chapter 48

Halal veer

Bayan yafita sallar ishaii ne ya ci karo da abidin ,lokaci daya sai maganar gwaggo amarya ta dawo masa ,
A take ya Kori shaidanin da yake neman hasala fitina tsakaninsa da dan uwansa ,amma surely they need to talk,
Alamu yamasa da hannu a kan yazo bayan an watse a cikin masallacin ,
Cike da farar sa ya karaso gareshi tareda mika masa hannu kana ya zauna yana fadin"bro yajikin in law kuwa ?inason shiga amma nace bari na hakura saida safe ,

Jiki alhamdulilah abid ta warware kawai traumatic amnesia dinan ya rage and temporary ne insha Allah ,
Yabasa amsa "

Cikeda faraa wadda yariga yasaba yace to Ai haka akeso ,amma kar fa naje tace wanene ni"
Naushin wasa adeel ya kaimasa tareda fadin ai ba dawanau ce a kantaba ,yauwa inason zamuyi magana "kasan kuwa motan da ka bama nuayma wanda tayi accident dashi babu birki?

wani dum abid yaji inda lokaci daya fara'ar  dake fuskansa ya dauke kana yace babu birki kuma?
No
No
Brother badai babu birki ba sabida i tested the car kafun nasiyeta  and for sure akwai birki a jiki.

Shiru adeel yayi inda abid ya dan kallesa a hankali yace "man don't tell me kana zargin inada hannu a hatsarin in law"

DA sauri adeel ya dago kai tareda fadin"haba dai ,kajika da wata maganan banza kawai dai ina nazarin wanene kesan yaga matana ta mutu da har zai cire mata birki and wait koda wasa bakaji labarin rashin birkin mota yasa hatsarinba "

Kada kai abid yayi yace "nope yanzu nakeji a abakinka and i don't think akwai wanda yasan hakan a masarautar nan dan ina yawan zama da dad kwana biu koda wasa kuma bai taba fada mun haka ba why do you ask?

Gwaggo amarya tazo gurin mu dazun and tayi maganan cire birkin wanda yaban mamaki domin ni kadai akai reporting ma sai abban nuayma da na fada ma so Data fadi hakan nayi tunanin kowa yasani ,tunda babu mamaki abban nuayma zai iya ma dad maganan.

Ahaf abid ya kama"dama wannan shegiyar matar  shedaniyace since from day one ,babu mamaki she knew something about this ,da hanzari yamike
"Aikuwa yau ta tabo ma kanta balai"

DA sauri adeel ya rikesa tareda fadin "kai sarkin fushi komai da taku ake yinsa ,inbaka iya kama barawo ba ai shi sai yakama,
Yanzu dai inma har da sa hannunta zamu gano a hankali sabida babban fucked up din datayi shine nazuwa gidana akan wannan maganan sabida kowa yasan cikin masarautar nan bani shiri da ita sannan ban shiga shirginta ,so hakan ya jefata cikin suspects"
Yanzu dai inaso ka saka ayi bincike cikin amintatun mutanenmu ,ayi bincike sosai akan shige da fice da ya wakana a gidana a ranar da aka kawo wannan motar zuwa washegari da nuayma ta hau ,im very sure zamu sami wani clue komai kankanta .

Kada kai abid yayi tareda dafa kafadar adeel "
Just leave Komai a hannuna insha Allahu koma wanene he /she will be down to justice"_

Lumshe idanu adeel yayi kafun ya mikewa yace "i trust you "

Hayaniya sukaji lokacinda suka fito a masallacin daga baya,kasancewar dole sai sunbi hanyar yasaka suka nufa gurin domin ganin maikee faruwa "

Sarkin yaki suka gani da wani barden bafade,inda bafaden ke ikirarin shifa bazai yardaba ,
Koda suka karasa gurin ai kaman anyi ruwa an dauke haka sarkin yaki da bafaden sukai shiru kafin kuma suka hada baki wajen fadin "
Ran yarima adeel da yarima abidin ya dade"

Kallonsu abid yayi cikeda rashin yarda yace lapia dai ko?

Da sauri sarkin yaki yabada amsa da lapia yarima babu abunda ya faru kawai dai muna dan musu ne namu na fadawa,.
Abid na kokarin kara magana adeel yakalla agogonsa yace  ,"mutafi dan Allah abid dare nayi and nabar nuayma ita kadai a gida ,
Gaba yayi inda abid baida option face ya bishi"

Wani mugun kallon sarkin yaki yabi zaki dashi lokacin da suka bar gurin kafun yace "kai kanka yagaji da zama a bisa gangar jikinka ko?
Hala kai mahaukacin inane?
Nasan dai kana da masaniyar wadannan dun suwanene so wane haukan ne zai sa ka daga min murya"

Cikeda murya irinta yan iskan yandaban nan zaki yace ,oga bafa haka mukai da kaiba ,yauwa ,
Cikon kudina nake bukata wanda yazama dole a bani domin aikin danayi ai kasan hadarin sa "

Dafa sa sarkin yaki yayi yace to naji"
Amma ai kasan nace maka gimbiya tace zata biya kudinan ko?

Eh nasani mana ,mace mai baki biyu ba "
Ina jin cewa tayi a ranar zata tura amma dayake bata da gaskiya ai kaji shiru kaman malam yaci shirwa,
To kaga bawani kure mure kawai abani eh"
KO wallahi na buga eh"
Kadai gane ,
Billahilazi kar killo taja bau "
Yauwa inji dilin kawai alaji"
Yana kai aya a maganarshi yayi gaba tareda barin sarkin yaki da share zufa "

Zaki na gaba sarkin yaki ma ya dauki hanyar  bangaren gwaggo amarya dan yasan tabbas kilo kan iya ja bau domin zaki bakaramin dan iska bane wanda yayi wuya ,dan ba domin kaurin wuyansa ba ai datuni ya kawar dashi amma ina kar zaki yake kallonsa"

Koda ya isa ya nema jakadiya tamasa iso nan suka fara ja ,Tace koma menene uzirinsa yabari sai da safe domin uwar dakinta bata jin dadi"_

Kaman daga sama tajiyo hayaniyarsu "
Tana lekawa taga wanda take fatan gani dama domin tunda ta baro gidansu adeel taji wani makirin zazzabi ya rufeta "

Barshi ya shigo jakadiya ,tabada umarni a takaice"

Tun kafun tayi magana ya rigata tareda fadin ranki shi dade anfa yanka ta tashi "

Kamar yafa "?

Kamar yadda nace dai "ran gimbiya ya dade cikon kudinan dai ,wallahi bakiga cin mutunci da zaki yamun ba ,shifa wannan akan kudi uwarsama zai iya sakata a balai,dan Allah ranki shi dade kibada cikon kudinnan kafun mudawo daga goma zuwa sifili"

Bazan bayarba "
Tadaka masa wata tsawa ,nace bazan bayarba sarkin yaki,
Dan kan babanshi aikin dayayi yayi kyau ne?
Mai na Karu Dashi inbanda bakin ciki ,hatta shegen dan dake ciki bai mutuba bare uwarsa sannan zaakawon maganar banza "
To dan Allah idan har bazaka iya kawar da wannan karamin alhakin ba kabarshi yasakaka a matsala domin kai zai saka bani ba danni da kaganni wallahi sai Allah"
Tashi kabar mun gida"

Yana kokarin kara wata maganar ta daka masa tsawa wanda babu yarda ya iya dole ya fita a dakin yana cizan lebe dan ya tabbata batasan hatsarin zaki bane,dan haka shi kam ya yanke shawarar guduwa yabar garin ma baki daya"

*********
Bayan kwana hudu"

Zaune adeel yake tareda abidin suna cin abinci a bangaren fulani wadda ta musu abincin da sukafi kauna da kanta wato tuwan alkama miyan kuka wadda taci albarkatun miya ,gawani kamshin manshanu na daban dayake tashi,

Kallonsu fasiya tayi wadda fitowanta falon kenan tace wai dan Allah bro adeel ba da matanka ba amma kasa yau ammi ta mana wannan abincin da babu kyau a ido bare a baki "

Rike baki abid yayi yace aa "yarinya tayi baki to ai shikenan karki fito da mijin aure ki zauna sai ammi ta dafa kici tunda a nan zaki dawwama ,mukuma musa ayi ta mana abincin yan aljanna"

Kai katsaya bata amsa ma abid taje chan gun auntynta taci abincin yan gayu dama ai sun saba "
Sallaman fulanine ya katse fasiya daga abunda tayi niyan fada"
Zama mahaifiyar tasu tayi kan cushion tace ana samin autan kuka ne manyan kawai?

A tare suka saka dariya lokacin da fasiya tawani zumburo baki wai ita dole auta ,
Karasawa tayi tareda fadawa jikin fulani tace ammi dan Allah kidaina mana tuwannan bro adeel yaje matansa ta masa shikuma bro abid yafito da mata dan Allah muyi masa aure "

Jan kumatunta Fulani tayi tace "shikenan auta your wish is my command dear princess siya"
.wani far tayi da ido kafun ta mike tareda fadin i love you mother Queen ,yanzu dai bari naje gurin aunty ayma naci better,
DA haka ta fita tana dan wakenta a hankali"

Kada kai fulani tayi tare da murmushi ,kwata kwata tarasa ranar da fasiya zata san ta girma ,
Maida hankalin ta tayi kan yayan nata tace kunji dai mai kanwarku tace .

A tare suka hada baki waje fadin "Ammii"

Bayan fitan fulani a dakinne abid ya maida kallonsa kan adeel yace yauwa bro ,ranar da nuayma ta hau motar nan mai baban daki taje gidanka sannan taje da bayi da dama wanda a yanzu haka duk nagana dasu mutum dayane babu wanda daya daga cikin bayi mazan dasukaje ya tabbatar mun dacewa ba bawan mai babban daki bane ,

Aje cup din da yake shan kunun gyadan dayake da karfi a kan table wanda sai da abid ya tsorata.

*****

Chu chu.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top