chapter 45
Halal veer❤
Cikeda rudani ya kalleta yana kada kai yace "nuayma no"
Please no"_
Kar ki min haka,nasani i did you bad amma babu ruwan abunda ke cikinki dan Allah kar laipina ya shafi babyn mu"
Wani side smirk tayi tace aw yau kuma sabida abunda kakeso for a long time a jikina ya bayyana shine zaka na wani nuna farin cikinka desperately?
Tsk tsk little prince kayi murna da farin ciki a banza dan haka shawara daya zan baka ba biyu ba shine ka ma yi kamar bakaji cewa inada cikiba ,
Kai ba kai kadai ba har wadanda suka mun katsalandan a rayuwa yakamata su sa a ransu cewa nuayma batazo da ciki gidannan ba domin wannan ciki da kake gani sunansa zubabbe "
Wani zaro idanu yayi lokacin da tafadi hakan inda itakuma ta daga masa gira daya tareda sake fadin "yes zubabbe domin am aborting this child,
Idan na haifa jininkama sunana yar iska kenan"
Kai dan Allah a tunaninka farin ciki zanyi sabida ina dauke da cikinka?
Gangan ma kenan"
Hannunta tasaka guda daya tana tapping kirjinsa tace "keep on dreaming spark "
Keep on dreaming "
Jakanta ta dauka har ta kai bakin kofa ta juyo tace oopz na manta zanje gida duk da i told you amma wai kasake sani kar na fita malaiku suyita tsine mun "
Da haka ta sakai tafita tareda barinshi kaman dolo a gurin
Lokaci daya kuma abunda ta fada suka fara dawo masa ,kada kansa yayi cikeda rudewa yace no she can't do this to me , bai masan unknown hawaye sun fara fitar masaba ,
Bai kara gigicewaba sai da yaji karar fitar motarta ,
Car key dinsa ya fincika tareda fita da gudu gudu dan take mata baya domin gani yake idan ta fita zataje ta cire masa cikinsa ne wanda idan duka duniya zata hadu bazai yarda ba "
Yayi saa kuwa yana fita ya hango ta tana hawa babban titi ,binta ya farayi abaya wanda saida yazamana mota biyu ke a tsakaninsu amma yanayin gudun da takeyi shine abunda yake kara bashi tsoro ."
..........tunda ta hau kan babban titi ta taka kan motan amma abun mamaki motan yafara mata wasu funny abubuwa wanda ta kasa gane kansu ,
Yes funny abubuwa domin a iya shekarun da tayi tana tukin mota tasan zaiyi wuya mota ta bata kashi saidai in wani ikon Allah,
Gani tayi funny thing yana kokarin zama gaskiya so a take tafara kokarin taka burki dan tayi duk yarda zatayi motan yayi slowing down yaki and wani abun mamaki shine burkin motar ya bace ,
Tirkashi ita dai tasan tana hawa maserati din ummi kuma lapia lau akwai burki to whats wrong with this ?
Motar dake gabanta taga ta nufar ma haikan da nakin dan haka ta kama sitiyarin motar domin kaucewa motar wanda hakan yayi dai dai da kwace mata da motar tayi tareda yin kiss da wata katuwar katangar makaranta"
A take balloon ya fito amma a banza dan tariga ta bugi kanta da karfi inda da taimakon glass din motan da ya fallatsa cikin motan wanda ya haifar mata da zubar jini"
Kaman a marfarki taji ihunsa inda a take kuma komai ya koma mata blank and black..
*****************************************
Sarkin yaki ka tabbatar wannan yaron naka da ka kawo yayi aikinsa yarda ya kamata"?
Washe baki mutumin da aka kira da sarkin yaki yayi tareda kamo hannun yaron nasa da aka ambata yace "ranki shidade na yarda da aikin zaki dari bisa dari domin ba yau yafara mun aikiba daga kisa zuwa kan duk wani kazamin aiki dan haka kar kiji wani wai ko dar aikinki kaman anyi angamane"
Juyowa tayi daga bayan da ta basu tace yayi kyau zan tura maka kudi a account dinka sai ka sallameshi sannan kasani wannan abun yazama daga ni sai kai sai shi wannan zakin ,
Kar ka kuskura naji sunan gwaggo amarya ya fita abakin kowa sabida idan hakan yafaru zaka mutune kuma mutuwa mai tsanananin radadi"
Alamun zip yayi da hanunsa a bakinsa inda itakuma ta kada kai tareda fadin zaka iya tafiya "
Suna kokarin fita Abba yana shigowa kallon kallo sukabi da juna kafun suka matsa masa yashigo.
Kallon mahaifiyar tasa yayi yace mai wannan tsohon shuumin kuma yake a nan,
Hade rai tayi dan kar ya fahimci wani abu tace kace kome zanyi yanzu sai nafada maka tunda kaine ubana to taimakon da muke ma marayu duk shekara yazo mu tattauna akai"
Kada kai kawai yayi dan yafi kowa sanin halinta sannan a rayuwarsa babu abunda ya tsana kaman ta jefa kanta kan yakin neman mulkin gidan wanda yasan dole sai kabi ta kazamar hanya bugu da kari sayeed din da take ma wanann fighting din ya bata rayuwarsa da shaye shaye wanda yake ganin shine hanyar bullewarsa "
Allah ya kyauta kawai ya iyacewa kafun ya fita a gidan inda ita kuma tabishi da tsaki tareda kiransa da sallamamme"
..tunda ta tsinci labarin cikin nuayma a yau din hankalinta yayi mutukar tashi ,ta tsorata dan wannan karanne bokanta yataba samun sabani a aiki dan haka tuni tashiga rudani,
Sake sake tafara yi aranta na yarda zata zubar da cikin dan karyazo duniya ,tana tsaka da wannan tunanine babbar baiwarta talle ta shigo tareda kara bata labarin da yafi komai mata daci wato na zuwan mai babban daki gidan adeel domin tayasu murna"
Karyar da kai talle tayi da ta fahimci uwar dakin nata na cikin rudani tace "ranki shidade ga shawara ,maizai hana anemo sarkin yaki yanzu amiki aiki kaman yankan wuka kinsan ba yau aka fara ba.
Zama gwaggo amarya ta dawo tayi kusa da talle tace talle kina nufin me kenan kinsan shifa sarkin yaki abunda aiki dashi yake nufi"
"Kwarai kuwa talle ta bata amsa "yana nufin mutum zai mutu kuma ranki shidade a ganina gwanda nuayma ta mutu da mu zubar mata da ciki sabida idan muka zubar zata iya samun wanine amma idan muka kashetafa "?
Sai tai ciki akiyama "gwaggo amarya ta karasa tareda saka wata bakar dariya "
"Maza je ki kira mun sarkin yaki"
Mintuna da basu wuce biyar ba saiga talle da sarkin yaki ,batayi wata boye boye ba wajen shaida masa bukatarta inda shi kuma ya bata tabbacin ai aiki kaman anyi an gamane in nuayma bata mutu yauba to zata mutu duk ranar da ta hau motar da yarima abidin yabata a matsayin kyauta"
Yana fita yakira yaron dake masa irin wadannan kazaman ayyukan ,
Babu tsoro ko shakka zaki yay shigar bayi tareda sajewa da mutanen mai babban daki inda su sunanta hidimunsu shikuma ya nufa inda aka tanada domin aje motocin gidan ya bata birkin motar nuayma ta kwarariyar hanya ,abunka da tsohon hannu a aikin,
Sannan bayan haka yakuma dawowa tareda sajewa da sauran bayin inda yayi nasarar fita lokacin da mai babban daki ta umarce kowa da ya basu guri...
********************
Kai Kawo adeel kawai yake a kofar dakin theater wanda anfi hour kenan da shiga da nuayma ,
Addua kawai yake ga ubangiji kan yabama nuayma lapia ,
Bakaramin tsorata yayi ba lokacin da yaga motar nuayma tana wasa akan titi ,ya firgita ainun amma bai gama tsorata ba sai da yaga ta nufa gini,baisan lokacin da ya faka motarsa ba tareda karasawa gurin da gudu wanda lokaci daya yasaka ihu da idanunsa sukayi tozali da ita ,
Kokari yafara na bude murfin motar sakamakon hayakin da motar ta fara,da kyar ya iya balle murfin Idan ya cirota cikin karfin hali.
Cikin lokaci kankani aka taru a gurin inda shi kuma adeel babu abunda ya iya banda kuka da rokanta kan ta tashi ta daina masa wasa'
Wani matashin saurayi wanda dandazon yajawo hankalinsa gurin ne yayi kokarin kiran 911"
Komawa yayi da sauri motarsa tareda dawowa da wani dan box da hand gloves then ya umarci adeel da rike mata wuyanta kar tayi twisting shikuma bari yayi kokarin tsayar mata da bleeding din da take"
Yana kokarin examine vein dinta adeel ya ture hannunsa tareda fadin " who are you"
A doctor" saurayin yabasa amsa tareda nuna masa id card dinsa yakarada doctor saleem topah"
Bayan lokaci kalilan ambulance ta zo inda dr saleem ya bisu a motarshi dan yasan definitely asibitinsu zaaje dan shine nearby"....
***
A hanzarce ya nufa kofar dakin ganin danjar ta dauke yasan likitocin nanan fitowa "
Dr saleem ne a gaba jikinsa sanye da korayen kayan likitoci inda bayansa kuma mutum uku ne suma cikin kayan,
A kidime adeel ya rike hannun doctor saleem tareda tambayarsa "doctor matana fa "
Dafa kafadarsa dr saleem yayi yace matarka lapian ta kalau Alhamdulilah munsamo kanta sannan "miracle happened" sabida dana fahimci matanka nada ciki sannan ta gamu da wannan-----
Da sauri adeel ya katse shi dan sai a lokacinne ma ya tuna wai nuayma na da cikin shi ,cikin kidima yace doctor how is the baby?
The baby is fine mr adeel kar ka damu as i was saying Allah ya cece babyn cikinku dan hardly ayi irin wannan accident din da ciki kuma cikin yayi surviving so kawai mubarshi ace wa matarka da abunda ke cikinta suna da saa domin buguwa kawai tayi sai karaya a hannu wadda akayi taking care of nothing serious so mugode ma Allah sannan zata iya farkawa anytime soon yanzu dai zaa sake mata daki then ka iya ganinta"
Da haka yatafi inda adeel babu abunda yake masa sai godia kaman shi yayi mata rai"
A hankali nutsuwa ta fara zuwar masa ,guri yasamu yazauna tareda ciro wayansa dan kiran abba ,
"Yakamata ace sun Sani"
Bayan ya kira abbane wanda ya shaida masa zuwansu kana yakira mai martaba shima ya shaida masa.
*
Ya jima zaune a gabanta a dakin da aka chanza mata yana kallon yarda fuskanta yayi pale kaman ba itane tagama masa tsiwa dazuba yanzu gatanan kwance kan gadan asibiti hanunta nannade da bandeji"
Wata soyayyarta yaji tana kara fizagarsa ,ya tabbata yau da yarasata baisan inda zai saka rayuwarsaba "
Da sallama yaji anbude kofan inda yafara jiyo sautin kukan ummi ,
Yana kokarin tashi domin juyawa garesu yaji ta damke hanunsa da hannunta mai lapia"
A take ya maida hankali gareta tareda fadin sunanta murya cike da murna ,
Idanunta ta sauke akansa ,wani zafi ya ziyarci kanta ,kara kallonsa tayi kafun ta bude baki da kyar tamasa tambayar da ta kusa wargaza duka maths din dayake kansa "
WHO ARE YOU?
I'm chu chu😂
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top