Starter
FITAR RANA...
_......faduwarsa_
BISMILLAHIRRAHMANIRAHEEM.
Tun sassafe suka shirya suka bar garin jos suka dau hanyarsu wanda tadauƙesu tsawon awanni uku zuwa hudu ana tuƙasu,Jan ƙura irin nakan titin ƙauye wanda baiga darajar samun gyara ko kwalta ba shiya bule jikin bus din gwamnati daya sauƙesu a bakin titin wani kauye acan kusa da garin kaduna ana ce dashi mararrabar saminaka, masu saida fresh fresh kayan lambu da fruits sun cikke bakin titi anata hada hadan kasuwanci da saida da sayarwa,anan motar tasu tsaya ta sauƙesu suka sassauka kusa da wani mai saida karas da ganyayyaki,tafe wasimé take cikin nitsuwa dauƙe da jakar kayanta tana bibiyar matar data zame mata tamkar uwa da uba a bainar duniya wacce take ƙira da innono kotace mata anono,anma asalin sunan matar Fatsuma,saidai anfi saninta da hajiya fatu mai tuwo sabida tsohuwar sana'arta ne dafa abinci tana siyarwa danta samu kudi,Allah ya dafa mata ta shahara a manyan ma'aikatar gwamnati da manyan makarantu a matsayinta na chief cook,wato shugaban masu kula da harkokin girke girke na manyan makarantu da ma'aikata,tun tanacin kuruciyarta take wann sana'ar har shekarunta yaja ta tsofe, fatu mai tuwo farace sol tana da murmurarren jiki,itana kowace,kowa yasanta da halayyar son ƙulla zumunci da kyautatawa, da iya taimakon mutane, da son tallafawa naƙasa da ita koda kuwa bata sanka ba,fatu bazaurace mijinta ya rasu,amma tana da danta kwalli daya tilo datake kiransa da suna"Qasimu" wanda aynxu har ya kammala karatunsa na jamia yay kudin rufin asiri yay aurensa a garin kaduna,inda ya ajiye mata daya da dansu kwalli daya namiji.
Tsawon lokaci tabarsu acikin aminci Suna rayuwarsu acan ita kuma ta shiga uwa duniya yawon gwagwrmaya akan abunda ta saba na taimakon yan uwa marasa ƙarfi da galihu da kuma sada zumunci da dangi da abokai.
Halayyarta na son mutane ya jawo take da mutanen data sani bila adadin, ta kuma shaƙu da dumbin mutanen ta akusan duk inda taje,bata da wani alaƙa ta jini kona yan uwantaka da hassan mahaifin wasimé,iyayensa yan gudun hijirane daga ƙasar somalia,baban sa da mamansa sun gudo ne,lokcin da tsohon cikin sa suka yada zango agarin ringin gani,da sukazo garin bamai kallonsu bare ajega taimakon su,wata rana kwasam saiga fatu.anan ta tsincesu a bakin gaɓa lkcin ciwon naƙuda ya turneƙe mahaifiyar hassan,ita tayi ruwa tayi tsaki ta taimakesu har aka haifeshi lpya, aka samai sunan sa Aliyu haidar,sukamasa inkiya da hassan.,sosai iyayen hassan suka shaku da fatu,alokaci ƙalilin suka saba,suka dawo tamkar wasu yan uwanjini sabida yadda tariƙesu take taimaka musu da zuciyarta daya take kuma taimakonsu da dukiyarta,Bayan watanni sha shida Allah yay ma mahaifyar hassan rasuwa,mahaifin sa kuma yabi bayanta randa ta cika kwana arba'ain da rasuwan,fatuce ta dauƙi dansu Aliyu ta cigaba da rainonshi tamkar danta na cikinta harya girma yay aure ya auro matarsa badiatu.Saidai izuwa yau kuma ga yadda qaddara ta juya tarihin rayuwarsu komi ya zamto tamkar wani mafarki.
Hannun wasimén taja suka shiga wani madaidaicin gida ginin block wanda baida wani tazara da bakin hanyar da suka sauƙa,kai tsaye innono ta kutso kai cikin gidan da sallama a bakinta"Asallama alaikum masu gidan suna nan kuwa? wata dattijuwar mata ce a tsakar gidan tana ƙalkale saman cementi da tsintsiyar laushi a hannunta, jin muryan innonon yasata dagowa da fara'a akan fuskanta tana cewa..wa'alaikin sallam oyoyo oyoyo maraba da xuwa anononmu,barkanku da isowa...innono ta sauƙe ajiyar xcya"laraba ina mutan gidan haka naji koina yadau shiru kamar wani makabarta,tana kkrin karban kayansu tace suna nan sun dan zaga yin ta'axiyane a makwafta amma yanzu zasu dawo, kushigo ciki kuzauna kusha ruwa,lale marhaba da zuwa..daga fadin haka ta wuce dakinta agaggauce cikin sauri ta aje kayansu sann ta dawo hannunta dauƙe da babban tabarma,akan cementin kofar dakinta ta shimfida musu suka zazzauna,kujerar tsakar gida taja itama ta zauna
"Sannu mama,Ina kwana? Wasimé ta furta da sanyin muryanta mai cike da alkunya tana satan kallon matar
Matar tay murmushi ta dubeta ganin ta kyakkwaya saitaji ta shige mata har cikin ranta a bugu daya, tace lpya lau yan mata masha Allah,daganan wasime bata kara ce uffan ba ta maida kallonta ƙasa ta kuma nitsu sabida bata taɓa xuwa wani waje ba arayuwanta duk sai tanajin kanta daban,matar tana satan kallonta tana washe baki cikin rada tace,uhumm innono kar ace nayi azarbabi karde wannan ƴar itace amaryan namu?Kyabe baki innono tayi murya ƙasa kasa tana murmushi tace"Kede laraba da son jin gulma,aikya barni in huta kafin a tsunduma cikin sana'a ko,dariya matar tayi mai dan ƙara"kinsan goshin amare baya boya,masha Allah yarinya shar shar a ƙauyen fulani wann ai amaryace,innono ta kyabe baki"..ni ynzu ina naga ta gulma yunwa fa nakeji ni banko ƙarya ba ,laraba ki hanzarta ki kawomin abinci kyaji duk wani shauran bayani daganan,miƙewa matar tay cikin tsokanarta ta wuce kitchen ta soma kkrin kawo musu abun taɓawa,lafiyayyan tuwon dawace da miyar kuka taji manja da busasshen kifi yanzun nan dama ta kwashesu ba ako yi rabo ba,a dan tray din silver ta saka musu tare da ruwa snn ta ajeshi agabansu
,nan da nan da innono suka sauƙa akai itada wasiménta datake cin abincin a hankli kamar bazata ci ba,kafin nan mata, da yan yara yara har sun daddawo sunciƙƙe gidan da surutansu,tray tray na tuwon nan an sakoshi agaba anajan lomomi
Ana hira,yara yan fici fici irin bini in bika nan kawai in ka kirga zasu iyakaiwa ashirin,iyayen ne a tsakiya su hudu casss kowaccce ta haɗe uwar ciki da teba, kallo daya zaka musu kasan ƙunika akeyi agidan gadan gadan,banda sa'oin juna da wanda suka ba juna watanni akwai wanda aka turasu ƙaratun allo acan yobe state,"Anono anono surutu ne da hatsaniyan tade tade ya cikke tsakar gidan,manya da yara Kowa na burin ta saurareshi,sai can da magidancin gidan ya shigo sannan kowa ya nitsu aka dan sarara daga nan Wani shiru gidan ya dauƙa, dan Kaf yaran gidan sun watse kowa ya fita neman nakai,aka bar manyan sukadai agida tareda wasimé data laɓe agefen innono tayi shiru tanajin tattaunawarsu wanda mafi akasari akanta ne.
Ta gama lura kamar aure ake shirin yi mata itama,dama can ita ko ajikinta dan bayau ta soma ji ko ganin aure ba,zaman su a sansanin fulani yasata fahimtar komi,daga ƴa mace takai shekaru 9 xuwa sha 11 to a al'adance ma ta isa ayi mata aure,halan itama takaine,taga duk kawayenta nacan ma an bijiro da maganan aurensu duk dama bata san menene shi auren ba amma haka dai suke cewa.
Dattijon dayake bayani bazai wuce shekaru 60 ba, yace wa matayen sa da suke zazzaune agefensa akan da su shirya tarban ɓaki dan Lokacin isowar waliyann angon kawai ake jira angama shirye shiryen komi afannin amarya,Innono tacigaba da masa godiya tana saka masa albarka da tare da danta Qasimu daya amince a aurawa jikarta dahiru aure da wasimé,"
Dama can angaya mata danta Qasimu yay sa'ar aure duk dama tasan ƙabila ya auro amma ta lura kamar matarsan tana iya bakin kokarinta wajen yin musu adalci,sosai innono taji dadi da suka bata hadin kai ta bawa jikarta dahiru auren wasimé badon komi ba kodan sabida ta inganta rayuwrta na nan gaba.
Around 3pm na yamma saigasu kuwa sun iso,danta qasimu da matarsa da dansu taher wanda a shekaru bazai wuce ashirin ba,yaron kyakkawane na bugawa a jarida yafima iyayen nasa muhibba,yanada sigar mulki da kuma ƙasaita irin na wayayyu yan birni,shi tunda yaxo baiyi magana da kowa bama, Hannu bibbiyu iyayensa suka amshe zancen aurensa wanda aka ƙullasa bayan sallahn la'asar ranar jumu'a.a bakin masallacin Kofar mai kasuwan anguwan mahuta .."Taheeeru Elqasim junaid da matarsa wasimé Aliyou denge Akan sadaki dubu dari da hamsin lakadan ba ajalan ba.,aure yaci darajar dumbin jama'ar gari sabida ranace ta cin kasuwar kauyen,da wanda yasansu da wanda baisansu ba kaf an halarta ankuma sakawa auren albarka.
Nan danan mata suka tada Yan raye raye da kade kade na al'ada guda ya cikka tsakar gidan kamar dagaske,kan kace kobo auren da akayi tsammanin yinshi cikin sirri da tsagaitawa saigashi yayi armashi har andanyi wasanni na al'ada antarawa amarya da ango kudi,Matsala daya aka samu kasancewar wasimé yar karamace batasan ma me akeyi ba,shekarunta tara ne kacal,shima taheer sam baiji dadin hakan ba a xuciyarsa dan baisan yaya xaiyi da wannan premature auren da aka musu ba,shikansa he is not ready to be a husband yet musmn ayanxu daya saka zancen karatunsa agaba,
toh inaga kuma yarinya ƙarama yar nine years wacce batama san zancen me akey ynzu ba,yasan wannan wani nauyi kawai aka dora masa,da kuma rainon ƴa wanda aka laƙa masa akansa,saidai shi mai tsananin biyayyane ga iyayensa, shiyasa bai nuna komi a yanayinsa ba,kuma yake biye musu a duk da wayewarsa da ajinsa hakan bai hana ya amshe batunsun hannu bibbiyu ba..besides kawai auren aka daura musu ,ba'ac su zamto tamkar mata da miji aynzu ba,saidai yasan ixuwa wani lokaci inta Girma hakan zai iya faruwa,Nasiha kam sunshata awajen su innono da mutanenta da ta bawa waliyayyancin wasimé.
Yaga ba'aje koina ba har iyayensa sun kwallafa yarinyar aransu, jin cewa ita marainiyace babu uwa ba uba babu dangi sai innono.,innono tasa a hada auren da jininta ne sabida gudun hannun da wasimé zata iya fadawa ciki inta tafi ta barta awani wajen.
Yanzu da akay mata aure tun tana yar ƙaramanta ai zata iya zama a karkashin surukunanta harsai ta girma snn ta tare a dakin mijinta,
Sannan shima dahiru zai iya cika duk wani burinshi nayin karatu da zamowa duk abunda zai zamo kafin wasimé ta gama balaga ta mallake hanklin kanta,Koda bata sani ba, tasan dai rayuwar wasime na nan gaba bazai sangarta a hannun wani jininta ba.
Washe gari sassafe suka bar garin suka doshi hanyar cikin garin kaduna bayan an kammala komi na al'ada.
Innono da danta Qasimu da matarsa sai amarya da ango wanda haryanxu acikinsu wani baice uffan ma wani ba,ya zamewa taheer jiki shi baiya saƙe fuskansa da kowa,da wuya kaga dariya akan fuskansa ko murmushi zaiyi baxai wuce na gefen baki ba.
Shi wani irin murdadden mutum ne dabaison cikia magana bare zancen shirme,yana da ƙarfi da izza,shiyasa Arayuwansa Yake mutuwar son yay millitary school ya dawo land army amma haka firrr iyayensa suka hanashi.
alhj Qasimu da matarsa
Sun nuna kamar likita kawai sukeso ya zamo,amma son da sukeyi wa dansu yasaka suka ƙasa yankemai babban burinshi na sob zama soja dan wani son zuciyarsu,Shima anashi fannin son dayake ma iyayensa yasaka ya ƙasa yankewa kanshi hukunci Dan a duniya babu wani abunda yake tsananin ƙauna yake kuma darajawa kamar iyayensa
Kaunar da yake musu yasashi yafara pursuing careersa ta zamowa likita, amma likitan sojoji.
Wanda Yana kammala sec schl 'dinsa at age of 16yrs ya samu scholarship mai kyau bisa kwaxonsa a NEET exams da suka zana na xuwa military school india,HPSP wato health profession schorlaship program ita ta dauki nauyinsa tana biya masa kudin makarntarsa harya kammala karatun nasa a india cos is just a 4yrs alkcin,ynzu haka baifi wata biyu da dawowarsa nigeria ba.
Har ila yau Mahaifinsa ne yaketa kkrin nema masa wata dama A "NAMC" nigerian medical millitary corps service,dan yayi 2yrs medical functions, wanda daya kammala zasu turashi can USU (uniformed service university of health) dats the national medical center in bethesta maryland,acan washintong D.C,inda zai ƙarkare karatun nasa sann ya dawo gida mai gaba daya.
Dukkan wani jajircewa da tanadinsu arayuwa wa dansu taheer kawai sukeyi shima dukkan soyayyarsa da biyayyarsu naga iyayensa,sunada burin bashi ingatacce kuma tsaftacacciyar rayuwa dake shine kadai Allah ya azurtasu dashi a duniya,Mahaifinsa al'Qasim baida wani sana'a face saida siyarwan motoci, ita mahaifiyarsa kuma malamar jamia ce amma yanzu tanata kokrine domin shiga matakin farfesa a fannin mecha-tronics and electrical engineering.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top