Թɑցҽ 16
❄️❄️❄️❄️❄️
*Ḧ̤Ï̤B̤̈B̤̈Ä̤T̤̈Ṳ̈L̤̈L̤̈Ä̤Ḧ̤*
❄️❄️❄️❄️❄️
*°•(ĸyaυтa daga Aℓℓαн)•°*
*°ιиιqυιту,ємραтну,нυмιℓιαтισи & яσмαитι¢ ℓσνє💑°*
*MALLAKAR:HAFSAT HAFNAN💕*
*WATTPAD:HAFNANCY*
https://m.facebook.com/Hafnans-Novell-246747739535534/
*•°ѕadaυĸarwa ga Dr. υмαя fαяυq вαнαgσ,ємιя σf иιgєя ѕтαтє мιииα•°*
*ιnтellιgenт wrιтer'ѕ aѕѕo✍*
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*°•yaυ ranarĸι ce dala,don нaĸa ĸι мaтѕo ĸυѕa ĸιyι нonoυrιng wannan ѕнaғιn,na мallaĸa мιĸι ѕнι нalaĸ мalaĸ,тanĸѕ ғor тнe тrυe love💑•°*
____________________________________
💥
*Թɑցҽ 1⃣6⃣*
Faruq bawan Allah kuwa sai misalin biyar saura kwata suka iso garejin Ikeja,ya gaji sosai don tunda yake arayuwarsa har ya girma haka bai taba yin doguwar tafiya irinta yau ba,awanninsu dai daya har goma sha daya akan hanya,kuma duk tsayuwar da ake tayi akan hanya don sanya abu aciki,toh shi babu abinda ya siya sai ruwan gora don ahalin yanxu burinsa kawai ya ganshi agarin lagos,sallace kawai yake fita yayi,ruwa kuwa lokaci xuwa lokaci yake dan kurba.Bayan kowanni awanni bibbiyu Haj.Babba ke ƙiransa taji yaya hanya?ko sun kai?sai shi kuma yace mata a'ah da saura.Abin har yazo ya soma isarta dake itama din bata taba xuwa lagos din ba,tace"Wai Faruq dama haka Lagos din keda uban nisa?sai kace zaku bangon duniya ganin yajuj da majuj?"
Murmushi kawai yayi yace"Hajiyata idan nakai zan kiraki.. " Toh tun asannan sun kwashi kusan awanni hudu basu sake waya ba,yanxu saukarsa kenan ah mota.Jan jikinsa yayi xuwa wani wurin zama inda aka tanadar domin matafiya,zamarsa keda wuya ya zaro hankicinsa daga aljihun wandonsa ya shiga goge zufar data tsassafo masa asaman goshi.Babu abinda yake buqata ahalin yanxu kamar ya samu lafiyayyiyar abinci yaci,bayan ya gama kuma ya nemi lafiyar gado,amma inaa! ayau dinnan yakeson ya soma yin abinda ya kawoshi kafin ma ya tafi hotel din da yayi booking online.Wani mai saida lemukan gora ya yafito da hannu,ya taho tare da ƙanwarsa dake dauke da tika tikan famke acikin roba.Saida ya siya yaci yayi kat dashi kafin ya latso Haj.Babba don gaya mata cewa yakai sabida hankulansu duk ya kwanta musamman na Abbansa.
Bayan sun gama gaisawa da Haj.Babba,sai data sake masa tsiya akan ita azatonta bangon duniya zasu ganin yajuj da majuj,dariya kawai yayi abinsa kana yace"Ina Abbana yake?Ya jikin nasa?da sauki ko?" ya jero mata tambayoyin nan alokaci guda.
"Da sauki sosai don yanxu likitocinsa suka zo dubashi kuma sun tabbatar mana da cewa akwai improvement.... "
Cike da farin ciki yace"Alhamdulillah! Wallahi harna ji dadi sosai,don Allah hajiyata taimaka kisa masa wayar akunne naji saukar numfashinsa kawai.... "
Murmushi tayi tare da jinjina irin kaunar da Faruq kewa mahaifinsa,sakala wayar tayi akunnen Mai martaba wanda yaketa sauraron hirarsu tun dazu,sai dai bata bari sunyi hirar Hayat agabansa ba,tace"Ranka shi dade Faruq ne keson yayi maka magana..... "
Daga can bangaren kuma Faruq yaji saukar numfashin Abbansa,wasu hawaye ne yaji sun tarun masa acikin ramin ido na tausayin mahaifinsa,cike da rauni yace"Abbana ubangiji Allah ya nuna mana ranar da zaka tashi tsaye akan kafafunka,Allah ya nuna mana ranar da magana zata sake fitowa daga baki mai kwatanta adalci da kuma fadin alheri,Abbana dama so nake na gaya maka cewa na isa garin Lagos kuma insha Allahu zanyi nasara kan abinda ya kawoni don ina tsananin son naga ka tashi daga wannan ciwon..... "
Bey kai ga karashe zancensa ba yaji ance"Faruq zaka soma ko?so kake kasa ya gane cewa Hayat kaje nema salon hankalinsa ya kara dagawa ko?" acewar Haj.Babba wacce itace ta wufce wayar daga kunnen mai martaba sabida speaker din aloud take shiyasa take iya jiyo duk abinda yake fada.
"Hajiyata don Allah kiyi haquri na kasa controlling kaina ne... "
Tace"Maza ka kama jiki kaje ka dubo mana inda kace yana zaune,duk yadda ake ciki ka kira ka sanar dani komai... "
"Naji Ummin Najmiy... " haka yake kiranta most of the time.
Ya sake cewa"Ammm.... Hajiya nace ba?... "
"Kace meh?" acewarta,shiru yayi mata,ya shiga sosa ƙeyarsa tamkar mara gaskiya.Ta gane nufinsa don haka daga murya tayi ta ƙirawo sunan Najmiy don ta tabbata muryarta yakeson yaji amma kunya ta hanashi fada.
Dake waje ta fito yin wayar,ta baro su Najmiy din awajen mai martaba,ai kuwa da gudu Najmiy ta fito don kiran Hajiyar ya daki dodon kunnenta dakyau.
"Ummii gani.... " mika mata wayar tayi tace mata Faruq keson magana da ita,cike da kunya ta soma ja da baya,Hajiya tace"Yauga iskanci ruwa-ruwa meye haka kikeyi?karbi man?"
Dakyar ta karbi wayar ta sakala akunne,ita kuwa Hajiya komawa wajen mai martaba tayi tana murmushin yarinta irinna Najmiy.
Ahankali ta furta"Assalamu alaykum_*Ya Hayati*_ (my life)"
Saukar da ajiyar xuciya yayi kana yace"Amin wa'alaikis salam _*Habib Albi*_ (Love of my heart).
Kuka ta fashe masa dashi tace"Ya Hayati don Allah ka yafemin,duk nice na sakaku cikin ƙalubalen da kuke ta fuskanta arayuwa,nice sanadiyyar barin Yaya prince karami gida,kuma nice..... "
"Ke wai meye haka?zaki soma haukarki ko?" ya katseta cikin tsananin fushin jin irin furucin daya fito daga bakinta.
Ahankali tace"Yayana kayi haquri karkayi fushi dani wallahi bazan kuma ba.. "
Murmushi yayi kawai,cike da qaunarta yace"Yauwa dats my gal,kiyi kokari ki kunna wayar dana baki kan na taho,idan na gama abinda nakeyi zan kiraki anjima.. "
"Okay,Ana bahibbak Ya Hayati (I love you my life). " ta fadi masa hakan ahankali.
Shima yace"wa'ana ahbuk ' aydaan Habib Albi (I love you too love of my heart)" hahaha duk itafa ta koya masa hakan.
Daga haka sukai sallama.Agogo ya duba yaga shidda saura,da hanzari ya mike ya fice daga garejin,abakin titi ya tare wani dan acab'a.Kiran spanzy yayi,kana ya baiwa dan acab'a wayar,ya gaya masa sunan unguwar da za'a kaishi donshi bai rike sunanta ba.Ai kuwa dan acaban ya gane unguwar,don haka babu wani b'ata lokaci sai gashi sun iso *'OJODU STREET'* inda anan ne su Hayat ke zaune.
Tun shigowarsu unguwar Faruq yaji kawai area din beyi masa bane becuz it's somehow crowdy kuma unguwar ya tara 'yan shaye-shaye ne sosai.Atake anan ya kara jinjinawa kokarin Hayat na iya rayuwa acikin irin wannan untidy environment din,acewarѕa.Wani dandalin samari ne ya hango zaune saman wani dogon benci kusa da wani shago,kowannensu rike yake da karan sigari yana zuƙa cike da kwarewa,hayaki na fita ta hanci da kuma baki.Har sun wucesu,sai kuma ya umarci dan acab'a daya dawo da baya.Adaidai wajensu ya dakatar dashi,yace masa yana xuwa.
Wani cikinsu ne ya ankarar da sauran ah sa'ilin da yaga Faruq ya nufosu,cewa yayi"Oboi! See one hot classic man... " sauran ne suka maida hankulansu ga Faruq suma suka shiga yaba haduwarsa.Gaisar dasu yayi sanda ya karaso inda suke,duk suka amsa.
Wani yace"Bros how may we help you?"
yace"Am looking for a guy named Hayatudden and his friend Abraham,sana'arsu itace tukin bus,a Danfo driver & conductor.... "
Gaba daya sukace"Oh!You mean Badman & Roughcoin?mun sansu,nawa zaka ban na kaika gidansu?"
Wani aciki yayi masa wannan tambayar,shi kuwa Faruq wuta ne ya dauke masa na dan wani lokaci jin irin banzan sunan da Hayat ke amfani dashi anan,ji yayi wani uban kuka na neman taho masa,da sauri yayi ta maza ta hanyar danneshi yace"Money isn't my problem Mr.man,juz take me there... "
Su biyu aciki ne suka taso don masa rakiya,yaje ya sallami dan acab'a,cike da kasaita da jan'aji yabi bayansu,duk inda suka gifta sai an bi Faruq da kallo har ya bacewa ganinsu,don Faruq karshe ne akyau da kuma iya daukar wanka,Sam Sam basa kama ko kadan da Hayat,kowanne kamanninsa daban,haka kuma k'yawunsa daban,idan ka gansu tare ma kana iya rantsewa da cewa basu hada jini ba,sabida basa kama,haka kuma bazaka iya cewa ai wannan yafi wancan kyau ba,kowa naji da kyan da Allah yayi masa ne,haske kawai Hayat zai nunawa Faruq.Tafiyar mintuna biyar kawai sukayi sannan suka iso wani gida wanda kofarsa an garkameta da k'aton kwado,nan akace masa gidan da suke zaune kenan,amma sai gab da sallar magrib suke dawowa.Yayi musu godia tare da fitar da dubu biyu ya basu,cike da murna suka karba suna godia,kana sukayi gaba.Shi kuwa ya bisu da kallon Allah ya shirya.samin wuri yayi ya zauna akan wani dakali dake kofar gidan.
Akalla ya share kusan mintuna goma zaune anan,can yaga wata matashiyar budurwa wacce tasha dogon hijabinta har kasa da kuma niƙabinta,da alamu ma daga islamiya take sabida Qur'anin dake rike ahannunta ta fitar dashi daga cikin hannun hijabin.Dan madaidaicin gidan dake kusa danasu Hayat yaga zata shige,da sauri ya mike yana fadin "Malama assalamu alaykum don Allah tambaya nake... "
Dakatawa tayi,ta kallo inda yake tace"Amin wa'alaykas salam ina jinka" ta fadi hakan cikin wani irin zazzakar muryarta.Shi kansa Faruq saida ya yabawa zakin muryarta kafin yace"Don Allah ko kinsan wani abu agame da wa'enda suke zaune acikin wannan gidan?" ya fadi hakan tare da yin nuni da gidansu Hayat.
Sai data kwashi kusan dakiku biyar kafin tace"Da fari dai meye alakarka dasu kafin na gaya maka komai?"
"Tambaya kan tambaya halin dan Nigeria Kenan,wallahi ni abinda na tsana kenan arayuwata wai kayiwa mutum tambaya amaimakon ya maido maka da amsar tambayarka,a'ah sai dai....."
Bai karashe fadarsa ba kawai yaga tasa kai tayi shigewarta cikin gidan ba tare da ta tankashi ba.Dogon tsaki yaja tare da furta"I wonder why some people behave like animals,yanxu mena fada anan da har ya bata mata rai?" (hahaha! A rhetorical question without an answer dear Prince Faruq).
Komawa wajen zamansa yayi,time to time yake duba agogon dake makale ah tsintsiyar hannun hagunsa,it's exactly 6:25pm.
Ita kuwa tana shiga cikin gida tsananin b'acin rai ma ya hanata gaida wanta da kuma mahaifinta wanda ake kira da 'Tsoho',wucesu tayi zata shige daki,da karfi Yah Rilwan yace"Ke! Maryam lafiyarki kuwa zaki shigo cikin gida babu ko sallama balle musa ran zaki gaidamu?iyyeh tambayarki nake?"
Daga nikabinta sama tayi,anan naga fuskarta,babu laifi tana da dan kyanta,ashagwab'ance tace "Yayah kayi haquri wallahi wani ne ya bata min rai awaje,wai tambaya yake akan samarin dake zaune acikin gidan can shine nace sai ya gayamin alakarsa dasu kafin na gaya masa komai akansu,shine ya hauni da fada ni kuma abin yaban haushi na shigo abina.. "
Tsoho yace"Maryam kina da gajen hakuri wallahi,wato dayake ke din bakison ayi miki fada arayuwarki shiyasa kika wulakantasнι kikayi shigowarkι,toh Allah ya shiryeki,kai Rilwanu tashi kaje ka dubo ko wanene ke nemansu?kuma meyasa yake nemansu din?don tunda yaran nan suka soma zama ah gidan nan ban taba ji ko kuma ganin wani mutumin kirkin yazo nemansu ba... "
"Toh tsoho bara na dubo... " ya mike ya fice,ita kuwa Maryam dan guntun tsaki ta saki kana tayi shigewarta daki don ita arayuwarta ta tsani aci mata fuska kamar yadda Faruq yayi mata.
_*тoғa! wacece мaryaм dιnnan?*_
_*ιna ĸυмa laвarιn нayaт da roυgнcoιn?*_
*тaĸυ ce*
*ⓗⓐⓕⓝⓐⓝ💕*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top