Chapter 12
"Sai data dauki tsawon 30 minutes tana kuka tukunna ta mike ta nufi gurin da sink yake ta wanke fuskarta sannan ta daura alwala ta gabatar da sallar magriba,ji tayi sam bazata iya zama cikin gidan ba ba tare data nemi shawarar kowaba ta dauki mayafinta ta nufi gidan zahra
"Cike da mamaki zahra ta saki baki tana kallon rahma cikin tsoro tace rahma kece da daddare haka meya faru?
"Murmushi tayi tace haba zahra meye don kin ganni da daddare a gidanki,tunda kinsan banida nisa tsakanina dake kuma rayuwata kasance cike da matsala
"Ajiyar zuciya zahra tayi tace rahma tunda na ganki yanzu nasan akwai matsala fadamin ko meye ina sauraronki
"Wata kyakkyawar yarinyace ta fito sanye da abaya da sallaya a hannunta tamkar balarabiya ta mikawa zahra tace gashi nagode sis idan ya dawo ki fada masa dukanin papers din ya daure yayi signing a daren nan don gobe zanyi amfani dasu,daga nai ta fice fuskarta cike da murmushi
"Tunda ta fara magana rahma tai suman zaune kallonta takeyi idonta ko kiftawa bayayi zuciyarta na dukan uku-uku,zahra ce ta taba ta tace haba rahma karki bayar da mata mana irin wannan sakin baki haka kema fa kyakkyawace wannan yarinyar kudi kawai zata nuna miki don kema da kina da kudin mahaifinta da tuni kin zama kamar ita ta karasa maganar tana yiwa rahma dariya
"Zahra wannan itace matsalata,zahra wannan itace ta kawoni gurinki,zahra wannan itace a jikin hoton da nake fada miki ita da moha wacce yake kira da deedee....ta karasa maganar cikin kuka
"A firgice zahra ta kalli rahma tace yanzu kina nufin maryam itace zabin moha
"Saurin daga mata kai tayi tace tabbas itace a jikin hoton wacce jiya ya mareni akanta tare da fadamin maganganun da hankalina bazai iya daukaba zahra wacece ita ne?kuma menene tsakaninki da ita da har nazo na ganta a gidanki yanzu
"Babu wani abu tsakanina da ita rahma kawai dai itace manager din M&M clothes and jewellery company kuma a wannan company din mijina yake aiki,kinsan company din babantane dake nan London shine yanzu tazo ta kawo mishi papers yayi signing don zata turawa dad dinta gobe wannan shine tsakanina da ita rahma trust me bansan komaiba wlh
"Doguwar ajiyar zuciya tai tace zahra inason shi,inason soyayyar shi meyasa baya sona yakeson wata daban kodan ban cancanci asoni bane zahra domin idan har ni namijice matukar ina tare da wannan yarinyar babu abinda zaisa in karbi tayin wata soyayyar,saurin rufe mata baki tai tace rahma so ba hauka bane,kada ki sake cewa ta fiki ke kyakkyawace,kina da addini kuma kinada tarbiya sannan kina da tsafta rahma sam baki da makusa matukar kin kwantar da hankalinki kuma kinyi amfani da shawarwarin da zan baki toh zaki zamo daya tamkar da dubu a zuciyar mijinki,karki manta karshen soyayya shine aure toh kisa aranki moha ya kai karshen soyayyar sa gareki tunda har ya aureki,meyasa dukkanin son da yake yiwa waccan yarinyar bai aureta?
"Amma ai takura mishi akai ya aureni zahra
"Murmushi zahra tayi tace rahma koma meye moha yana sonki don inda baya sonki meyasa yake zaune dake?aida sai ya sakeki ko to soyayyar da yake miki ce yasa yake zaune tare dake don yana son kasancewa tare dake,dukanin wasu nasiha da zahra tayiwa rahma ta dauka sai dai sam ta kasa gasgata moha yana sonta
"A bakin gate din gidan taxi ya sauketa,ta karasa shiga gidan cikin sanyin jiki ta tura kofar palour din sedai ganin moha tsaye yana kai kawo yasa gabanta saurin faduwa har tana fitar da kalmar "subhanallah" ba tare da tasan da karfi ta fada ba
"A wulakance ya kalleta yace daga ina kike?
"Cikin rawar murya tace gidan......
"Shhhh!!ya katseta da karfin gaske yace i don't care koma daga ina kike sedai inason ki san cewar this is my house not yours...you most follow all my rules ko karen gidan nan seya sanar dani kafin ya fita take note,yana gama fadar haka ya juya yayi hanyar fita waje,murmushi tayi don ita yanzu komai yayi birgeta yakeyi
"A cikin mota yake zaune don ya kasa shiga cikin gidan ma don deedee tayi mishi warning cewar kada ya sake shiga gidan idan har yanason farin cikinta,sedai shi kuma ganinta shine cikar farin cikinsa a dole ya kutsa kan motar cikin gidan jikinsa a sanyaye
"Parking yai ya fito daga mota sanye cikin shirt baqa da wando baqi sunyi matukar amsar jikinsa,knocking kofar yayi
"Who is that? Ta fada
"Ganin tana neman bata mishi lokaci yasa shi tura kofar ya shiga palour din,a fusace ta mike tace get out
"Qarasa tura kofar yayi ba tare daya saurari me take fada ba ya samu guri ya zauna yana fuskantarta
"I said get out,sau nawa zan fada maka bana bukatar ganinka,bana sonka I hate you....saukar mari taji a kumatunta cike da tsoro ta dafe kumatun nata taci gaba da kallon moha ganin yanda idonsa ya kada yayi jaa jijiyoyin jikinsa sun firfito sosai,turata yai ta fada kan kujerar cike da bacin rai yace na marekine don ki gane waye yake tsaye a gabanki ku sani moha ne mutumin da baya jure kowanne raini sai naki,meyasa bazaki yimin uzuriba deedee,meyasa bazaki dena fadan kalmar tsana a tsakanina dakeba duk sanda kikace kin tsaneni sai zuciyata ta buga bugun da bata tabayin irinsaba,deedee meyasa kika kasa yiwa super hero dinki uzuri?meyasa kika manta da duk wani memories namu kike fadan kalamai marasa kyau a kaina,Deedee i didn't betrayed you and i will never try to understand me please ya karasa maganar yana rike hannunta,fisge hannunta tai ta shiga kitchen ta dauko wuqa tace ka fita wlh idan baka fitaba sai na caka maka wukar nan nima kuma zan kashe kaina kowa ya huta
"Murmushi yayi sannan ya kara matsowa daf da wukar yace bismillah i'm always ready idan har wannan ne hukuncin da kika yanke akaina idan har hakan zaisa ki dena fushi da super hero
"Fashewa tai da kuka da sauri ya tallafota yace c'mon baby i know you missed me sannan ya janyota jikinsa sosai har suna iya jiyo bugun zuciyoyinsu
*Mrs Abideen*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top