Chapter 1
Epigraph
Love many things, for therein lies the true strength,
And whosoever loves much perform much
And can accomplish much
And what is done in love
Is done well!
Epigram
Never let the odds keep you
From doing what you
Know in your heart
You were
Meant to
Do it!
A/N
Thank y'all for being with me through thick and thin, ikr I'm such a slacker ass, so thank y'all for being patient!
I assure y'all!
So do vote, comment If possible, and don't forget to recommend it to your frnds if you find it to your liking! Thank you
🖊CHU²
Halal veer 📝
Ambassador yunus yakasance mutumin kano ne wanda ke cikin siyasa sosai, dan kuwa Alhamdulillah siyasa takaimasu yarda ya kamata, dan bayan gwamnatin su ta haye, da taimakon Allah akamasa ambassador na Ukraine, domin dama yakaranta international relationship ne a jamiar bayero dake kano!
Zaune yayi a parlor dinsa ga dai Tv nayi amma kallo daya zaka masa kasan ba ita din yake kallo ba,
Kyakyawar matarsa ce tashigo parlorn bakinta dauke da sallama amma ba amsa, da sauri ta karasa da ta fahimci maigidan nata ya zurfafa wata duniyar wadda yazama bata jin dadin hakan, a yan kwanakinnan duka yasama Kansa damuwa, tsoranta daya kar bp dinsa ya kara hawa!
Kusa dashi ta samu ta zauna tareda zare tagumin da yayi, sassanyan Murmushi yayi mata tareda san kawar da Wancan tunanin dayake dan yasan yanzun nan Zata fara masa mitan batason wannan tunanin da yake, kafun kuwa ya gama tunanin hakan tafara magana cikeda nustuwa da san kwantar masa da hankali!
"Honey ni narasa ya kakeso nayi da rayuwana, nafada maka wannan tunanin is not good for your health Amman kaki barinsa, komenene yayi zafi maganinsa Allah, babu bawanda zaka gani aduniya ya cigaba batareda, Allah ya jarrabeshi ba, shikuma bawan sai yayi kokari yaga yacinye wannan jarabawan, and ni na yarda da mijina mutum ne mai karfin imani da tawakkali Akan duk abunda yazo masa, so ina ka kai mun wannan mijin Nawa? Dan wannan nagabana an sake munshi" takarasa maganan ta cike da barkwancen da saida tasasa yayi murmushinsa wanda ya ke tafiya da ita a kullum!
Hannayenta biyu yakama tareda caressing dinsu yace "salma bawai ina ja da abunda, Allah ya jarabceni da shi bane aa, kawai ina tunanin nan gaba ne, kinsa shi Abu idan ya zo da siyasa dama sai tsarin Allah, I don't know how on earth lokaci daya akeso na bada matsayin da nake nan da one month dan batan kudinda bansan dasuba, wallahi ke shaida nace a duniya sannan Allah ma shaida nane, bantaba cin kudin da Nasan ba halal Dina bane, dan da ace ina cin kudin da banawaba kinsan da yanzu kudin da zanyi bama Gaskiya bane,
Ki Kalla duk abokaina ambsds irin kudin da suke da shi ba a magana and mostly bazance duka ba, sun bar hanyan Halal wanda nima da inaso da nabarta tuntuni, amma menene amfanin katara dukiyar haram ma iyalaina sannan kai kuma ka mutu kace ma Allah menene, shiyasa komai nake takatsantsan akai, amma ina mutane baa taba iya musu, bazasu taba barinka ka zauna lapia ba, sai Susan hanyan da Zasu bataka ka wulakanta, yanzu kudinan wallahi bansan da zamansu bama amma kinji lokaci daya an kirkiresu anyi setting min trap, yanzun I have to pay 1 billion, wanda banci ba bansha ba, abun yana damuna sosai!
Ajiyan zuciya salma ta sauke tareda shafa gefen fuskanta cike da kulawa tace, abban moha, Nasan baka daukan musu kudi ba nasani, I know you best, kudi zamu biya su insha Allahu, and Allah zai ninninka maka finsu, sukuma Zasu biyaka lokacin da basu da shi I'm an independent doctor ina daukan kudi mai yawa Alhamdulillah, I gathered some and you gathered too zamu biya su kudinsu, saukin abun basuyi sueing ba, so we will pay them hankali kwance,suje dan kansu, ai Allah baya barin Azalumi hakanan sai ya nuna masa karshensa,
Lokaci daya yaji wata nustuwa da kaunar matarsa yasake saukan masa, hugging dinta yayi tareda cewa "Allah ubangiji ya shimiki Albarka salma bansan dame zan saka miki ba, hakika ke mace ne ta gari wadda samin irinki sai Antona, you married me lokacin da banida komai har Nazo nasamu, Koda sau daya baki taba mun complain din babu ba, kin zauna Dani through thick and thin, sannan yanzu ga wata jarabban ta sameni wadda da wata ce bazata Duba yaran da mukai Haifa tareba Zara rabu dani, amma ke kwarin gwiwa kike Bani,
Where will I be without you?
Bazana taba iya saka maki ba sai dai Allah, Allah ya biyaki da Aljanna, Indai Aljannar ki kar kashin kafana take na daga miki ki wuce!
Wani hawayen dadi taji Suna zubar mata cikeda murna tace na gode honey, and namaka alkawari duk rintsi duk wahala Bazana taba iya rabuwa da kaiba, sabida bazan taba iyawa bane, matsalata daya Ibrahim shine babba a cikin yaranmu sannan munyi kuskure da muka fi Gina sa Akan cewa Koda bamu zai dauke nauyin kannesa, amma ina duk da bamu neman wani Abu gunsa yanzun amma tunda yabar Ukraine da matarsa shiru kakeji Malam yaci shirwa, yaron nan Koya kira gida amma shiru kakeji, shi dan dadi mata, wadda tafi family, is not that we need his money amma at least he should ne great full mun kawosa duniya, right ace gidanka ma ya gagari kanwarka zama wadda take kasa daya gari daya da kai amma sai dai tasamu gida wannan wane irin rayuwane?
Dan Jan hanci tayi tareda lafewa kan cinyarsa jin yarda take shafa mata kai, dago kai tayi ta kallesa tace abban NU'AYMA Anya ba Yanke mata karatun England dinan zamuyi ba inzamu tafi Nigeria mutafi da ita ba, I'm just finding it hard na barinta on her own a wata kasan bawani mai taimakonta and first year for that matter sai tayi wajen 4 years banajin dadin hakan she's just 19 fa, tunda shi ibi din yacire mu cikin family dinsa fine Gashi ga duniya a---
Da sauri yarufe mata baki tareda girgiza mata kai "no salma bansan ki da hakaba, yaran yanzu sai da adduaa, idan kikayi masa Baki yakenan, kinsan yarda bakin Uwa yake ci, and Nasan Kema bazakiso hakan ba , addua kawai zamuyi ta musu, maganan nu'ayma kuma we can't cancel karatun da tafara kuma kinfi kowa sanin yarda take kaunar karatun, kinganni bazataso a katse mata ba, kingan in Nigeria din muka tafi da ita samin admission din,
So adduaa kawai zamu cigaba da mata, mu dorata kan tarbiyya mai kyau wanda very sure Zata tsare mutuncinta, sai dai kinsan kawaye, and ayman mu yarinya ce mara san mutane im very sure Allah zai cigaba da kareta, kafun wannan sakaran twin din nata yagama last year a high school dinsan nan next year yayi joining dinta!
Ajiyan zuciya tayi tace wallahi abban moha ni kaina abun nusayr yana damuna, tarefa suka fara makarantan nan da nu'ayma amma tagama ta barsa Allah yasa yanzun ganin ta tafi uni din yasa ya dage shima, tunda month daya yarage mana a kasar nan sai mu barsa yagama inyaso yataho gida after sai anema masa school din su ayma, autana kuwa kafata kafarsa,
Rufe bakinta kuwa keda wuya muhammad autanta ya shigo , tashitayi daga cinyan maigidanta ta nufesa " auta why are you frowning daga dawowanka a school, what's wrong,
Kara kangwabe kai yayi tareda pouting cute lips dinsa kaman zai kuka, inda Maman san hankalinta yakara tashi da hanzari ta karasa garesa, kaman jira yake kuwa tana karasowa ya Dane ta, saida ta dan yi gasping kafun tasa dariya I gatchu yaran nan wai ni zai ma wayau abban moha,
Dariya yasaka yace wanan tsakaninku ina ni ina shiga anjima a gwaleni +kin rike katon grown up kid a kafada dont beg me for any massage anjima, 12 years old ya tsofa ai,
Pouting moha yasake yi yace ni ni ni ummi kinga abba ba wai nine Kato, haryanzun fa a freshman year one nake fa, ai ummi ban wuce a goya ni ba ko Adda ayma ne da su Hamma nusayr da ibi ne Kato ko ummi?
Gada masa kai tayi da sauri "yes sweetheart sune amma kai kam har goyanka ma zanayi and soon zakasha fura da nono na inno, amma yanzun namaka wani delicious krispy kremes!
Ai da sauri yasaka wani yay din murna inda sukai ciki yanata dariya,
Gada kai ambsd yunus yayi tareda jin kaunar iyalinsa ta kaina sannan da adduan Allah kar ya Kawo ranan da zai Gaza musu ta ko ina,
Asalin salma mutuniyar adamawa ce inda Karatu yakawo ta kano nan jamiar bayero, lokacin yana final year dinsa ita kuma Suna new intake, sosai soyyaya yashiga tsakaninsu wadda har ta kaisu da aure, sai bayan auren su ta samu ta kammala karatunta!
Sosai akasha tataburza lokacin auren nasu dan kakanninta kafewa sukayi sam Akan cewa ai da alkawarin auren dan uwanta a kanta, kasan cewar mahaifinta gogaggen dan bokone yasaka yabi duk yarda zaiyi Akan lallai sai dai abi raayin yarinya tunda zamanin ai yazo da chanji,
karshe suka hakura akayi auren da aduaan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi!
LONDON
Next
Till I see y'all in London ahaaaaaaa rrrrrrrrrnrrn👻
Chu²jay
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top