lokaci ne part 1 ,by leema
*⚜BRILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_
*🌍GUGUWAR ZAMANI🌍*
_{ƘALUBALEN RAYUWAR MU A YAU}_
_Daga alƙalamin marubutan zamani da suka yi zarra_
TURMI NA UKU
*title 003:LOKACI NE*
*Daga alƙalamin:L££MA*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*SHAFI NA:1*
Matashiyar budurwa yar qimanin Shekaru ashirin da takwas(28) da haihuwa ne tsaye gaban madubi tana ƙare wa hallitar jikinta kallo.., sanye take cikin tsadaddiyar rigar bacci shara shara iya gwiwa,tuni hawaye ya wanke Kyakkyawar fuskarta!
Batayi Aune ba taji bakinta na furta meye makosata!? ,Me ya hanani aure har yanzu!?, Me yasa duk namijn da yazo gareni baya kwana biyu bai sake Dawowa!? ,Sauran ƙawaye na da muka taso tare daga mai yara biyu sai uku!?,Wani laifi na yiwa Allah!?,"da sauri ta furta astagfirullah".
A hankali cikin sanyi da rarrashi zuciyarta tace," ba kiyi wa Allah komai ba Raihana kiyi Hakuri *LOKACI NE* wata Rana sai labari hallau da yawa wani jinkiri Alkhairi ne!
Silalewa tayi ta zauna saman babban gadon ta gami da share hawayen da ke kwaranya A Idonta.., tana furta na tuba Allah ka yafe mun,Ni musulma ce na yadda da ƙaddara haka zalika komi
*LOKACI NE* ,idan lokacin aure na yayi babu wanda ya isa ya hana,haka idan lokaci bai yiba babu wanda ya isa ya ɗaura mun aure!,hawayen ta share tare da gyara kwanciyarta bayan ta karanto addu'ar kwanciya bacci,ta cigaba da maimaita istigfari A zuciyarta har bacci ya sureta...
Washe gari tunda safe ta shirya kamar kullum ta fito..., Da momyn su tafara Karo Suka gaisa ta d'an zauna tana kallon A gogon da ke d'aure Ah tsintiyar hannunta, kafun tad'ago momy tace," Raihana kince Abbas zai turo iyayen shi tun jiya Amma Shiru!
Kina ganin wanan rayuwar na korar SAMARI da kika ɗauko zai haifa maki ɗa mai ido?, ita fa macce y'ar *LOKACI CE*,wallahi da zarar LOKACIN ki ya wuce an daina yayin ki shike nan haka zaki wayi gari kina neman ko tsoho ne yazo hirar banza ma baki samu ba!
Ɗan yake tayi irrin mai ciwoooo ga mak'oshi A hankali tace, momy ba laifina bane daga shine dan baki ga yadda na matsa ba kafun da kyar ya amince zai turo ɗin,sai gashi tun jiya koda na kira baya daga wayar a karshe ma a kashe take har yanzu!
A yatsine tace ,kullum zancenki ɗaya," kin ce saurayi yazooo bai sake kiran ki ba".
yanzu ke Raihana ko kunya bakyaji ga k'annenki zahida da jannat ko wacce na gidan mijinta lafiya lau har sun haihu,ke kin tsaya ruwan ido?, wallahi ai da wata tsohuwar budurwa gwara karamar bazawara!
Kalaman mommyn su ya matukar qona mata zuciya amma ta ɗaure,kuyi hakuri mommy wallahi nafi kowa son AUREN nan sai dai
*LOKACI NA NE BAI YI BA*,zan fita wurin aiki.
Me akeci da wani aikin banza godai godai dake a gida ba aure,don Allah tafi can ki bani wuri ai duk mahaifin ku ya ɗaure maki sai yadda kike so kike yi.
Kamar zata yi kuka ta gyara zaman mayafinta a kafaɗa ko karin safe bata tsaya yiba ta fice daga gidan domin mahaifin su baya gari.
A makare ta isa babban pharmacy da take aiki,sai data shiga ofishin maigidan su ta gaishe shi..., faɗa ya shiga yi domin ta makara..
Hakuri ta bashi sannan ta fito ta gaisa da sauran abokan aikin ta,tare da saka farar rigar(lab coat)a Saman kayanta ta zaune a inda take zama tana sake sake cikin zuciyarta!
*WACECE RAIHANA IBRAHIM?*
_Asalin su fulanin ka'oje ne bagudo local government dake jahar Kebbi,birnin Kebbi mahaifin su tsohon babban officer ne a immigration office a cikin birnin Kebbi wanda har yayi gidan kanshi suna zaune a kwatas din gwadangaji yanzu haka ya kusa aje aiki(retired)._
_Su uku ne kacal wurin iyayen su;Raihana,zahida da jannat.,, aƙalla akwai shekaru biyar masu kyau tsakanin Raihana da zahida,sai ƙaramar su jannat,,,tun bayan kammala karatun sakandari samari suka yiwa Raihana caaa suna sonta da aure...,sai dai wani babban ikon Allah duk wanda akace ya turo magabatan shi shike nan baa sake Jin labarin shi._
_Har ta shafe shekara ɗaya a gida babu tsayayya,wanan dalili yasa mahaifin su saya mata Form ta samu gurbin karatu a"COLLEGE OF HEALTH SCIENCE AND TECHNOLOGY JEGA",inda aka bata pharmacy technician,,, kwata kwata mommyn su bata so wanan karatun ba domin a ganinta ruwan ido Raihana take yi wurin fidda miji amma dole ta hakura!...,a kwana a tashi tana karatun ta cikin kwanciyar hankali bata da da komi har tayi nisa lokacin tana da shekaru ashirin da biyu samari kuma sai tururuwa suke wurin ta sai wanda taga daman kulawa !_
_A hankali rayuwa ke tafiya har ta kamala karatun lokacin tana da shekaru ashirin da huɗu daidai yan kanen ta sun Kamala sekandiri Allah ya kawo masu mazajen aure wanda baa ɗauki lokaci ba abban su ya aurar dasu kasancewar shi cikakken Hausa/Fulani yana koyi da al'adun su...,Bayan auren ne abubuwa suka fara samun Raihana domin gashi ta kamala karatun da sakamakon mai kyau amma babu mijin aure babu aiki har aka maimaita shekara yan kanen nata suka haihu lokacin mommyn su ta dauki zafi da ita kullum cikin bak'ar magana da habaice gashi zahida nada ɗan ta mai sunan mahaifin su,jannat nada macce kuma suna cigaba da karatun su,,gani zaman ba zai mata haka ba tayi applying wani babban pharmacy da aka buɗe sabo cikin ikon Allah suka ɗauke ta aiki shine ke rage mata kewa domin samarin sun gudu sai Abba dake zuwa shima daga ya turo ya gudu!!_
*L££MA*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top