23-25
❄️❄️❄️❄️❄️
*Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°•ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑•°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*°•ѕα∂αυкαяωα gα Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*
*°•ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍•°*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
__________________________________
💥
*NOT EDITED*
*Թɑցҽ 23-25*
_________*'TEWI'* wani dan karamin ƙauye ne dake ƙarkashin *'BOSSO lOCAL GOVERNMENT'* wanda ke ah jihar *'MINNA'* .Tewi ƙauye ne sosai wanda wutar lantarki ta Nepa ma basu dashi,ƙauye ne wanda beyi wani suna ba sabida Karancin mutanen ciki,mutanen wannan kauyen ko dari shidda basu kai ba,Allah ya albarqaci ƙauyen Tewi da kasar noma,shukunansu nan da nan suke girma,hakanan zaka gan ganyayyakin fresh dasu abin gwanin ban sha'awa dai.Yaren da akafi yi shine *'GWARANCI'* kasancewarsu gwarawa.Sunan mai unguwar wannan ƙauyen *'MAL.MUHAMMADU NAZIRU'*.Shugaba ne mai kirkin gaske da kuma taimako saidai kuma beyi sa'an matan aure ba.
*°•GIDAN MAL.MUHAMMADU NASIRU•°*
Uwale wacce ta kasance amaryar Mal.Muhammadu ce ta bada himma wajen dakar dawa dake acikin wani katoton turmi ayayin da uwargida ran gida mai mulki wato Mariya take zaune akan kujera 'yar tsugunno tana tankad'e wanda Uwale ta riga ta daka,sai taga yayi lukwi dashi kafin ta juye awani kafcecen kwano mai dan zurfi da kuma fadi.
Can Uwale ta dakata tare da sanya hannu daya ta rike ƙwanƙwasonta,dayan kuma rike da tabarya,yamutsa fuska tayi wanda ya nuna alamun gajiya atattare da ita.
Mariya ta dago kai ta kalleta jin tayi shiru da dakar,ganin yanayinta yasa ta dan murmusa tace"Yadai Uwale kin gaji koh?"
Uwale tace"washhh! Yayah Mariya wallahi ƙwanƙwasona kamar zai karye,Allah na gaji don Allah zoki karashe ni kuma na cigaba da tankad'en ko kuma aƙira Fulani ta ƙarashe......"
Saurin dafe ƙirji Mariya tayi,cikin daga murya tace"Wah zai kira Fulani anan?ke tunda ma ta soma yoyon fitsarinta kin sake ganin na bata aiki ta min?Ni Mariya bazan ci kazanta ma don haka ni bani tabarya na karashe idan da gaske kin gajin ne...." Ta mike ta kwace tabaryar ahannun Uwale wacce tunda Mariya ta soma maganarta take ta tikar dariya son ranta.
Tace"Kai Yayah baki da sauki in har akan Fulani ce...."
Ko kala Mariya bata ce mata ba illa maida hankali da tayi akan dakarta.Jan jiki tayi xuwa ga kujerar da Mariyar ta tashi,ta cigaba da tankad'en.
Fulani kuwa dake can dakinta taji duka hirarsu akanta,wani hawaye masu dumi suka gangaro mata saman kunci,da sauri ta sanya bayan hannunta ta daukesu,cikin rawar murya ta daga hannunta sama tace"Yah Allah! na rokeka ka kubutar dani daga hannun wa'ennan azzaluman matan,nasan da nawa laifin aciki amma Yah Allah ka karkato da hankalin Muhammadu gareni ya maidani gaban iyayena...." Kuka yaci ƙarfinta,takai hannu tana shafa fuskar 'yar 3days old baby dinta,ahankali tace"'Yata don Allah ki yafemin don duk nice silar shigowarki cikin wannan kuncin rayuwar,baki san komai ba amma har kin soma dandanar dacin rayuwa....."
'Yar kuwa kamar taji abinda uwar ke fada don wani uban ihun jirajirai ta fasa abin gwanin ban tausayi,da sauri Fulani takai hannu ta ciccib'ota ta mannata saman kirjinta,kana ta shiga jijjigata alamun rarrashi,tana kuka itama Fulanin tana yi.
Mariya taji koke-kokensu na shigar mata kunnuwa,abin ya soma isarta don haka ta jefar da tabarya kana ta nufi dakin Fulani tana masifa"Wai Fulani wannan wani irin iskancin banza ne haka zaku bi ku dami mutane da koke-koken iskanci daga ke har shegiyar aljanar 'yarki?iyyeh magana nake miki?"
Ta daga labulen dakin ta hango Fulani ta sanyawa 'yarta nono abaki,ita kuwa 'yar ta hau tsotsa da sauri da sauri don dama yunwa takeji sosai.
Ahankali Fulani tace"Yayah don Allah kiyi haquri tayi shiru ma...."
Dariyar sheƙiyanci Mariya ta sakar,sai datayi mai isarta kana ta daure fuska tace"Malam na dawowa wallahi zaki bar gidan nan,zaman dadironcin ya isa hakanan,gashi har nema kike ki shafa mana muguwar cuta,toh wallahi yau zaki bar gidan nan kinji dai na gaya miki,Allah na tuba ma waya sani ko ke karuwarsa ce bamu sani ba yake mana karya wai taimakonki yayi?"
"A'uzubillahi! A'uzubillah!!! Ni Aishatu ba dadiron kowa bace,sannan kuma 'yar nan tawa ta hanyar raya sunnar ma'aiki na sameta,kaddarace kawai ta rab'ani da mahaifinta,sannan kuma labarin da Malam ya baku ku yadda dani labarin gaskiyace bawai ƙarya ya shimfid'a muku ba.... " ta rushe da kuka,mutumin kirki ne kadai zai iya yadda da cewa iya gaskiyarta ne ta fada,amma mace jahila kamar Mariya ai tayi nisa ah iya kulla makirci iri-iri hadda na siyarwa kuwa.
Kallon uku saura kwata Mariya ta mata kana tace"Ammah malam ce mana yayi kamaki akai da kwarto kuna aikata sab'on Allah adakinki sannan kuma akan gadon aurenki....."
Gaban Fulani ya bada rass!!!! don bata tab'a zato ko tunanin cewa har akwai ranar da Mal.Muhammadu zai iya fallasa sirrinta ga maƙiran matansa ba.koda yake ba abin mamaki bane idan akayi duba da irin yadda ya sauya mata lokaci guda kuma duk makircin matarsa Mariya ce.
Cikin rawar murya tace"Shi....malaaam.... din...shine....ya...gaya muku hakan?"
"Yayah Mariya nifa naga kokarinki na tsayawa kina tanka maganarta wai ke bakya jin doyi da kuma zarni ne?" Uwale ce tayi wannan maganar daga inda take zaune.
Don iskanci sai gashi Mariya ta sanya hannu tana toshe hancinta wai nan ita zarnin take ji.Ta saki labulen ba tare da ta baiwa Fulani amsar tambayarta ba.Ta nufi inda Uwale take ta mata rad'a akunne,Uwale ta saki sowa da murna tace"Kai Yayah kin kawo shawara mai ƙyau,ai kuwa yana dawowa mu tasashi agaba ya korar mana ita...."
Daga haka suka cigaba da gulmar Fulani suna kyakyatar dariya,suna yi suna aikinsu har suka gaba.
Ita kuwa baiwar Allah Fulani kuka taci sosai da maganganun da Mariya ta sossoka mata,daga baya ta share hawayenta.
***
Bayan awa daya da rabi ta dauki 'yarta ta fito waje don yin wanka dake yanxu lokacin wankanta kenan idan rana tayi sanyi.Sau daya take samu tayi wanka arana tunda ta haihu.Tana fitowa su Mariya suka bita da kallon tsana,taje zata dauki bokitin Mariya,da sauri tace"Karki kuskura ki daukar min bokiti...."
"Nima haka karki daukar min tawa idan ba haka ba ubanki zanci..." acewar Uwale wacce take bakin murhu take tuka tuwon dare,ita kuwa Mariya alayyahu take yankawa.
Fulani ta rasa yadda zatayi don tun jiya bokitinta ya fashe,bata tsaya rokansu ba don tasan ko tana shure-shuren mutuwa ne ba ara mata zasuyi ba,ta aiki almajirin dake musu aikatau xuwa makobta aro mata bokitin awajen wata wacce suke dan shiri da ita.Can sai gashi ya dawo dashi ya mika mata"Wai tace ki basshi ta baki kyauta..."
Dan murmusawa tayi tace"Allah sarki Uwani je kace mata nagode..."
"Toh" shine abinda al'majirin ya fada kana ya fice da gudu,ita kuma taje ta cika ruwa abokiti daga rijiya takai bandaki,su Mariya sai toshe toshen hanci suke tayi,kuma duk tana lure dasu amma sai ta danne ta baiwa banza ajiyarsu.Ta dauki 'yarta data kwantar akan tabarma sukaje sukayi wankansu don duk ita take wankan jegonta babu mai taimakonta,ranar farko Uwani ce tazo ta mata,kuma aranar malam ya tsawatar mata akan karta kuma zuwa duk kuma makircin su Mariya ne,ita kuwa Fulani duk taga yadda Uwanin tayi mata shiyasa ta dan iya wankan,sai ta soma yiwa 'yar wanka sannan takai daki ta kwantar da ita,kana ta koma bandaki tayi nata da sauri da sauri don bata yadda dasu Mariya ba,suna iya iya 'yar wani mugun abu.
*WACECE AISHATU FULANI?*
Aishatu wacce akafi sani da Fulani haifaffen kauyen wudil ne dake ah jihar kano,fulanin usuli ne,mahaifinta Aminu Muntari malami ne sosai don har almajirai yana dasu,akofar gidan yake tarasu ya koyar dasu karatu,matarsa daya mai suna Furera,sannan 'ya'yansu hudu,uku maza sai kuma Fulani wacce ta kasance auta kuma 'ya mace tilo agun iyayenta,Fulani ta taso cikin so kulawa,da kuma gata daga gun iyayenta da kuma yayunta,gata mace ce fara tas da ita mai masifar kyau wacce maza har rushing suke akanta amma itafa mutum daya takeso kuma shine wani mai suna Alu wato Aliyu.Alu kuwa irin yan iskan samarin kauyen nan ne don har fyad'e yakewa yan mata kuma babu wanda ya isa ya tunkareshi kasancewar mahaifinsa yana cikin mutanen da ake tsananin tsoro awannan kauyen.Ita kuwa Fulani bata damu da halayyarsa ba tace itafa shi takeso.Mahaifinta kuma yace bata isa ta b'ata masa suna agari ba,alokacin da ta cika shekaru goma sha tara Mal.Aminu ya hadata aure da daya daga cikin manya-manyan almajiransa wanda ake kira da *'DAN MALAM'* kasancewarsa na hannun damar Mal.Aminu ne.
Dan malam yayi murna sosai da wannan kyautar da Malaminsa yayi masa don dama can ya jima yana fama sa soyayyar Fulani acikin xuciyarsa kawai yadai gagara gaya mata ne ganin ita dai Alu takeso.Bayan auransu Alu ya shiga gwada mata qauna da kuma bata kulawa daidai gwargwado amma ita kuwa rashin mutuncin yau daban haka kuma na gobe daban,sau daya suka tab'a hada shimfid'a shima din cewa tayi kaddarace.Fulani zata haqura amma ina ta kasa cire Alu aranta,ita dashi suka hada plan akan cewa yazo gidanta ya zauna adakin auranta,watakila dan malam na ganinshi zaice kwartonci yazo yi sannan kuma ya sauwake mata,bayan ya sawwake mata sai su gudu.
Sosai Alu yayi na'am da wannan shawarar data kawo masa ranar da suka hade awani wuri asirrance.Ai kuwa ranar da Dan Malam ya fita,sai ga Alu yazo,kuma harga Allah babu abinda ya shiga tsakaninsu,sai akayi rashin sa'a da Dan Malam ya tashi dawowa sai suka taho had'e da sirikinsa wato Mal.Aminu.
Mal.Aminu har kuka yayi da ganin wannan abin kunyar da 'yarsa ta jawo masa agidan auranta,shi kuwa Dan Malam jikinsa ne yayi sanyi qalau harma ya kasa furta komai,kafin sukai ga daukar wani mataki Alu ya tsere,kuma garin ya bari gabaki daya.Malam ya zane Fulani sosai kuma yace dolene Dan Malam ya sawwake mata,dan malam kuma yace shi bazai iya ba ayi haquri yana son matarsa ahakan.Babu yadda suka iya illa barinsa da matar tasa,ita kuwa Fulani taci kuka sosai sanda taji labarin wai an nemi Alu an rasa, bayan watanni biyar saiga ciki ya bullo ajikinta,mahaifinta yace wannan cikin bana Dan malam bane,shima Dan malam ya soma zarginta don tunda sukayi aure sau daya ya kusanceta,sai yayi tunanin kila cikin na Alun ne.
Malam ya matsa masa akan dole saiya saketa kuma saita bar kauyen don bazai bari ta janyo masa abin fada ba agarin.Babu yadda dan malam ya iya illa sawwake matan sabida mutane suna ganin cikin za'ace ai cikin Alu ne.
Babu irin rokan da fulani batayi ba akan mahaifinta yayi haquri karya koreta amma fir! yaki.Yayunta da mamanta ma sukace babu ruwansu da ita ta tafi can ta karata da shegen danta.Bata da kalmar da zata kare kanta dashi don an riga an kama Alu adakinta,don haka komai zata fada akan babu abinda ya shiga tsakaninsu ba yadda zasuyi ba,amma harga Allah cikin jikinta na Dan malam ne.
Haka ta baro kauyen tana kuka,Mal.Muhammadu sarkin taimako alokacin yazo siyen sa ne akauyen,sai yaga yadda take kuka tana tafiya,kiranta yayi ya tambayeta abinda ke damunta ta gaya masa,yace ta masa jagora xuwa gidansu,bayan sunce yayi roko amma fir! Mal.Aminu yace bazai karbeta ba.
Haka dai suka baro gidan rai ba dadi,mal.Muhammadu yace"Toh yarinya idan zaki iya bina garinmu har xuwa lokacin da Allah zai saukeki lafiya asannan kuma mahaifinki ya huce sai mu dawo toh bismillah muje...."
"Ni kowani gari ne muje idan har kana da mata wacce zan zauna agunta...." Fulani ta fada tana mai kuka.
Murmushi yayi yace"Matana biyu saidai babu wacce ta taba haihuwa...." Fulani duk ta rasa abinyi shiyasa kawai ta yanke shawara ta bishi minna.
Acan kuwa rigimace babba ta kaure tsakaninsa da matansa musamman da suka ga Fulani dauke da ciki,sai suke ganin kamar karuwarsa ce,kila cikin da tayi ne yasa aka koreta daga gida shi kuma ya rasa abinyi shiyasa ya kawota nan. Kan kuce meye wannan har magana ya bazu agari cewa ai mai unguwa ya kawo karuwarsa ga iyalinsa.
Shi kuwa ya nuna ikonsa akansu,ya nuna musu cewa ya isa da gidansa,ya baiwa Fulani dakin da zata zauna ta reni cikinta harta haihu.Ya sayo mata wasu en kaya na amfaninta ya xuba adakin.
_*чαnzu wαccє írín zαmα nє fulαní tαчí αgídαn?*_
_*чα αkαчí mαl.muhαmmαdu чα ѕαuчα mαtα dαgα вαчα?*_
_*ѕαnnαn kumα чα αkαчí tα kαmu dα cutαr чσчσn fítѕαrí (fíѕtulα)?*_
_*ínα kumα lαвαrín tαfíчαr mαí mαrtαвα umαr fαruwα?*_
ku вíчσ hαfnαn
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top