Twenty-two - Pound Of Flesh
In retrospect, kowa ya tsane Mahfooz. Shikenan babu wanda yake ganin nashi perspective ɗîn? Kanjamau fah aka ce, aids mai karya garkuwan jiki? Shine kuka zauna kukayi ta tsine ma Mijin Tauraruwa baiji ba bai gani ba. Especially yan Taskar Dimples kamar yayi maku wani gagarumin laifi. Anyway team Mahfooz dumu dumu, yan baƙin ciki su koma gidan Fauziyya da zama, ehe! #FullyDimplated
Tuƙi yakeyi zuciyar sa yana mugun tafasa, baya ko ganin gabansa. Saura ƙiris yayi arangama da motoci da suke lodin pasinja. Haka suka watsa mashi zagi sosai suna tsine mashi tareda kiransa ƙatan wawa. Bai ko kulasu ba ya danna motansa ya wuce. Sanda ya fito daga motarsa, bai samu damar ya rufe ƙofar ba, da sauri ya wuce cikin gida.
A hanyar ɗakinsa wanda suke kwana shida Faash ya iske Hajia Fatu Maman Faash, a gurguje ya gaida ta saiya shiga ciki. Wani zugi kansa ya soma mashi. Anan ya ɗauko ƙanƙara dake gefen gado ya saka a saman kanshi, har lokacin bai bar ganin dishi dishi ba. Nan take ya yanke shawara akan ya kashe wutan ɗakin, babu duhun daya wuce abinda yake wakana a rayuwar sa yanzu.
Yana san Naseera, tabbas yana santa. Amma ta cuce shi, ta ɗane shi da dafin da baya zaton zai iya warkewa daga gareshi. Bai taɓa soyayya kamar nata ba, kuma baya tsammanin zai taɓa irinsa. Ta gurɓanar da zuciyar sa. Ya sakankance akan soyayyar ta. Amma ashe duk yaudara ne, tayi komai domin ta cuce shi saidai kuma ta Allah ba nata ba. Ba dai mutum ba saidai Allah.
Tunani ya somayi kala kala akan yadda zai ɗauki fansa a gareta, shi baida zuciyar mugunta. Amma yanaso ya koya mata darasi, bama ita kaɗai ba duk matan duniya masu mugun hali. Yanaso ta zama ishara akan masu tunanin aiwatar da irin abinda tayi. Idan ya gama da ita, ko ruwan kwata zai fita daraja.
Anan dabara ya faɗo masa, nan take ya soma murmushi daga nan abin ya girma ya rinƙa babbaka dariya. Haka yayita ƙyalƙyatawa yana tafa hannayen sa.
“Qwaro kenan, hanjin jimina, an buga an barka.” Yayi ma kansa kirari.
Ita kuma Naseera tana kwance a gefe, har Rumasa'u taso tayi mirsisi ta tafi. Saita tuna cewa idan aka ga Naseera a mace gagarumin matsala zata shiga, gashi bataso ta sake komawa gidan yarin da aka kaita. Kallon gefe tayi hagu da dama, sai taga butan da ake bama furanni ruwa a gefe. Da sauri ta ƙarasa wajen, saita wuce famfo dake garden ta ɗebo ruwa. Kusan rabi haka ta cika, sannan taje inda Naseera take kwance rai hannun Allah. Gaba daya ta sheƙa mata tana zare ido, nan take Naseera ta soma tari a hankali kafin kuma abin ya tsananta. Buɗe idonta tayi tana ajiyar zuciya, duk ta birkice kamar gashin tsohuwa.
Tana zaune zaman dirshan a wajen, kallon gajimari takeyi, sai komai ya soma dawo mata. Cikin ƙanƙanin lokaci duka rayuwar data ke mafarki zatayi da mijinta ya ruguje. Akan wani dalili? Na ƙauran baki kokuma na gulmar Rumasa'u? Menene tayi ma Rumasa'u a duniya datake neman ta raba ta da duk wani farin ciki nata? Da farko ta dawo wajen Dr Abdallah, yanzu kuma Mahfooz.
Kuka ta fashe dashi data tuna cewa Mahfooz ya saketa. meyasa ya wurgar da soyayyar su ba tareda da bincike ba. Dama soyayyar dayake ikirari kenan duk baida zurfi. A fatar baki ne bai kai zuciyar sa ba. Yanzu akan wannan magana har ya danƙara mata saki. Idan baiso wani alaƙa ya shiga tsakanin su, ita taji ta gani zata iya jurewa, zata iya zama dashi a haka saboda tana bala'in sanshi. Sannan kuma idan da za'a juya lamarin zuwa gareta, tasan bazata guje shiba. Tare zasu magance kowane matsala saboda sun riga sun zama ɗaya. Amma kuma ashe iska yana wahalar da mai kayan kara ne bata sani ba.
Banda Alhamdulillahi rabbil alamin, Rumasa'u bata faɗin komai cikin ranta saboda tayi mugun jin daɗin sakin da akayi. Cikin sati kusan uku yau yana ɗaya daga cikin ranakun data ambaci sunan Allah. Idan tace ta mance yadda ake sallah babu mamaki. Babu mai shiga harkan ta, itama sabgar gabanta takeyi. Babu kuma wanda zaiyi tunanin zata iya aiwatar da gurmutsun kafirci. Sau ɗaya ta karanta Fatiha, wani rana datayi mugun mafarki, à firgice ta farka tana neman ceto shine tayi addu'a ta kwanta.
Ta samu taje gidansu Inna ta kwashe kayanta tas, ranar Inna tasha kuka kamar idanta zai tsiyaya amma ko a jikin Kankana. Ita Inna tasan babu haufi akwai jini tsakaninta da Rumasa'u amma ta rasa gane ta wani fanni. Dubu goma Dr Abdallah ya bama Rumasa'u domin ta siya su sabulu, toiletries da sauran su. Tayi bala'in raina kuɗin, kallon girman gidan tayi tana mamakin cewa wai ita ne za'a bama 10k. Toh wai me zatayi dashi, ta siya toothpick tayi sakucen haƙoran ta ko menene? Ita a ganinta masu kuɗi basu da aiki sai kashewa, ba'a investment ba'a komai. Tayi tsammanin za'a dire mata koba komai a tsiyace kamar rabin miliyan irin na welcome to the family. Nan take ta siya Kimono na 8k a meena parrot stores dake Instagram, sauran dubu biyun tayi subscription abinta.
Tana kallon Naseera ta tashi dakyar, bata taimaka mata ba. Ita dai tayi wanda zata iya ta sheƙa mata ruwa ta farfaɗo. Miƙewar ta keda wuya ta soma jin sabon jiri, haka ta sake durƙusawa. A haka Barira ta riske ta.
“Innalillahi meya sameta?” Tace cikin damuwa. Ita kuma Kankana wanda batada hijabi a baki ta soma magana, “Sakinta yayi wallahi, yanzun nan a gabana. Ina zai iya da salalan tsiya za'a shafa mashi kanjamau,” tace sannan ta wuce wajen garden domin ta huta.
Barira bata ce komai ba, tallabo Naseera tayi suka wuce ɗaki. Da hannu Naseera ta nuna mata durowan ta, tanaso a miƙa mata AVR ɗinta kafin wani abun kuma ya faru. Sannan kuma ta wuce bayi domin ta canza kayan Jikinta. Kafin ta dawo har Barira taje ɗakin Hajia Binti domin ta gaya mata abinda ake ciki. Lokacin suna zantawa da Anty Jawahir matar Uncle Sadiq ƙanin Dr Abdallah. Tana gaya mata gobe zata zo dasu Samosa da meatpie wanda za'a bama yan tarban lefe.
Su biyun suka wuce ɗakin Naseera, sanda ta fito sai ta gansu. Anan ta soma kuka, magana take kokarin yi amma baƙinta ya bushe. Duk wani ɗaci takeji kamar taci ganyen shuwaka. Anty Jawahir taje ta rungume ta, sarai taji abinda aka ce na batun aids amma bata damu ba. Emphaty before anything, ita kuma Naseera kuka ta cigaba da yi. Gashi kanta kamar ba nata ba, duk ciwo yake mata. Idanta shima kamar an lulluɓe da takunkumi bata iya buɗewa.
“Ya sake ni.... Mahfooz ya sakeni.... Ya sake ni kamar banida wani amfani a rayuwarsa, shikenan rayuwa na ya ƙare....” Saita fashe da kuka.
“Shhhh, karki ce haka. Komai ya faru da bawa daga Allah ne. Dama Allah bazai bar bawa bai jarabce shi da wani abun ba, kota lafiyar sa, ko arzikin sa, ko yaransa, kokuma miji ko mata. Dole akwai inda mutum yake fuskantar wani qalubali. Fatan da zamuyi Naseera shine muci wannan jarabawan ba tareda mun baranta akan turban kwarai ba.”
Hajia Binti ta ɗauki waya ta gayama Dr Abdallah abinda ya faru, dama yana chan gidan da zasu zauna da Mahfooz da masu decoration, duk notikan gadon ana kokarin haɗawa. Da kansa yakeso yayi abinsa tunda yana fatan aure ne na muddin rayuwar ta. Kwata kwata baya tunawa da Rumasa'u a matsayin ƴarsa. Shi yana ganin baƙuwa ce kuma wata rana zata tafi. Da sauri yabar wajen ya dawo gida. Anan yayi ma Naseera faɗa sosai akan rashin faɗin gaskiya, ai ba'a haka. HIV ba zazzabi bane da mutum zai ɓoye. Tayi kokarin ta faɗa mashi cewa sau da dama tana kokarin faɗa ma Mahfooz amma yana dakatar da ita, duk da wannan batun Dr Abdallah bai saurara mata ba. Shima saiya kira Daddyn Faash ya gaya mashi abinda ke ƙasa, baya garin yana Bauchi amma yace in sha gobe zai dawo. Kuma kai tsaye zai zo su zanta.
Kashe gari...
Naseera batayi wani barcin kirki ba, saƙo kala kala ta aika ma Mahfooz tana bashi haƙuri, tanaso ya fahimci batada niyyar cutar da shi. Babu abinda ya karanta. Bari yakeyi ya taru sai ya goge su. Yanzu ya dawo daga rakiyar ta, babu wani zancen yaudara da zatayi mashi kuma. Chan ƙasan ransa yana santa, yasa kuma yake tsoron idan ya bari magana ta shiga tsakanin su zai iya yafe mata. Kuma bata chanchanci yafiyar sa ba. Blocking ɗinta yayi a duka shafukan yaɗa zumunta, komai nata baya so ya gani. Ko hotunan da suka ɗauka tare yaso gogewa amma ya kasa. Anan ya kwashe a hard drive, saiya kaima Hajia Fatu yace ta ajiye mashi. Sannan yace koda nan gaba yace ta bashi karta bashi, baiso ya sake waiwayan su.
Ana zaune a falon da Dr Abdallah da Hajia Binti sai Naseera a gefe, Mahfooz ne yace Rumasa'u tazo taron tunda itama dangi ne. Abin kuma yayi mata mugun daɗi. Sai ta ɗayan ɓangaren da Faash ne, Daddy ɗinsa da Hajia Fatu da Mahfooz. Hankalin Faash yayi mugun tashi da yaji labarin, saboda sun soma shaƙuwa da Naseera. Ta fita daban daga sauran yanmatan dayake mu'amala dasu. Kuma shima yaga meyasa Mahfooz ɗin ya ruɗe. Hajia Fatu wanda ranar suka fara arba da Naseera taji ta cikin ranta. Domin ta riƙe ta tareda bata haƙuri. Kowa yaga gangancin Mahfooz.
Dr Abdallah yayi gyaran Murya saiya soma zayyana masu labarin Naseera, yanda ya aiketa tiryen tiryen har akayi mata fyaɗe, daga nan kuma ta kwashi HIV. Sannan yayi masu bayani tun ran farko aka sani ana treating ɗinta akai akai. An sheda masu aids ne critical stage, sannan kuma shine idan kanada shi ka zama abin gudu saboda tsautsayi kaɗan zaka shafa ma mutum. Duk bayanin da akayi kowa ya gamsu banda Mahfooz. Shifa ya kwana yana tunani, kwata kwata baiyi mashi ma'ana ba zata soshi bayan yaƙi taimaka mata, sannan ta kwashe kanjamau kuma zata shafa mashi ba. Gashi daren ranar Rumasa'u faɗa mashi makirci kala kala tayi yadda suka dauki alwashin cutar dashi yayi mutuwar wulakanci. Balle shi ɗin ya saba ji a labarai kala kala yadda yaɗuwan HIV yake, wai wata an shafa mata shine tace saita rama. Zance dai marasa kan gado irin wannan. Kuma tabbas Naseera auren fansa take so tayi dashi.
“Yanzu Mahfooz ka tabbata ba kaso ka mayar da matar ka duk da kaji bayanin da akayi?” Daddyn Faash yace. Saboda shi ya gamsu sosai. Dama baisan haka abin yake ba.
“Eh Daddy, na riga na gama magana.”
Sautin kukan Naseera aka ji yana tashi, tana bala'in ganin tashin hankali. Ta riga ta soma sabawa da soyayyar Mahfooz, bata tunanin zatayi rayuwa ba tareda shi ba. Tun da take karatu ta saka a gaba, wannan karan ne ta maida hankali sosai akan soyayya. Yanzu kuma an datse shi. Magana ta soma yi, koda bazai mayar da ita ba gwara ta faɗa abinda yake ranta.
“Hakiƙa baki shi ke yanke wuya, nasha gaya maka na tsane ka. Na sha gaya maka cewa bazan taɓa yafe maka ba. Nasan kuma na bika da kalamai masu zafi. Yasa duk abinda zance yanzu zakayi tunanin cewa saboda na samu ciwo ne kuma zan rama....” shiru tayi na wasu dakikai. Maganar bazai bada ma'ana ba ga sauran mutane banda Mahfooz. Kwata kwata ta kasa faɗa ma kowa shine yaƙi taimaka mata. Tabbas za'a rabata dashi, tunda rashin imanin yayi yawa. Ya roƙeta gafara kuma ta yafe mashi akan wannan batun. Saidai tayi fushi da wani abu daban amma indai akan rashin taimako ne ta yafe. She loves him that much, bataso ta ɓata mashi suna ko kaɗan. Sirrin shi sirrin tane.
“Laifi na babba ne Mahfooz, kuma bana tsammanin ka yafe min nan take. Kawai inaso ka tausasa zuciyarka ka dubeni da idon rahama kayi haƙuri, kalle ni Mahfooz, I am hurt fiye da yadda kake zato. Though bana tsammanin ka fahimta, kuma wallahi ina dana sanin rashin faɗa maka komai,” saita cigaba da kuka. Kamar gini ya faɗo mata a saman kirjinta, ranar ko abincin kirki bata ci. Banda ɓari babu abinda jikinta keyi. Bai tanka ba, kuma bashida niyyar tankawa. Ɗakin yayi tsit babu abin ke tashi. Dr Abdallah ne yayi magana.
“Toh yanzu zamu mayar maku da duk wani kuɗi da kuka kashe, sannan zance ma masu decoration su bari,”
“A'a Baba, idan babu damuwa ina neman alfarma wajen ka,” Mahfooz ya tare numfashin sa.
“Ina jinka...”
“Dama... Dama....”saiya soma inda inda. Shima yasan abinda yake shirin ambata hankali bazai ɗauka ba.
“Daman mène ?"Hajia Fatu ta faɗa. Ranta ya ɓaci sosai saboda har kannenta sunzo sai aka ce an fasa biki.
“Dama inaso a bani damar na aure Rumasa'u. Tunda itama dai yar gidan nan ce. Kuma tun asali ita na fara sani. Yanzu duk shirye shirye baza'a fasa ba, komai za'a cigaba kamar yadda aka soma...”ya ƙarasa fadi ƙasa ƙasa.
Gaban Naseera ne yayi mugun faɗi, da sauri ta zaro idanu tana kallonsa wanda shikam ko bin ta kanta baiyi ba. Miƙewa tsaye tayi tana hawaye tareda girgiza kai da hannu, “Mahfooz dan Allah kar kayi min. Dan Allah na roƙe ka.... Innalillahi na shiga uku na lalace!”
A hasalce ya soma magana, “Toh menene aibun ta? Kinaso ki tozarta iyayen ki ne bayan duk sun tara mutane? Besides it's for the best, Allah ne ya musanya min da wanda tafi alheri, da wanda tafi ki komai. Kuma ina gode masa.”
“Duk wannan hayaniya bai taso ba, ku dakata. Ke kina sanshi ?” Daddyn Faash ya tambaye Rumasa'u. Ita kuma ta kasa gasgata abinda ya faru. Dama ashe haƙuri yanada riba. Gashi yanzu ta samu Qwaro hankali kwance. Shine ma yake santa tareda begenta. Duk fairy tales ɗinta zai faru. Prince charming ɗinta yazo har gidansu.
“Ina sanshi wallahi... Sosai ma kuwa ai na daɗe ina following ɗinsa a Instagram.....” Nan ta fara zuba masu zance saida Hajia Binti ta dakatar da ita.
“Toh shikenan, Allah ya baku zaman lafiya,” Dr Abdallah yace, ransa a ɓace amma babu yadda zaiyi. Faash ne ya miƙe tsaye da sauri, cikin zafin nama ya nuna Qwaro, “Man you'll live to regret this, na rantse maka!” Yace tareda fita zuwa farfajiyar gidan. Shikam Mahfooz ko a jikinsa. Ranshi yayi farin fat kamar auduga. Wannan yana cikin abinda zaiyi ma Naseera wanda zata gigice taji kamar zatayi hauka. Shima yadda ta shayar dashi gubar baƙin ciki saiya shayar da ita dubun sa.
Wannan kenan!
Wash! Gashi babu yawa but still I came through as promised. Thanks again for the awesome comments, Allah ya barmu tare. My day was hectic, how was yours???
#Naseera
#Rumasau
#Mahfooz
#Tauraruwa
#MijinTauraruwa
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilicious
#FullyDimplated
Ainakatiti 💫
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top