22

❄️❄️❄️❄️❄️
*Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
❄️❄️❄️❄️❄️

*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*

*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*

*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*

*WATTPAD:HAFNANCY*

https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/

*°•ѕα∂αυкαяωα gα Dr.υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιнєя ѕтαтє,мιииα•°*

*°•ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍•°*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
__________________________________
💥

_*°•hαhαhα! ѕσrrч guчѕ í dєcídєd gívє αn updαtє σn híввαtullαh cuz ít'ѕ вєíng α whílє,fαtαlwαrku wαtσ lєσnα lukαѕ tαnα nαn tαfє αnjímα kαdαn kσ kumα gσвє dα ѕαfє ínѕhα Allαh•°*

_*°•wαnnαn ѕhαfín nα mαllαkα muku ѕhí hαlαk mαlαk dσn hαkα kuчí чαddα kukєѕσ dαѕhí👇

_*°•ѕíѕ mugírαt muѕα(mαruвucíчαr 'kíѕhín jαhílcí)•°*_

_*°•ѕíѕ ѕαfíччα Alíчu wαkílí(mαruвucíчαr 'mαѕαukín ѕσn)•°*_
____________________________________

*Թɑցҽ 22*

Har Najmiy ta gyara filonta zata kwanta,sai taji kawai an turo kofar dakin an shigo,ahankali takai hannu ta kunna dim light din dake gefen gadon,hasken ya taimaka wajen bayyana mata wanda ya shigon,ajiyar xuciya ta saukar kana tace"Ooh Ya hayati ashe kaine?"

Murmushi ya sakar kasa kasa yace"Ada wa kike tunanin zai iya shigowa dakin baccinki acikin wannan daran face mijinki my habib albi?uhm gayamin?" ya fada tare da zaunawa agefen gadon,ya jawota ta fado jikinsa,daga shi har ita wani irin bakon yanayi ne suka tsinci kansu ciki wanda basu taba jinsa ba kuwa.

Ta soma kokarin raba jikinta daga nashi,kara janyota yayi ta shige jikinsa dakyau,ya shiga shinshina gashin kanta yana mai yamutsa fuskarsa aciki,numfashinsa yaji kawai ya soma haurawa sama sama,cikin wata dasasshiyar murya yace"Habib albi ina son kamshin nan sosai.... "

Kukan shagwab'a ta sakar masa ganin abin nasa na kokarin soma wuce gona da iri amma aranta farin cikine fal acikinsa na ganin yau mijinta ya kusanto inda take har yana mata wasa irinta ma'aurata ba kallon qanwarsa kuma ba.Shagwab'ar tata ta taimaka wajen kara masa kaimin abinda yakeyi,romance dinta ya shiga yi sosai babu gaggautawa,itama ta cire kunya da shakku ta shiga maida masa da martani,can ya dakata yana maida numfashi,idanuwansa ƙyam akanta,ita kuma rausayar dakai tayi gefe don bazata juri kallon ƙwayar idanuwansa ba.

Cikin wani salon Jan hankali yace"Najmiiiiiiyya kalli cikin ƙwayar idanuwana.... "

Dakyar ta kalleshi,amma tana yi tana dan rufe idanuwan lokaci xuwa lokaci,sauka yayi daga samanta ta hanyar mirginawa gefenta,ya sanya hannu ya tallafo fuskarta gareshi,fuskokinsu tamkar su manne da juna tsabar kusanci,murmushi yayi kana yace"Najmiy na mace akan sonki,don haka inason ayau dinnan ki bani dama na gwada miki irin kalar son da nake miki,inason ayau ki karbeni amatsayin mijinki ba dan'uwa kuma ba,pls Najmita can I move on?"

Sanya hannu tayi ta rufe fuskarta dashi alamun kunya,kuma alokaci guda taji gabanta ya hau dukan chalugude,hakan da tayi kuwa ba karamin birgeshi yayi ba don arayuwarsa yana mugun son mace mai alkunya.

"Toh shikenan tunda baki yarda ba nina tafi,aduk lokacin da kika yanke shawara da xuciyarki ta kuma amince miki dani toh sai kiyi gaggawar sanar dani..... " yayi yunkurin mikewa don barin dakin,da sauri ta ruƙo hannunsa tace cikin sanyin murya"Na amince Ya hayati.... " cike da tsantsar farin ciki ya rungumota yana fadin"Masha Allah thank you my lovely wife Allah yayi miki albarqa matata... "

Ahankali ya rad'a mata akunne"Akwai wata alfarma da nake nema kuma awurinki,shin zaki iya daurewa ki min ita?"

"Ka wuce gaban ayi maka alfarma awurina,bada umarni kawai Ya Hayatina... " acewarta cikin shagwab'a,sosai yaji dadin kalaman nata wanda hakan yasa kawai yaji sonta ya mugun karun masa acikin xuciya.

Ahankali ya soma magana"Najmiy dama so nake kiyi just 2month awajen aikinki don kici moriyar karatunki,bayan wannan watanni biyun kuma sun cika na sanya araina cewa zansa kiyi resigning don tun ina karamina bani da burin wai ace matata tayi aiki,all I want her to be is to become a full house wife,nata kawai ta dunga kula dani da kuma 'ya'yanmu,Najmiy jiya watannin naki biyu ya cika da soma aikin,so pls can u kindly show some love to ur lovely husband by resigning?"

Jikinta ne yayi sanyi qalau da maganganun nasa,tana matukar son aikinta amma ya zame mata dole ta ajjeshi tunda mijinta ya nuna bayaso,bata ankara ba kawai taji hawaye ya soma kwaranyo mata saman kunci,takai bayan hannu zata sanya ta goge,sai taga ya rigata saukar da harshensa saman kuncin nata,ya shiga lashewa,sai daya gama lashewa tass kana yace"Hakan ba zata samu bako?"

Cikin raunin murya tace"Tunda mijina ya bada umarni kuma yace haka yakeso ai dole nabi,na maka alqawari daga yau na ijje aikina.... "

Beyi wata wata ba ya rungumota tsam jikinsa ya shiga shi mata albarqa mara iyaka,daga bisani sukaje suka dauro alwala sukayi sallah raka'a uku,ya dade yana musu addu'ar samun zaman lafiya da kuma zuria dayyaba,can ya shafa,ya juyo ya kinkimeta sai gado,saida ya soma ciyar dasu da gasasshiyar namar daya shigo da ita da kuma fresh milk,kana suka bi lafiyar gado,daga nan kuma labarin ya soma sauya zani.

Faruq ya rikice akan Najmiy,dama gashi akullum cikin gyarata Haj.Babba take,don haka ni'ima ya gama ratsata ta ko'ina shiyasa gogan naku ya rikicen,ita kuwa tasha kuka don azaba abinka da sabuwar shiga,Faruq yasha yakushi dasu cizo amma duk abanza don bema san duniyar da yake ba,awannan daran sun rayashi,sun gurzashi don samun albarqar ubangiji da kuma ladarsa duk da cewa Faruq dinne kawai yayi ta fama shi daya.

***
Tun daga wannan ranar kuwa ita da Faruq suka dinke da juna,wani irin mugun shaquwa da qaunar junansu ya dada yin karfi atsakaninsu,kuma adaran farkon nasu ne Allah ya azurta Najmiy da samun shigar ciki,sai da yayi watanni uku kafin su gane sabida batayi wani laulayi ba,wannan cikin kowa yayi murna da samuwarsa musamman Hayat wanda dama can plan dinsa na akan dansu ne,duk da cewa ya danji zafin samun cikin da Najmiy tayi da waninsa amma murnar ya dara bakin cikin.Tattalin cikin ake sosai bana wasa ba,sai tanadi ake tayi na tarar babyn har Haj.Babba,wani abin bakin ciki da tausayi,duk yadda wannan family din suka ci buri sosai akan wannan cikin na Najmiy sai d'an baizo da rai ba,haqiqa abin beyi musu dadi ba amma sai suka rungumi kaddararsu suka kuma lallashi Najmiy wacce har kuka tayi akan hakan,Hayat yafi kowa jin haushin wannan abin sabida plan dinsa ya ruguje.

Cikin hukuncin ubangiji kuma Najmiy bayan watanni biyar ta sake samun wani cikin,wannan karon tayi laulayi sosai akansa tamkar bazata rayu ba.Samuwar wannan cikin Na Najmiy yasa Maryam ta tadawa Hayat da rigima don haqurinta ya soma karewa,ce masa tayi kiri-kiri "Hayat nima inason naga gudan jinina,wallahi kaji tsoron Allah Hayat kana daukar alhakina da yawa,shekaru kusan biyu muna tare amma ko hannuna baka tab'a tabawa ba da sunan jindadi,idan kuwa har anga ka rikenin toh zalina zakaci......"

Kwance belt dinsa yayi,ya soma kokarin saukar da wandonsa kasa yana fadin"Don ubanki kwanta na miki cikin tunda ke 'yar iska ce,so kike na kusanceki,toh maza kwanta shegiya jarababbiya kawai....."

"Tunda agidan mijina nayi iskancin ai da sauki,kuma badai ubana ba.... "

Zaro belt din yayi daga jikin wandon ya matso kusa da ita yana fadin"Sai uban waye?"

Kan ta ankara har ya soma shaud'a mata belt din ajiki,kasa ihu tayi don xuwa yanxu ta riga ta saba da bugun da takesha daga hannunsa,kuma harwa yau taki gayawa kowa don harga Allah tana masifar son mijinta.Kowa na zaton suna zaune lafiya qalau ne musamman ma Faruq,don har zama suke suyi hira agaban jama'a amma na ciki na ciki,kowa na tunanin kila lokacin samun rabon maryam dinne beyi ba,alhalin basu san cewa akwai gagarumar badakala akasa ba.

Cikin Najmiy nada 2months ya bare,wannan karon har kuka saida Hayat yayi aboye,koda yaje gaisheta kasa haquri yayi yace"Don Allah asarar ya isa hakanan,kiyi kokari idan kin dauka next time kar wata matsalar ta sameshi idan ba haka ba xansa dan'uwana ya karo aure don muna da buqatar samun *'YARIMA MAI JIRAN GADO'*..... " fuuuu! ya tashi ya fice,angode babu kowa afalon sai ita,ta dade tana mamakin wannan furucin na Hayat wanda hakan har kuka ya sanyata amma taki gayawa kowa.

Tun asannan kuma Najmiy bata sake daukar wani cikin ba,Hayat ya shiga cikin tashin hankali sabida gabaki daya ta ruguza masa plan din da suka shirya da Rougcoin don Hayat ya sake nemoshi awaya,kuma har sau biyu yaje garinsu Ibadan.Haka dai ya haqura tare da xubawa sarautar Allah ido don yayi yayi da Faruq ya kara aure amma yace shi sam bayada ra'ayin ajje mace fiye da daya.

Sai bayan shekaru biyu Najmiy ta samu wani cikin,wannan karon ta haifeshi lafiya qalau,Hayat ji yayi tamkar ya xuba ruwa akasa yasha don murnar wannan haihuwar,kai kace ko shi akai wa haihuwar don yadda ya kasa tsaye haka kuma ya kasa zaune,abin ma har mamaki yaketa baiwa sauran yan'uwansa,aganinsu qaunar d'an yake ba tare da sanin cewa yana da wani mugun nufi akasan ranshi akan yaron ba.

Najmiy ta roki alfarman asanyawa yaro sunan dan'uwanta daya bata kuma bataso asakaye sunan wato *'ARYAAN'* sunan da yaro yaci kenan.Aryaan ya taso cikin so da kuma kulawar iyayensa,kakarsa Haj.Babba da kuma anties nasa,Abida 'ya'yanta biyu ayanxu,hidaya ma tana da 'ya.Hayat sai ya dunga nan da nan da yaron,shima Aryaan ya saba dαshi don duk wani motsi ídαn чαji zakaji yace"Uncle ne?".

Wata rana Maryam ta tashi da wani irin matsanancin ciwon ciki wanda har saida aka kaita asibiti,iya binciken likita an gano cewa muguwar sha'awa ce ta taru tayi mata yawa,ya kira Hayat office ya gargadesa akan ya dunga kula da buqatunta don ciwon sha'awa nada illa sosai,toh tun asannan ya danji tausayinta ya soma hada shimfida da ita ba don yaso ba,kota gamsu ko bata gamsu ba dagawa yake abinsa ya kyaleta,Aryaan nada shekaru uku aduniya Maryam ta haifi 'yarta kyakkyawa mai kama da ubanta Hayat,ranar suna akayiwa Haj.Babba kara aka sanyawa yarinya sunanta wato *'KHADEEJAH'*,za ana kiranta da *'ILHAM'*.

Akwai wani aminin Mai martaba Umar Faruq mai suna *'DR.ABUBAKAR SADIQ BATURE'* (kun tunashi ah first page?likitan Aryaan).

Aminai ne sosai,tare sukai karatu ah Udus,ah inda Faruq ya karanci *'POLITICAL SCIENCE'* shi kuma Bature kamar yadda ake kiransa sabida mamarsa baturiyace,da baban zai aureta sai ta musulunta,toh shi baturen ya karanci *'MEDICINE'* ne,bayan ya hada degree dinsa sai iyayensa suka turashi masters ah qasar india,toh bayan ya kare sai babban asibitin india suka rikeshi don ya kasance mai gwazo da kokari,ya zama shahararran likitan kwakwalwa ah inda kasashe daban daban har gayyatarsa yin surgery suke.

Dakyar yazo ya dawo Nigeria ya auri wata Nabila wacce dama akwai alqawarin aure atsakaninsu,koda ya aureta ya ijjeta gaban iyayensa ne yace daga baya idan komai yayi masa daidai zai taho ya dauketa xuwa India da zama.bayan watanni uku uku yake squeezing lokaci yazo yaga gida,yakan yi musu a week kafin ya koma,Allah yazo ya azurta Nabila da haihuwar twins mace da namiji (My dream😀). *'NADEEM'* da *'NADEEMAH'*, shekara daya kacal Aryaan ya basu.

Akan kai twins gidansu Mai martaba don sada xumunci,haka zalika akan kai shi Aryaan din gidansu suma,wata irin muguwar shaquwace ta shiga tsakanin yaran musamman Aryaan da Nadeemah.Aryaan nada shekaru biyar Najmiy ta sake haihuwar 'ya mace wacce taci sunan Haj.Karama wato *'MAYMUNERH'* sai suna kiranta da *'ZAITON'*,ba Aryaan kadai aka haifawa wannan 'yar ba hatta su twins da kuma Ilham sunyi farin ciki sosai,acewarsu sun sami qanwa don suma twins mamarsu bata sake haihuwa ba bayan su,haka ma Maryam shiru kake ji tun bayan haihuwar Ilham.

Acikin wannan lokacin ne kuma Dr.Bature ya dawo ya dauke iyalinsa suka koma qasar india inda yake aiki,Aryaan da Nadeemah har zazzabi sukai na rabuwa da juna.Tunda suka wuce sau daya sukazo ganin gida.

Bayan shekara daya,Aryaan ya soma experiencing some strange symptoms atare dashi,abin takai har suma yakanyi,awannan lokacin kuma su Dr.Bature suka sake xuwa ganin gida shine Mai martaba ya labarta masa lalurar Aryaan,bayan wasu yan gwaje-gwaje ya tabbatar musu da cewa ya kamu ne da cutar *'MEDULLOBLASTOMA CANCEROUS BRAIN TUMOR'*,yace dole za'a fita dashi waje aje ayi masa surgery.ba tare da wani b'ata lokaci ba aka fita dashi xuwa qasar India.

Anyi aiki cikin nasara,amma wani abin mamaki aduk lokacin da yayi yunkurin dawowa cikin rayuwa sai wani gagarumin shock from no where yakai masa attack ah kwakwalwa kuma iya binciken likitocin sun kasa gano wannan shock din,kamfutocinsu sai nuna musu suke *'NOT DETECTED'* harna tsawon shekara daya babu magana mai dadi.

Wannan kuwa aikin Hayat ne,akwai wata bayerabiya wacce Roughcoin ya amsowa Hayat wani abu haka da already an riga anyi programming dinsa,wani babyn roba ne karami mai suffar mutum sak!,toh aduk lokacin da Aryaan yayi yunkurin dawowa cikin rayuwa sai kaga Hayat ya dauki wannan babyn robar ya shiga caccaka mata allura aka,toh allurar nan da ake caccakawa wannan babyn shine ya zamo shock din dake kaiwa Aryaan attack,zakaji Hayat yana kuka yana fadin"Dana kayi haquri iyayenka ne suka jawo maka,na tabbata yanxu Faruq da Najmiy suna matukar jin radadi da kuma zafin halin da kake ciki,kadan kenan daga cikin irin abinda ni nake ji agame da mamarka..... "

Xuwan Hayat sau biyar India tunda Aryaan ya kwanta rashin lafiya,agidan Dr.Bature su mai martaba suka sauka,lokaci xuwa lokaci mai martaba yake xuwa ganin gida sabida mutanensa.

Ayau kuma Haj.Babba itama lokaci yayi,kwananta ya kare aduniya,ciwon siga ya zamo ajalinta shine mai martaba ke kokarin komawa gida kamar yadda kuka gani ah first page.Sai ya bar Najmiy donta tsaya da Aryaan.

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

_*Masha Allah am xoxo happy da yau muka kawo karshen wannan tuna baya din,yanxu sai mu koma kan ainihin labarin *_

_*ku biyoni don jin tsintuwar da mai martaba umar Faruq zai yi🏃,amma kafin nan bari mu hanzarta mu dubo wani ƙauye mai suna 'TEWI' wanda ke cikin garin minna*_

_*Masu son Hayat yanxu ina fatar zaku dan rage 😂*_

_*Abinda kuma nakeson ku gane shine,ciwon brain tumor ba Hayat ne ya haddasa masa ba,ciwonsa daga Allah ne,nashi dai wannan shock dinne yake bashi.*_

*íntєrmíѕѕíσn (tѕαkíчαr lαвαrí)💘💘*

*tαku*

*mσm híввαh💕*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top