No!

FITAR RANA 16

Da wani irin zafin nama saheeb ya karaso wajen Jikinshi har na rawa ya saka hannu ya finciko wasime a hannun zee snn ya juya yanamai dora ma fuskan zee din wani gawurtaccen mari mai saurin rikitar da kwakwala..

tattaba fuskan wasimen ya shigayi ganin batako motsi hanklinsa tashe ya runtse idanuwansa snn ya bude, yana cewa"oh my gosh,zainab What did u do?..tsawa mai cike da kufula ya daka mata,kuka zee ta fashe dashi snn ta koma gefe ta rakubu da jikib bango sosai tay narai narai da idanunta Cikinta duk ya gama durar ruwa a tunaninta mutuwa ma wasimen tayi.

Tattaba fuskan wasimen ya rinka yi hanklinsa a mugun tashe jikinshi gaba daya na rawa duk ya rude yabi ya rasa ta inane ma zai fara tunkarar abun,shimfidar da wasimen yay a kasa yana kkrin tabbatar makansa cewa ba mutuwa tay ba,wayarsa ya lalubo daga cikin aljihun wandonsa snn ya danna kirar gaggawa ma emergency,Acikin yanayin raxana sosai zee ta matsa kusa da su jikinta na rawa sosai

,leken fuskan wasimen takeyi a sace cikin ranta tana cewa wayyo Allah na na shiga uku shikenan yau nayi kisan kai, muryanta na rawa rawa sosai tana sauƙe hawaye tace "babe pls ishe alive..,wayyo ni na shiga uku, anya kuwa ba mutuwa tay ba?

Tsabar fushi saheeb baisan sanda ya tureta tayi ƙasa ba"...get the hell out of here you witch"..abun bai masa bama,tashi yy ya soma dukanta da kafarsa yana takata cikin tsananin fushi da harzuka ..
Yana cewa "Zainab mekika aikata min?
Har muguntan naki yakai ki kashe yar mutane akaina?...wani maraitacen kuka ta rushe da shi acikin yanayin rudani tana cewa
"wallahy sharrin shedan ne,saheeb dan Allah ka fahimce ni..I didnt mean for this to happen,nifa tsoro kawai naso in bata danta dena shiga harkanmu.Ba kasheta nasoyi ba....i swear to u..

Ko kulata baiyi ba domin kuwa hnklinsa ya mugun tashi ganin yadda wasime take kwance akasa almost lifeless bata ko fidda gudan numfashi.

Jim kadan saiga team din emergency sun shigo wajen hilimi guda, acikin gaggawa suka daga wasime suka jefata a motarsu ta emergency atake atake aka sankaya mata engine din taya numfashi emergency nurses dake tare da ita suka shiga kkrin bata taimakon gaggawa.

wani makaken private hospital suka wuce da ita wanda yakasance mallakin mahaifyar saheeb din ne dan haka likitoci har biyu ne suka amshe case dinta Akayi marmaza akayi da ita ciki ana duddubata .

Ciwon Asthmanta ne ya tashi but in xtreme conditon,sukansu likitocin sunsha mamaki yadda take kkrin fighting.

Ziriya kawai saheeb yakey shikadansa a bakin kofar inda aka shiga da ita yana salati a zucyarsa duk yarasa abunda yake masa dadi

Can saiga shigowar anisa tare da zee suna karasowa cikin asibitin suna tahowa cikin sauri kowannen su hanklinta a tashe ,zee harta bawa anisa labarin duk abunda ya afku tsakaninta da wasime, saidai bata nuna mata cewa abisa qudirinta na mugunta lamarin ya afku ba,sai tay manipulating mind dinta kamar yadda ta saba da cewa sharrin shedan ne ,Ayanzu zee tasani sarai bata da wani makama face anisa,sabida bukatun anisa awajen saheeb kamar yankar wuka ne,inhar tace ya yafe mata toh fa komin girman lefin dolene ya hkra ya yafe dan bakaramin son yar uwansan yakeyi ba...

Cirko cirko sukayi a bakin ward kowa yay zugum ana jiran sakamakon jikin wasime daga bakin likitoci.
Shiru shiru har sukaci kusan mintina arba'in a tsaye amma babu wanda ya leko

Wayarsa ce ta dinga ringing yay banza da ita bai daga kirar kowa ba dan koda bai sani ba yasan cewa bilti ce kawai zata iya nemansa a wannan lokacin.

Agogon hannunsa ya duba hanklinsa a tashe yaga wai har karfe bakwai shaura gashi har yanzu likitoci basu ce komi akan condition din wasime  ba.

Gaba daya sai yabi ya rude mancewa ma yay da cewa bai gabatar da sallahn magrib ba.
Anisa ce ta matso kusa dashi ta dan rugumesa tanamai comforting dinshi cikin yanayin nuna tausayinta agareshi wanda hakan ne yasaka ya dan ji dama dama.

Tashi yay ya dan fita snn yaje yay sallahn magrib din, har ya kammala ya dawo wayarsa baidena ruri ba,Anisa ta kallesa "big B..Wai meyasa bazaka dauki wayarka ba ne..Tun dazufa naga anata kirarka what if its important...nannauyar ajiyan zcyace ta kufce masa yanamai shafe fuskansa datayi jaaa da tafukan hannayensa cikin jann numfashin sa sama sosai.

Muryansa cike da amon damuwa Yace "I dont knw how to start explaining to u,Inna dauki wayar nan ma bansan mezance ba...am fucked up right now..duk wancan yarinyr ce tajawomin...ya furta hakan yana aikawa zee wasu matsiyatan harara.

A mamaknce Anisa tace toh who is calling you kode iyayen yarinyar ne?shiru taga yay, ta damko hannayen sa cikin son ta tursashi tace karkayi haka yaa saheeb  they need to knw ai, this is serious fa.. saheeb
Zaka aje musu yarinya acikin wani mayuyacin haline batare da ka sanar dasu ba? This is btwn life nd death...inta mutu daureka ma zasuyi ko suce basu yadda ba
Bro u have to let them know right away....

Juyowa yy idanunshi cike da damuwa yanacewa
"I know...i knw anisa...but you have no idea how we got here.Saida fa na roke alfarma awajen bilti kuma namata alkwari before 6pm yarinya tana gida but just look at what happen now..

Cikin sauri bai hankara ba anisa ta kwace wayar dake hannunshi tana cewa nikam bani lambar ta toh ni zan kira ingaya musu gaskiyan abunda ya faru,ita biltin batada fahimta ne Aiba lefinka bane...its an accident fa..kuma babu wanda yafi karfin hakan tafaru dashi.

Ransa a hargitse yace Anisa give me that phone u wont understand me.

Boyewa ta dadayi ta matse wayar da rigarta cikin bijire masa, a bayadda ya iya haka ya kyaleta dashi.

Kwafar lambar tay awayanta snn ta kira layin bilti Tana karawa a kunne taji service provider tanacewa the number ure trying to call is curently switched off pls try again or call back later...

A Lokacin numfashin saheeb kamar zai tsinke yabar jikinshi tsabar fargaba,"ganin anisa tayi shiru da waya a kunne bata kuma ce komi yasashi yace "Did she pick up?Ajiyar zcya ta sauƙe snn ta Sauke wayar a kunnenta cikin girgiza kai tace
"the line is swichd offf....

Ajiyar zcya ya sauƙe feeling relieved yana dan lekawa,yace nidama likitocin nake jira sufito inji ta bakinsu tukuna kafin sai in nemesu on sanar dasu.

Anisa batace mishi uffan ba tay wucewarta wajen zee data manne da bango tana matse idanun karya,dan harga Allah bawai nadaman abunda tayi wa wasime ya sakata damuwa ba,damuwarta shine kar ace tayi kisan kai ko saheeb yace zai guje ta,duk damuwarta kar ace wasime mutuwa tayi azo ace za'a kamata.
Gashi mahaifyarta irin mata masu daukar zafin nan ne...dama can ubanta ne kawai yake daure mata gindi kuma ahalin da ake ciki ynzu uban nata yy tafiya izuwa europe baya ma ƙasar.

A fannin bilti kuwa tun ficewarsu a gidan baifi da awa guda ba saiga taheer ya dawo daga tafiyarsa.

Bata ma sanda shigowar sa gidan ba tana can cikin kitchen tana yan aikace aikace.

Dakinshi kawai ya nufa direct yaje yadan huta gajiyar da ya debo ajikinshi sabida kwana sukayi a mota suna tafiya tsakanin adamawa da cameroun,sai can snn ya tashi da kyar jikinshi duk yay tsami,haka ya lallaba kansa yaje yay refrshing kansa a bathrum ya fito yay glaming kansa acikin wata simple polo shirt light yellow in colour da bakin wando,da soft sneakers shima baki
Turarensa mai sanyin qamshi ya fetsa yanamai
Lura da time a agogon guccin dake sakale da tsintsiyar hannun sa

Wajajen biyar da rabi lkcin ana neman shida saura taheer ya samu saukowa,a bkin kofar kitchen din ya tsaya snn yay gyaran murya,dan raxana bilti tayi musmmn data gansa gatsau haka acikin gidan duk dama tasan hakan zai iya yuwa tunda yanada personal keys dinshi..

murmushi mai sanyi ta sakar masa shima ya mayar mata a takaice, cikin kulawa tace"Taheer yaushe agari?Looking really stressd up cikin kyabe bakinshi yace "ai nafi awa guda agidan nan kawai dai nagaji ne shiyasa naje na dan kwanta danna huta...bilti da akwai abincine?wallh yunwa nakeji...tun safe fa banci komi ba,..
da mamaki ta dubesa tana wondering tace"akanme toh? Shiru yay mata bai amsa ba..tace toh zauna nan bari dai naje na kawo maka dan abunda ya samu sai samu kaci.

Waje ya samu ya xauna a falo snn ya dauki remote din tv yana danne danne

Bilti kuwa tunda ta shige kitchen take dannawa saheeb ƙira amma bai daga ba,gabaki daya saitaji hanklinta bai kwanta ba. ranta sai ya soma harzuka,bacin rai na neman ya rufe mata ido, acikn zcyarta tana cewa yaya yaron nan zaimin haka..toh ga taheer dinma ya dawo niyanzu mezanje masa gameda fitar wasime? Duk fargabanta kada Allah yasa su shigo su iske shi a falon.

Harta kammala hada masa abincin saheeb bai daga wayar ba.haka ta basar da lamarin ta danne fushinta ta fito fuska ba yabo ba fallasa ta kawo mishi  abincin acikin yanayin dubara tace "inkai maka dakinka ko inaga can dinma ai zaifi..Nan wajen duk yay kura bari inzo indan goge
Kai saika shiga daki karna takuraka

duk salon wayon waidan ta koreshi ne ya shige room dinsa karyaga shigowarsu wasime cos at any moment tana tsammanin jin sallamar su...

Haka taheer yay taurin kai shima yaki tafiya dakin duk wayonta baihau kansa ba..
Yace kibarshi anan kawai bilti"Ni anan kawai zanci"

Bilti bata taɓa kasancewa a halin baraxana da razana irin na yau ba sai cizan yatsa takeyi a zucyarta tana mita "kassh amma yaron nan baimun adalci ba...ziriya takeyi ita kadanta a kitchen da waya a hannunta tana mai dada neman layin saheeb din

Taheer nadaga falo yanacin abincinsa hanklinsa kwance.
Duk A tunaninsa wasime tana can daki a kumshe kamar dai yadda ta saba.

Bilti ta kira saheeb yafi sau hamsin amma shiru bai daga wayar ba,kowani dakikanin wucewar scnds na agogo saita kirga

Hanklinta bakaramin tashi yake dadayi ba
Musamman dataga har an kusa a kammala sallahn isha i bai daga kiraba kuma basu dawo ba...

Wani zucyar nata tunzirata akan taje kawai ta gayama taheer komi iyakaci ne yay fushi ai ba dukanta zaiyi ba.

But dat isnt fair to him
Matarsa ce fa wasime, nd she rmbr how he gave
her Strict oders akan kar abarta tafuta taje koina face inshi ne ya bada izinin yin haka.

Ganin takwas yay har yana shirin gaucewa yasaka bilti ta cire ranta da tsumayin fushi da bacin rai ayanayinta

Fitowa tay jikinta a mugun sanyaye da niyyar kawai zata fallasawa taheer abunda ake ciki,tana isa falon ta samu taheer din bayanan da alaman sallahn ishai yaje gabatarwa a masjid.

Kwanukan dayaci abincin ta tattara takai cikin kitchen ta zuzzuba su a sink ayayinda wani tukukin ajiyan zuciya ya kufce mata..wanke wanke ta hauyi kodama zai gushar mata da tashin hanklin datake ciki amma ina abun saima karuwa yakeyi acikin zcyarta..tambayar kanta takeyi "meyasa saheeb zai mata haka?

Kallon agogo tayi taga
Har karfe takwas da rabi shaura Wayarta ta kama ta kashe ranta a mugun bace snn ta fito da niyyar dauƙo hijabinta zata je har gidan su saheeb din kawai dakanta.

Agaggauce ta haura sama ta sauko cikin shigarta na doguwar hijabi dark green in colour duk fargabanta kar Allah yasa ta gamu da taheer,ai gwara taje sharp sharp taji meke faruwa koma minene zai farudin yakasance dai ta dawo da yarinya gida.

Tana saka hannu a door handle din falo zata ja ta fito waje sai taji alaman kmr ankama ne ta waje da alaman ana kkrin shigowa ne ciki.

Bugawa da karfi kirjinta ya soma yi,she was seriously hoping taga wasime sai kawai taga taheeer ya shigo

Da Kallo daya yabita
Ina zuwa haka?

Dan shiru tayi kanta na kallon ƙasa wanda hakan yasashi fahimtar cewa da akwai matsala
Amma baice mata uffan ba ya wuceta yay zaman sa a falon yanamai harde kafa daya akan daya...

Dakanta ta yanke hukunci bayan tay doguwar muhawa da zcyarta snn ta juyo ta fuskance shi ta shiga fayyace masa halin da ake ciki

Baice mata uffan ba ya dauki key din motar sa kawai ya fice a falon...

Direct yay gidan su saheeb tundaga bakin gate na farko ya danna horn,take security suka sanar dashi cewa saheeb bayanan suna asibiti a sashen emergency.
Tambayar sunan asibiti yay akamasa kwatance

Wani iri ya dingaji a zciyrshi ayayin da yake tuki cikin gaggawa,duk tunanin shi mezai saka saheeb ya kasance a emergency by this time,to ina wasimen ita kuma? Duk sai ya dauka ko hatsari sukayi,.har ya isa asibitin hanklinsa bai gama dawowa jikinshi ba

Yana isa ya samu daidai lkcin likitoci sunfito har sunyi inviting dinsu ciki domin suga patient dinsu cos she is stable now

bayan zee ya hango daga can nesa Dake itace tay shigewr karshe,direct ya nufi dakin data shigen cikin sauri yana isa daf da bakin kofar Ya somajin muryan wasime cikin tsorata da kuka sosai ayayinda take maida wa saheeb duka labarin abunda xee ta aikata mata acikin washroom dazu

..idanun saheeb ya kada yay jaaaaa kamar zaiy mata kuka, He was sooo furious ransa sosai ya harzuka ya dagule akan lamarin.

...mannuwa Da bango zee tay tanata kukan munafurci just tryn to gain pity from anisa kanwarsa,duk wani abun da wasime take fadi saida ta karyata, kusan ma musu ne ya kaure a tsakaninsu. Kowa na kuka na fidda abunda kecikin ranshi.

Taheer yana daga bakin kofar yanajin komi da suke zantawa,wani irin zafi ya dingaji acikin zcyarshi, wani tukikin abu yaji aransa na ingizashi akan ya dauki mummunan mataki.

Jikinta is queit serious Likita yace subarta anan ta zama stable kafin zuwa gobe sai akaita gida.

"Shirin ƙirar bilti saheeb yakeyi domin ya sanar da ita halin da ake ciki caraf saiga sallamar taheer akansu wanda yayishi ciki ciki kamar an sakashi dan dole, mugun haden ransa yy yana huci kamar wani mayunwacin zaki fuskarsa babu alaman rahma bare sauki

suna hade ido da saheeb kusan subucewa wayan shi Tasoyi a hannun sa zata fada kasa yy surin cabewa jikinshi a sanyaye, wasime tana ganinsa ita kankame jikinta tanamai runtse idanunta cike da fargaba mai gauraye da bugun zuciya mai tsanani.

..cike da karfin hali saheeb yy dan murmushi yanamai miko mai hannu suyi musabaha yace "
"Wow Guy yaushe a gari, kuma waya fada maka muna nan? Tsimewa Taheer yy Baiko kalle hannun sa daya miko ba bare ya kulashi bare  ma harya amsa maganan sa,acikin yanayin fizga da bacin rai yabita gefen sa ya wuceshi ya nufi inda wasimen take yatsaya yana kallonta,take jikinta yahau rawa wani sabon kukan ta fashe dashi mai ban tausayi,yana tsaye yana shiru baice mata uffan ba

Igiyar ruwan da aka jona mata ya kama ya tsinke  snnan ya zuba hannayen sa ya tattarota gaba daya ya dagata cancak a hannun sa ya rungumeta a kafadunshi ta lafe ya kama hanyarsa zai fita tare da ita

Saheeb kamar zaiyi kuka yabi bayansa da gudu kuma a rude,cike da hanzari  yana cewa
"Taheer..'kamar baisan shi ba haka yay masa shiru,tafyarsa yake a nitse kamar ba tafasa yakeyi ta ciki ba.

"Taheer pls wait nd hear me out...ya zakay kazo ka dauke yarinya anakan mata jinya...wai meye haka ne?taheer pls now..
Listen to me give me a chnce to explain wallh ba laifi na bane..
Saheeb ya karashe maganan hanklinsa a matukar tashe

Da kamar bazai kulashi ba can kuma saiya juyo ya dubesa game da
haderansa cikin sigar kashe masa wata xaxxafar warning wanda tazo a xafafe dan lumshe idanunsa yay snn ya bude "muryansa a karsace yace"...Saheeb,
i do not want to see u near this girl again, har abada!!..kuma nafada maka kenan.
yanakaiwa nan ya juya abunshi ya saka kai yana tafiya yana huci

"Taheer no pls.."

Saheeb ya furta hakan a cikin sautin magiya sosai bakaramin faduwa gabansa yakeyi ba don yafi kuwa sanin taheer,he will say it once kuma bazai taba sauya ra'ayin sa cikin sauki ba yana cikin wannan yanayi saiga su anisa sun firfito atare da zee duka suka dunguma sukabi bayan taheer din har suka kai waje.......

Is not free to subcribe dm 08060712446

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top