eat ur eat
3
Saican wajejen bayan magrib suka iso cikin garin kaduna,lkcin kowa ya gaji,wasime kam tanata sharban baccin ta
A kofar gate din babban gidan qasimu sukayi horn mai gadi ya taho ya bude musu ƙofa, tunda sukayi parking taheer ya sabule jikinshi ya haura sama can dakinshi babu abunda ya kuma sauƙowa dashi,yana shiga dakinsa ya fada akan gado yana maida gajiyayyen numfashin shi dayake fitowa daga can ƙasar huhunsa a hankli.
kirjinshi da zuciyarsa sai racing sukeyi yabi ya rasa kwakkwaran dalilin faruwar haka,duk yadda yaso ya mance da zancen auren a zcyarsa ya ƙasa,ynzu shknan fa yay aure..kwantaccen gashin kanshi ya shafa ahankli cikin jan numfashi ya furta"what the fuck,wani irin mixed feelings na i cant believe this shi ya mamaye sigarshi wanda yy kama da kamar zai yi murmushi kamar kuma zaiyi kuka a lokaci guda,daga nan miƙewa yay gaban wani dan mini freezer ya buɗe ciki,2 rows ne mai dauƙe da chilled bootle water sai chapman ansha rabi an bar saura,Ruwan kawai ya dauƙa ya bude ya kurɓa kadan yana lumshe idanunshi after each sip snn ya mayar ya ajiye ya mike ya shige bathrum,wanka yy yabiya sallolin dake kanshi,tuna wayarsa a kashe yasashi kunnata,dan kadan yay scrolling baiga wani abu intresting ba ya ƙara kashewa,da kyar yau yay bacci dan aranshi babu abunda yake face juye juye da tunanin auren da aka dora masa,a bangaren wasime kuwa saiyau taga babban gida ƙere tunaninta,yo duk kauyensu bataga i irinsa ba,da xuciyarta kawai taketa shagalin hira tana maganganu kai kace nazarin wani abu muhimmi takeyi ,gidane irin na zamani yasha interlocks ga motoci a parke 1,2,3 saida ta tsaya kirgawa tass acikin zuciyarta,motoci guda uku ne harda wanda sukazo aciki making 4cars,sai kuma jincheng rubber rubber da tagani agefe,baki bude tace"laaah gidanma harda Achaba? Bakinta ta washe a tunaninta ai zatana xuwa gida tunda a machine kawai taga ake shiga kauyensu data fito,...sai kalle kalle kawai take abunta tana leken wajajen da suka burgeta kamar wawiya,da alama tamance wai yau an dora mata wani abu akanta waishi aure Hahaha inza a yankata aynxu ma bazata iya tuna komi ba .
karshe babban mai aiki kuma nannyn gidan wanda suke ambata da suna Bilti ita ta riƙo hannunta tajata izuwa ciki tayi mata wanka fesss ta shafa mata mai tasa kaya nan danan bacci mai nauyi ya saceta danko abinci bata iyaci ba,washe gari da asubahin fari taheer ya farka ya fice sallahr fajr shikadai danyau bai jin zai iya jiran dad dinsa kamar yadda ya saba dan harynzu basuyi wani dogon hira akan lamarin aurensan ba,kuma yasan da maganganu sosai a bakin mahaifin nasa,shidai baison yay tattaunawa maizurfi, he dont really care inde hakan zabinsu ne shimai musu biyayya ne ako wani irin hali so long as dis marriage bazai hanasa cika burikansa na rayuwa ba.guntun ajiyar zciya ya sauke ayayin dayake sauƙa ahankli daga kan matakala,jallabiya brown ce ajikinshi tasha karin guga ta masa damas ,a hnkli yake takawa alaman baison kowa yaji motsin fitarsa daga gidan,tunda yy alwala ya zauna cikin masallaci bai ƙara fitowa ba,yau sai wajajen bakwai saura ya dawo cikin gidan sallama yy a kofar falonsu,
Abbansa na zaune da jarida a hannu ya amsa,waje ya nema ya zauna a kasa sai ynxu ya lurada innono data fito ta shirya tsafff tana zaune a falon itama tana kallon tv tare da mahaifinsan bazaiwuce suna tattaunawa akan lamarin aurensa ba,wani haɗe ransa yay tamau kmar bai taɓa dariya arayuwarsa ba,mentally ya datse zcyrsa daga bugun datake snn ya dan cixa labbansa a asirce,idanunshi yay rolling snn yy ƙasa dasu a miskilance "Anono kintashi lpya? Da sauri ta amsa shi...lpya lau dahiru Angon jiya har anhito kenan,ajiyar zciya ya sauƙe irinta cikin wuyar nan baice uffan ba
Tahau bada labarin shagalin jiya,da yadda aka tara musu kudi wajen gasar rawan ango da amarya da akayi,amarya ta samu dubu uku cas cas ango ya same dubu biyu da dari biyar,tace Sai dai fa kuyi hkri dashi na sallame yan biki kunsan abun bawai na shirya masa bane,alhj Qasimu yanata murmushi uffan taher baice ba,shikansa yasan jin sallamar san yasata ƙara himman maimaita maganar da sukeyi na batun auren na sa,hirarsa ma a sama sama takomo amsawa tana jaddada masa cewa tabar musu yarinya marainiyan Allah
.tace"nide ba zama zanyi anan ba saiku riƙeta amana inmakun zalunceta Allah na kallonku, nide zan tafi tasha can anjima motar shayibu zaibiyo tashar sai kacewa danka daheru ya ajeni can.,alhj qasimu dake satar kallon dan nasa yaga ya sunkuyar da kansa can ƙasa ya bata shiru,yace babu damuwa mama ai gashi nan yanajinki,"my son kanajinta ko?kau da kai
Taher yy baice uffan ba ya gyara zamansa, suna cikin tattauna haka saiga shigowar matar gidan hannunta dauƙe da flask din ruwan zafi da wainar kwai da kayan karyawa
...ferfesun kan ragone cikin cooler da kayan tande tande an naɗe shi a babban leda wanda innono xata wuce da shi sabida yunwa dan sukansu basu san inata dosa ba zama innono tayi ta ƙarya sann
Ta sassaka musu albarka,tare da zuriarsu.
Ƙarfe Takwas saura wasimé ta farka bacci hannunta bisa baka tana kkrin tare wagegen Hamma daya taso mata hartakai hannunta baki saikuma ta firgita ta sauƙe tahau tattaba jikinta jin duk ta jiƙe da fitsarin datayi a kwance,subuhanalillah!!
da mugun gudu ta sauƙa akan gadon ta riƙe kirjinta dake bugawa da karfi fuskanta tamkar zatay kuka ta doƙa salati" innallahi wa inna ilaihi rajiun na Higa uku !!fitsari nayi,ta tattaba gadon sann ta tattaba jikinta"ayyy ashe fitsari nayi..yau na higga uku,a hargitse ta juyo cikin magagin bacci Da muryan tsoro tana neman innononta.innono
Ano..Cin karo da idon mutum akanta yasata yin tsit ta koma baya a tsomare kamar wata barauniya,"wata mata tagani agabanta sanye da riga da zani da wani baƙin hijabi,gashi Allah ya xuba mata ruwan ciki gaba daya sai taji hanjinta na curewa tsabar tsoro,suna hade ido taji gabanta ya fadi rass duk sai taji ta rude,duk damuwarta fitsarin datayi musu akan gadonsu tanayi tana waiwayen wajen,wayyo Allah rabonta datay fitsarin kwance fa yau yakai shekara guda kenan amma meyasa yau taga tayi kuma a gidan mutane?sai satar kallon jikakken gadon take da gefen idanunta da suka firfito tanayi tana damƙe zaninta da hannunta dake karkarwa, kiris ya rage Bilti ta fashe da dariyar yanayinta dan sosai ta bata dariya.
Cikin gyaran murya tace yan mata harkin farka?..zatayi magana bilti ta katse ta cikin sauri "natasheki kiyi sallah kince min toh ko harkinyi sallahn kenan?kanta ta sauƙar ƙasa kirjinta na bugawa fat fat,ta rasa mema zatace daga nan wani shirune ya dauƙe Wajen,murmushi kawai bilti tay snn tajanye hannun ta tay da ita bathrum,"Cire kayanki, ta umarceta sannan ta soma hada ruwan wanka mai dumi a bath,da kyar wasime ta kammala cire kayan nata ta tsaya daga ita sai pants,duk ta kame jikinta waje guda sabida tsoro da kunya jikinta duk rawa yake,haka ta dunkula kayantan a hankli ta ajesu kusa da wani empty bucket tana ta kallan inda tajikasu da fitsarin cikin nisan tunani,"Uuhum uhnmmm
Gyaran muryan matan ya ƙara firgitata ta dago kanta a firgice tace naam 'brush ta gani a hannun matar sabo dal a ledansa aka budesa,a hnkli tace,"xo nan kiyi maza ki goge bakinki saimu tafiko?tune din lallami datasa yasaka wasime gyada kanta batare da tay niyya ba, Ƙarasowa tayi kamar mai tsoron wani abu ta tsaya agefenta,Sink bilti ta kunna ta mika mata brush din tana kallonta harta kammala yi dakanta,She was bit relieve dataga ta iya batayi wani kuskure ba,bayan nan tayi mata wanka suka jajjaba alwala,.dan karamin towl ta dora mata sann ta jawota dakin ta koma ciki after like 5mint ta dawo ta sameta a inda ta barta tana tsaye,Batace mata uffan ba ta kalli gaban madubi "mikomin vasaline"babu musu maza taje ta dauko ta kawo,tana ajewa bilti ta dan jawota kusa snn ta soma tsantsane mata jiki ahankli snn ta shafa mata mai ta mulƙe ta tass ta gyarata..ganin ta runtse idanunta tana kakkame jikinta yasata sakin numfashi ta kyaleta mamaki da fargaba duk ya cika kirjin wasime,a nutse bilti ta kammala mata komi ya rage saura saka ƙaya saiga sallamar innono ta fado dakin fusknta murtuke,tsaye bilti ta miƙe da dan fara a a fuskanta tace "Kaka karde har an fito,kiyi hkri saura kiris inkammala shiryata,ganin wasime fess fesss yasa innono sakin fuska tana washe baki.."lahhh baiwar Allah harkunyi wanka.. kai sannunki da aiki,karki damu wallh dama ainice mai tafiyar ita kuma wasimé inazata ai tazo gidanta kenan, nima zuwa nay nan indan jira anan,ina ni ina kallon kayan takaici,mtsew Allah yabaka jika mai shegen mulki,".kinga na shirya zan tafi dayakaini tasha in samu shayibu shine wai saina jirashi yay wanka kuma fa fess jikinshi yake,aikoda na shunshuna dandamalin rigarsa da zai wuceni harwani qamshin inibi yakey,yo saide in hammatar sa ne bai wankeba,kenifa na lura dahiru fa dan walakanci ne dama shide akomi sai anjirashi..neman yayi mun kora da haline kawai
A gidan nan..nide ina ƙara baku amanar ƴata yannan kusamin ido sosai akansa karyaga kamar sadaqa aka basa ya wofantar da ita da jan fuskarsa awajen fatashhh kamar anja baya an kalli agogo..
hahahaha Bilti ta kyalkale da dariyar yanayin maganan nata dayazo da yanayin barkwanci tace "kai kaka toh karki damu da wannan indan wannan ne ai zamu kula miki sosai da wasimé surutai innono ta cigaba dayi abunta,daga nan bilti batace komi kawai tajanye zanin gadon da wasime tay fitsari ta wuce bathrum dashi,ganin anbarsu su biyu ta riƙo kafadun wasimê data cuno bakinta gaba tanajinta tamkar wacce zata sakar mata kuka, "kema sai sime sime kike ban kayan toh in saka maki,tasa hannu ta fauce kayan,Riga da sket ne mai kyau na back of fish
Amber colour dinkinsu na karkara ba amasa style din komi ajiki ba,Sosai wasime ta tsane Saka sket a rayuwanta,ita tafi sabawa da riga da zani galau galau taganta Kamar yadda ta saba acan kauyansu a jos,wani langwame wuya tayi ta larne kamar zatay kuka,"Innono wannan matsatsen abun kika samin?,keyanta taji an dungure ta baya"ke kinci uwaki,ki tsaya ingama sakamiki tukun zaki gani bazai matseki ba,tafin hannunta takai saman fuskarta tana turo bakinta a shagwabe har innono ta gama sakamata kayan yai mata rass kuwa sabida tanada ginannen jiki ba ita tsiririya sosai bace"
"yawwa baga ki nan kin fito ba,innyeeeee gangariya tsiren mangu..wazai ganki ahaka fess yace katuwa irinki kina fitsarin kwance?,cikin gatse innono ta furta hakan tana hararta sabida ta tsare farfarun rikicinta dantasan wasime da naci akan abunda bataso yanzu saitasa acanza' kayan nan,shiru wasime tay tana wasa da yatsun hannunta,kan gadon innono ta kalla snn ta kalli idanunta sai tafara mata magana ahankli Kuma cikin sigar lallami,yanzu fisabillahi wasimé saiki rasa abunda zaki kawo tsaraba a gidan surukanan naki sai fitsarin kwance?garinya akay haka..shiru tayi daga bisani idanunta ya cikko da ruwa ta dago muryanta a sanyaye tace
"Innono..ba laifina bane nifa Wani abu na dingaji yana fifitani cikin dare,sai naji kamar ana watsamin ruwa toh dana farka sainaga har waje ya jiƙa"
Wayyooo ahhhshh inno..no ..Kunnenta taji anƙama, sai kuma aka sake aka rungumeta sosai,ajiyar zuciya ta saki tanamai ƙara sakejikinta a kirjin innononta data kwantar da muryanta ƙasa kasa ta dada mannota da jikinta sosai,'"kinaji na ko?..toh karki ƙarayi ina gaya miki nan ba inda ya kamace ki da kiyi fitsarin kwance bane..nan fa gidan surukunaki ne kiyi musu biyayya kinji?..lafewa tay tanamai gyada kai childishly,jinta kawai take amma batasan komi ba, "ga nan BILTI zatana miki dukkan abunda kikeso,bance kuma ki sake jikinki ba,yadda kike aiki a gida can nan ma ki saki jikinki kiyi,nan ma gidane,inkina bukatar abu ki tambayeta kada kuma inji anyi kuka dake.
Ruwane suka cikko idanunta muryanta na rawa tace"innono wai barina anan zakiyine komi?ina zakije Ano?nide wallhy bazan zauna ba zan biki ..Ayanayin tausayawa tana kuma hararata tace "Sau nawa zan gaya miki da kizauna anan?hannu tasa a fuskanta snn ta fashe da kuka ni yaushe kika fadamin Kawai cewa kikay inshirya zamuzo binni Jiya naji kina cewa anmin aure,yau kuma shine zaki tafi kibarni anan wajen yoo akanme?ƙara sautin kukan tayi,innono cikin kyabe baki ta miƙe tsaye ta doshi kofar fita dan tasan batada amsar wannan rikici"ai saikiyi
Ni kinga tafiya,harta fara takawa sai kuma ta komo ta leka bayi lkcin bilti harta kammala dauraye bedding din ta fito dashi a bucket zatakai waje rana ya bugashi ya bushe,innono ta washe baki..."baiwal Allah bilti ni na wuce saduwar Alheri nagode nagode da dawainiya Allah yamiki albarka Allah yajikan magabata ,bilti tana murmushi tace karki damu kaka ai aikina ne.
Allah kaiki lpya ya kareki
Innono tace ameen,tana juyawa ta kalli wasime harta kammala hada jakarta ta runguma asigar bori,da sauri ta dauƙe ido kamar bata ganta ba tayo waje
Wanii fuuuuu wasimên ta biyo bayanta tafin hannunta bisa kan fusknta tanajin aranta kamar bazata ƙara ganin inonon ba,wani jan zuciyarta take dagske kamar wata mai aljanu idanunta na tara kwalla har ƙasa suka sauƙo cikin babban falon gidan,lokcin babu kowa a falon face Alhaj Qasimu da matarsa duk sun miƙe tsaye da shirinsu zasuyi rakiya wa innono,"matar gidan ne ta jawo hannunta tsakiya kowa na mata barka da safiya
Har suka kammala maganansu batace dasu uffan ba.Tana hankare da inononta,tana fita itama tabita kafa da kafa"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un innono dan ALLAH karki tafi kibarni anan wajen.ni wallhy saina biki,ni wallh bazan zauna ba. Wayyyo Allah na na sshhiga uku ta tumu aƙasan tiles ta dora hannunta aka,innono na innono na wayyo innono nikam saina biki ..Acikin rudani da firgici ta furta hakan tana tsananta kukanta daya kufce mata bazata.Kuka kawai wasimê take babu kakkautawa kowa na kkrin rarrashinta
Innono kam ko ajikinta danko kallanta batayi baretaji tausayinta,
zamanta anan din shiyafi,dan wannan shine rayuwa mafi daraja da inganci data bawa wani wanda ta taimakawa arayuwanta,ta haɗa jininta da wasime aganinta tayiwa iyayen wasimé dukkan halacci da amanan daya dace ace tayi musu izuwa ynzu,acikin zuciyarta tana matkar kaunar wasimenta amma haka tayi kamr batasan anayi ba Allah Allah ma take tabar wajen "Suna fitowa waje wasimé ta bude sabuwar shafin kuka "wayyo Allah na,innono innono,innono zanbiki dan Allah zan biki,wayyyooh Allah na kaf gidan saida ya dauƙa da ihun ta tana bubbuga kafafunta a ƙasa tana kuka sosai.,kusan hanklin kowa awajen saida ya tashi banda innono data cure bakinta sama tayi gum,tasan sukam sabone basuyi dajin kukan yaro ba barinma yaro mai rikici,a sace ta kalle wasime da gefen idanunta aranta ta kyabe baki ganin yadda ta turje ana fama da ita,dan kada kanta tay tace "zataxo ta saba ai,"danta Alhj qasimu ne ya riko hannunta cikin lallami kiyi shiru mama na,baya taja tace o o o o cikin sheshehka, kanta take girgizawa tana rabza ihu tana kiran innonon da ƙarfi,hanklin matarsa ya tashi ta rirriko kafadunta tanata lallashinta amma duk hakan baisa tay shiru ba,sunai mata kallan yarinyane amma basusan aranta tasan mame takeyiwa kuka ba.
Duk sanda innononta tace zatayi tafiya wani wajen dabaida suna toh tasan zata iya daɗewa sosai bata dawo ba.
Wajajen goma shaura anakan rikici da ita saiga taheer ya fito daga cikin gidan yana tfyarsa cikin sauri, murmurarren jikinshin nan yasha kwalliyar kananan kaya blue shit da black trousers data amshesa tamasa kyau, wani Sassanyar Qamshin bold rasasi da ck shiya mamaye iskan wajen wanda ya sakasu duka suka maida hankulansu kansa,wasimé ce kawai batako kallesa ba dan bakaramin ihu takey ita kawai a kyaleta tabi innononta ba,tun daga stairs yakejin ihun nata wanda hakan ya dada sa stern mood dinshi dada harzuƙa yabi ya ƙara harɗe fuskanshi tam yanajin haushin yarinyar aransa,wajen da akayi parking motar da zai kaita ya dosa,Innono da tayi tsinin baki taja ajiyan zuciya dataganshi,gyara tsyawurta tayi tana matsowa kusa da inda yake,toh Alhamdullh gama daheru ya samu fitowa ni kunga tafiyata,qasimu sai anjimanku,sauri tayi ta haubinshi abaya baya
Alhaj Qasimu ya fidda kudi mai dan yawa dayakai dubu biyar ya damƙa mata a hannu nashan ruwa,matarsa ma haka ta bata gashi suma sauri suke zasu fita,hannunta ta rike tam duk dama sai dukan hannun take tana ihu tana firgici,innono ta soma ƙirar "bilti, bilti,.,bilti tana isowa ta dauke wasimen cak ta miƙa mata ita sabida cikamasu kunne da takeyi,cikin masifa tanacewa"marar kunya kawai,ki wuce cikin gida da ita Intagaji zatayi shiru,da kyar bilti ta kamota ta riketa tana fifficikewa"innono tana ta sassaka musu albarka wani horn ya danna
da mugun ƙarfi kukan nan kam ya isheshi da gudu wasime ta hargitso wajen motar itama zata shige cikin motar aikuwa tana dososu,tsigar jikinta ya wani tashi sakamakon wasu dararan idanuwan sa masu ban tsoro da taga sun tsareta masu mugun firgitarwa,"kibace min anan wajen, a mugun razane taja da baya kamar an hanƙadata ta tsomare waje guda tana gunjin kuka tana kallon bakinsa daya furta mata hakan wnda kamar bada ita yay ba.Tunda suka hade ido dashi sai yanxu wata kalma ta shiga tsakaninsu,wani irin muguwar tsoronsa taji ya shigeta a take.
Wani shiru wajen ya dauƙa Baice mata uffan ba ya rufe motarsa a mugun fusace sanda ta razana ta ƙara ja baya a firgice..innono ta harareshi sabida sam batason rashin mutunci irin nashi,itade taja Allah ya isa in Advance dan bazata lamunci adaka mata yarinya ba mahaifyarsa tana dan murmushin yanayinsu "Allah ya kare,Alhj qasimu duk suka daga musu hannu,innono tahau matse idanunta tana daga musu hannun itama, dan ita saiyanzu ma taji tausayin wasime ya shige zuciyarta,Allah sarki wasimé,gashi basuy wani doguwar xama ba,kwata kwata shekarun nata tara ne kacal tayi mata aure,murmushin tasu ta tsoffi ta saki tana goge idanunta da bakin zaninta,"tasan hala kafin ta dawo hala harta ƙara girma daheeru ya maidata matarsa,yoo ko zataxo ma ta girma taso shi?inshi yaxo baisonta fa!!..kai duk dai tunanin shiirme suka soma dagula mata kwakalwa
sun bar gidan da kamar minti tara baice mata uffan ba ya kunna music a motar,biltice tay kkrin janye hannun wasime suka nufi cikin gidan wanda bacin razana datayi wani sabuwar shafin kuka da bori ta ƙara budewa, tun suna rarrashinta har suka gaji suka kyaleta,haka kowa ya fice akabarta agidan daga ita sai bilti,
ƙarshenta basuji sakat a kunnensu ba,har saida wasime ta samu tayi bacci danko abinci taƙi sam tasaka abakinta.
Bagaren su innono kuwa har suka isa kai tasha bata dawo daga tafkin tunanin shirme data shige ciki ba,wani irin horn mai ƙarfi yay sanda ta firgita taja innallalhi sann ta dawo hayyacinta
Babu halin yin masa magana sabida waƙar daya cikama mata kunne dashi,katon wajene mai dauƙe da yan union da fasinjoji anata hada hadan tafiye tafiye,adai dai gaban motar kauyen dazataje in yashawo kwana daf gaban wata rumfa yay parking snn yy lowering music dinsa,kansa ya maida baya ya jingina da seat ahankli alaman yana jira ta fita,nan da nan Saiga masinjojin tasha sun iso,malam tafiya ne?ina za'a kaiku,innono sai sime sime take sabida bakinta cikke yake da maganganu datake so ta masa, zuciyarta sai halbawa yake shiko ko ajikinshi,dan saiynzu taji ta balain damuwa tana sonjin raayin shi,ta kuma ji tabbacin amincewar akan auransa da wasimé,karfa suga suna yara ƙanana anmusu auren gata sudauƙa wasa ake musu ko aure bai dauru ba,in de balaga ne ai dahiru yanxu kam ya balaga,a kiyasce tasan yakai ashirin,wasime ne ma za'a ce batasan metake ba yanxu saita ƙara girma,amma tana fatan ratan hakan bazai sauya alaƙarsu ko matsayinta agunsa ba,shikam tagama kamar ko ajikinshi.,glass din gefenta yay winning snn ya bude mata ƙofa toh mun iso,tadan saci kallonsa ,wai ahakan ma itace kawai takan iyayi dashi iyayensa kam duka sun sangartashi,sai abunda yace dadin abun dai kawai yanai musu biyayya mai tsanani.
Ƙamewa tay cikin kkrin nemo notsuwa makanta
"Dahiru kozan iya magana dakai?..shiru yay
Can snn yace inajinki amma kiyi sauri ina da inda zanje,wani nunfashi taja Akan maganan auran nan ne dahiru kaji tsoron Allah,Hannu ya daga mata Alaman ya isa
Cikin lumshe ido da buɗewa yace"Kije naji!!..kada kanta tayi ta sauƙa sikinini saiga nan yaran motan shayibu sun dosu, kayanta suka deba suka kai mata har bayan mota,tana samun wajen zama taji kamar tsayuwar mutum agefen ta windonta tana waiwayowa kuwa taganshi a tsaye da wani abu ya dunƙule a hannunsa ya jefo mata yace"toh ga wannan kisha ruwa budewa tayi da mamaki taga dubunan kudi zasukai dubu goma sababbi, wanda ko iyayensa basu bata irinsa ba,murmushin baxata ya kufce mata tace Ahhhh toh masha Allah nagode dahiru Allah ya saka da alheri nagode,baice uffan ba ya juya ya tafi abunsa.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top