proloque
PROLOGUE
#Surayyahms
*FITAR RANA...*
_......faduwarsa_
Alhamdullahi rabbil Aalameen.This is a short, hopely amazing story of a witty-smart girl wasimé Aliyou in her love_hate relationship with her biggest critic yet wildest fantasy,i hope u'did enjoy it.thanks!😘
BISMILLAHIRRAHMANIRAHEEM.
6:15pm Bunu: Shammo cluster,east language of kainji,toro L.G.A bauchi state.
Lokacine da almuru ya ƙeto gab gabotawar sallahn magriba. wata ƙibabbiyar matace wacce a shekaru bazata haura sama da arba'in ba, kalar fatar jikinta ɓaki kirin ta ƙife irin fallen zanin atamfar dake jikinta akanta tayi lullubi dashi har saman idanunta tamkar wacce bataso a kalli tsananin munin fuskarta, dauƙe take da man fetur da kuma ashana ahannunta, ta tsaya a ƙofar wani matsaikaicin gida ginin blo dayajima sosai duk ya balangwaje ya tsofe ginin ya karsashe wanda ana taɓa bangon ƙasane kawai ke zuba.
Daga cikin gidan Babu abunda ke tashi acikin dan tsurkukun dakin nasu sama da zautaccen bugun sautin wahalallaleyar numfashin mace wacce amonsa tayi kama da kamar ranta ake zarewa acikin tukikin ciwon naƙuda mai azabtarwa da kuma radadi,ita kadai sai murƙususu takeyi acikin dakinta tana tauna laɓɓanta tana wayyo Allahnta amma kashh!! shiru kakeji babu wanda ya kawo mata doƙi.
Bisa Kallo daya kayiwa matar zaka fahimce cewa bazata wuce kimanin shekaru arbain da takwas a haife ba,murmurarreyar mace ce mai ginannen jiki wanda duk da alamun wahala da talauci dayayi mata naso ajikinta da kangon dakinta bazai taba hanaka kallon kyakkwar surar halitta da Allah yay mata ba.,ba kuma ina nufin tsantsar kyauna kwatantacin siffar ƴayan aljanu ba,a a, .ina nufin itama baqace sidik original melanin beauty, mai dauke da natural skin na matanmu na mutan _biu(a jahar maiduguri)_ tabbas matar nan ta mallaki sulbabben sheqin fatar su mai kyau da daukar ido,game da dirarren shape da baƙin suman kai dai dai cikon misali.
Har kwatankwacin Misalin tara na dare amma haryanzu shiru,iska ne ya cigaba da kadawa sakamakon yanayin damina ne duhun inya rufa har ba a iya kallon hasken tafin hannu.
Matar can tana waje,mai naƙudar nan itama tana cikin gida tana kkrin fidda nishi,kuma Dukkansu basu rusuna akan qudurorinsu ba.
Duk wani addua daya fixgo kanshi cikin bakinta da zucyarta yinshi kawai takeyi danta samu saukin azabar naƙuda datake sha ajikinta dan kuwa yau Shekarunta 30 kenan da yin aure a duniya amma bata taɓa samun haihuwa ba sai a wannan ƙaron da jiki ya riga ya ragwabe tsufa kuma yaxo mata rayuwa ya kuma musu tsanani ita da mijinta malam hassan(aliyu) denge a hannun muguwar amaryasa Anmuna.
Maimunatu garba,
wacce akafi sani da Anmunah mayya yar gidan garba maye ta kasance tamkar wata mujiya ce acikin alummar shammo ta kabilar ribinawa a jihar bauchi, kasancewar zargin da akeyiwa mahaifinta nacewa shi mayene Shekara da shekaru bacin duk wani alamu sun nuna hakan amma rashin ƙwakkwarn shaidu shi ya hana a gurfanar dashi.Qaddara shiya janyo aure tsakanin anmuna da malam hassan mijin badiatu wanda tunda suka ƙafa alƙalmin tarihin zaman auren su basu taba sabawa juna ba,mutane ne masu tsantsar hkuri da juriya tare da takantsantsan da rayuwarsu gameda kyakkwar zuciya,a tunanin su kawo anmuna cikin zamantakewar su zai iya jawo musu albarkan haihuwa bayan tsawon shekaru da sukaja basu samu ɗa ko ƴa ba,anmuna takai shekaru sama da arba'in babu wanda ya taba taya aurenta sabida halin mahaifinta na maita,acikin tsangwama tay rayuwarta,malam hassan da badiatu ne kawai suka tausaya mata, amma sai abun yazo musu da sabuwar qaddara wanda basu tabayin tsammanin cin karo dashi ba.
Dan kuwa tunda anmuna ta shigo cikin gidan su da sunan aure yau shekaru goma kenan malam hassan da matarsa badiatu suke cikin tasƙon rayuwa mai tsanani.
Duk wani albarkan Rayuwarsu saida tayi fatali dashi,ta talautasu ta muzanta su,tayi zaman diris akan dukiyarsu sannan ta sassaka musu ciwuka kala kala ajikinsu.
Tunda badiatu ta same wann cikin yakasance malam hassan bayada wani kwanciyar hankli
Yaushine nan gobe shine can duk dan ya ƙare matarsa badiatu daga mummunan kaidin anmuna,ahakan ma da ikon Allah ne kawai sukaci nasara dan kuwa tasha alwashin dauƙar ransu duka inhar ya sake badiatu ta haihu mata acikin gida.
Yau tun safe ya fita neman taimako awajen wani babban malamin addini dake taimaka musu sosai wajen ƙaresu awani dan kauye,duk hanklinshi baijikinshi, ya tafi yabar badiatu cikin ciwon ciki yasan izuwa yanzu ta galabaice,yana amsar magungunan da malam ya damƙa masa ya kamo hanyar gida cikin gaggawa,tafiya yake kamar zaici da baki tsabar sauri amma sai yaga kamar ana komar dashi baya, ko yayi lalume yaga ya ɓata a jejin,gaba daya saiyaga ya ruɗe hanyar ya bace mishi baiya fahimtar inda ya dosa,ko haka kawai yaji ya firgita,wani sa'in ji yake anai masa maganganu marasa ma ana masu kuma firgitarwa da tsaki mai ƙauri acikin kunnen sa,Ahaka dai ya danne xuciyarsa bai karaya ko yaji tsoro ba,Adduoi ya dingayi har Allah ya kawo sauƙin abin sannan ya soma fahimtar hanyarsa harya gabato ixuwa gida.
Goma shaura dot na dare saigashi ya iso kusa da kofar gidansa inda baifi taƙu ashirin haka yakai inda matar can take ba,kirjinshi na tsananta bugu duk jikinshi na rawa cikin sauri ya hau warware kullin dake hannunsa kamar yadda malamin ya umarceshi daya shafa turaren dake ciki ajikinshi kafin ya gabatota hakan kuwa yay babu ɓata lokaci,shiyasa harya xo ya wuceta suduk cikin duhun dare bata ganesa ba..
Tari take tana zage zage ita kadanta "Durun uwa!!! wannan wani irin kazamin turarene haka?
Da addua abakinsa ya shiga gidan ya samu badiatu tana kwance cikin jikata harta fara ɓarin jini,tana ganinsa ta soma kkrin miƙa mai hannunta dake rawa rawa cikin kakkalallen murmushi mai mugun rauni ta riƙosa tace "Aliyu"..Aliyu harka dawo?..raunatattun hawayensa ne suka soma gangarowa bisa kuncinsa yanamai gyadamata kansa yanacewa "eh",agabanta ya durkusa bisa gwiwonsa duk gabobin jikinsa sun nakarkashe jikinshi baida wani sauran laka,wani malalaciyar numfashin tausayin kansu suka sakar ma junansu.
Rungumeta yay ajikinshi
Tsammm yana maida ajiyar numfashi muryansa can ƙasa sann yace "sannu...kiyafe ni Badi'atuh na..kiyafeni daya kasance bana tare dake a wann lkcin dakike matukar bukata...sannu kinji..Allah ya sauƙeki lpya yar aljannata...kanta kawai ta iya gyadawa cikin ciwo...Ya dauƙi shauran turaren ya shashhafa mata ajikinta itama,yabi ya hada ruwan maganin daya amso awajen malam ya bata tasha wasu ya wanketa dashi dan malam ya gaya masa aljanu ke azbtar da ita ba zallan ciwon naƙudar ba,Aikuwa tana shan maganin gadan gadan saiga ciwon naƙuda ya tasomata babuji babu gani,da murƙususu da komi haka badiatu ta sauka lpya cikin ikon Allah ta haifo lafiyayyar ƴa mace
Wacce ta debo kamannin uwa da uba batada nakason komi.
Malam hassan(aliyu)tuni ya zauce wajen kallon yarinyar dake cikin jini rauntattun hawayensa na diga yuuuuuuuu akanta tamkar koramar datayi ambaliya,bakinsa dake karkarwa babu abunda yake furtawa sai Allahn sa "Alhamdullahi rabbil samawati wai al'ardi...ya rabbil alameen,anta noorul samawati wama fi hinn,Rabbil arshill azeeem.Allah maiyi duk yadda yaso a kuma lokacin dayaso,yah Allah nagode maka!!Allah nagode maka,ya rungume yariyar tsam ajikinshi yana mai fidda sautin kukansa mai cike da gamsuwa da ni'imar da Allah ya saƙa musu dashi daya azurtasu da haihuwa sakamakon hakuri da juriyarsu tsawon shekaru 30 da aure.
Cikin kalilin lokacin suka tsaftace kansu da diyarsu wacce taci sunanta.."WASIMÉ"
Ma'ana wani kyautar karramawa mai girma kuma ta musamman daga wajen ubangiji,
kalman "wasimé" yana nufin "the mercy of God", as distinguished from His justice;a divine love or pardon,a state of acceptance with God.
Tare da dayar ma'anarsa dayake nufin "Sa'a,(fortune)or someone who helps odas selflessly,divine beauty or lets say graceful nd preety..
in greek philosopy wasimé is a historical name of 3 beautiful sister goddesses
(Aglaia,euphrosyne,and thalia) represnted by ancient writers for apollo nd ofteners of venus and are regarded as inspirers of good qualities like wisdom, love nd social spirits.Kalman wasimé har ila yau kalmace mafi daraja ga masarautar england as thy often refer to their dukes nd dutchesss with its kinds.
Sunan da suma suka zabarwa yarsu kenan sabida su nuna wa Allah godiyarsu,Saidai ciwon ciki da xubar jini shiyaci ƙarfin badiatu ayanzu,
babu yadda malam hassan baiyi dan subar wajen akan lokci ba amma ina duk kkrinsa yaci tura gashi malam ya gargadesa da suyi maza subar gidan kafun anmuna ta hankaro
,Saidai akowani dakikanln wucewar lokaci jikin na badiatu dada rakwabewa yake daɗayi..."yarinyarsu wasimé da suka nannade acikin zani tana baiwa nono ta fincikota a hankli tana kallonta idanunta na fidda kwalla ta damka masa ita a hannunsa ,ɓari hannunta yake alamun ta jikata muryanta na fita a rarrabe cikin wahaliyar
Tace"Ali...Al...iyu ka tsira tare da wasimé,kayi sauri..sauri kuje kakaita matsera sann kadawo gareni...Aliyu ka..kkaje bamu da lokaci..kar mumm..mujefa rayuwar yarmu da batasan komi ba acikin ukubar maimunatu,kanaji na kuwa Aliyuhhhh?..Ya rasa abun da zaice mata sai kukan zuci dayake rabzawa,ahnkli ya rungume ƴarsa a kafadun sa hannunsa saƙale dana matarsa yana murzawa a hnkli
duk jikinshi na rawa,can ya miƙe tsaye kamar an tsakureshi yanata kallonta da raunatattun idanunshi wanda sukayi naso da kaunarta yanaji kamar zai hadiyeta,wani wawan shauki ya kuma yunkuro da shi ya gurfana ajikinta kamar sabon mahaukaci wanda baiya cikin hayyacinsa Tare da sakar mata wata shaukakkiyar runguma mai tsuna yanamai sumbatar koina ajikinta araunane
"..muryan sa a dishe yake cewa'..Badiatu kiyimin alkwarin zaki jirani kinji?...bazan daɗe ba wannan karon zan dawo gareki badi'atu..nayi miki alkwari rabin raina...kijirani anan kinji badi'atu na...ta gyada kanta a hankli tana sumbatar sa,wani
Murmushi mai taushi suka sakar ma juna sannan ya share fuskarsa ya share mata nata itama,nan yay ta maza ya saɓi jinjirarsu a kafadunsa ya shafa musu turaren sannan suka doshi hanyar yamma..,lkcin ana neman ƙarfe 2:00 na dare
Cikin murkususun ciwon cikin badiatu ta kasancel mai tsananin azabtarwa.
Malam hassan kuwa bai tsaya ba tafiya kawai yakey acikin jeji burinsa baifi yaga ya iso wani dan ƙaramin gari da ake ƙira Ringin gani ba.
yadda ya rungume jinjirar babu abunda yake jansa sai amon sautin murya matarsa dake yawo akansa yana ƙara ma zciyarsaa rauni da ƙarsashi.
Hudu da rabi shaura na dare ya iso ƙofar wani gidan ƙasa wanda ya samu kofar zaurenta a buɗe shiga yayi cikin sauri zuciyarsa tamkar zatay tsalle ta fice daga kirjinsa,direct kofar wani rumfa ya shiga ya kwankwasa sau daya sai gashi an buɗe kofar.
Wata matace sanye da hijabi dogo har ƙasa,ta fito hannunta riƙe da carbi,da kuma fitilar obasanjo ya gaza tana mai ƙare mai kallo cikin mamakin ganin yanayin sa..muryanta kamar na wacce zatayi kuka ganinsa da jaririya a hannu ta dada kwalo idanunta waje tace "Tubarkallahu masha Allah Aliyu har badiatu ta sauƙa? kun iso ne toh ina ita badia'atun take?
..gani tayi yay shiru dik ya kasa furta wata magana lkcin numfashin shi ma sama sama yakei kamar zai dauƙe ya rabu da jikinshi, da kyar maganan ya kufce masa bacin kuka mai tsuma da tsofuwar ta sakar ganin duk ya gigice. Aliyu lpya kuwa?a hnkli yace"umma na ki riƙe mana wasimé amana ni zanje in dauƙo badiatu a shammo!!
Umma nabar badiatu cikin ciwo...umma saina dawo!!!..."gyada kanta kawai take tana hawaye tanacewa toh toh toh Aliyu kayi maza ka jeka Aliyu Allah ya ƙareku gabadayanku ya dawomin daku lpya.
Allah yay ma wasimé Albarka tana magana tana kuka sosai...harya juya zai bar wajen sai taga ya juyo ya riko hannayenta tare dana babyn Ahnkli yace "umma inbaki ganmu ba Wasimé takice har abada mun barmiki ita amana!!umma kiyafe min dukkan kuskuren dana aikata miki arashin sani ki kuma yafewa matata badia,!!kanta take girgizawa cikin kuka"zaku dawo Aliyu,kadena fadar haka kaje ka dauƙo badia insha Allahu zaku cinye wann jarabawar,baice komi ba ,tanata magana harya bar wajen bata sani ba sabida kuka mai taɓa zuciya da tausayinsu da ya mamayeta.
Malam Hassan ya kasa hakuri yayi tafiya bisa sawunsa aguje kamar sabon mahaukaci
Ya yanka cikin jeji duk jikinshi babu guzari amma shaukin son ya tseratar da matarsa yasa yakejin kanshi kamar su wani lafiyayyen doki,
Idanunshi da suka sauya suka dawo jajawur suna fidda sassanyar kwalla,
Babu abinda yake ambata sai Allah sai badiatunsa..
Daf Ƙetowar alfijir Allah yay isowarsa shammo ganin cincirindon ciyayi a kofar gidansa bai hanasa ƙarasawa ciki,bai hadu da kowa baa har ya iske badiatu zaune akan tabarma ta jingina bayanta da bango tana layi cikin wani mayuyacin hali,baiy wata wata ba ya dauƙeta cak ya saɓa ta a bayanshi ya goyeta da murmushi akan fuskanta ganin ya dawo mata, ta kuma san ƴarta wasime ta tsira kenan na har abada,lafewa tayi a bayanshin tayi lamo banda sunansa babu abunda take firtawa acikin numfashinta, yana kaiwa bakin kofa da zasu fita sai kofar ta kullesu kirif taciki.Tun yana kkrin budewa da badiatu a bayansa harya gaji ya sauƙeta ƙasa yay iyayinsa amma kofar sam taki buduwa ya rasa abunda yake masa dadi, jin da yay kmar ana riƙe masa kafafunsa ta baya yasaka shi ya juyo gani yay badiatu ta riƙe kafafunsa kamar mai neman gafararsa.
Cikin wata wahalliyar yanayin nishi da murya dake fitowa da kyar tace "Aliyu kashe mu zatayi..Aliyu kashe mu zasuyi ita da baba garba...kabar wahaldakan ka kaxo muyi wa Allah godiya akan ni'imomin sa daya dora akanmu,ko kasan jarabawa nadaga alamar soyayyarsa?Aliyu inaa fatan nay rayuwa ta dakai a aljanna,kai namijin kwaraine abun alfahari,Ina fatan Allah ya bamu wata kamar ƴarmu acikin aljanna, Allah ya sa muyi kyakkyawan ƙarshe Aliyu.
Jikinshi a ragwabe ya zuɓe ƙasa kanta a gurfane ya rungumeta ya kuma dukunkuneta ajikinshi suka gamutsa tare Shida ita a waje daya.cikin muryan lallashi Yace'Badiatu karki cire ranki mana ga rahman ubangiji,ikon Allah fa da girma yake wani mutum ko aljan bai isa ya dau ranmu bada san ran ubangijn mu ba,shiya fidda ibrahima acikin wuta,ya ceci musa daga kaidin fir auna sannan yonousa ya rayu bayan kifi ta haɗiyeshi.
To ke kuma Tsoron me kikeji badiatu?.."
numfashinta ta fetsar waje"aliyu ba tsoro nakeji ba jiki na ne yake bani cewa hala bazamu iya kufcewa wnn
Qaddarar ba.."zata ƙara furta wani kalman taga ya yunkuro ya rufe bakinta idanunsu cikin na juna yace"kiyi shiru karki ƙarar da ruwan jikinki,kina bukatar ƙarfi badiatu,kanta ta gyada sann ya kwantar da ita akan faffadan kirjinshi ta dan lafe tana maida numfashi,sunfi minti uku ahakan snn ya dagota a hankli ya miƙe ixuwa baki kofar dan ya ƙara jarrabawa koxai budu
Kalman shahada ya rinƙa maimaitawa yana ambaton Allah a fili da acikin zuciyarsa,
Bismilllahi ya furta yanamai miƙa hannunsa ixuwa taɓa mamurdin kofar,cikin kiftawar ido da bisimilla wata ƙara mai gigitarwa kamar na nakiyar bomb ta cillar dashi baya ya fado ragwab ajikin badiatun sa matacce,lumshe idunuwanta tayi tana kkrin furta kalman shahadar itama ayayin da shauran ginin wajen daya bangaro sakamakon girgixan da dakin yy ya ragaxo mata akai ya ƙarasa ta, bayan haka hayakine da gobarar wuta ta gamutse wajen suka ƙone kurmus.
Agaban maimunatu da mahaifinta garba maye komi ya faru,suna kallon wutar yanaci balbal suna dariyar mugunta tamkar ma zasu saka ruwa a ƙasa susha sabida su suka shirya komi ya tafi cikin samun nasara.
Duk wani abun da suka hanɗame na gonaki da dabbobi da rumbunan abincin hassan da badiatu dashi suka cikawa rigarsu iska tunma kafin mutanen anguwa su hanƙara da abunda suka aiƙata.
Daga kauyen ringin gani kuwa matar datake riƙe da jaririyar su ganin har safiya batagansu ba yasa jikinta yay mugun sanyi,dan tamkar ɗanta na cikinta haka takejin aliyu dik dama bata haifesa ba rainonsa kawai tayi, xuciyarta sosai ya bata cewa tabbas wani mummunan abune ya afku dasu wanda yay sanadin rashin dawowarsu ga ɗiyarsu, dan dama tasan da wuyane, su iya fidda kansu a ƙaidin shaharren matsafi kamar garba maye da shaidaniyar ƴarsa anmuna.
Bayan ƙwana bakwai da afkuwar komi matar nan ta dauƙi jaririyar nan acikin mafi sirrikan lokacin dare suka yi hijira ixuwa garin jos,inda ta nemi haya acikin wata ƙauyen makiyayan fulani ,anan tay zamanta ta raine Wasimé,har ta girma. ranar da wasimé ta cika shekaru 9 a duniya anan ta ƙara hada kayansu a jaka da zimman kaita inda xatayi rayuwarta na dindin .....
SHARE SHARE PLS.
ATAIMAKA A SASSAKA MISHI COMENTS Lovely fans💯💕🥰💃
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top