fights

FITAR RANA 15

Suna isaga dakin wasimé tayi gudu cikin murna da annashuwa ta isa wajen da aka aje kayayyakin ledojin shoping din,atake tahau bubbudesu tana fiddo su waje daya bayan daya.

tsayuwa bilti tay akanta tana famar lura da yanayinta, she seems soo happy right now,rabonta dataga wasime acikin irin wannan yanayin farincikin harta manta sabida kullum a taƙure take cikin tsoro da fargaban gamuwarta da taheer,".."bilti bilti zoki ga babyn danake fada miki wanne yafi miki kyau"
murmushi bilti tay snn tace "Kai masha Allah ai dukansu ma sunada kyau,..Tace Allah ko bilti?..Toh Ga alawa ma nan ince dai zakisha?
Su chokolates dinta ta firfitar dasu nutella, choclate creamy, sneakers,fresh up,fantisiya,coco balls cream crckers duk saida ta ciccirowa bilti waidan ta zabà,a cikin surutayya tace bilti,Ingaya miki ko?da mukaje gidansu ba..bilti kinga gidan sun kuwa, wani rangajeje dashi wallhi Allah ai gidan ba irin gidan nan bane yafi gidan nan kato..kuma da akwai wasu yara da mukay wasanmu da su akwai ahmadu,teema,bello..siyama..da shatu...dayan antyn mai hankli ne takaimu mukayita wasa dayan antyn kan hmmmm  Bata da kirki,Bilti ta tsaya kallon bakinta da mamki "Au wayanan duk a gidan su saheeb din kuka hadu dasu?,"tace eh man..bilti bakiji ba, wancan muguwar antyn ko sai wani tambayata take wai ni ƙanwar dahiru ne? Kuma Kamar zata hadiyeni fa take magana.

Hmm kawai Bilti taja, toh ya isa haka wasime surutun nan naki yay yawa,maida kayayyakin ki kimtsa wajen in taheer yazo kya nunasa masa sai Kice masa saheeb ne ya siya miki..cikin gwalo idanunta waje tace TAB nikuma sai in gayamai!!
a'a kam,nide wallh bazan je wajenshi ba,kedai kije..ai shi masifa kawai zaimin.

Bilti tace "Masifan me zai miki?ai inkinga taheer yay miki masifa to kece bakiyi dadai ba

Dan dakatawa tay da abunda takeyi snn ta kalli bilti cike da son ta fahimce ta"Amma bilti, ni mena taɓa yi masa yakejin haushi na kullum?yo mesa halinsa ba irinna yaa saheeb ba ne? shifa ko dariya bai taɓa min ba barema ya siyamin dan sweet ko babyn robber..

Hmm kawai bilti tace snn ta sauke boyayyar ajiyar zuciya cikin shashantar da zancen tace "wasime ina fatan dai bake kika roke saheeb ya siyamiki kayan nan bako?

Wani Dafe kirjinta tayi
Cikin zaro idanu waje
"Tace Ni?..wallahi tallahi wabillahillazi ban rokesa ba,shine fa yakaini wajen waidan nace mishi ya dawo dani gida shine mukaje wani babban shago ya sissiyamin wayannan.
Tana dasa aya bilti tace
"Toh nide ina gargadin ki da ki kama kanki Wasime banda roko banda kuma kwadayi,Kai daga yauma inya kara cewa zai siya miki abu ko zai baki kudi karki amsa kice kin gode kawai,inya takura ne saiki karba shima bavkoda yaushe ba..kuma ki tabbata kin kawo gida kin nuna min kowa taheer
Idan ba hakaba duk abunda ya biyo baya ke kadanki zakiji dashi.
Kwadayi ba abunyi bane wasime,kwadayi da son abun duniya yana saurin jefa mutum halaka koda kuwa shi mai imani ne.
Kiyi hankli da rayuwa karki jefa kanki a tsabgar da bazaki iya ficewa ba.
Karkiga waike yarince nitsuwa da sanin yakamata shine kadai girman ba yawan shekaru ba,yakamata kisani ke marainiyar Allah ce wasime kiji tsoron Allah mahaliccin ki kiyaye dorawa zuciyanki kwadayin abun hannun wani..

Wani Shiru wasimen tayi cikin yanayin nitsuwa tanajin abunda din biltin take cewa dan bada wasa taga tanayi mata maganan ba,sosai bilti ta gargade ta ta kuma ja mata kunne sosai musmn akan ƙarban abun duniya a hannun mutane musmmn ma shi saheeb.

Atake Jikin wasime yay sanyi har bilti ta gama maganganunta ta fita bata dago kanta dake kallon ƙasa ba..ajiyar zcya kawai ta sauƙe zcyarta cike da fargaba ta mike tsaye ta cire kayan jikinta snn ta shiga bathrum tay wanka tare da yin alwala,sharp sharp ta idar da sallahnta wanda bawai ta gama iya shi bane,yau kam ma kwata kwata zcyarta da mind dinta gaba daya sun raja'a ne akan kayan wasa.

Tana idarwa ta kimtsa dakin tsaf, snn ta kwaso su teddies da barbie dolls dn ta jerasu akasa daganan kuma ta tsunduma wasan baby bataji bata gani.

A fannin saheeb kuwa fitarsa a gidan ya same su tolu da malam musa awaje sun kasa sun tsare a bakin motarsa suna jiran fitowarsa, haka ya ciro sabbin kudade ya rarraba masu goron sallah kowa yana washe baki, a bakinsu yakejin labarin cewa Taheer yy tafya baya gari,Perfect oppurtunty for him ya gayyace wasime zuwa asalin gidan iyayen sa domin suganta cos in two days time za'a ayi big birthday party blast ma kanwarsa anisa duk dama abun na gidane kawai so shiga wajen sai wane da wane sabida a cikin family house dinsu za'ayi.

Burinsa ayanzu baifi yakai wasime wajen mahaifyarsa ba kodama zasu soma sabawa da junansu, ta inda xata nan gaba zai iya dogara da cewa mahaifyar tasa zata taimaka masa wajen yaƙin kwato ragamar kulawa da rayuwar wasime daga wajen familynta, danso yake ta girma tasan cewa shi yay mata komi na rayuwarta kafin suyi aure.

Mahaifyarsa hajiya mufidat Garba bakare babban jamiar kare hakkin dan adam ce,snn ta karance fannin lauyanci tana da doctorate degree dinta.
Tana kuma bada gudumawa mai matukar
Muhimmanci wajen taimakawa marayu da marasa galihu (humanatarian)a reshen ƙasar amurka.

Washe gari da safe wasime tana farkawa a bacci ta soma lalubar ababen wasanta sanda tay wasa iya isarta snn ta tashi tay sallah
Ahakan ma Saida bilti ta tsawatar mata snn ta aje taje tayi sallahn a nitse,kayan datay fitsarin dasu ma yau kasa wankesu tay ta dukunkuna su kawai ta aje a bayan gida,yau hatta abinci shareshi tayi koda bilti ta tursasa mata a gaggauce taci dan kadan snn ta koma kan ababen wasanta ranan gaba daya bilti bata gane kan wasimé ba.

Washe gari da safe ma hakan abun ya kasance saidai sukayi fada sosai da bilti snn ta nitsu tay ababen dake gabanta wasan sosai ya shige cikin ranta, Duk abun duniya ya dame zucyar bilti ,at around 12am lkcin bilti ta kammala dukkan wani ayyukanta ta fito kenan tana zaune a falo akan kujera riƙe da remote din tv a hannunta tana neman tashar arewa tanata famar scrolling har tazo ta wuce kan tashar bata lura ba saboda harga Allah babu wani cikakken nitsuwa atattare da ita,tunanin rayuwar wasime tasaka agabanta tun jiya,da shi ta kwana dashi ta kuma farka,kuma haryanzu tana kai bata fasa ba.

Tunani kashi biyu ke wanzuwa a kwakwalnta har yanzu dai itama hanklinta bai wani kwanta sosai akan tarayyar wasimé da saheeb ba,koda ma ace babu wani cutarwa acikin tarayyar nasu, amma dai tasan dolene salonshi na kashe mata kudi da bata ababen duniya yaxo ya gurbata mata rayuwarta na nan gaba.

Takanyi duba da yanayib bambaci dake tsakanin su da saheeb,shifa dan gidan masu shine masu fada aji..anan kuma su basu mallaki arzikin komi ba face iya wanda Allah ya basu na rufin asiri.

Toh ta ina kenan zasu iya da wasime nan gaba inhar ta kyaleta ta saba da kalar rayuwar da batata ba?yarinya marainiyar Allah kuma ga igiyar Auren wani akanta.
Kamata yay wasime ta zamto killataciya tun yanzu,ita kanta tarasa dalilin dayasa taheer yaki cewa komi akan tarayyar wasime da saheeb aganinta sam sam bai dace ba, duba da yadda sabo na yau da kullum daa kuma shaƙuwa da juna yakeson ya soma yin tasiri a zukatansu.

Bawai iya nan ne ciwon nata ba,hatta sauyawar halayyar wasime yana daya daga cikin abunda yake tada mata hankli.
Lokacin da anono ta kawo wasimé ko kara kasaka abakinta bazata tauna ba,amma yanzu gabaki daya ta sauya ta dawo wata marar da'a gashi bata son girmama na gaba da ita.

Tasan hala dan bata taba haihuwa ba batasan zafin ɗa ba amma rayuwar taheer da na wasime tamkar wani babban responsibilty ne akanta tunda amana iyayensa suka damka mata,bazata ce tayi nasarar rayuwarta ba inhar ta kyale tarbiyan dayan su ya gurbace.

aynzu kam taheer ya dan girma,tasan ba lallaine ya bata ciwon kai mai yawa ba,duk dama yakan dan taba yarintar,amma aynzu batashi take ba yazame mata dole tasaka ido akan rayuwar wasime,dole ne tasan yadda zatayi ta saita tarbiyanta dan kwata kwata wnn sabbin dabiu da halayyar nata sam basu dace da ita ba.

Tana cikin wannan tunanin wayarta ya soma ringing saheeb tagani akan screen da kamar bazata dauka ba can dai ta hakra ta dauƙa gameda kara wayar a kunne..babu yabo ba fallasa tace "salamu alaikum  saheeb? As usual da fararsa ya amsa suka gaisa..kai tsaye ya tambayeta ko zai iya zuwa ya dauƙi wasime izuwa birthday partyn sistersa yau.."tace a'a saheeb kasan dai wasime bata fita acikin gidan nan saida umarnin taheer kuma kaga taher din bayanan kabari mana sai wani lokaci inyaso by then taheer ya dawo amma ynzu kam baya gari.
..,yace eh nasan da hakan shiyasa ma nake neman alfarman ta wajenki dan Allah bilti,namiki alkwarin  baxata jima ba zamu dawo,taheer dont even need to knw this, ana yanka cake akayi dan hotona shikenan saina dawo da ita,it wunt take dat long...please kitemaka min .  ya karashe maganan cikin magiya..dan shiru bilti tay sabida rashin sanin hukuncin da zata yanke
Wasime ne ta dosu falon
Goye da white teddy bear a gadon bayanta tana tafiya tana wasa da wani abu mai balls balls aciki.
Bilti bilti doramin abuna ya tsinke...
Saheeb yana tsinkayo muryanta yace
'Is that beauty?bilti bata amsa ba,yace bilti dan Allah hadani da ita..
Mika mata wayar tayi kiyi magana saheeb ne,"da uban zumudi ta amsa taa kara a kunnenta tace "Alo?yeeeeyyy yaa saheeb...dariya yay beauty beauty..beauty na kitayani rokon bilti mana tabari in zo in dauƙeki kije kiga mummy na.

Wani daka tsalle tayi cikin murna tace haba?
Kace Allah zan ganta?
Dariya yay sosai snn yace eh mana amma ai sai bilti ta amince...dan shiru tay tana mai satar kallon biltin da gefen idanunta,gani tay kamar bilti ta hade fuska.

Gaba daya zuciyar bilti bai wani kwanta da abun ba amma dai zata kyalesu din suje kawai da sharadin saheeb zai cika alkwarin sa na dawowa da ita akan kari.

Tunda ta basu go ahead dukansu suke cikin halin murna at arnd 3 na yamma saiga saheeb ya shigo,yau half jumfa yasaka ajikinshi ta masa cas cas dake bugun kamfani ce ya sako hularsa mai shegen tsada. Riga da zani na leshi wasime ta saka sky blue in colour shima duk acikin sabbin dinkunan da akayi mata ne,saheeb yana isowa tay gudu taje ta hau jikinshi tanai mai oyoyo.Duk dama yau bataga wani sakewar fuska awajen bilti ba

Da zasu fita bilti ta kirawo saheeb gefe
"Dan Allah karku dade dayuwar taheer ya dawo yau kuma kasan dai bazaiji dadi ba inyazo ya tarar da cewa bata nan.

Cike da assuring dinta yace insha Allahu zan cika alkwari.

40min drive yakaisu makaken gidan su saheeb ko ina a shirye yake tsaf da kawatattun decorations wanda akayi su musamman don shagalin partyn,kusan rudewa wasime tayi ganin wnn gidan ma yafi wancan wanda sukaje shekaran jiya girma Surutu kam yau yashata harsaida yaji babu dadi.

Everything went well,saidai plan din saheeb na bayyana wasime ma mahaifyarsa bai samu yay aiki akan tsarinsa ba..

muhimman baki ne suka tsareta a babban falon gidansu cikin wata muhimmiyar zantawa ta kasuwanci.,tunda aka yanka cake da ita suka dan daddauki hoto shikenan bata ƙara samun daman lekowa wajen ba,su wasimé kam tuni ta saje cikin yan uwanta yara,saidai kaf cikinsu itace tay daban sabida yanayin suturarsu yasha bambam da nata.

Kusan kowani yaro awajen dan masu shine kuma ancan caɗa ma kowannen su kwalliya da hadaddun ready made gowns nd expensive suits, amma ita kam riga da zani nema ajikinta wanda a kiyasce kudin leshin bazaifi dubu takwas ba.

While da party is going on kowa yanata enjoying kanshi da abinci kala kala ana rawa ana games amma gaba daya hklin saheeb baya jikinshi,baida wani abunyi a zcyarshi face sake sake,And zee was there to annoy him more, dan tunda taga zuwansa wajen tareda wasime take famar tsine masa albarka duk inda ya zauna haka zata bishi ta nanike mishi Snn bata da wani magana mai armashi sai Aibata alakarsa da wasime.

Aranta ta tsane Duk wani abunda ya shafe taheer.
Ayanzu sosai take nuna adawarta da shi.

Da abun ya ishe sa ne yay zciya ya tashi yabar mata wajen yabarta a zaune ita kadai akan table a tsakiyar idanun mutane, Hakan dayay sosai ya bata haushi,aftr like 2 mint tana kkrin latsa wayarta zata turawa kawarta eesha text messg caraf sai idanunta suka sauka akan wasime.

Tun daga can ta zuba mata ido tanamai hararata, wucewar ta ta gani ta hanyar guest washroom tana doka uban sauri,mammtase kafafunta datakeyi ya nuna alaman fitsari ne ya matseta.

Wani Dariyar mugunta zee tay snn ta tashi tsaye a gaggauce cikin satar idon mutane tabi bayanta washroom din

ahnkli take lekawa cikin sanda a Lokacin data shigo lkcin har wasime ta kammala yin tsarki tana kkrin maida panties dinta bata hankara ba taji an wani fincikota tayi baya,wani irin bugawa da karfi kirjinta yay acikin yanayin firgita da tsoro har ta karkace baki zata saki ihu Da ƙarfi zee ta buge bakinta sanda jini ya tsittu..,bata jira ba ta fixgo ta ta cakume mata wuya ta shaketa sosai tanamai hadeta da jikin bango"

tuni hancin cikin wasime ya cure, cikin nata ya duro ruwa tanajin kamar zata saki fitsari ajikinta
,"ihu tayi niyyar sakawa...zee din ta zare mata ido tare da daka mata tsawa "kiyimin shiru da bakinki,kikq yadda kikayi ihu anan saina kasheki,mayya kawai shahsha yau saina kasheki,in kashe banza.

Kukan bazata wasimevta barke dashi wani mari zee ta dora mata snn ta turata ta fada akasan toilet din cikin ruwan datti,karkar jikin wasime yake rawa jin kanta kamar wata mutacciya

Kuka takeyi mai tsananin nuna firgita saidai marar sauti sabida toshe bakinta da zee din tayi.."wato ke bakiji ko?Uban wa yace miki kizo nan...uban wayace miki kinabin saurayina?zare mata ido take kamar zata hadiyeta cikin masifa

Da baya baya wasime takejan kanta hawaye sungama wanke mata fuskanta tana famar girgiza kanta alaman ta balain jijjiga da tsoro.

Toh Daga yau saiyau
Naƙara ganin ki a inda saheeb yake saina yanka ki...saina hallakaki kin bar duniya.. kina ji ko bakiji?Wasime Bata iya daurewa ba ta saki kuka mai firgitarwa.Au baxaki yi min shiru ba munafuka?Janta tayi akasa tanamai wurgi da ita..ajijjiya take ya soma rufewa wasime ido,cikin kokawa da numfashinta ta soma cewa cikin kuka"..anty anty anty dan Allah dan Annabi kiyi hkri bazan ƙara ba waayyo Allah na kasheni zakiyi anty? kallo daya kay ma wasime zaka tabbatar da cewa bata cikin hayyacinta dan bakaramin raxana tayi ba

Haka zee ta bushe idonta ta cakumo ta kamar yar tsana ta mikar da ita tsaye tana kallonta babu ko digon tausayawa a idanunta taja tsaki mtsww"bangama dake ba"..wani janta tay izuwa bakin water flush system suna kaiwa wajen ta danna kanta acikin bututun kashi ta murda flush ruwa ya rinka zuba akan fuskar wasime yana suffocating dinta,numfashinta ta dinga jaaaa da ƙarfi tanajin kamar ranta zai fice ajikinta,yarinya sai bari take tana tsananta kuka mai ban tausayi amma zee bataji kamar zata dena muguntar ta ba.

Daga waje kuwa saheeb ne yaketa neman ta bai ganta ba,duk saiyaji hanklnsa ya tashi sabida biyar da rabi ya gauce yana matukar son ya maishe ta gida kamar yadda yay ma bilti alkwari...

Da kyar wani basira tazo masa ya fara bibiyar yara yaran yana tuhumarsu ko sunganta daya daga cikin kannen zee din ne ya ce masa ai yaganta dazu tabi nan..sai ya masa nuni da hnyar washroom.
Cikin gaggawa ya doshi wajen,yana shiga kuwa yasoma tuamali da ihun wasime,a guje ya isa kofar inda ihun yake tashi yana bankadewa daidai lokacin zee ta cakka kan wasimen acikin latrine ta danna mata ruwan flush akanta data wani fixgo ta sai gani tayi Yarinya ta sanɗare bata  numfashi,......
Na kudine 300 naira,subcribe via
0152983148
Mohd  sule surayya
Gtb send ur evidence to
08060712446.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top