Chapter 2

"Mom wai yaya moha yana nufin yarinyar batayi masa ba yusrah ta karasa maganar tana zare ido

"Nima dai tun dazu nake tambayar kaina amma amsar taki samuwa

"Toh mom tunda batayu masa ba ni tayimin mahmud ya fadi maganar cikin tsokana

"Mom ce ta kai masa duka tace tashi ka bani guri silly boy

"Mikewa yai har yana cin tuntube yace shikenan tunda an hanani nima zanje na samo kyakkyawa wacce tafi kushi kumari gupta singh raizada kyau,amma ni bazan zama so hard ba kamar arnav singh raizada zan zame mata tamkar sham a ciki film din IPKKND

"Gaba daya suka kwashe da dariya don mahmud yana da abin dariya sosai

Tana shiga daki ta kira anna inda ta sanar mata
yaronta moha yaga hoton rahma ya amince yana sonta 100% zai aureta

"Farin ciki gurin anna kam baya misaltuwa sedai tunaninta daya Allah yasa rahma ta amince da zancen auren,koda kuwa rahma bata amince da zancen auren moha ba tabbas wannan karon anna ta yarda tayiwa rahma auren dole

"Kwance take a daki inda take wasa da wayarta da alama tana cikin nishadi,mom ta shigo jikinta sanyaye ta zauna gefen gadon ta fuskanci rahma,da sauri rahma ta mike tare da fadin anna lafiya naga kin shigo babu kuzari

"Murmushi tayi tace lafiya lau rahma hasalima yau tafiye min kowacce rana farin ciki

"Itama rahma murmushin tayi a hankali tace toh anna ina jinki

"Rahma kinsan dai ko yaushe dake nake tashi kuma dake nake kwana a raina domin rashin aurenki yana matukar damuna

"Cigaba da kallon anna rahma tayi a zuciyarta tace labarin gizo ai baya wuce na koki

"A takaice dai rahma kin samu miji wanda yake sonki kuma zai aureki,wanda ya fito daga gidan mutunci,irin mijin da kowacce mace takeson mallaka a matsayin mijin da zata aura don haka ina fata bazaki bani kunyaba domin mun gama magana da mahaifiyarsa kasancewar shi marayane mahaifinsa ya rasu kuma na amince dari bisa dari

"A firgice rahma ta mike zaune tace anna kamar ya kin amince?taya za'a yanke min hukunci ba tare dana saniba,ni gaskiya anna ba'a kyautamin ba ai sai a zata ma tallana kike kawai daga an fadi magana kice kin amince,don haka ni gaskiya ina kan bakana ban shiryawa yin aure yanzuba kuma koma waye ni beyiminba......saukar marin da taji ne yasata saurin yin shiru da bakinta hannunta na kan kumatunta cike da mamaki don wannan shine karo na farko da anna ta mareta

"Rahma ni kike kallo kice min ban kyauta mikiba?nie uwar taki ko kece uwar tawa?ina tabbatar miki daga yau na gaji da wannan iskancin naki da kikeyi a cikin gidan nan,don iskanci dame kikeso muji da mahaifinki da yake kwance yana paralyse ko kuma da takaicin rashin aurenki shekara 26,keba muniba keba rasa miji kikaiba amma kice ke bazaki aureba,to wallahi na riga na yanke hukunci na amince na basu aurenki sedai ki mutu,kuma wlhy indai kika musamin akan cewar bazaki aureshiba sedai ki tattara kayanki kibar gidan nan don bazan iya zama dakeba,tana karasa fadar haka tai ficewarta zuciyarta na matukar tafarfasa

"Granny da aunty marka ne sukai saurin tambayar anna meyake faruwa inda tai musu bayanin komai suma suka nuna amincewarsu 100%

"Murda kofar dakin moha tayi ta shiga ta sameshi zaune yana shan fruits hannunsa daya yana danna wayarsa,a hankali ta zauna gefensa tace yanzu moha akan na nuna maka hoton wacce nakeso ka aura shine har zaka kwana ka tashi kana fushi dani ko gaisheni baka fito kayiba

"Kallonta yayi ya juyar da kansa gefe cikin fushi yace mom get out please ko kuma nina fita daga dakin

"Bazan fitaba moha kaima kuma baka isa ka fitaba saika fadamin dalilinka nayin fushi dani

"Mom nifa ba mace bane taya za'a takuramin akan cewar senayi aure,haba mom it's annoying ace har kin kawo ni level din da za'a dinga nuna min pictures din wasu mata wai in zaba in aura,ni mom ban shirya yin wani aureba yanzu don haka kar a sake nunamin cewar anaso nai aure don ni har yanzu i'm so young kawai inyi aure nan da next year sai kaji an fara kirana da daddy daga nan na zama condemned fah kenan impossible mom karki sake min haka please i don't like it at all

"Sakin baki mom tayi tana kallonsa tace i'm sorry moha bazan sake ba stay blessed my son ta mike ta nufi hanyar fita waje idonta na zubar da hawaye

"Mom ya kira sunanta a sanyaye
"Da sauri ta juyo ta zuba masa jajayen idanunta
"Gobe zan koma london
"Allah ya kaimu ta fada a sanyaye

"Tana shiga daki ta janyo waya inda ta sanarwa anna cewar ya sukai da rahma,itama anna cewa tai babu matsala ta amince

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top