Chapter 3

Da sassafe moha yabi morning flight cike da takaicin abinda akeyi masa akan dole sai yayi aure alhalin shi ba mace ba

"Rahma tamkar tayi hauka don takaici banda zubar da hawaye babu abinda takeyi,kuka takeyi sosai,a hankali aunty marka ta murza key din dakin ta shigo ta zauna gefen gadon rahma,wannan karon aunty marka ta tausayawa rahma matuka don cikin kwana 1 harta rame ta kara haske dama rahma ba mai jiki bace siririyace

"A hankali ta dafa mata kafada tace yanzu rahma akan zakiyi aure shine kike zubar da hawaye haka?karki manta mata dayawa suna zaune suna jiran mazajen aure amma har yanzu sunki zuwa,toh menene abin damuwa tunda Allah ya kawo miki miji sai kiyi aurenki kije inda ake sonki mu dama burinmu kiyi auren da ake sonki bawai inda ke kikesoba

"Haba aunty marka taya anna kawai zata yanke hukunci akan abinda ban shiryawa yinsaba,ko dan tana ganin Alhaji bashi da lafiya kuma bashi da damar yi mata magana rahma ta fada cikin kuka

"Aunty marka ce tai saurin dakatar da ita cikin lallashi tace rahma har yanxu ke yarinyace karama,inda Alhaji yana nan da lafiyarsa da tuntuni ya zaba miki miji yayi miki auren dole kuma kisan da cewa yanzun ma da yake kwance babu lafiya yana tare da bakin cikin rashin yin aurenki kuma ki sani Allah seya kamaki da lefin kuntatawa zuciyar mahaifinki

"Gaba daya jikin rahma ne yai sanyi a hankali ta goge hawayen daya zubo mata daga idonta ta dubi aunty marka cikin ladabi tace to shikenan aunty marka na amince zan aureshi ba don ina sonsaba se don farantawa zuciyar iyayena sedai ina neman wata alfarma a gurinku ku fadawa koma waye zan aura din cewar bana bukatar ganinsa ko jin muryarsa daga nan har ranar da za'ayi auren

"A firgice aunty marka ta dubeta tace meyasa rahma

"Saboda gani ko jin muryar abinda bakaso yana matukar tayar maka da hankali

"Murmushi aunty marka tayi tace zaki soshi ne rahma domin kinyi sa'ar miji ba karamin namiji zaki auraba

"Aunty marka bazan taba sonshiba koma waye don Allah karki sake min zancen shi

"Da sauri ya daga wayar yana karasa tsane jikinsa da towel yace hello mom
"Hey moha ya london
"Lafiya lau mom ya 9ja
"9ja gamu cikinsa moha as usual
"Shirune ya dan ratsa tsakani cikin sanyin jiki moha yace mom akwai magana ko
"Murmushi tayi kamar yana ganinta tace kwarai kuwa don haka ka bude kunnenka da kyau ka saurari maganar da zan fada maka
"A sanyaye yace ina sauraronki
"Moha wannan maganar tawa umarni nake baka ba neman shawara nakeyi dakaiba,moha na zabar maka yarinyar da zaka aura har naje gidansu na nema maka aurenta gobe insha Allah su kawu Adamu da Kawu lawan zasu kai maka kudin aure gidansu
"Wani gajeran tari ne ya sarkeshi shiru yai na seconds 40 sannan yace nasan dai ba april muke ba balle kicemin april fool,mom jokes apart please zancen auren wa kike yimin ne?

"Kaci gidanku moha,ba wasa nakeyi maka ba gaskiyar zance nake sanar dakai cewar gobe za'a kai kudin aurenka kuma za'a tsayar da magana 7th December za'a daura auren naka don haka kai saving date din auren naka inason ganinka 3rd ko 4th

"Hahahahaa yaci gaba da dariya

"Mamakine ya kama mom cikin tsawa tace are you stupid?ko kuma ka fara haukane?

"Da sauri ya gimtse dariyar tashi cike da kulawa yace naji duk abinda kikace mom kuma zanzo kamar yanda kikace sedai kisa a ranki ba moha kika yiwa aureba,gangar jikin moha zaki yiwa aure....bai saurari komaiba ya katse wayar inda ya fada kan gado zuciyarsa na matukar tafarfasa

"Bangaren mom bataji dadiba sedai bata damuba sam domin tunda moha ya amince zai auri rahma toh anyi mai wuyar tasan yana hada ido da ita zai fada tarkon kaunarta

"Both sides shirye-shiryen bikin rahma da moha akeyi se dai cikin amarya da ango babu wanda ya damu da sanin junansu

"Saura 7 days biki amma har yanzu rahma taki yarda ta saki jikinta tayi gyare gyare kamar yanda sauran amare keyi

"Granny ce ta danyi mata nasiha masu shiga zuciya da kyar ta amince tabi su khairat inda aka fara yi mata gyaran jiki da sauransu

"An kawo lefe na gani na fada duk wanda yaga lefen rahma seya yabawa angon yana kara tabbatarwa rahma cewar gaskiya mijinta yana matukar sonta,itama rahma hankalinta ya fara kwanciya ganin ko banza duk wanda yayi maka abu har duniya ta yaba to ba karamin masoyinka bane,ta wani bangaren kuma zuciyarta na matukar tsanar mijin da ya katse mata jindadin rayuwarta

"5th December moha ya dawo nigeria,sam bai damuba domin ya gama sawa zuciyarsa cewar shifa ba aure zeyiba

Bayan ya hutane mom ta dubeshi cikin fara'a tace moha ya zancen events din bikin naku,kana ganin events nawa za'ayi?

"Cikin rashin kulawa da damuwa yace mom gaskiya i'm very tired bani da wannan lokacin zama yin events don haka kawai a daura aure kawai a kawo miki amaryarki

"Jefa mishi pillow tayi cikin wasa tace moha zakaci uwaka fah ka mayar dani kakar kako

"Nop mom ai ke uwace kinsan a mother can answer morethan 100 names,you mean alot to me so i can call you a sister,friend and daughter.....i love you so much ya karasa maganar cikin dariya

"Murmushi tayi tace i love you too mohammad

"Itama rahma ba karamin dadi taji ba jin cewar ba wasu events za'ayiba domin tunaninta bai wuce shin waye zata aura?farine ko baqine?gajere ko dogo?tsoho ko dattijo ko saurayi?a hankali tayi tsaki tare da dafe kanta tace oho masa koma waye nidai bazan taba sonshiba

"An daura auren rahma da moha,inda gaba daya bangare biyun dangi sun cika gidajen anata shan shagali inda amarya ta yi kyau kamar a kasar india

"Karfe 6 ta fito daga wanka cikin ruwan dayasha turare da sauran tsumi na magani (lol)bata yi wani kwalliyaba sosai don tuni motocin daukan amarya sun dade waje sunata jiran amarya,french lace royal blue ta saka dinkin daya zauna jikinta tare da dauri me kyau,lifaya sky blue ta nada tuni rahma ta dauki kyau kowa burinsa ya dauketa picture yayi posting,tuni social media ya gauraye da pictures din rahma inka bude Facebook,what'sapp status,Snapchat da instagram duk posting din pictures dinta ake saboda tsabar kyau

"Apartment guda aka warewa rahma cikin gidansu moha don mom tace anan zata fara zama har sai taga gudun ruwan moha tukunna sai su tare a nasu gidan....

"Ita kanta rahma bin gidan take da kallo ganin irin daular da take cikin gidan duk zuwa gidajenta bata taba zuwa gida mai kyau irin wannan ba,komai da aka zuba mata sunyi matukar kyau da tsaruwa

"Bayan kowa ya watse ya rage saura ita kadai,a hankali ta mike ta lalubi toilet ta dauro alwala ta dinga sallar nafila don jin saukin radadin dake zuciyarta,idonta ne yakai kan katon hoton moha dayayi matukar kyau,a hankali ta mike ta kunna sauran globes din da aka kashe tuni dakin ya dauki haske inda ta tsaya dai-dai kan hoton tanata kallo a zuciyarta tana sake tunanin shi kuma wanene wannan?tsaki tai a zuciyarta tace inajin irin frames dinnan ne na hoton indiyawa da ake sakawa don in kaga moha bazaka taba tunanin a 9ja yakeba

"Tsaye yake ya harde hannu yana kallon yanda ta dage tanata kallon hotonsa har tana taba hoton

"A firgice ta juyo bayanta,jin motsin mutum da tayi,tamkar ta nutse don kunya don sam bataji shigowar moha ba,gabanta ne yai muguwar faduwa inda ta tabbatarwa kanta tabbas na jikin hoton nan shine tsaye gabanta a matsayin mijinta....cikin i'ina tace ina wuni

"Cikin isa da gadara ya nuna mata dining area dun yace ga abincin kinan inji wacce tasani na aureki,bai jira tace komaiba ya fice tare da janyo mata kofar dakin yace good night

"Binshi tayi da kallo inda kalamansa ke faman yi mata yawo a cikin kwakwalwarta "wacce tasani na aureki"shine abinda yake ta yawo a kwakwalwarta....shima kenan auren dolen akayi masa kamar yanda akayi mata?

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top