burning fur
4
Da kyar ya fita acikin tashar sabida cunƙuson motoci da suke shige da fice,haka kawai yaji ransa ya mugun ɓaci dan abu kadan yakan iya bata mai ransa wani lkci,tunda yahau kan titi ya rinƙa sharara gudu batare dama yasan ina ya dosa ba baijin kuma zai iya komawa gida ynzu,tsaki yakeja aransa shikadai yana furxan iska ta bakinshi yana fetsarwa waje,ya rasa meye takamamme ya ɓata masa ransa,a hnkli ya limshe idanunsa snn ya bude hannunsa dake kan stirring ya buga yace "damn it" daf yana kkrin shan kwanan anguwar GRA wayarsa ya dau ruri da kmar bazai kulaba can ya dauka a gaggauce
Kallo daya yay mata yaga Unknown caller ne akan screen,tsaki yaja snn ya jefar agefe yy banza da ita tacigaba dayi yana driving dinshi ahnkli,after like 2 more misd calls ya juya ya kallo wayar,ajiyar zciya ya sauƙe Cikin samar makansa nitsuwa ya sassauto da tuƙin dayakei sosai snn ya jona wayar da speaker.
,ba sallama ba komi muryansa a makurar shaƙe yace"Who is dis?..daga dayan bangaren akace"marar mutunci kawai..lumshe kyawawan idanunshi yay ya saki malalaciyar murmushi datazo mai a bazata bayan ya dago muryan mai maganan, babban abokinshine saheeb madugu, his one nd only best friend in the whole wide world sassauto da voice nashi kasa yy kamar bashi ya shaƙeshi yanxun ba,ahnkl yace heyyyyy mr
Saheeb..my guy how far na,Wallh yanxu nake tunanin nemanka,."daga dayan bangaren saheeb yaja tsaki mai tsayi acikin yanayin dariya "Kaidin ne kake tunanin nemana?asifff i dont knw u,abeg tsaya anan da ƙaryanka waye baisan kaba TEJ?Mama boy kawai, yana fadin haka ya yy yar dariya dan yasan da easiest way to annoy him is to call him dis name "mama boy"
..jin baima kulasa ba yasashi cigaba da maganan sa normal dan inda sabo ansabayin haka..yace"so how far na kana ina ne?yanzu na diro nigeria fa, there is serious problem mama boy u need to see me Asap,kaji mamaa boyyy,so where r u now?..ajyr zxcy TEJ ya sauƙe cikin shanye shirmensa yace "no where"kai kana inane ynzu?..kafin ya amsa shi cikin datsar numfashinsa yace just send me ur location gani nan xuwa dama akwai wata muhimmiyar maganan nima danakeso mu tattauna akai,da mamaki a yanayin saheeb yace okay amma lpya daiko,ya taɓe bakinsa akasalance irin in nazoma aizakaji,murya kasa kasa yace lpya lau,with much sight relieve saheeb yace aright sai kaxo toh ina gida ina jira,baice komi ba ya katse wayar.
Ajiyar zuciya ya sauƙe har ynxu wayar tana hannun shi ya riƙe duk tunanin yazai fara tattauna fears dinshi da saheeb ne,ya jingina bayanshi da kujera ahankli yy resting mind dinshi,after like 3mins of silent thoughts, ya murxa kan motarsa a slow ya nufi hanyar gidansu saheeb yana tukin a hankli kamar bazai yi ba,after 30 mins of driving ya iso kofar gidan
Babban gidane ƙirar gidan yan siyasa,gidan yaji security ciki da waje,ya iso lokcin duk yan ƙoram da mabarata sun mamaye waje ana kwalema dasu da jamian tsaro da Alama baban su saheeb din ne ya dawo nigeria,saheeb dan gidan masushi ne,suna da abunda ake ƙira kudi da gata,mahaifinsa both business/ politician ne he is curently a member house of represntatives
Yau gaban gidansu babu matsaka tsinke ancikka da motocin yan siyasa koina Ana jiran fitowarsa
horn Tej yyta doƙawa a bashi hanya ya wuce yaga bawanda ma ya kulashi Wani space yagani agaba yana Allah Allah yabi wajen ya wuce wani hilux cike da gayu suka datseshi,frm no wher yaji kiii iiii har ansha gabansa aanyi parking,baki bude yana kallon su suna dira da sanduna da adda "sai oga...sai oga...sai oga abamu hanya kai,tuni samaruka suka cikke kan hanyar da kyar yaja baya baya baya harsanda yaji yakai karshe "shit, ransa a mugun bace ya danna horn da ƙarfi cikin masifa shikadai yana cewa "what sort of rubbish is dis? Wani runtse idanunsa yy snn ya bude ya ƙara danna horn mai ƙarfin balai tamkar zai tsagawa kowa konne "bunch of idiots!!!Ya leƙo ta windon motarsa ya furta hakan cikin masifa kamar zai tashi sama meye haka Da Allah kubawa mutane hanya su wuce...garori kawai!"daga masu kallon sa a gatse sai masu maida masa martani acikin yanayin neman ayi,bai tsaya jin kowa ba ya koma cikin motarsa yay winning glass ya cigaba da danna horn,
Tuni yy drwing attention security da mutanen dake wajen kowa najan tsaki sabida dashi"wani dan bura ubane wannan?kutumar babban bura ubansaaa zai gwada mana danyen kaine eeehhhh waye wannan....dan gidan uban waye....bammm bamm bammm yan tarar aradu da ka suka hau bugamai jikin motarsa "malam Dallah kana cikamana kunne,yadda kaxo nan fa haka kowa ma yazo ubanwa zai aje maka hanya?inkasan kacika marar kunya ka bude motar kafito mana who are u dan ubanka? Aranshi yace"who want to know who i am,wayarsa kawai ya dauƙa ya kira layin saheeb akacemai not reachable,Kyam yy cikin car din idanunshi a lumshe hannunshi nakan horn din"Baidena danna horn din ba,shide kawai abasa hanya ya wuce and he wants it right now saboda wann jinin izza da mulƙi dayakei mamaya ajinin' jikinshi,akwai wani natural abu dayakesa shi ji dakanshi,sumtimes u feel too big at certain level,but not proud, if he wants sumtin he wants it to go his way nd nothing else...
Securityn dayazo kansa yy yay ya winning glasss suyi magana amma shiru baiko kulasa ba,"ai akwai yan sanda da sojoji aciki kawai akiramai su suci ubansa,kusan kowa hakan yake murmuring lkcin kusan kowa ransa ya baci da ƙaran daya cikamusu kunne dashi, ana cikin haka saiga tawagar mata da tsofaffi sun faso a bus din gwmnati da alaman yau ranan rabone Ganinsu yasashi dakatawa da abunda yakeiyi yabi motar da kallo,key yay ma motarsa kawai ya bar wajen ya nufi hanyar gidansu almost 10 mis calls daga saheeb yana kallo amma baiji zai iya dagawa ba,sallama yy ya tarar gidansun shiru tamkar babu kowa aciki,definatly yasan iyayensa sun fice harkokin gabansu,sanda da ya kalli hanyar room din mamanshi snn ya dauƙe idanunshi yasakai, room dinshi ya nufa yana tafiya a hnkli kamar wanda ruwa ya kwasosa duk ilahirin jikinshi babu wani kwari.,a hnkli ya turo kofa gameda sauƙe yar karamar ajiyar zciya waje ya samu ya zauna akan sofa yana shafa kansa gently,kai yaga kamar zaman bazai masa ba a malalace ya sulale ya kwanta tareda naɗuwa yanamai tattare kanshi kamar dan jariri,a rigingine ya kwanta tare da lafar da kanshi dayaji kamar tana neman mai ciwo.
cike da sanyin jiki ya rungume jikinshi datasomayin dumi a hnkli ya lumshe idanunshi tsawon mintuna bai budeba sai can daya tuna ashe ko ƙaryawafa baiyi ba Da kyar ya miƙe tsaye' sabida kasalar datacimma gabobin jikin shi,gaban wardrbe dinsa ya nufa ya bude wani site inda zallan kananan kayansa suƙe anlinƙesu tsaf komi na wajen is neatly arranged su boxers dinsa duk ajere,hannun shi ya zura ciki kan wata thick Armless shirt da black thr qtr,shap shap yay exchanging da kayan jiknshi tamasa kyau Bedroom sleepers fari ya zura akafarsa sann ya sauƙo ƙasa cikin sauri
Direct ya wuce dakin bilti nannynsa tun yana ƙaramin ya kwankwasa kofa"Bilti?..biltiiii..jin ba amsa ba ya bar wajen ya nufi hanyar kitchen danya sameta mamakine ya cika shi akirji dan wani irin ƙara ya dingaji harya ƙaraso kusa,yarinya ce take kuka kamar ba gobe rikicinta ya karaɗe gidan,da kamar bazai bude kofar kitchen din ba wani zuciya tace ya bude,aikuwa yana bude kofar kitchen din yagan wasimé a ƙasa tana firo da kwanuƙa tana cilla kafafunta bilti na tsaye akanta tayi tsinin baki..
"Wayyyooo Allah na waayyyiii nikam banason insha!!!bazansha ba..kuka kawai takeyi baji bagani tawani ƙankame jikinta idanunta na ruwan hawaye sharkaf...Tej ya daure ya matso kusa duk kunu ne a ƙasa an xubar ransa a dagule yace "Meye faru anan haka bilti?.a gajiye bilti tace Wallh nima na rasa tun fa dazu yarinyarnan take kuka taƙi tasaka komi a cikinta. "toh wai naga tay bacci ta farka nace hala yunwa zai dameta shine na dama mata kunun gyada amma kaga inda tayi firo dashi ya xube anan wajen wai bazata sha ba.."bilti tana cikin maganan wasimé tasa ihu tanamai datseta "wayyiii wayoo innono na nide kikaini wajenta..
wani fincikota sama taji anyi bazata,ranshi sosai ya baci sai yaji ya hatsala da sakarcinta
,tuni bilti taja baya dan wani ihu mai kara wasime tasa"Wayyooo Allah na na higgga uku dan Allah kayahakuri karka bugeniiiiiiii!
Da karfi Ya dangwalata a ƙasa tare da daka mata tsawa "shut up!!!kimin shiru kona tattaki anan,bakinta ta kama a birkice bata san tamayi hakan ba'yabi kanta da ihu kamar zai hadiyeta "kina hauka ne?.Nace kina hauka ne.. kar kar ta soma ɓari tana neman ragwabewa har ƙasa a zauce dan baƙaramin kadawa hanjin cikinta yay ba,shauran kunun data xubar ya kalla da gefen idonshiyaga akwai shaura dan ƙadan a cup wanda baigama tuntudewa ba yace wuce kije ki dauƙa kisha.."inda yatsarsa yabi tabi da kallo kafafunta sun ƙasa motsi suna ɓari bari karkar kar, wani tsawar ya ƙara daka mata saida ta fadi har kasa taci da bakinta bilti zata dagata ya ture ta. Ya fincikota sama ya tsayar da ita akan kafafunta,"ure very stupid ya dungureta, ƙiris ya rage tayi firsari ajikinta danhar wani awilo lonkomba kafafunta sukeyi tana gunjin kuka,..babu dandanin rahma a fusknsa ihu yake daka mata a tsakar kanta kamar baiga kankantar ta ba..kiyimin shiru nace miki ko..."kika ƙara bude baki agidan nan saina gijiyeki Are u mad?,gunjin kukan datakeyi ma tarasa yadda zaty dashi sai jan jan nunfashinta sama sama take kamr mai iska,tasan da wuya in ciwonta bai tashi ba, Sulalewa tayi da gudu zata bar kitchn din ya cakumota baya,wani ihu ta tsala mai ƙara yace..keeeee!!!ina wasa dakene?kalar kukan daya kufce mata ma batasan irinsa ba ta soma jajja da baya baya,wani irin cillata yay gaba a jirkice bilti tay wani zugum dik tarasa mezatace wasime saita fara bata tausayi, "take it now nd drink oll of it,stupid girl!!!a mugun birkice ta rarrafa ta jawo kofin kunun daya miƙa mata tahausha agabansa koinanta na ɓari lkcin kirjinta kamar zaiyi tsalle ya ballo waje,
yana tsaye akanta yana diri jikin bilti sai yay sanyi ganin yadda yarinyar ta birkice tana tuttusa kunu dan dole a hanjin cikinta,but she knows dole ne ana zare mata ido if not rikicintan yy yawa,uhumm yarodai yarone,mopper ta dauka zata soma kimtsa wajen tadan dauƙe kai akansu,tsakinshi ya katse mata zancen xucin datakei,direct ya dubeta yace..."Bilti im hungry..abunda take shirinyi ta bari ta kallesa,tace"toh me zakaci?..dan shiru yy
Snn yace "noodles..tace shikenan?kansa kawai ya gyada mata alaman "eh". Kallon wasime yake da ƙasar idanunshi yanajin kamar ya hadiyeta dan haushi,ya tsani fitina arayuwarshi,itako sai sheshhekar kukanta takei a hnkli aranta tana ganin kamar an zalunceta ne,acikin ranshi yaja wata arniyar tsaki, Wayarsa datai ƙara tasakashi fita agaggauce ganin Saheeb ne,and right now he is not even in the mood to xplain anything sama sama sukay magana yafada mashi dalilin dayasa ya fasa shigowa cikin gidansu ya datse wayarsa after like 15 mins ya dawo kitchen din ya samu bilti ce ita kadai babu wasime,kallo daya yy ma inda yabarta a tsaye din ya dauƙe idanunsa awajen,aransa yanataso ya furta ina wann yarinyar anma sai ya basar,qamshi mai dadi ketashi alamun bilti ta gama dafa masa indomie da soyayyen kwai dinshi suna hade ido ta murmusa tace "inkai maka cikin dakinka ne? Ko inkai...datsar numfashinta yy yace...no thanks i will take it myself a ladabce ya ƙarba plate din ya nemi waje a wajen ya zauna ya faracin indomie din a hankli,wani shirune ya dauƙe wajen bilti ta cigaba da ayyukan ta a sink,dan ƙadan ya tattaba indomien kwan ma baifi yanka daya yay masa ba yaji kamar ya koshi,abubuwa ne ciƙe aransa but irin feeling din nan na feeling too big yana so ya hanashi fiddasu waje haushin knshi ma yakeji,ransa na baci fa,he just dont seems to understand himself anymore He feel unnesssary worried for nothing dis days..
Baice uffan ba ya aje fork din agefe ya tashi ya fita,dakinsa ya nufa yana shiga ya bar kofarsa a bude bai kulle kofar ba ya kwanta akan gadonsa a rigingine yanamaida ajiyayayyen numfashi
Mirginowa yay can tsakiyar gadon tare da pillow a kirjinshi yanamai runtse kyawawan idanun sa wanda suke nan farare tas kamar ana wankesu da ruwan madara,ya dau mintina ahaka snn ya soma jin wasu abubuwa namasa yawo atsakar kanshi,...."a heart"...he just imagined a heart in his head,Sai kuma yafara kallon hoton xuciya acikin rufaffen idanunshi,zcyar tana bugawa da ƙarfi,so whats special about a human heart beating so fast?,fuskar wasimé ne ya bijiro masa cikin tunanin shi at once,zaune ya miƙe Asap,ya tuna how he saw her hrt gushing out with fear when she was crying dazu,something is wrong her heart aint beating normal, yes!!cikin sauri ya katse tunanin hakan ya bude idanunshi da sukayi sanyi ya miƙe tsaye a hankli yana ziriya cikin yin lissafi a brain dinsa.,inhar ya fahimce wani abu kamr her chest(esp bronchal) actually pump along with her heart.
...bayan ya kammala drawing conclusion dinsa a gaggauce ya durkusa gaban wata reading table ya bude gaban drwarsa ya fiddo da crayons nd oda drawing materials dazaiyi zane,dabiarsa ne yanada wani irin curiosity ne akan field dinsa na medicine da military,saidai in baiga ciwo ajikin dan Adam ba tofa zai gane,hakama inyaga criminal ko crime he must definatly find out the root
Zama yay yana mai baje babban white afo paper mai dan kauri akan flat drwing table dinsa until d paper is perfctly set nd flat,wasu kananun pins ya manna yayi pinning both sides of the ppr frm angles N,S,E,W ta inda ppr bazai taɓa yin wani motsi ba har agama zanen,a nitsen shi ya zauna idanunsa nakan paper yana shafawa,ya matso daf da drawing lamb ya kunna dim flourecent light control lamb Mai inganta lpyan idanu,Ajiyar zcya ya sauƙe sann ya soma aza tsadadden pencil dinshi na drawing akan papr tryn to capture a racing heart dats going round his mind,cikin mintina kalilan kuwa ya zana ƙatotuwar racing hrt mai azabar kama da zciyar mutum na gasken gaske,from seeing it kasan ya traino a fannin zane cos evrything was perfrct nd offhead bai kuma duba misali akoina ba.Tej is not just intelligent but a genious 'Wanda babu ƙarya hakan ya dada sawa yakejin kanshi cewa he is a big deal,dan wasu abubuwan dole sai dashi inbabu shi kuwa babu mai iyawa acikin field dinsu.
Pencil din ya soka agefen kunnenshi ya dauƙi zanen ya daga sama yana kalla,wani waje yaga kamar bai masa daidai ba ya aje kenan zai gyara wani irin ƙara mai karfi ya firgitashi a firgit ya miƙe Yana shaƙo muryan yay waje a gaggauce,direct yay hanyar ƙasa da niyyar duba kitchen yana Allah Allah ya iso,ƙaraf idanunshi yaci karo dasu a falo shauran indomien sa ne agaban wasimē bilti tana kkrin dura mata
Amma takici sam,daga zarar ya shiga bakinta saita tuntudoshi waje.
Haushin ƙwalemar kazantar datakei da abinci yasakashi dungule hannunshi batare da sannunshi ba...
Wani irin zaro jajayen idanunshi waje yay gwanin ban tsoro,take ya saki amon muryansa mai dibi dana balagaggen zaki"Waye yake cikamin kunne a gidan nan?wani tsit wajen ya dauƙa dukansu suka juyo a take suna kallonsa cikin yanayin matukar tsorata take ya kankance idanunsa ransa a ɓace yace."bilti turota tazo nan wajen,arikice bilti ta mika wuya zatayi magana..yaƙara daka musu wani gawurtaccen tsawa"ke!!!tashi kizo nan,Come here!!,sanda wasimé miƙe batasani ba tafara tafiya a tangal tangal kurwanta kamar zaiyi tsalle yabar gangan jikinta,abunka da danyen kai irinna sabbin deɓa wanda yasha Alluran sojoji nan kusa daya zare mata idanunshi sai caraf kuwa suka hade idanun su wani ihu ya daka mata....."RUN!!!..i said run are u Mad,faduwa a ƙasa tayi azabar tsoro ya sata miƙewa, ina miki magana kina min tafiyar yanga da sauri ta girgiza kanta sideways. "at the count of 3.a tsawace ya soma counting 1..2. Yana furta 3 yaji timmmmmmmm
A ƙasa yarinya ta sandare a sumammiya.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top