baya da kura 03

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION🖊*
_{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}_

     *🌍GUGUWAR ZAMANI🌍*      _{ƙALUBALEN RAYUWAR MU A YAU}_

_Daga alƙalamin marubutan zamani da suka yi zarra._

'''TURMI NA FARKO'''
*tittle 001:BAYA DA ƘURA*
  _{illar zina akan ƴaƴan mazinaci}♣_
*A TRUE LIFE STORY*

  _*Daga Alƙalamin:SIYAMAIBRAHIM*_

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*SHAFI NA:3*
_Finale_

Ranar girkin amarya ce yau wato Mariya a yau ɗin ne kuma Buba ya mata kaca kaca yayi wucewar sa maɗaɗin ya bata kuɗin cefane sai ya ƙi ya zazzaga mata yayi tafiyar sa,a yau ɗin ne kuma ranar juma'a ranar da ba zai taɓa mantawa da ita ba a rayuwar sa dan yana barin gidan amaryar kasancewar ita gidan ta daban yake da sauran matayen sa su ukun tunda ya aure ta..
Yana barin gidan ta ko rabin hanya bai kai ba Allah ya sauko mai da wata jarabta dan kuwa yana shawo kwanar da zai sada sa da titin da zai miƙe yayi hanyar gidan farkar sa mashin ya ƙwace mai kafin a sani har ya haɗe da wani ɗan a daidaita,sai gashi a ƙasa..
  Nan da nan aka taru ana mai sannu amma ina bai san inda kan sa yake ba shi kuwa mai a daidaita yayi gaba abin sa..
Haka jama'an wurin suka ɗauko wayar sa dake yashe gefe suka laluɓo lambar da yayi kira da shi ƙarshe dan ko wayar zamani bai da sai Tecno ta dubu biyar da ɗari biyar itama na hannu ya saya amma farkokin sa waya har ta dubu saba'in sai ya siya masu sutura kam ba'a magana..
Da muntari yayi wayar ƙarshe dan haka aka kira layin aka sanar da shi mai wayar ya sami hatsari yana nan wuri kaza aka mai kwatance...

  Da hanzarin sa ya nufi inda aka mai kwatancen yana zuwa ya masu godiya ya nemo mai a daidaita suka saka sa ciki aka wuce da shi wata ƙaramar primary health care mafi kusa da hanyar da yayi hatsarin..
  Har aka shigar da shi cikin PHC ɗin bai san inda kan sa yake ba,ranga ranga aka shigar da shi aka bashi kujera muntari ya zaunar da shi aka fara ƙoƙarain dakatar da jinin da ke zuba a wasu sassan jikin sa...
  Kiran amaryar Buba muntari yayi ya sanar da ita abin da ke faruwa..Allah sarki baiwar Allah sai ta ruɗe girkin da take yi ta rufe har tana ƙonewa da garwashin abin girkin amma bata ji zafin ba ta tashi ta rinƙa kai kawo ta rasa ta ina zata fara sai can ƴar ta ɗaya mai suna Hasiya ta riƙo hannun ta ta ce da ita su je ta sauya kaya su nufi asibitin..
Da taimakon wannan ƴar tata suka kama hanya suka nufi asibitin dan ƴar ma ba ƴar sa bace wacce kafin ya auri uwar ƴar komai ta ce tana so yana mata tun ma kafin ta furta zai mata ga yarinyar da hankali da kawaici dan ta kammala karatun ta har ta fara aiki sannan ya shigo rayuwar su ita kuma ganin mahaifiyar ta na zaune tsawon shekaru goma sha shida babu miji tun bayan rasuwar mahaifin ta sai ta rinƙa tursasa zuciyar mahaifiyar tata akan wannan mayaudarin azzalumin mutumi dan ya nuna ma ɗiyar ya daɗe yana son mahaifiyar ta tun tana budurwa kafin tayi aure Allah bai nufa shi zai fara auren ta ya nunawa yarinyar da gaske yake akan mahaifiyar ta yarinyar kuwa ta dage ta tsaya har sai da ya auri mahaifiyar ta ba wai dan mahaifiyar nata na so ba sai dan ganin ƴar ta ta damu da ita sosai amma bayan wannan basu rasa ci ko sha ko sutura ba,,auren wannan mutumi da tayi sai ya zama kamar farar ƙafa ne a gare ta sana'oin da take yi na siya da sayarwa kamar haɗa kayan ɗakin amarya da siyar da zanuwan gadaje da atamfofi su turaruka da takalma wanda da su suke rufawa junan su asiri ita da ƴar ta haɗe da albashin ƴar in an kai ƙarshen wata duk baƙin cikin ka ba zaka kalli Mariya da ɗiyar ta kace da su matsiyata ba amma auren ta da Buba komai sai ya dawo masu a rikirkice komai ya tsaya cak babu gaba sai baya tun ana karame karame har aka haƙura hatta da albashin ɗiyar ma ba wani isar su yake yi ba suka dawo sutura sai mahaifiyar ta haɗa da satar kuɗin sa suke samin damar yi babu takalmin a zo a gani babu hijabai,godiyar ɗiyar ɗaya tana da tsayayyen saurayin da zai aure ta wanda shi ke mata ƙoƙari toh in ya mata alkhairi ne ma take taimakon mahaifiyar ta su rufawa kan su asiri amma lokuta da dama mahaifiyar ta so kai ƙara kotu akan a raba ta mijin dan zama da miji mazinaci mai zargi bai dace ba amma ɗiyar ke tausa ta akan kamar tonawa kan su asiri ne in suka ɗaukaka abin ta dai ƙara haƙuri watarana sai labari...

  Suna isowa asibitin suka gan sa zaune kamar wanda zai gangara bakin nan ya kumburo dan sai ma an ɗinke sa ga hannu nan yayi suntum suntum alamar akwai karaya ta ciki ga ƙafa nan sai an juya shi fuskar duk ya kumburo babu kyawun gani..
  Magana amaryar ke masa amma sai kiran sunan ta yake kamar mashayi ita kuma tana ta yi mai sannu..
  Suna a haka ne uwargidan sa ta zo takalmin ƙafar ta daban daban tsabar ruɗewa dama sun ɗan fi kusa da anaryar bisa ga sauran matayen sa.
  Da hawayen ta ta ƙaraso dan bata fatar ya tafi ya bar ta duk da asirin da take mai da sace sace wanda ba dan kishiyoyi da suka taso ta gaba ba da bata mai hakan ba... 
  Mariyar ce dai ta rinƙa rarrashin ta sai ga sauran matayen nasa sun zo daga baya suna tambayar ina yake aka nuna masu shi..
Wani abin mamaki sai annurin fuskar su ta kau wato tun da suka ji labarin da inno da Azumi sai addu'a suke yi Allah ya sa ya gangara dan ita Azumi tana da ɗa ɗaya da shi ita kuma inno ƴar ta ɗaya mai kama da uban ta Buba ba zata fi shekara biyar ba amma ta sha baƙin nono haka take da baƙar hali irin na mahaifiyar ta..

Suna zaune ƴaƴan nasa suka zo Aminu shi ya fara zuwa sannan sauran suka zo ita kuwa Aminar kamar a buge take haka dai ɗiyar amaryar Buba ta rinƙa bin su da ido ɗaya bayan ɗaya tana masu addu'ar shiriya..
  Shigar da shi ɗakin ɗinki aka yi aka ɗinke mai bakin sa aka gyara sa sannan suka fito aka biya kuɗi suka shiga a daidaita shi da muntari da amaryar sai uwargidan sauran biyun suka nufi ɗaya a daidaitar suka kama hanyar gidan mai gyara karaya wanda nan gidan ma gidan mahaifin wata farkar tasa ce itama ɗin da auren ta amma yadda take ha'intar mijin ta abin ba'a cewa komai...
  Bayan an mai gyaran da ƙyar ma sannan aka dawo da shi gida ita dai amaryar da girkin ta ne ita ta zauna tare da shi har zuwa lokacin da ya ɗan farfaɗo ya buƙaci abinci,sai ta kirawo ɗiyar ta ta kawo abincin dan dama ita gida ta koma tuntuni..

  A ranar dai Buba ya ga kan sa dan kuwa ɗan lelen da yake iƙirarin yana so wato Ashiru,sannu bai shiga tsakanin sa da shi ba sai ma satar mai kuɗin da yayi ya kama gaban sa ya tafi bushashar sa da ƴan matan sa ƴaƴan wasu ƙabilun kusan su biyar shi da abokan sa..
Duk ƴaƴan babu wanda ya bi ta kan mahaifin nasu sai aikin gaban sa yake yi Aminun dai ba'a cika yi da shi ba shine yake zaune tare da mahaifin nasu duk abin da yake so yana mai...

Kusan satin sa uku yana jinya kafin ya warke ya dawo kan ƙafafun sa,a lokacin ne ya gane lallai inno da Azumi ba son sa suke ba dukiyar sa suke so dan haka ya fara canza masu amma madaɗin ya gyaru sai bai gyaru ba ya cigaba da aikata alfashar sa dan tsabar sakacin sa da addu'a da rashin sanin ciwon kai wanda ya sa duk son canzawa Azumi da inno da ya so yi abin ya faskara dan kuwa asirai da suke ta tafka mai na ta galaba a kan sa...

Wani faithful day ya tafi aikata alfashar sa a wani ƙauye wun wata farkar sa Amina da ta ƙi yin aure tun bayan rabuwar ta da mijin ta,komai ya gama wakana tsakanin su ya kama hanya ya fita yana jan babur ɗin sa yana wangale baki sai ya hango wani kamar ɗan sa Ashiru sai ya ja baya ya tsaya har ya gama kallon inda ɗan ya nufa..
Gidan da ya baro ne ɗan ya nufa dan haka ya biyo sa a baya sai ya ga ya shige wani ƙaramin ɗaki ya rufe can gaba da ɗakin da shi Buban ya fito,yaron nan kusan awowi biyu ya share bai fito ba sai daga baya wanda mahaifin na ganin fitowar sa ya ja baya ya tsaya har ɗan ya wuce sannan ya biyo sa a baya suka dawo gida kusan tare...
  Da ya nemi sanin abin da ɗan ya tafi yi wuri kaza sai ya ce da shi ai karatu ya tafi yi ba wani abin ba sai mahaifin ya yarda ya ƙyale sa..
A haka yaron nan ke tambaɗewa da ƴaƴan mutani sa'oin sa da waɗanda suka girme sa sam ƙannen shi basu mutunta shi dan sun san halin sa na shaye shaye da bin mata haka baya ganin mahaifin sa da mahaifiyar sa da wani mutunci ko daraja dan abin da suke yi shi yake yi da ƴaƴan wasi haka abin da mahaifin sa ke yi shi yakae yi...

  *************
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya masu bambancin da aka samu shine Buba ya fara sakarwa amaryar sa aljihun sa yana ƙoƙarin bata abinci ba sai ta siya ta ciyar da shi ba kamar yadda ta saba yi da dan ta sanar da shi idan ya ƙara cutar da ita toh bata yafe mai ba kuma Allah ya isa,toh shi kam ya tsani ya ji kalmar Allah ya isar shi yasa yake ɗan ƙwazawa ba dan ran sa na so ba dan shi ɗin ba jahilin daƙiƙi bane yana da ɗan ilimin sa na zamani ya kai wani mataki a karatun boko saɓanin matayen sa da babu wacce tayi bokon wanda da bokon nasa yake cutar da su...

Rannan yana tare da farkar sa sun kammala alfashar su sai ta fiddo mai da wasu papers na ƙadarorin sa akan ya cike mata su sai su cigaba da harkar su amma da yake shi ɗin mai wayo ne ya ƙi cike mata su sai da ya ga ta tashi tsaye riƙe da wuƙa mai kaifi sannan ya cike jiki na rawa dan in akwai abin da ya tsana a rayuwar sa shine mutuwa..
  Yana gama signing yayi gaba jikin sa na ɓari yana nadamar rayuwar sa ko ba komai ya rasa gidajen sa biyu kuma yana tsoron kai ta ƙara ta fallasa shi dan ita kam magajiya ce ƴar duniya bata da kunya kuma tana da iyayen gida zasu tsaya mata shi kuwa ko ba komai reputations ɗin sa zai ɓaci ga bad image da zai barwa ahalin sa..
  Yana zuwa gida ya tarar da wata asarar dan ƴar sa mommy ta tafka shaye shayen ta ta bige wata yarinya wanda yayi sanadiyar rasa ran yarinyar an kawo zance gida za'a tafi da ita police station dan ta ba da statement ɗan sa kuwa Aahiru is no where to be found dan kwanakin sa shida baya kwana a gidan sai gidan abokan sa suna faman shashancin su..
  Ranar kamar ya haukace ga matayen sa Azumi da inno kamar su zuba ruwa a ƙasa su sha dan murnar ƴaƴa biyu daga ɗakin uwargidan an kama su da laifi dan bayan bincike an gano ciki Ashirun ya ma wata ƴar inyamurai yayi yayi ta cire cikin ta ƙi shine shi da abokan sa suka ƙulle ta a ɗaki suka banka mata maganin zubar da ciki ta hanyar yi mata dole toh ba jimawa yarinyar ta ɗauke numfashi sai da aka kai ta asibiti aka saisaita ta su kuma aka kame su aka saka tara iyayen abokan suka ɗora blame akan Ashiru dan haka mahaifin Ashiru ne ya biya kuɗin damages ɗin sannan ya biya kuɗin hospital expenses na yarinyar kafin ya koma ya biya kuɗin beli dana diyar yarinyar da ɗiyar sa ta hankaɗa wanda yayi sanadiyar rasa ran ta...

***********
_5 months later_

  Zuwa yanzu komai nasa yayi ƙasa kasuwar ma sai a hankali baby kuɗi babu matan banza dan tun ranar da ya gama yin wannan asarar yayi nadamar rayuwar sa dan gaskiya ta fito ƙarara cewa cin amanar sa ga matayen wasu kuma ƴaƴan wasu ne ke ta bin sa dan zinar da Allah ya haramta shi kuma ya halastawa kan sa ne Allah ya jarabce sa dama tuntuni yana ta yi Allah bai nuna mai ishara ba sai yanzu...

  Duniyar ta juya mai babu daɗi bai san ribar da ya samu a cikin ta ba ga ƴaƴa nan kamar yanzu suka fara tambaɗewa kuma bai isa ya hana su ba  dan ishara ce ta riske sa..
  As for his wives kuwa,sun gaji sun haƙura dan abin da suke farautar samu yanzu kam babu shi duk ya ƙare haka suka natsu suna tafiyar da rayuwar su dan basu san wanda zai aure su ba in suka bar gidan sa dan kowa nada labarin baƙar halin su a gidan mai iyawa da su sai shi abin sa Buban..

  Aminun ne kaɗai da mamanni ke taimakawa mahaifin nasu amma sauran kam duk sai gyara rabbi ta'ala..

_MASHALLAH A NAN NA KAWO ƘARSHEN WANNAN TAƘAITACCEN LABARI NAWA MAI SUNA BAYA DA ƘURA WANDA YA KASANCE LABARI NE DA YA FARU DA GASKE KUMA BA WANI SABON ABU BANE DAN YANA REVOLVING A WURARE DABAN DABAN SAI DAI RASHIN SANI DA WASU BASU SANI BA..ABIN DA NAKE SON JANYO MANA HANKULAN MU AKAN SA CIKIN WANNAN LABARI NAWA SHINE MU KIYAYE DOKOKIN ALLAH SWT DAN KUWA YA HANE MU DAGA AIKATA ABUBUWA DA DAMA YA GARGAƊE MU DA KAR MU KUSANCI ZINA AMMA SAI GASHI WANNAN MUTUMI BA KUSANTAR SA KAƊAI YAYI BA HAR AIKATA SA YAKE YI DA GADARA KAMAR ABIN HALAS KUMA DAI MUN GA ƘARSHEN WANNAN MUTUMI DAN YA KASANCE MAI SAKACI DA ADDU'A GA TAKEN DOKOKIN ALLAH GA ƘIN SAUKE HAƘƘIN SA NA MATAYEN SA A GIDA GA CIN AMANAR MAZAJEN MATAYEN DA YAKE FASIƘANCI DA SU,MATAYEN SA NA TAFKA MAI ASIRI KUMA YANA KAMA SA SAKAMAKON SAKACIN SA DA YAKE YI DA ADDU'A GA ƳAƳAN SA DA BASU JI BA BASU GANI BA SUN TASHI SUNA GIRBAN ABIN DA MAHAIFIN SU YA SHUƘA SHEKARA DA SHEKARU TUN YANA ƊAN SAURAYIN SA HAR TSUFAR SA WANDA ANA IYA KIRAN HAKAN DA HAƘƘI.._
  _JAN KUNNE GARE MU AL'UMA MU YI ƘOƘARIN KIYAYE DOKOKIN MAHALICCIN MU DAN MU GAMA DA DUNIYA LAFIYA DAN WANNAN ƘUNGIYA TA BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION DA TA ƊAUKI NAUYIN KAWO MAKU WANNAN SHIRI MAI SUNA GUGUWAR ZAMANI BA DAN KOMAI TA ƊAUKI NAUYIN KAWO MAKU WANNAN SHIRI BA SAI DAN TA GYARA AL'UMA KUMA TA WAYAR DA KAWUNAN MUTANI AKAN CURRENT TRENDS DAKE FARUWA A RAYUWAR MU TA YAU DA KULLUM WANDA WASU MUN SANI WASU BAMU SANI BA_
_ALLAH YA SA MU AMFANA DA WANNAN SHIRI_

A MADAƊIN NI SIYAMA IBRAHIM DA KAFATANIN ƘUNGIYAR MU TA BRILLIANT WRITERS MUNA MASU YIWA AL'UMA ADDU'AR KARIYA DAGA FAƊAWA CIKIN WANNAN IRIN HALI KO MA MAKAMANCIN SA..A NAN NA AJIYE TAƁARYA TA SAI KUMA KUN JI DAGA MADAKIYA TA GABA DOMIN CIGABA DA KAWO MAKU WASU AWARENESS SA ƊIN DA ZAKU ƘARU DA SHI.._

*_26/01/20_*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top