Chapter 4
"A hankali ta mike ta shiga bathroom ta watsa ruwa ta fito,night gown fara ta saka jikinta inda ta nufi dinning area dun da moha ya nuna mata dazu don yunwa takeji matuka,food flask din farko ta bude kaza ce gashashiya gefenta chips ne,daya flask din kuma pepper soup din kayan cikine sai jug da aka cikashi da coconut juice din da yaji madara,ta danci abincin kadan musamman kazar taci da yawa ta kora da lemon kwawar inda ta haye gado hankalinta kwance ta fara baccinta mai matukar dadi....
"Karfe 6 na safiya rahma ta bude idonta,da sauri ta bude idonta ganin ta makara har gari yayi haske batayi sallar asuba ba,da sauri ta ziro kafafuwanta daga kan gadon sai dai abinda taji tayi tuntube dashine yasata saurin kallon gurin,moha ne kwance a kasa ya shimfida bargo yasa pillow yana ta baccinsa hankalinsa kwance...gabanta ne yayi mugun faduwa da sauri ta kewayeshi ta wuce ta dauro alwala ta gabatar da sallah,ruwa ta hada ta shiga tai wanka ta fito duk yana kwancen bai farkaba...doguwar rigar lace sky blue colour ta saka wacce ta karbeta matukar gaske,a hankali ta zagayeshi ta fice daga dakin ta nufi kitchen kusan 10 minutes ta dauka tana kallon kitchen din don tsaruwarsa ya wuce misali,tab gaskiya sunada kudi sosai ta fada cikin zuciyarta
"Chips da omelette sai ruwan tea sannan tai warming ragowar kazar shine abinda rahma ta dafa don ba wata gwana bace gurin yin girki don suma gidan nasu masu aikine sukeyi musu girki
"A dinning ta jera komai inda ta shiga dakin jikinta sanyaye,jikin mirror ta tarar dashi tsaye yana taje gashin kansa da alama ya fito daga wankane,da sauri ta juya ta fice daga dakin jikinta na rawa don wannan shine karo na farko data taba ganin namiji dagashi sai boxer
"Wayarta ta janyo ta fara karanta messages na fatan alkhairi da kawayenta da abokananta suke turo mata,jin shirun yayi yawa yasata sake mikewa ta koma dakin
"Zaune ta tarar dashi yana aiki a laptop ,sai dai tana shiga ya kafe ta da zafafan idonsa wanda zan iya kiransu sexy eyes sannan kuma zan iya kiransu bold eyes,ji tai jikinta na rawa inda ta kasa ce mishi komai ta tsaya akanshine kawai,ganin bata da niyyar cewa komai ya sashi sake kallonta a zafafe yace what?
"Food is ready......ta karasa maganar cikin i'ina
"Don't you know how to knock the door before entering inside?ya fada in a romantic voice
"Naga kofar bude yake ai ta fada a hankali
"Ok then what?
"Kazo muci abinci ta fadi maganar cikin sanyin murya
"Shiru yai na seconds 40 don har rahma ta fidda rai zai bata amsa
"Dont ever disturb me again,kuma zanci abincine duk lokacin da nake ra'ayi i'm not a kid....ya fada yana zuba mata kyawawan idanunsa
"Sannan you can do whatever you want ,i don't want to know anything that will happen when i'm around or away and lastly you can only talk to me when it's necessary Okay!ya karasa maganar yana janyo kofar dakin yai ficewarsa
"Ji banza sai kace wani dan sarki to dama ubanwa yace aurenka nai don ina sonka,don haka koma me zakayi min i will never fucking care,useless kawai ta fadi maganar a zuciyarta inda ta fice ta nufi dinning area,a bakin kofa suka hadu da mom a hankali ta zube kasa tana gaisheta
"Cike da murna mom tai hugging rahma tana mai nuna farin ciki,sai yanzu ta kara tabbatar da kyau irin na rahma kamar ita tayi kanta,sake godewa Allah tayi don tasan tabbas moha yayi sa'ar mata tasan duk taurin kansa tuni ya zubar da makamansa daren jiya
"Murmushi mom tayi inda ta sake yiwa rahma nasiha ta riko hannunta suka wuce dinning area din....yusrah ce zaune da mahmud,da sauri suka mike suka gaishe da rahma cike da girmamawa da kauna,mamaki takeyi matuka ganin yanda duk yan gidan suke sonta,maimakon ace sune basa sonta kamar yanda take karantawa a novel da fina-finan tana ganin cewar yan uwan miji basu fiye son maceba sai dai ace miji yana son matarsa sai ya kasance taga akasin haka
"Bayan sun kammala cin abincin mahmud sarkin tsokana yanata zuba musu tsokanar tashi,mikewa tai ta kalli mom tace mom zanje na dan huta tin kafin wayannan tom and jerry din su saka cikina ciwo
"Ai nida kike gani na nan jaruma priyanka chopra har kuka takeyi akan sona da takeyi aunty rahma,mahmud ya fadi maganar cikin tsokana
"Yusrah ce tai saurin kallonsa tace ni kuma sharukhan har suma yayi saboda nace bashi nakesoba dansa nakeso aryan khan
"Sake bushewa sukai da dariya inda rahma tace mom kin gansu ko nace miki zasu sa cikina yai ciwo
"Murmushi mom tayi tace maza tashi kije ki huta dafatan baki da damuwa?
"Tunowa tayi da kiran da manager yayi mata dazu cewar ta fito aiki gobe,da sauri ta dubi mom tace ba wata matsala mom sai dai dazu manager bankin mu ya kirani yace in koma aiki gobe
"Murmushi mom tayi tace to banda abinki rahma ai mijinki zaki fadawa,maza jeki fada masa
"A sanyaye ta mike tana matukar tsoron yanda zata tunkari moha da zancen yanda ko warning dinsa na dazu bai gama sakin jikintaba
"Wannan karon knocking kofar tayi,yes come in ya fada cikin rashin kulawa,murza kofar tai ta shiga wannan karon wayace a hannunsa inda yake kwance akan kujera kansa na kallon ceiling,dauke kansa yai daga kallonta inda yaci gaba da wasa da wayarsa
"Zama tai gefen kujerar dake kusa dashi inda ta fuskanceshi
"What again? Ya fada yana cigaba da danna wayarsa
"Dama zan koma office ne gobe,manager ya kirani yace hutun kwana 2 kawai suka bani
"Ohh yanzu don wannan har sai kin fadamin,ai tuntuni na fada miki cewar you can do whatever you want duk abinda kikeso kiyi kawai babu matsala,sannan na manta ban fada miki ba niba anan nake zauneba a London nake aiki kuma gobe zan koma.....so you can do whatever you like i don't fucking care
"Zuba mishi ido tayi ganin yanda yake magana tamkar bada ita yake magana ba domin a hankali yake magana fuskarsa na kan wayarsa...
Cike da takaici tace amma aiba haka musulunci ya koya mana ba domin wajibine duk inda zani na sanar dakai domin ni matarkace ta karasa maganar a zafafe
"Don't you ever dare raised your voice at me,this is my house not yours,so stay in your limits,ya fada a zafafe
"Cike da takaici ta dubeshi tace but.........
"Shut up!will you please kindly get out from my room? Ya karasa maganar yana nuna mata hanyar fita
Don't forget to vote,share and comment
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top