Chapter 16



"A fusace mom ta mike ta nufi dakin moha tuni itama yusrah tabi bayanta jikinta a matukar sanyaye

"Da karfi ta tura kofar dakin nashi,da sauri ya dago ya kalleta zuciyarsa na dukan uku-uku ganin yanayin da mom ta shigo masa daki bai saba ganiba hasalima mom bata shigar masa daki

"Takardar ta cilla mishi a jikinsa tace nagode moha bansan haka ka rainaniba balle maganata

"Am sorry mom ba.......saurin daga mishi hannu tayi ta dakatar dashi tace you have nothing to tell me,bansan haka ka daukeniba har da zan baka auren yarinya cikin 2 months ka saketa,da wanne idon zan bude in kalli iyayen yarinyar nan

"Mom i don't mean to hurt you kawai nayi hakane don samar mata sauki Actually ni banason yarinyar sam she's not my type akan me zan zauna da abinda banaso

"Who told you ita sonka takeyi,kamar yanda baka sonta itama bata taba sonkaba biyayyar iyaye ce tasata zama tare dakai bawai don tana sonkaba,kaman yanda nai maka auren dole itama haka iyayenta sukai mata aure badon tana sonkaba shine zaka wulakantani a idon jama'a hakan ya nuna tun bayan rasuwar mahaifinka ni baka daukeni komaiba,ta karasa maganar cikin kuka

"Jikinsa ne yai sanyi inda ya dago ya dubi yusrah da jajayen idonsa yace get out,harararshi tai tare da turo baki ta fita daga dakin ta buga kofar da karfi cikin bacin rai tace wlh kai dai yaya moha shame on you

"A fusace ya bita sedai kafin yaje bakin kofar tuni ta zura da gudu cikin zafin nama yace wlh yusrah am gonna kill you badly sekin fadamin ubanwa kike cewa shame on you idiot kawai

"Mom ce ta kalleshi tace you have to kill me first moha

"Sunkuyar da kansa yai kasa yace am sorry mom

"Sorry for yourself ta fada a zafafe

"Cikin bacin rai yace haba mom wai akan waccan shashashar yarinyar har kike fushi dani,what did i do bad da har zakiyi fushi dani mom,banasonta bana kaunarta and finally i divorced her then what else it's by force?

"Marin data kai masane ya sashi saurin rike kumatu yace mom kika mareni?akan waccan bitch she goat din kika mareni

"Koma me zaka kirata dashi na mareka akanta kayi duk abinda zakayi

"Hawaye ne suka gangaro daga kumatunsa a fusace ya fice daga dakin ya bar mom tsaye tana binsa da kallo ita kanta tasan zafin rai irinna moha,tausayinsa ne ya kamata itama ta karasa goge hawayen dake kokarin zubo mata

"Da kafarsa ya tura dakin a mugun fusace,cike da tsoro ta juyo tana kallonsa wuyanta ya shaqo da kyar take iya fitar da numfashi cikin muryarsa mai bata tsoro yace what the hell do you think you are,shashasha idan baki fita a hanyataba sai nayi maganinki

"Murmushi tayi mai hade da takaici tace point of correction don't you dare try to pass your limits,kaine babban shashasha baniba da kake taba matar da ba muharramarka ba mr arrogant

"Wani irin takaici yake ji a zuciyarsa a fusace ya shaqi wuyanta sannan ya hada kanta da dressing mirror tuni mudubin ya tawarwatse inda jini ya fara fita daga goshin rahma tare da kwalla kara

"Da gudu mom da yusrah suka shigo dakin,gefensu ya ratsa ya fice daga dakin ba tare da wani tsoro ko nadama a zuciyarsaba

"Subhanallahi na shiga 3 na lalace moha ka kashe musu yarinya,innalillahi wa'ina..........

"Mahmud ne ya dauketa cak cikin rudewa yasata a mota,su mom da yusrah suka karasa shiga motar da gudu ya figesu suka wuce asibiti

"Dakinsa ya shiga ya kulle zuciyarsa na matukar tafarfasa,wayanshine ya fara ringing ganin number deedee ya sashi murmushi saurin goge gumin fuskarsa yai ganin video call ne ta kirashi

"A hankali yai connecting tare da sakar mata murmushi yace hi deedee

"Itama murmushin tayi har dimple dinta na lomawa tace i missed you badly super hero meyasa baka kiraniba ta karasa maganar cikin shagwaba

"Sorry baby am about to call you kika kirani amma ki kalli idona kinsan definitely komai nawa yayi missing dinki

"Bata rai tayi tace super hero you are so bored,meyake damunka ne?

"Murmushi ya kakalo yace deedee babu abinda yake damuna indai kina tare dani but I guess missing dinki da nakeyi shi ya mayar dani boredom

"Really ta fada cikin shagwaba

"Yes baby trust me ya karasa maganar yana miqa

"Murmushi tayi tace super hero are you pregnant?

"Kwashewa yayi da dariya har yana dafe ciki yace deedee you are my trouble darling,bazaki taba girmaba,yaushe kika taba ganin chocolate yai melting ai sedai ice-cream right?

"Saurin kallon wayanshi yai yace sorry deedee mom na kirana,we will talk later i love you and take care

"Ok baby daga nan ta kashe waya

"Da sauri ya daga wayar yace mom

"Cikin tashin hankali tace moha shikenan ka cuceni ka cuceta kuma ka cuci iyayenta

"A firgice yace mom what's wrong?

*I don't know😁

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top