part
FITAR RANA11
Tashi kawai saheb yay zai fita a falon wayarsa ta hau ƙara,hakan ne kawai ya tsayar dashi ganin sunan zee baby na yawo akan screen din yasashi limshe idanunsa dan har wani tsoron dagawa yakei sabida baisan mezai ce mata aynzu ba.
shikansa yasan babe din ta mummunan saka ranta akan TEJ gashi abun baiyu masa a yadda yaso ba...
kiran na yankewa ta sake ƙira bai daga ba after like 3min saiga tolu ya shigo falon a raƙube ya tsaya daga bakin door sabida kallon da taher ya watsa masa na debar albarka
Tuni yy baya baya Yana wani abu sum sum kamar tsohon munafuki
Shikansa yasani cewa kayan jikinshi sam basu dace dayana yawo dasu acikin gidan ba,wando ce amma ta jean,kuma three gtr ce wanda aka datseta da almakaci. gata ta matse shi tagaban inda shatin burarsa take tayi baja baja bata da wani zip din kirki duk ya kayayyade ta da igiyan tsumma.
Kafafunsa harna rawa ya furta"Gud mrng sir
Ya rusuna kai yana gaishe da taheer with full respect wanda ko lokacin sake kallansa bai karayi ba bare ya amsashi, juyawa yy ya kalle saheeb ya gaishe sa shikam ya amsa cikin mamaki yace lpya?..
cikin ynayin sosa kai tolu ya kalli saheeb dib directly yace"oga one fine madam dey look for u for outside gate.
Saheeb ya haɗe rai yace "are u sure its me?..
gyada kai tolu yy yace "yes sir..
Baice komi ba ya juya baya yana cizon yatsa cikin kunkuni yanacewa
"Shit...ynxu bby bina nan tayi?
Taheer dake jinsu yana shiru baice uffan va..
Tolu yace sir mekai tellam say u dey come ba?
saheeb ya juyo a take yace yeah..kace ta jirani awajen
Wani juyi da ido Taher yay cikin dakewa yace "mene?..
Shima bata ransa yyi
Yace " zee baby ne tazo tana waje ko zamujene ku gaisa ne?
..da wata matsiyaciyar harara yabisa, yace "To kaje kace mata tabar kofar gidan nan dan nan ba gidanku bane.
"Saheeb bai kulasa ba kawai yay waje ransa a dan dagule..yanata mita shikadai har ya isa bakin gate din ya bude ya fita
Tashi taherr yay yabi bayansa dan Allah ya zuba masa zafin rai har baiya iya controling kanshi,sauri yakei amma kafin ya fito ya samu saheeb har ya wuce can waje ya iskesu
samun zee yay tare da wasu hadaddun yan mata sun cika mota ga uban loud music na tashi aciki suna wani ihu irinta yan mata masu tasowa marasa da'a da tarbiya
Zee Tana ganinshi ta sauko aguje ta zo ta wani rungemsa tana wani irin karairaya jikinta tana langwabewa ajikinshi"shafe sajensa tayi tana cabbulan fuskarshi da wani irin salon dayafi karfin dan shekarunta dabazaifi sha takwas ba"awwnn baby!! yane inata kirar wayarka baka daukawa..dan tureta yy kadan daga jikinshi snn yace"babe u need to go right now?kuje club zanzo in same ku acan.
Wani ja da baya tayi a harzuke kamar an dana ma zuciyarta garwashin wuta daya furta hakan
'Babe me kake nifi da zakazo ka same mu?
Shi Tej din fa?
Shiru yyi bai bata amsa ba"...kedai kije mana! banace zanzo ba? Da dan ƙarfi ya mannota kirjinshi ya janyota kusa inda zata kalli cikin kwayar idanunshi ta gane cewa he is not joking abt it yace "see babe,i dont want him to come out nd find u here kinsan gidan su da akwai doka nd not evryone is alowd here...
You understand?
Ture hannunsa tayi game da fashewa da tsinannen Dariya irinna rainin wayo
Din nan,Baya taja tana hararsa snn ta juya ta kare ma gidansu taher din kallo cikin yanayib gatsine
Gani tay ko gidan P.A din ubanta baikai ba,gidan ubanta kuma ya taka wann gidan nasu sau hamsin a kyau da tsari da komi da komi.Yanzu akan wann tsukukun gidan ne har ake saka wani doka?..
Adaidai lokacin data juyo ta fadi wannan kalman tej ke fitowa daga gidan su tare da wani shirgegen belt din sojoji a hannunsa ya riƙe fuskansa bada wasa ba yana dosuso da no nonsense face dinsa
dama shi kowa ya shedesa da akwaishi da saurin kufula abu kadan ne yake irritating nasa yaji ya tsana abun har abada,kamar yadda ya tsani dabiun zee kamar mutuwarsa..kuma harga Allah baison harkan saheeb da zee amma saheeb sam yakijinshi wai kawai shi ita yake so.
Zee tana kallonsa ta wani ja da baya ta ƙime ta dora hannunta a kugu tana zuba yauqi tana wani gatsine up and down wai ita gata babban yarinya wacce bata shayin kowa.
Saheeb ya dora hannunshi a goshi ransa a mugun dagule yana kallonta ke waimesa bakijene"babe jeki mana..ki shiga cikin mota kawai kutafi
Wani uban harara ta watsa mai a fuska snn tace"haka kawai toh Akan me?kai bari kaji Inkana tsoronsa ni wallhy banaji.Dan haka babu inda zanje..inkaga na barnan to ganin damatace..ta karashe maganan cikin jiji dakai
Riko hannayenta saheeb yay yana kkrin janta cikin lallami yana cewa"baby please now.. Bafa wannan maganan akeyi ynxu ba just do wat i ask u to..
cikin zare masa ido da masifar karfin hali ta fauce hannunta Tace
"nace baxan barnan bako,dokan kirjinshi tahauyi yana matsawa baya baya"..matsoraci kawai!Saheeb kai wawane tufff,banza..jaki kawai!kare..doki!
taheer dake tahowa yanajinsu take idanuwansa suka sauya kala sukayi wani jaaa danji yay kamar washi aka watsa ma wann zagin...
matse lababbansa yycda ƙarfi yau Da kuwa shi ne ta zaga haka da saidai uwarta ta haifo wata mai kamanta amma ba dai ita ba.
Saheeb kam ko ajikinshi yanata kkrin controling nata ita kuwa sai dada hawa takeyi tun abu na cikin fushi sai tamayar da abun ya dawo kamar wani kokawa a tsakanin su,yana tattaro hannunta tana fixgewa,tana zaginshi tana kaimasa duka yana kaucewa.
A daidai wann gabar dukka kawayenta suka sassauko ƙasa kowacce da kalar barazanarta dukkansu su daddame jikinsu da kananan kaya
kallo daya kamasu ya isheka ka fahimci cewa ƴayan masu shine ,kuma sakaltattu yan gata,dudu dai bazasu wuce shekaru 17 zuwa 18 ba dan ko zee din datayi girman jiki sosai bata gama cika shekaru sha takwas din a duniya ba,Wanda isowarsu yay daidai da isowar taher wajen"
..wai meyeke faruwa anan ne?daya daga cikinsu ta tambaya tana wani gatsine tana turo kirjinta dayaci uwar acucin dunlop bra gaba
Cike da hade rai taheer ya kallesu."Cewa nayi kubar kofar gidan nan yanxu yanxun nan koda matsala ne?Taher na bata amsa dukansu matan suka zubamai idanu kowacce da kalar kallon datakemishi
Gabaki daya Farin fatar namiji kabila daban take wajen dauƙe ido,ga taheer agabansu ya hada komi da komi na cikakken namiji, jarumi, kuma kyakkwawa, wanda ko dan sarkin saudiya aka ƙirasa dashi ai zai amsa sunan sabida ya cika kota ina!shi hasken sa ba dau bace tay wani irin pale yellowish colour mai daukar hankli gata tana sheki yana glowing kamar kullum ne ake wankesa da madara
daya daga cikin babes din ta zubawa gefen wuyarsa idanu tana kallon tsantsar freshness da kyaun kalar fatar wajen kamar xata shanyemishi jini...
Daya kuma tsantsar hasken hannayensa da kafafunsa kawai take kalla...
Juyowa saheeb yay yace "guy pls dont do this"
Kabarsu yanzu zasu wuce.
Ransa a ɓace yace
'right now!
cikin runtse ido Saheeb yace guy waimesa kakemin hakane?nace maka thy r leaving..why me?
Yace"saheeb this Is not my wish but my compulsion"ai nafada ma,banason tarukucen mata musmmn ma irin wayannan..in suna son ganinka sunsan inda zasuje su sameka amma not here infront of my parents house.
Tuni xee baby ta caɓe maganar cikin masifa da nuna izza tana wani hura hancinta cikin zafin zcya
.."aikin banza aikin wofi..Da makaho ya rasa ido ai dole yace ido da wari ana wani jiji da talauci da tsiya?meye wannan?ni fa banga gida anan ba, akan wannan
Dan tsurkun gidan ne har za'a mana iko sai kace gidan gwal..
Toh dakai da gidan naku sai insaka a walakntaku..
Kaji ko taheer?...yatsa ta nunamai cike da bushe idanunta"...Kasanni kuwa..i think ure yet to knw who i am,am the unshakable zee...bana gudu bana ja da baya kuma tsoron kowa...yau inna ga dama saina saka anrushe gidan nan mark my words,sainasa anmaida wannan ragajajjen gidan naku ta dawo toooka...
Bata ƙarasa zancen ba taji saukar wata gangariyar mari wargajaujau akan dandamalin fuskarta
Layi ta soma yi,snn jiri ya debeta zai kwaɓata akasa kawayenta suka rirriketa,suna furta inna lillahi,zee dake riƙe da kanta Bata taɓa sanin cewa dagaske ne ana iya kallon yan wuta suna tsinan wake sabida zafin mari ba saiyau, kuka ta saka mai ƙara hannunta dafe da kuncinta.
kawayenta duk ransu ya ɓaci zasuyi magana kenan ya bisu da wata tsawa
"No one is talking to u bitches! Wata ta yarda tay magana anan saina tattaka ta.
A lokaci guda gabaki dayansu suka rife bakinsu suka tsuramai ido..
Babu abunda xee take sai rabza uban kuka jini da majina duk sun wanke mata haɓarta
Saheeb ne yajanye hannunta cikin sauri suka doshi inda motar su yake ya bude ya jefata aciki...wani irin kuka ta kara fashewa da shi
Ta kallesa da jajayen idanunta,acikin fushi mai tsanani tace sakarya kawai!Wallahi saheeb saika ramamin
Ko ni inje in rama dakaina
Juyowa yy ransa a bace
Yace "shut the hell up.
Meya hanaki ramawaa dazu?
Shiru tay tacigaba da rabza kuka kamar andaketa
Taheer Yana huci ya juya ya kalle kawayenta daga can nesa inda suka tsatsaya tsuliyarsu a zage, Bulalansa ya kuma zargewa ya faudeta wa iska tayi kara feewww
"snn ya haɗe ransa yace ku kumafa?ubanwa kuke jira anan?ko kuma zakusa a rushe gidan ne in zazzane ku?
Daga wann ta kalle wancan sai wannan ta kalli wancen atare duka sukayi yaƙen fargaba.
Turancin karya kowa tasako saiji kake ana "no..issakay...sai anjima bros!kaga tafiyarmu
Tsaki yaja snn ya koma ƙofar gidansu ya tsaya kikam yana kallonsu har suka tada motar suka tafi.wani fuuu ya wuce cikin gida Ko ajikinshi bai damu ba dan sunsaba indan wannan ne.
Yasan in akayine saheeb yace zaiyi zuciya ya shareshi kwana biyu bazai masa magana ba.
.kada kafadarsa yay irin kodata faru baidamu ba..dakinsa ya nufa ya dauƙi jakar karatunsa snn ya bar gidan,barrack din sojoji ya dosa inda ake musu cikakken medical classes dinsu
,bai dawo ba sai wajajen tara na dare
Samu yay har an kammala dinner,yau bilti tay wani lafiyayyen tuwon eba da miyar egushi da yaji barkwano da dagedagen kifi, dan kadan yaci snn ya koma dakinsa yacigaba da koyan zanensa,dan aranshi so yake yaga yay kkri ya jajirce snn yafi kowa kwarancewa a fannin sanin tsala tsala na gangan jikin dan adam da kuma dukkan wani jijiyoyin da suke cikin kwakwalwa.
Karatunsa na farko dayay acan baya general surgery ya karanta a can makarntr su ta sojoji,shekara hudune kacal,yanzu kuma ya dawo takan area of specialization dinsa which is neurosugeon
Wato likitan cututtukan dake cikin kwakwalwa.
Wanda shine ahalin yanxu yafi kowani course a medical line wuyan sha'ani..ba kowa yake iya jure yinshi ba sai daddaya.
Burinsa arayuwa shine ya zamto "surgeon general" kamar yadda suke ƙira a a fannin sojoji.
Cos Thats when u wll be the most fast_fowarded physician,nd perfom life saving treatment while at war field.nd also combat diseases with immidiete effect so that soldiers will progress to the next health care level.
Bayan haka Kuma araywansa yana son yaga yay kudi,He really wants to be rich, ko dai ince to lead a peaceful nd comfortable life with his family.shiyasa aransa bai taɓa tunanin zai ƙarayin wani aure ba dan kwata kwata baida ra'ayin auren mata biyu
Tun yana dan yaro ya kuɗurta hakan a zciyarshi kuma haryau wann burin nasa tana nan, Kullum insuna hira saiya fadawa mamansa shi mace daya kawai zai aura kamar dai yadda yaga baban sa
Qasimu yy,yaji ance mace daya babansa ya nema arayuwarsa kuma itace wannan mahaifyarsan daya aura.
...shikuma sai gashi abun Baiwanizo masa cikin sauki ba,gashi wai har yay auren,da kuma unkwn girl a lokacin da bai taɓa yin tsammani ba,ya dauka rayuwa zata aramai lokacin dazai tantance matar dayake so a zuciyarshi ne snn ya aureta suyi rayuwarsu mai tsananin dadi mai cikke da soyayya da sassanyar shakuwa.
Saidai tunda lamarin nan yafaru tsakaninsa da wasime tuni yafadawa zucyarshi weda he likes it or not wasimen ce dai kawai matarsa ta har abada.he most have to learn how to love her danshi gani yake kamar baida zcyar da zaiso mutane biyu equally..
Dan sosai ya fahimce kalar zuciyarsa,aganinsa zucyarsa wawiyace bata iya son abu ba,kamar yadda bata iya ɓoye ƙiyayya ba..zcyarsa inta tsane mutum toh fa bata sarara masa.
Shidai koma yayane shi zaiyi hkri da wannan qaddarar daya riga ya doreshi da wasimé ya kuma saka ta zamto tamkr rabin jikinshi.
He neva expected this but its ok..ai yarinyar ma is not dat bad ta fuska
Halayyarta ne kawai bazai iya cewa komi akai ba...Dama can shi baida wani babban buri ajikin ƴa mace, baidamu da sai ya samu tsaleleya kyakkywa ko doguwa fara maya yar wace da wane ba
All he needs is a simple pretty girl dazata masa biyayya snn ta kula masa sosai da iyayensa ababen kaunarsa,shisam baidamu da kyan mace ba tundashi din kyakkwane sosai.
Ƙarfe biyu da rabi na dare yau yay bacci.bai farka ba sai wajen to six ƙarar alarm clock ya tadashi lokacin har an fito daga sallan subh,a cikin sauri ya tashi firgit ya shiga toilet ya doro alwala yazo ya gabatar da sallahn nashi a dakinshi
Shikadai
Yau da wani irin nishadi da murna wasime ta farka,yau zasuje yawo da amininta yaa saheeb,yau ji take kamar hajji za'a kaita ta shafo dakin ka'aba,tsabar doki da diddiri yau batayi wani gamsashen bacci ba.
tun ana kirar asubahin
Fari ta farka ta sauko daga kan gadonta ta kwashi kayan datay fitsari ta dukunkune su ta yo dasu hanyar fita waje ,acikin sanda take tafiya babu ko takalmi akafafunta.sadaf sadaf tasaci jiki don karma bilti taji motsinta ta farka ta bude kofar baya a hankli dan karya ƙara tayi waje,da sauri taje bakin tap ta kunna kan famfo sai shaaaa ruwa mai sanyi ya soma zuba,wani jan zcyarta tayi sama jin tsabar snyin ruwan,tsugunawa tayi awajen kamar yadda ta saba ta hau wanke kayan fitsarinta ta,saidai yau bata wani dade awajen ba ta dawo cikin gida.
Lkcin babu kowa koina yay shiru,dan Daga ido tay sama snn ta kalle agogo taga ana neman karfe bakwai na safiya ahnkli ta dawo cikin dakinsun toshe da bakinta sabida iska tana ɓari barin sanyi,jagwab ta jike jikinta da ruwan sanyi, numfashinta sai hawa da sauƙa yake ta kuma kakkame jikinta saboda muguwar sanyin ac dayake busa iska acikin dakin.
Kayan jikinta ta sauya cikin sauri izuwa towel snn ta miƙe wai zata shiga wanka,a daidai lokcin bilti tay juyi cikin bacci daga kanta keda wuya ta hango wasime na sauri sauri zata shiga cikin bathrum
A cikin gigin bacci bilti ta daka mata tsawa tace"Ke wasime?
..tsayawa cakkk tayi daga bakin kofar tana zazaxxare idanuwanta waje kamar wadda taci kudin aika.
Bilti ta dada murmusa ido ta kalleta da kyau snn tace"wai me zakiyi da safen nan?kinma yi sallah kuwa?
Girgiza kanta tayi cikin zumburo baki tace
'Nifa banyi ba tukun,ince wanka zanyi kafin ya iso!.
Cikeda sakalci ta karashe mgann tana wasa da yatsun hannunta.
Tashi bilti tayi ta zauna
"Kinci kaniyarki wasimé.
Kizo nan marar kunya kawai,da sassafen nan ne zaki tashi ko gaida ubangijinki bakiyi ba zaki ce wai zakiyi wankan jiran wani saheeb?Shi saheeb din ne yace miki asubanci zaiyi.Yanzu halama yana can yana baccinsa kuma bazai karaso ba sai can wajen karfe goma...ki wuce kije kiyi alola kizo kiyi sallah.Inba haka ba babu inda zakije.
Batasan sanda tafara bubbuga kafafunta akasa ba...murya kamar mai shirin yin kuka tace
Haba bilti,haba bilti
"Ɗan wankan ma?kaiiii bilti..warin fitsari fa nakeyi,..yanzu da kike cewa bazaizo ba inyay batan kai yay asubanci yazo faaa, basai kawai na saka sabuwar atamfata da matar Qasimu ta siya min in bishi ba?
Tsaye bilti ta miƙe sann ta capko hannayenta gameda buge mata baki
"Kewai meyasa bakida kunya?kina kirar sunayen mutane gatsau babu respect ko?uban waye kikaji yanace mata matar Qasimu?ehhh
Hannu ta dora akan fuskarta cikin muryan kuka dik tabi ta firgita
Amma bakin dai bai mutu ba"yo ni ai bansan sunanta ba..mezance mata!
Bilti ta dungureta
"Kice mata "mama" mana!Ita sa'arki ne? toh Wallh zamu saka kafar wando daya dake agidan nan inbaki shiga taitayinki ba wasime
Wani Zirrr hawayenta suka zubo kasa batace komi taja tayi shiru
Kije kiyi alwala kixo kiyi sallah,ahankli tace Toh snn ta ja kafafunta kamar mai ciwon aljanu ta shige cikin bayi ta kulle kofar da dan karfi ,kada kai bilti tayi snn ta bar wajen..sharp sharp wasime tayi alwala ta fito ta samu babu bilti
Dan haka batayi sallahn ba kawai ta shafa'a ta bude jakarta tahau fidda sabbin kayanta na dinkin sallah waje..
da akwai takalmin kwas kwas ma da jaka da aka siya mata,ita duk sanda ta debo su tana kalla sai ta dada shafasu..
Lallai matar Qasimun nan akwaita da kokari
Ai bilti tariga ta gayamata cewa itace tayi mata dinkin sallahn ta har kalaloli biyar,masu dan karan kyau.,tsadarsu ma bai dameta kamar yawansu ba.
Yatsarta ta cusa a bakinta tana ciza cikeda da tunanin zuci mai yawa
"Wayyoo Inaga yanzu tana can ƙauyensu cikin kawayenta su hansatutu da indodo da kuluwa dasu yar ficcika?,aiko da anga wankar cakarewa da caku gaye,wannan irin kaya masu hegen kyau haka?yo Kaff kauyensu tasan baza a yi mai irinsa ba,yau farinciki fall ranta..Ta shafasu ta dada shafasu fuskarta cikke da murmushin jin dadi,yau duk ta rasa wani irin ma kwalliya yakamata tayi ma fuskarta dake tana tsantsar natural beauty mai daukar hankli so bata saba da yin kwalliya ba" ..saidai fa yau din na daban ne acikin zcyarta.
Yaune ranar da zata soma ganin garin kaduna
..sosai ta zaƙu ta kuma saka komi a ranta,musmm sabawa datayi da irin labaran da saheeb yake bata akan inside town da yadda abubuwan nishadi na yara ke gudana..yau gashi Allah yay itama zata leƙa taje tagani da idanuwanta
Jin motsin bude kofa yasata firgita a firgit ta kama sallahn ƙarya kanta babu ko dankwali...
Wani galala bilti ta tsaya tana kallanta,cikin sauƙe ajiyan zuciya harta ƙaraso ta tsaya a gefenta bata hankara ba.
"Kunnenta taja saida tayi ƙara."ni zaki maida shashasha wasime?wai meye ya shiga jikinki ne yau kiketa wann haukar rawan jikin?Wato ina wasa dake ko?Toh bari inje in ƙira taheer infada masa bakyason sallah kinga sai ya hanaki fitar mai gaba daya inga ta tsiyar ko..
Wani ragab ta fado ƙasa ta kamo kafafun bilti
"Bilti dan Allah karki ƙira wancan mayen !!namiki alkwari,na rantse miki bazan ƙara ba..Nifa Yanzu zan yi sallar. wallahi kitsaya ma zaki gani..Bilti da mamaki yacikata tace"wasimé Kikace mene?waye Maye kuma?Au,maye kika ƙira taher din dashi?
.....bakinta ta kama agurguje kuma a tsorace da alaman bata masan hakan ya futa daga bakinta ba,atake tayi wani lagwas fuska kalar tausayi,kada kai kawai bilti tayi tace ehhhhh
Lallai kam,wasimé ina ganin saina farsa bakinki..duk sanda taheer ya riƙe ki wallh bana cewa komi.
Na kudine if u want to read pls Subcribe,its 300# kacal pay urs
Via *0152983148*
Mohd sule surayya
GTB
Or contact me 08060712446
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top