haka komai zaizo muku da sauki,idan kun kaita sai ku juyo,Dr.Philip will take care of everything....."

"An gama ranka shi dade....."acewar Jabir.

Mai martaba ya kalleta yace"Aishatu kuje akaiki asibitin saina zo kinji ko?"

Tace"Toh yallabai nagode,kana da kirki sosai wlh Allah ya rabaka da sharrin mak'iya...."

  Murmushi kawai yayi abinsa,ya cire sweater dinsa daya sanya don sanyi,ya rufe mata jiki yace"Aisha akwai sanyi,ki dada kankame yarinya dak'yau...."

Atake kawai taji ya mugun birgeta,ashe har yanxu ana samun mutane masu kirki kamar Mai martaba haka?

  Gani yayi tana b'ata musu lokaci,ya karbe yarinya daga hannunta sukayi gaba ayayin data take musu baya,ya mikawa Jabir Yarinyar yace ya riketa awajensa,ita kuwa ya bude mata gidan baya ta zauna,6:15pm daidai motar ta dauki hanyar Bida.

Mai martaba ya sauke wata sassanyar ajiyar xuciya bayan motar tasu ta b'acewa ganinsa,ya juya yaje ya shige daya daga cikin sauran motocin,sukayi gaba,ahanya ya shiga tunanin *'AISHATU FULANI'*...........

 

_*Don't allow ur mind to do a negative thinking on them😉*_

    _*more comment more typing,iya kudinka iya shagalinka😘*_


*COMMENT*

    *VOTE &*
     
*SHARE*

*MOM HIBBAH💕*

  

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top