chapter 44
Halal veer ❤
Koda tafito daga toilet bataga ladi ba dan haka ta fito parlour tareda kunna tv domin kalan maimaicin shirin da take masifanso na fashion a spice TV"
Bowl din fruit din dake gabanta ta jawo tareda daukan Apple daya wanda suddenly taji tana san ci "
Bite daya ta kaimasa taji ana sallama a kofar dakinta tareda neman izinin shigowa,
Izini tamusu da su shigo inda ladi tafara shigowa domin shaida mata tana tareda doctor habib "
Koda ta sanar ma da nuayma zuwan doctor habib din shiru tayi tana nazari kan abunda ya kawosa domin idan zata iya tunawa doctor habib likitan masarauta ne "_
Kallonta ta mayar kan ladi tace "baba ladi wane bashida lapia koma ?
Dan murmishin yake tayi tace eh ai mai babban daki ce tace yazo nandin zai dan duba ki,
Shiru tayi na dan mintuna tana jinjina alamarin kafun ta gyara tareda fadin "bakomai shigo dashi"
So take Kawai taga wannan wane sabon abunne kuma "
Da sallama dattijon likittan yashigo tare gaisheta cike da girmamawa ,
Nauyin amsashi tayi dan haka tamayar masa da martani ta hanyar gaisheshi a maimakon amsawa,zuba musu ido tayi tana neman karin bayani ,
Bata gama tsinkewa da alamarinba saida taga ya ciro syringe a cikin jakan da yazo da ita,
Batasa lokacin da ta tsinci kanta da cewa "anya bakuyi batan hanya ba kuwa"
Murmishi doctor habib yayi dan a tunanisa ko tana tsoran allurane dan haka yayi assuring dita da cewa zaibi a hankali after all jini kadan zai diba"
Ai nantake hanjin cikinta yakada tareda wata irin faduwan gaba da ta ziyarceta ,
Jini ?
Mai kuma zaayi da jininta,kar dai asirin masaurata yabiyo ta kanta da har zaazo daukan jininta openly ido naganin ido"
A zabure ta mike tareda fara zazzare idanu cikin in'ina tace m-m-m-ee za-aayi da jinina kuma i don't understand"
Ganin tsoratan da tayine yasaka ladi tadan murmusa tareda cewa ranki ya dade ki kwantar da hankalinki sannan laipinane da ban fada mikiba ,mai babban daki ce tasa yazo ya dauka jinin ki domin zaayi maki gwajin jini"
Shiru nuayma tayi tana nazarin abun,she don't get it at all kaman yaya a auna jininta"
Sanin mai babban dakin bazata cutar da ita bane yasaka ta zauna jiki babu kwari sannan tana gudun kar mai babban dakin taga kaman ta raina umarninta so batareda tasake cewa wani abuba tamika hannunta inda yabi a hankali ya zuga jininta"
Sallama doctor habib yamata tareda fada mata cewa anjima kadan zai bada result ga mai babban daki"
Har suka fita abun bai daina bata mamaki ba amma daga karshe ta dangana hakan amatsayin wata aladarsu wadda bata saniba ta idan mutum ya dawo daga kasar waje sai an auna jininsa anga lapian sa .
Bayan mintina kadan da fitan su ladi tatsinkayi sallaman namiji wanda muryansa kusan daya da adeel ,
Shiru tayi da fari ganin yaki shigowa dan a tunaninta adeel ne da wani sabon salon dan haka ta maida hankalinta kan kallonda take batareda ta bi ta kanshiba "
Kara sallama akai a karo na biyu amma sai wannan lokacin taji ance in-law na shigo ne ko na koma ?
Zama ta gyara da ta tabbatar ba adeel bane sannan ta bada izinin ga mai sallaman kan ya shigo "_
Da faraar sa mai kyau ya shigo tareda zama a kujeran dake dan nesa da ita yace "barka da hutawa auntyn mu "
Tabbas ta gane shi duk da bata taba ganinsa a fili ba sakamakon haduwa da basu tabayi ba amma tasan shi a hoto dan haka cikeda yanayi na wadda kaman ta dade da haduwa dashi tace "abidin yau kai a gari sannu da zuwa"
Dan shafa gemunsa yayi yace "aunt ai ku zaace ma yau ku agari danni na dade a nigeria beside naso kaimuki ziyara uk but nafara running asibitina ,
So to cut it short I'm here with your gift dama ban baki na aureba yanzun gana gama school so --
Ya karashe maganan tareda aje mata dan box a kan hannun kujeran da take "
Murmushi tayi dan lokaci daya abidin ya shiga ranta gentleness dinsa ya burgeta,
Daukan box din tayi tace bansan yazan gode makabama ko ruwa ban bakaba"
Hannu yayi waving tareda cewa "no aunt karki wahalar da kanki ai dan nazo gun aunty na bana wahalar da itaba and banayi bakuntaba beside I'm okay wallahi"
Komawa tayi tace to shikenan tunda kanina yayi rejecting offer na bari na bude naga mai kanina na kaina ya kawo mun "
Sunkuyar da kai yayi tareda shafa cleaned cut gemunsa wanda a zamansa ta fahimci hakan sabonsa ne
"Aunt ai bayawa ma ban shirya ma abunba so i bought the gift in a rush I just wish you like it"..
Bude box din tayi finally inda taci karo da car key na Maserati "
Hannunta ta dora kan bakinta tace how do you know my favorite car ,
Omg thank you very much abidin best gift danayi receiving so far ,
I really really appreciate thank you"
Murmushi ya kumayi tareda jin dadin ta yaba da kyautar nasa tun kannta gani "_
The white maserati look stunning "
Muryan adeel ya jawo hankalinsu gareshi"
Thank you very much little man yakarasa maganan tareda masa dukan wasa a arm dinsa "mungode da sabon car din da kasiya mana"
Nasiyama aunt dina dai abidin yayi saurin gyara masa cikin wasa "
Guri adeel yasamu yazauna kusa da ita yace madam kinjifa mai kanin nan naki yake cewa wai motankine ke kadai"
Murmushin da bai kai ciki ba kawai ta bashi kafun tace abidin muje naga new car dinnawa "
Abidin ne yafara fita kafun ta bishi a baya"
Bai maganaba kuma bayyi kokarin binsuba"
*************************
Washe gari da safe tana shirin zuwa gida domin rananne ranar liyafan da su abba suka hada mata '
Hayaniya taji a harabar gidan nasu wanda kaman kar ta fita amma sai ta fita domin ganin mai yake wakana cikin gidan nasu tunda su basuda geji ga jamaar gidan in tasu ta tashi kaji hayaniyarsu"
Mai babban daki tagani zaune a gurin shan iskan su na sarauta a farfajiyan gidan nasu inda gefenta kuma kuyanguntane guda biyu,batayi mamakin rashin shiganta tareda birkin da tayiba dan yanzu wannan jamaar gida sun daina bata mamaki ,
Karasawa tayi cikin nutsuwa tareda zama daga gefe ta kwashi gaisuwa ,
Fadada faraa mai babban daki tayi tareda amsata inda tace "ina kokarin sawa ashiga ciki a miki iso bayan an gama hada miki gurin zama kuwa ashema kinji mu".
Alamu tayima wasu bayi tace kuzo ku taimakawa gimbiya ta zauna akan kujeran alfarma ,
Itadai takasa cewa komai sai gyara gyalen da ta yafo kan ta fito take '
Algaita taji anfara busawa daga bakin gate dinsu irin wadda akanyi a gidan lokacin farin ciki then gradually sautin yana nufota ,
Kuyangune gaba dauke da wata kwarya sai bayansu kuma masu wannan busan ,
Gabanta aka aje kwaryan inda aka umarceta da ta wanke hannunta ciki,
Batayi musuba ta saka hannu cikin ruwan da yayi mata kama dana lalle sannan wani kamshi na daban ke tashi a cikinsa ,
Bayan ta wanke hannunne aka sake umarta da ta saka kafafunta ,
Kamar yadda aka bukata din haka tayi batareda tayi gardama ba"
Bayan sun gama ne sukafita da abun inda nan mai babban daki ta umarci kowa da ya fita ya basu guri kana tasa nuayma ta dawo inda take a zaune "
Cikeda faraarta tace congratulations ina taya gimbiya da yarima farin ciki samun rabo a tsakani wanda da fari nayi tunanin kuna boye mana ne then da result kuma ya fito na tabbatar da bakusan da shiba domin cikin wata dayane da sati daya ,
Kuma sai kinyi hakuri da yanayin gidan sabida nasan zakiyi tunanin yarda aka miki katsalandan kan personal life dinki amma wannan ba personal bane a cikin gidannan domin hatta mai martaba baida burin da ya wuce ya ga jikan sa daga gurin yarima adeel "
Yanzu tsarin cin abincinki ma zai dawo hannuna sabida kinga abunka da farko sai kuciyo abunda zaizo not healthy for the unborn child at all,
Allah ya miki albarka ,da haka tamata sallama inda hajiya nuayma ta kasa tashi daga inda take zaune ,
Wani kululun bakin ciki da wasu zafafan hawaye suka fara mata gudu a fuska,
Ciki!!
Ciki!!!?
Nashiga uku ni nuayma ,cikifa ta fada a fili then kuma procedure din da akabi dan sanin tana da cikin yakara dawo mata take taji wata sabowar tsanar adeel da tsanar gidansu da aladarsu ya darsar mata .
Koda ta shiga daki wayarta ta tarar tana kara ,
Da hanzari ta dauka ganin sunan ummi na yawo kan screen din ,
Saita kanta tayi gudun kar ummi din ta gane wani abu na damunta ,
DA sallama ta amsa wayan inda ta tsikayi muryan ummi da alamun damuwa tace "ayma mai ya samu wayankine tun dazu ake ta kira ,
Na kira
Abbanki ma nusayr ma sannan ibi ma yakira amma shiru lapia dai ko?
Munjiki shiru "
Share hawayen da suka zubar mata tayi tanajin ina ma zata iya sharing damuwanta da mahaifiyar tata amma ina ta janye kudirinta na fada musu tukunna sai ta zubar da wannan cikin domin babu mai sakata ta haifeshi, ba dai jikan soyayya ba to zata zubar dashi inyaso mutanen gidan sa saka ya saketa da hujja ba sai ta bama kanta wata wahalaba "
!!Ummi bacci ya dan daukeni walh kuma wayan yana silent shiyasa tashina kenan amma yanzunnan zan taho hope ummi kin aje mun favorite dambun accan da namiki magana jiya "
Ta tsinci kanta da fada".
Daga daya bangaren ummi tayi dariya dan ta fahimta sarai nuaymanta takusa bata jika dan haka tunda ta fara maganar dambun accan tashiga kasuwa da kanta domin hado kayan hadi"
"Kedai sai kinzo har sai kin gaji da dambun acca "
Tabata amsa "
Hanging wayanta keda wuya taji anyi hugging dinta ta baya then kuma kaman wata mota ya juyo da ita tareda mata kiss a goshi ,
Cikeda murna yace "thank you very much sweet heart
Nayi matukar farin ciki da labarin da na iske cikin gidan nan, that's the best gift i could ever ask of you "
Naso na miki babban surprise na graduation Dinki amma wannan labarin dana iske ya ruguza mun komai ,i dont even know what to give you "
Hannunsa ya saka tareda shafa cikinta cikeda farin ciki ya kuma cewa thank you babe "
Yana kokarin sake taba cikin ta turesa wanda sai a lokacinne ya kula da yanayinta.
C
hu chu.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top