Chapter 1
"A hankali ta bude kofar palour din ta shiga,sanye take cikin black suits riga da skirt din daya karbi jikinta sosai,gaba daya kowa zaune ta tarar dashi da alama shirye-shiryen cin abinci sukeyi,cike da fara'a ta zauna gefen anna wato mahaifiyarta tace wash anna wlhy na gaji,khairat ce ta kalleta tace aunty rahma ya naga sai dariya kikeyi yau kodai kin samo mana saurayine?
"Ah wlhy zamusha biki ashe maryam ta karasa maganar cikin tsokana
"Kai dalla malamai ku sauraramin haka,babu dama mutum ya dawo sai an bata mishi rai
"Da sauri anna ta dubeta tace rahma yanzu don an miki zancen aure shine zai zama abin bacin rai?
"Toh ni anna gaskiya ban shiryawa yin aureba taya za'a sani a gaba ada mu mutun da zancen aure anna baki ganin duka duka banfi 7 months fa da samun upper ba har yanshe na tsayar da hankalina gurin aikina?
"Aunty marka kanwar mahaifinta ce ta dubeta baki bude tace au sannu alhudahuda sarkin karatu da aiki,kinqi kiyi aure sai aiki karfa ki manta yanzu shekararki ashirin da shida har yanzu kinqi ki tsayar da miji kin tsaya shegen ruwan ido kinaso ki tsufa a gida
"Fada mata dai shegen ruwan ido da tsatsauran ra'ayi na rasa inda ta samosu rahma kinason ganin farin cikinmu kuwa,karki manta burin kowacce mace taga diyarta ta samu miji tayi aure tun da ranta kafin ta mutu,sannan karki manta qannenki 4 kowacce ta samu miji ke kawai ake jira ki fara yin aure sai ayi musu
"Ajiyar zuciya rahma tayi a hankali ta cije lebenta na kasa tace anna taya za'ace dole sai an jira nayi aure sannan su khairat zasuyi,aishi aure lokacine kuma ina ganin tunda sun samu miji kawai suyi aurensu aishi aure ba'a jiran wani don ni gaskiya ban shiryawa yin wani aure ba yanzu
"Baza ai musu dinba,tunda ke bakya gudun a zagemu muna zaune da zabgegiyar budurwa sedai ki tashi ki fice aiki ki dawo ki zauna gososo dake cikinmu to wlh dole ki fito da mijin aure inji aunty marka
"Ji tayi abin ya fara isarta da sauri ta mike tace ni gaskiya i am not ready for marriage kuma babu wanda ya isa yamin auren dole tai shigewarta daki ta kulle
Seda tayi wanka ta huta tukunna ta fito sanye cikin doguwar riga abaya ba wata kwalliyace a fuskarta ba,anna da granny ta tarar zaune suna kallo,murmushi tayi tace tsohuwa mai ran karfe sannu da hutawa irin wannan daurin fah granny
"Ai wannan daurin shi ake kira full over granny ta fada
"Gaba daya suka kwashe da dariya rahma tace haba granny bafa full over ake cewaba,fly over ake cewa
"Ohh ni ina na sani to ai ban saniba granny ta fada tana sake kallon mudubi tana gyara daurin
"Anna ina yaran nan suka tafi banji suba
"Suna chan sama kowacce tana sana'ar tata
"Wacce sana'a kuma anna?
"Waya da samarinsu mana
"Tsaki rahma tayi tace shashashu marasa aikin yi,ni su taso muje mu karbo dinkunan mu sunsan sarai gobe za'a fara event din bikin yaya kamal kuma sunsan dai dinkinmu bai zama ready ba
"To sai kije ki tasasu ai ku tafi
"Cikin bacin rai ta bude dakin kamar yanda tai tunani dukaninsu waya sukeyi khairat ce ma take video call
"Rike kugu tai ta fisge wayar hannun zainab tace love birds dalla ku tashi mu tafi shagon tela don wallahi idan na fita babu yarinyar da zan karbowa dinki
"Haba aunty rahma ke bakiyiba mu sai ki hanamu soyewa da samarinmu
"Ke banason rashin kunya dalla ku taso 2 minutes kawai na baku ku shirya
"Da sauri suka shirya don sunsan halin rahma da zafin kai
"A hankali ya tsaya bakin door din ya danna bell din da gudu yusrah ta bude inda tai hugging dinsa tana oyoyo yaya moha you are welcome
"Thank you sis ya karasa maganar yana murmushi
"Mom ce ta fito fuskarta cike da fara'a tai hugging din yaron nata duk daya fita tsawo don moha dogone sosai
Mutanen london ai tun jiya nake sauraron ganinka amma shiru
Wlh mom naso tahowa tun jiya amma office basu sake niba sai 8pm shiyasa kawai na hakura nayo sammako yau
Aina zata ma bazakazo bikin fatima din ba
mom aiya zama dole inzo don idan banzoba inaga fatima seta bini har london ta cimun mutunci ya karasa maganar yana dariya
"Iyye kaga mutanen london babban gwauron family,mahmud ne yake maganar yana saukowa daga upstairs cike da tsokana
Pillow ya dauka ya cilla masa yace ka fara ko wlh zanyi maganinka mahmud
"Ah ah karka sake dokar min yaro toh karya yayi maka ne?ba gwauron bane 29 years amma ba aure sai shegen ruwan ido dason zuwa bikin wasu amma kai kaki ka fitar da mata mom ta karasa maganar tana kallonsa
"You don start ba mom kefa baki da aikin yi sai takurawa mutum yayi aure,ko ruwa ba'a baniba daga zuwana an fara min maganar aure
"Murmushi mom tai tace okay to an barka yanzu kaje kai refreshing ka dawo ga abinci nan yusrah ta dafa maka
"Tab mom ai bazan iya yin komaiba ba tare da naci abinciba,nifa saboda son ganinku ko a jirgi banci komaiba
Ok lets go ai komai ya zama ready mom ta fada tana murmushi
What? Mom waye ya dafa abincin nan duk ya dame haka
"Yusrah ce mana
"Wai meyasa ake min haka mom kinsan yusrah ba wani iya girki tayiba amma sai a bata ta dafa min kuma kinsan ma ni noodles be dameniba
"Yaya moha nice ban iya girkinba in daddage tun safe in dafa maka abinci amma kace babu dadi,meya hanaka yin aure kaga da tuni inlaw dinmuce zata dafa muci yusra ta karasa maganar tana harararsa
"Ai ki dena damuwa da auren yaya moha don inajin bazeyi aureba sai yakai 50 years mahmud ya fada yana satar kallon moha
"Kut fif....what kai ku tashi ku bani guri in baso kuke inyi ball dakuba
"A'a karka korar mun yara ai lefin kane tunda kaki kayi aure tun inada rai so kake saina mutu tukunna kayi aure ko kamar yanda mahaifinka ya mutu ba tare da yaga jikokin saba
"Mom shifa yaya moha ko so yake yaga mace fara tamkar hasken gwal,mai gashi har gadon baya idan ta tsaya kusada fanka gashinta zai taya fankar kadawa yana bawa gurin iska,kyakkyawa kuma tamkar madhubala ko sarauniya padmavati ta kasar india sannan ya samu mai dadin murya kamar ta shreya goshal,daga nan sai tazo gabansa ta tsuguna tace hey handsome will you marry me?daga nan sai ya kalleta sama da kasa yace ta bashi lokaci zai yi tunani.....toh mom kinji fa irin matar da yaya moha yake jira tazo ta sameshi
"Gaba daya suka kwashe da dariya banda moha daya hade rai yace shut up!!!am i your mate?idan baki ja bakinki kinyi shiru ba sena cire miki haukan da yake kanki idiot kawai
"Saurin rufe baki tai ta sauke kanta kasa tana dariya ciki ciki
"Toh karya tayine ba irin matar da kake nema dinba,kai fa don tsabar gudun aure da kakeyi bacin ka gama karatu maimakon ka dawo nigeria ka samu aiki sai ka gudu london kakeyin aiki kaga babu niyar yin aure a tare dakai don nasan matan london ba kyau ne dasuba balle har kace zaka zaba anan mom ta karasa maganar tana shan ruwa
"Nifa mom wai wayace muku kyakkyawar mace nake nema?mom nifa ba mace bane da zaa takura min se nayi aure i'm just 29 years old
"29 years going to 30,from 30 to 40,from 40 to 50,50 to 60 thats how life is running mom ta karasa maganar tana kallonsa
"Kai mom lokaci yana kurewa abar zancen nan kawai kowa ya tashi muyi sallah kowa ya shirya mu tafi gurin dinner dinnan kinga 7 yayi
"Tashi kowa yayi ya nufi bangarensa don shiryawa
"Basu dade da zuwaba amarya fatima da ango kamal suka karaso cikin shigarsu mai kyau da birgewa
"Cike da mamaki anna taga hajiya binta tace rai kanga rai anna tun secondary rabon da a sake haduwa,wlh kuwa to ya bayan saduwa?sai alkhairi
"Yusra dake gefen hajiya binta ta tsuguna ta gaida anna
"Wannan wacece inji anna
"Murmushi hajiya binta tayi tace yar auta tace sunanta yusrah,akwai moha babban su yanzu ya fita sai mahmud kuma dagashi sai yusra
"Allah ya raya inji anna inda ta tabo rahma data juya tana daukar amarya da ango hoto
"Rahma ga hajiya binta kawata ta kuruciya tun muna secondary
"Da sauri rahma ta tsuguna tace ina wuni
"Lafiya lau yarinya,ina gajiya
"Saurin matsawa tai daga kusa dasu ta basu guri
"Hajiya binta ce ta dubi anna tace wannan itace wa kenan
"Cike da murmushi tace rahma ce first born dina shekararta 26
"Allah sarki kyakyawa da ita,a ina take aure?hajiya binta ta tambaya cike da fara'a
"Bata da aure ai,wlh ta ki fitar da miji kowa ita beyi mataba ko saurayi ma bata dashi
"Da sauri hajiya binta ta sake kallon rahma data zauna gefe ita kadai tana wasa da wayarta,sannan ta dubi anna tace yanzu kina nufin bata da aure?duk kyan nan nata kice min bata da saurayi
"Murmushi anna tai tace wlh kuwa kinga dai aiki takeyi a bank,daga gurin aiki sai gida ko yawo ma bai dametaba,kinsan yaran zamani abinda kake hango musu daban kuma abinda sukeso daban,aure dai shine mutuncin ya mace
"Hakane wlh nima ina nan moha shekararsa 29 amma yaqi yayi aure aiki yakeyi a london babu abinda yake jira amma yaro sai ruwan ido,Allah dai ya shige mana gaba amin
"Sun dade suna hira har sukayi sallama kowa ya watse bacin sunyi exchange number
"11am yusrah ta fito ta tarar da mom zaune tana kallo,murmushi yusrah tai inda ta mikawa mom waya tace mom kalli nan
"Saurin karbar wayar tai inda taci gaba da kallon hoton rahma tace yusrah ina kika samu hoton yarinyar nan nan?
"Jiya na dauki hotonta gurin bikin nan ai naji hirar da kukeyi ashema bata da saurayi,kinga mom kawai a nunawa yaya moha hotonta tunda kinga mom she's very beautiful intayi masa shikenan
"Saurin mikewa zaune mom tayi tace perfect idea yusrah,mahmud ne ya karbi wayar yace kuma fa hakane wannan dai duk jarabar yaya moha nasan dole ta tafi da tunaninsa don wlh ko balarabe idan ya ga wannan yarinyar dole ya rikice
"Kamar an jefoshi ya shigo palour din hannunsa dauke da coffee yace mom sannu da hutawa
"Yawwa sannu moha,kamar kasan zancenka muke dan halak sannan ta mika masa wayar tace kalli nan
"A hankali ya karbi wayar inda yake tabin hoton da kallo,sai daya dauki kusan minti 3 tukunna ya dago yace mom wacece wannan?
"Murmushi tayi tace yarinyace ce kyakkyawa gata nan dai kana ganinta idan tayi maka sai na nema maka aurenta
"Wurgar da wayar yayi cike da bacin rai yace akai kasuwa,Allah dai yasa kamar yadda ake tallanta nima baki fara tallan nawa hotonba,bai jira tace komaiba yai ficewarsa daga dakin ransa a matukar bace
Can i continue or not?
Dont forget to vote,share and comment...
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top