Twenty-five - Love That Hurts
Bayan fitan Mahfooz sai Salima ta kira Kankana, anan ta sheda mata ai yayi zuciya ya fita. Nan take Salima ta bukaci ta tura mata address domin tazo ta ganta kafin ya dawo. Ran Kankana baiso ba, tana san mijinta. Abu daban ne waya da Salima akwai aure kanta, amma kuma wani mu'amala daban bata so tayi da ita.
Amma Salima ta zare mata ido tareda tuna mata cewa akwai alkawari tsakanin su, mutuwa ce zata raba su gwara ta daina nokewa. Rai baiso ba tayi mata text ɗin address ɗin. Ita karin kanta Salima gidan ya birgeta, saboda kusan komai Hajia Binti ta zaɓa domin Naseera.
“Kankana uwar ruwa, kwallon ki da ɓawanki magani,”
Hajia Salima tayi mata kirari sanda take shiga cikin gidan. Kankana kam murmushi tayi sosai mai bayyana haƙora saita amsa ledan hannun Salima. Kaji ne tasa masu aikinta suka gasa mata wanda yasha karas dasu albasa sai kamshi yakeyi, kuma tanada sinasir wanda akayi micro waving ɗinsa. Ita a tunanin ta Mahfooz zai kai dare bai dawo ba domin baƙin ciki. Sai tayi amfani da wannan damar suyi ƙaramar picnic. Ga kuma farm fresh masu sanyi cikin ledan. Duk wani ɓacin rai da Kankana take ciki saiya soma washe wa. Dama ita tunanin yadda zatayi yau takeyi, saboda kwata kwata ta gaji da cin dublan. Tanaso taci wani abu mai ɗan Maggi amma bazata iya dafawa ba. Tsabaragen ƙiwiya ke ɗawainiya da ita kuma gashi bata iya kunna gas cooker ba.
“Amaryan Mahfooz koko nawa ne?” Salima tace tana dariya. Ita kuma Kankana yaƙe tayi mata bata so wani yaji zancen.
A two seater Salima ta zauna tana ajiyar zuciya, har lokacin Kankana tana tsaya kerere bata ce komai ba.
“Ki saka mana abincin mana a kwano ni yunwa nake ji,” har Kankana ta soma tafiya sai Salima ta sake magana, “Sannan kuma ki haɗa min kofin shayi,”
Kankana ta rasa yadda zatace ma Salima cewa basuda madara, gwangwanin mediun wanda Mahfooz ya siyo tun ranar farko ta shanye shi tas. Haka tasa a gaba tayita lasa, ita a ganinta an saba takura mata akan ta ɗiba cokali biyu ko ɗaya, yasa yanzu tana gidanta zatayi abinda taga dama.
“Meye haka? Ina madarar kin kawo min shayi kamar fitsari?” Salima tace a hasalce, ta mance yaushe rabon data sha shayi ba madara, ko dan marmari batayi.
“Hajia Wallahi madarar ya kare ne, kuma ɗazu yana fushi ban samu damar gaya mashi ba,"
Kallonta Salima tayi, idan ba madarar gwangwani ƙarami ba babu yadda za'a ce aure kwana biyu har abinci ya soma ƙarewa. Balle tana hangen gwangwani medium akan dinning table.
“Mayar da abin ki bana sha,” tace saita fara yago kaza. Kankana itama da sauri takai kitchen ta koma falon. Bataso Salima ta shammace ta harta cinye bata samu ba. Haka ita ma ta saka hannu sukayi ta ci babu kakkautawa.
Sam Mahfooz baiga laifin Rumasa'u ba yadda ta guje shi, saboda shima yana gudun Naseera ai. Saidai zai wayar ma Rumasa'u da kai akan cewa shifa lafiyarsa ƙalau babu abinda ya kama shi. Ya lura akwai tsoro fal a idonta, saiya je gidan wani abokinsa wanda suke aiki a Julius Berger. Anan ya wuni saboda ya bama Rumasa'u dama harta huce sosai.
Da la'asar sakaliya, da kanshi yaje wani shago inda ake haɗa su kyaututuka ya siya fulawa, teddy bear da Chocolates masu yawan gaske. Yanaso ya bama Rumasa'u haƙuri akan shigo shigo ba zurfin da yake kokarin yin mata.
Ya ɗau hanyar gida kenan sai aka soma gagarumin hadari, da sauri ya ƙara gudun mota baiso ruwa ta riske shi a waje. Amma dayake kaddara ta riga fata ruwan nan take ta sauko kuma da ƙarfin gaske. Lokacin Salima tana ɗakin Kankana suna kwance, tun azahar suke barci babu abinda yasha masu kai.
Saboda ƙarar ruwa basuji dawowan Mahfooz ba, dama gate ne kawai suka saka mashi makulli kuma Mahfooz yanada wani a motarsa, yaga motar Salima a cikin gidan amma bai kawo komai cikin ransa ba. Duk tsammanin sa irin wanda suka zo ganin ɗakin amarya ne. Balle ance amare akwai su da farin jini kamar kuɗi.
Koda ya murɗa ƙofar falo baiga kowa ba, sai ya wuce ɗakinsa kai tsaye domin yayi wanka da ruwan dumi. Ita kuma Salima cewa tayi dole Kankana ta bita suje ɗakin Mahfooz su kwanta chan, tunda dai ta fishi matsayi a wajenta. Yana cikin murɗa ƙofar ɗaki Kankana ta ɗirko daga kan gadon da gudu. Dayake batada wani kayan kirki kuma Mahfooz yagan su haka sai ya saɓa mata sosai. Ita kuma Salima ɗaurin kirji gareta tayi male male Kamar gadonta.
“My husband, muje falo Gwaggon muce ta wajen su Mallam tazo ganina shine ruwa ya riske ta,” saita janye mashi hannu suka koma falo. Jinin jikinsa bai bashi ba, kwata kwata bai yarda da maganar ba, shi a nasa sanin basuda yar uwa hamshaƙiya, saboda kalar motarta daya gani a waje yafi nashi armashi. Sai kuma ya tuna cewa Rumasa'u ba zatayi mashi ƙarya ba, sai hankalin sa ya kwanta.
Ita kuma Salima likimo tayi dataji Mahfooz, gabanta ya rinƙa duka uku uku. Ta bala'in jin daɗin yanda Rumasa'u ta gyara masu wasa bai gane dawar garin ba. Dan kuwa daya ci masu uwa duka su biyun. Tabbas saiya kusan halaka su.
“My husband me ka kawo min?” tace tareda amsan ledan hannun sa. Da wata ce daban da yaji haushi, saboda abin babu aji ba'a baka abu ba amma ka amsa. Saidai wannan daban ce, matarsa ce abin ƙaunar sa kuma taji daɗin ganin sa ne. Ta bala'in birge shi yadda bata ɗauki abu da zafi ba tana kumbura fuska. Ya nuna mashi ita ɗin daban ce cikin mata.
Haka ta rinka fito da ledan tana duba abinda yazo dashi, kallo tayi taga dalilin daya sa ya kawo mata fulawa da yar bebi watau teddy. Ashe receipt ɗin cinikin dayayi yana cikin ledan ya mance bai cire ba, nan taga dubu sha takwas.
“Haba my husband aini da kuɗin ka kawo min akan wannan shirmen!” tace cikin takaici. Saita ɗago ta kalle shi, “Dan Allah idan ba waya ba ko kaya ni karka sake kawo min fulawa, Haba jama'a ubana aiba gardener bane!” ta soma sababi. Lokacin Hajia Salima ta fito zata tafi, sanye cikin kayanta wanda ta watsar gefe ɗazu. Har ƙasa Mahfooz ya durƙusa ya gaida Salima. Ta yaba da halinsa sosai kuma ta tausaya mashi.
Kankana da kayanta na badala wanda duk baya a waje gashi gareje ta raka Salima mota. Anan Salima ta sake jaddada mata akan alƙawarin su. Koda Rumasa'u ta dawo ɗaki Mahfooz ya shiga wanka. Duk tsammanin sa kafin ya fito zata jera mashi abinci kala kala akan dinning table kamar yadda amare keyi.
Farin Jallabiya ya saka, saiya feshe jikinsa da turaren Creed. Ita tana Instagram tana kallon faɗa a shafukan gulmace gulmace tanata dariya. Kamshin turaren sa ya janyo mata hankali, yayi kyau sosai kuma ya bala'in birgeta. Murmushi sukayi ma juna daukar sa abincin yana kitchen.
“Baby kawo min abinci wallahi banci komai ba,” yace saiya zauna akan one seater.
Ko kallon shi batayi ba ta soma magana, “Nifa ban girka komai.” Saita cigaba da danna waya. Har yaso yaji haushi saiya saisaita kansa, bayaso yayi mata faɗa kuma babu hakkinta. Kila wani abu yana damunta ne.
“Meyasa?” yace muryan sa yana rawa. Cikin yanayin ko in kula tace, “Saboda banjin daɗin jikina. Har yanzu gajiyar biki bai sakeni ba,”
Bai ce komai ba ya tashi ya wuce kitchen, kallo ya somayi ko ya dafa jollof ɗin taliya, sai yaga zai daɗe. Anan ya fasa masu Indomie guda uku ya daura. Koda ya buɗe fridge ɗinta yaga su kayan miya sosai wanda Hajia Binti ta aika mata. Sannan ga albasa a wani kwando gefe. Haka ya zauna ya girka masu mai rai da lafiya ya juye a faranti yakai masu.
Shi fa bayaso ya sake firgita ta, domin yaga bala'in kokarin ta ma data yarda ta aure shi dukda tasan mu'amalan su da Naseera. Inda ya barta nan ya sameta. Ita tama mance dashi tasha ya kwanta ne. Koda taji kamshin abinci tana tunanin daga maƙota ne yake ɓakunta su. Hannunta ɗaya take dannan waya ɗayan kuma chocolate ne wanda ta gama kushewa tana ci.
Murmushi tayi sosai mai bayyana haƙora, bata ta yashi karɓa ba shi kuma bai damu ba. Da kansa yaje fridge ya ɗauko masu lemu. Robon ya ƙare saura daya, saiya bar mata shi zai ci da ruwa.
“Baby sauko mana muci,” yace tareda miƙa mata cokali mai yatsu. Data sauko ta soma bincika abincin, sai daga bisani tayi magana, “My Husband haka kayi mana abinci lami kamar talakawa? Mummy ta kawo bushenshen kifi ai,” tace tana yatsina fuska.
Takaici yaji sosai, rainin wayon dayawa yake, tun yana mata uzuri sai kuma ya lura asalin mara mutunci ne. Saidai kuma yau fushi ba nashi bane. Yazo ne domin suyi sulhu. Bai amsata ba ya soma cin abinsa, duk ransa ya jagule. Itama babu arziki ta fara ci, wanda taci yafi na Mahfooz yawa. Sannan ta tashi tabar kwanan ta hau kujera. Bawai Mahfooz takema haka ba, ita bata iya cin abinci takai kwano kitchen ba. Nan take bari. Kuma koda ta zubar da wasu garin ci haka zata tashi. Wani ne zai kauda mata shi. Haka kuwa ya kwashe kwanonin sannan ya wanke su kafin ya fito. Lokacin ana kiran magrib. Yasan zata iya mashi tsiya ta rufe ɗaki kafin ya dawo yasa yayi sallah a gida.
“Baby muje muyi sallah,” ya umurce ta.
Ranta bai so ba. Tun zuwanta gidan batayi sallah ba. Ko ɗazu da azahar tana kallon Salima tana sallah amma tayi burus abinta tana danna waya. Rashin sallan ta ya samo asali ne tun tana make-up kuma bazata iya sake alwala ba kafin ta chaɓa, yasa take burus tace zatayi cikin dare. Lokacin kuma tayi mugun gajiya barci yayi gaba da ita. Dama su Inna suke tilasta mata sanda suke tare yanzu kuma basa nan.
Shine ya jasu jam'i, anan yayita binsu da addu'a kala kala. Dayawa daga ciki tasani kawai iya shege ne yasa batayi. Ita kanta tasan cewa taji daban cikin ranta. Wani sanyi yayita sirara cikin zuciyar ta. Da ta saba jin kanta cukus amma yanzu she felt light. Tunba yauba tasan cewa akwai wani sanyi da sallah yake dauke dashi, kawai dai lokacin tana yawan gajiya ne kokuma tana barci.
Janyota jikinsa yayi ya riƙe, saiya soma magana a hankali, “Nasan kina tsorona saboda kina tunanin inada HIV. Amma wallahi ban kwasa ba.”
"In ji wa?” tace. Ita fah tana nufin inji wa yace akan HIV ne, shi kuma ɗaukar sa tana nufin inji wa yace masa baida kanjamau.
“Na duba a asibiti, wallahi ance banda komai. Kinga wannan gudun dake kiyi bashida amfani. Wallahi lafiyana lau.”
“Wai kana nufin ina rufe ƙofa saboda ina tunanin kanada kanjamau ne?” tace, sai kuma tayi tunanin wannan dalilin zata iya amfani dashi domin kaucewa hauka. Ita da badin Hajia Salima ba, bata ganin tana jin tsoron kanjamau. Musamman tunda Mahfooz nada kuɗin sa a aljihu. Bai kashe Naseera ba bata tunanin zai iya kasheta.
“Allah babu abinda zai kamaki,” ya sake jaddada mata. Tana sanshi amma wannan abin yafi karfin ta, taso ta gaya mashi yaje wajen Hajia Salima su roketa alfarma, idan kwana zasu rinƙa raba wa harda ita toh. Dan dai bazata taɓa aminta dashi ba. Bataso ta gwada balle taga ko hauka zai kamata. Saidai kuma taga dabarar baida ma'ana. Anan taji haushin kanta ainun. Sam batada zurfin tunani ta kubutar da kanta daga cikin matsala.
Ɓanɓare kanta tayi daga jikinsa ta soma sosa ido, “Ni fa gaskiya ka kyale ni,” tace masa tana hamma. Ɗaci yaji cikin zuciyar sa. Wannan wani irin ango ne mai baƙin jini wajen amarya. Saidai yana mata uzuri.
"Zan baki lokaci kiyi tunanin, kinji babyna.” saiya miƙe tsaye. Yaso yace mata yana santa domin ya karfafa mata gwiwa, amma kuma ya kasa. Wannan kalma yanada muhimmaci wajen sa kuma ba kowa zai iya furtama wa ba.
Shafa mata kai yayi saiya hau saman kujera, ita kuma batace ko ƙala ba ta wuce ɗaki. Yau bata rufe ƙofa ba, tanada yakinin cewa Mahfooz bazai shigo ba. Baje baje tayi akan gado tareda kunna AC yana shigan mata jiki.
Kashe gari Mahfooz yazo tada Rumasa'u domin tayi sallah, shima yaji daɗi sosai dayaga ƙofa a buɗe. Wannan kawai ya nuna mashi cewa ta soma nazarin maganar dayayi kuma tana dabda haƙura akan abinda tace. Ita kuma ce masa tayi bata sallah dan Allah ya kyaleta, ko kallonsa batayi ba asali ma cikin tsawa ta gaya mashi haka. Gwiwa a sanyaye ya fita yabar ɗakin. Da wasa da wasa auren ya fita daban da abinda yayi tunanin zai faru dashi. Komai ya cunkushe mashi, ba abinci, ba magana mai daɗi, gashi tunda suke gidan ba'a share ba. Uwa uba kuma tana gudunsa. Wani zuciya ya raya masa cewa da Naseera ne ba zatayi mashi haka ba, anan ya tuna da kamshin girkin ta wanda ta saba mashi idan yaje lokacin. Da sauri ya kauda tunanin daya tuna cewa Naseera tanada kanjamau.
Haka zaman su ya kasance har sukayi kusan wata ɗaya, kuma cikin kwanakin nan sau uku tayi mashi girki. Shima duka Indomie ne. Idan Mahfooz bai siyo masu takeaway ba toh zai dafa ma kansa indomie. Salima ce ta kuma koya mata yadda zata kunna gas. Shima randa taso girka abin kirki zatayi shinkafa da miya haka ta kona shinkafar a tafasar farko, gidan yayita ƙauri kamar anyi gobara, har aka kwana gidan yanata ƙauri. Ga kuma tukunyar yayi baƙin ƙirin. Mancewa tayi sai ta shiga group ɗinsu na one love tana chatting dasu. Yanzu sun san time table ɗin Mahfooz, musamman sanda yake zuwa training ɗin kwallo sai Salima ta lallaba wajen Kankana domin su ha'ince shi. Shikuma yanata haƙuri yana jiran randa zata aminta dashi.
Dr Abdallah baida lafiya sai Mahfooz ya ɗauke Rumasa'u domin suje gaida shi. Ranar murna fal ranta saboda tanaso taje taga yadda yanayin Naseera yake. A kayan data kai ɗinki na cikin lefenta ta ɗauko leshi ɗaya ta saka. Swiss ne mai kalar omo kuma ya amsheta. Haka ta saka zobuna da warwaro sai sheƙi takeyi. Gashi fuskanta ya dauki make-up kamar ranar ne aurenta. Duk daukar Mahfooz zata haƙura ranar tayi ma Dr abinci domin su kai, shi ya riga ya cire rai cewa iyayen sa zasu ci abincin surikar su.
Ƙememe tayi tace bazata yi ba, ai Barira tana nan kuma zata girka suci sannan har dinner zasu dawo dashi. Yana kokarin nuna mata fa'idan abin amma tayi burus dashi. Asali ma waya ta ɗauko ta kunna waƙar Naira Marley na Opotoyi ta soma rawa ko a jikinta. A hanya ya biya wani bakery ya siya su snacks saiya haɗa da drinks da fruits. Kwata kwata abin babu girma suje hannunsu yana dukan cinya.
A gida aka kwantar da Dr Abdallah, Naseera ce ta ɗauki ragamar dubashi. Itama jikinta ya soma warwarewa kuma tace tanaso ta koma bakin aikinta. Ummanta bataso ba amma kuma babu yanda zatayi, tasan zai rage mata zaman ɗaki da tunani kala kala.
Tana ɗakin ta canza masa drip, magana sukeyi dashi jefi jefi. Koda yake shine yaketa binta da surutu kamar baya ciwo. Idan kaji muryan sa a waya zaka rantse lafiyar sa ƙalau.
“Assalamu Alaikum,” Mahfooz yace sanda suka murɗa ƙofar. Rumasa'u tana biye dashi a baya tana ware ido kamar ragon da aka yanka da layya.
“Waalaikumus Salam,” Naseera ta amsa. Amma bata ɗago ta kalle suba. Kirjinta yake bala'in harbawa kamar zai fashe. Stethoscope ɗinta ta soma tattara wa da kuma sauran kayan aikinta. Su kuma suka samu waje akan kujera suka zauna.
“Baba ya jikin?” Mahfooz yace.
“Sannu Daddy!” Rumasa'u tace.
“Alhamdulillahi, ai da baku zoba. Wallahi ba abin tashin hankali bane. Kawai dan inada likita cikin gida shine ta kwantar dani.” Ya amsa yana dariya tareda kallon Naseera. Yaƙe tayi mashi saita fita da sauri. Data kai bakin ƙofa saida tayi tuntube inda komai ya watse ƙasa. Da sauri Rumasa'u taje domin ta taimaka mata.
Ba Naseera ba harta Dr abin yayi mashi daɗi, koba komai they are relating. Da sauri Naseera tabar wajen ta koma ɗaki tana ajiyar zuciya. Bata san cewa Rumasa'u ta biyo bayanta ba, sai kawai ta ganta tsaye saman kanta tana mata kallon hadarin kaji. Sai ta soma safa da marwa cikin ɗakin tana dube dube. Daga bisani ta dawo ta kafa mata ido kana ta soma magana.
“Idan zan baki shawara kiji gwara tun wuri ki zubar da shegen dake cikin jikin ki,”
Zaro idanu Naseera tayi, watau bayan Mahfooz har Rumasa'u tasan da zancen shine yayi banza da ita. Bata san sanda hawaye ya fara fito mata ba. Tasan yana fushi da ita bata san cewa abin ya kai haka ba. Domin ita bata cire rai da komawa ɗakinsa ba.
“Wai mamaki kike na san da zancen? Lallai shiya faɗa min kuma yace yayi banza dake saboda yana kyautata zaton cewa yaron ba nashi bane,” saita taɓe baki, “Kuma ko ni ce bazan yarda ba tunda dai ba'a san asalin labarin yadda kika samu kanjamau ba,”
“Bazan zubar ba, tunda kece yar aike. Kije kice masa bazan zubar ba, kuma koda bazai amsa yaron a matsayin nasa ba ni ina san abina,” tace mata saita share hawayen idanta.
“Wallahi tun wuri kisan me kike yi ki zubar, kila ki samu wanda zai aure ki. Kina tunanin cewa akwai wanda zai aure ki da Kanjamau da kuma yaro?”
“Toh wai ina ruwan ki? Tashin hankalin menene kika shiga? Inace yanzu kina auren sa sai kema ki haifan masa yara mana ki barni na huta.”
“Banaso a ɓata ma mijina suna ace shine uban shegen jikin ki, balle kuma ta ina kike da Kanjamau shi bai kamaba idan shine uban yaro. Malama karki raina mana wayo dan Allah. Muddin shine uban yaro yaci ace shima ya kwashi salalan tsiya... Nima fah naje boko kuma ina kallon BBC,”
Tashi Naseera tayi zata je wajen Mahfooz, abu ɗaya ne ya wulakanta ta amma kuma bazata jure matarsa tana cin zarafin ta ba. A hanyar sauka ƙasa ta ganshi yana tafiya.
“Mahfoozz....” Tace mashi.
Cak ya tsaya kamar an dasa shi, akwai yanda muryanta ke mashi tasiri cikin zuciya. Saidai ya kasa kwatantawa tsakanin soyayya kokuma kiyayya. Juyawa yayi fuska babu wasa tareda saka hannu ɗaya cikin aljihun wandonsa.
“Menene ?”
Runtse ido tayi cikin takaici, duk wani masifa data zo yin masa ta kasa. Wai yau wanda zuciyar ta yake so yake mata haka. Tafiya ta somayi zuwa wajensa, saidai gwiwanta yayi mata mugun sanyi. Ji take kamar zai zubar da ita ta faɗi ƙasa. Amma a haka ta daure domin ta je wajensa. Miyan bakinta yayi bala'in bushewa kamar takarda. Harta hannunta rawa yakeyi, zuciyar ta banda gudu baya komai.
“Kaine kace ma matarka ta gaya min cewa na...” saita dakata. Ta kasa tambaya akan zubar da cikin.
“Look Naseera, babu abinda zai sake haɗani dake. Koma menene kawai ki kyale ni,” Saiya juya.
“Wait,” tace saita kama mashi hannu da sauri.
“Dan Allah ka saurare ni,” saita soma kuka. “Dan Allah kayi magana dani just this once, Mahfooz I'm hurting fiye da yadda kake tsammani. Yanzu shikenan duka soyayyar da mukayi ya tafi a banza?” saita share fuskanta, “Haba mijin tauraruwa, ni ce fah. Naseera ɗinka harka mance dani so soon. Ka mance da irin alkawarin da kayi min sanda muke ruga. Kaine fah ka koya min yadda zan soka. Kaine ka raine zuciyata domin ta aminta dakai. Yanzu duk bugun da yake yi sunan ka yake faɗi. Meyasa zaka watsar da komai. I made you happy, we used to be happy. Ni da kai against the universe.” saita ƙara matsawa dab dashi. Ta lura cewa ya soma saukowa daga dokin ƙarfe.
“Couples fight mana, ai aure ya gaji haka. Kuma mistakes are what makes us human. Na fahimci meyasa ranka ya ɓaci. Kuma I promise you bazan sake maka ƙarya ba. Please Baby ka yafe min. Ka maidani duk abinda kake so wallahi zan maka babu musu.” saita durƙusa ƙasa tana kuka tareda riƙe mashi ƙafa. Sannan kuma ta cigaba da yin mashi magiya.
“Mahfooz rayuwa ta bazata taɓa samun natsuwa ba idan babu kai ciki, idan ka guje ni bazan sake murmushi ba, I'll live a sad life and refuse to be happy. Dan Allah ka agaza min.”
Anan Hajia Binti tazo ta ganta, da farko sakin baki tayi tana mamaki sai kuma taje da sauri ta janye ta. Mari ta zabga mata saita soma masifa.
“Yaushe kika koma haka? Meyasa baki san darajar kanki ba? Yace bayayi ana dole ko shi ne autan maza. Ance maki ko sujjada kika kwana kinayi zaki birge shine?”
Shiru Mahfooz yayi ya sunkuyar da kai, baiji daɗin yanda Hajia Binti taga haka ba. Duk sai yaji babu daɗi zuciyar sa ya jagule.
“Ni bazan iya rayuwa ba tareda shi ba.... Rayuwa na baida amfani Umma.... Koda yaushe komai a kaina yake faruwa, Why always me?” ta faɗa tana kuka saita soma ja da baya. Anan cikin tsautsayi ashe bata taka bene ɗaya da kyau ba. Nan ta zame ta mirgina ƙasa.
“Innalillahi wa inna ilayhi raji'un!” Umma da Mahfooz suka faɗa da karfi a tare tareda sauka ƙasa domin ta. Ita kuma ta buge kanta jini ya soma fita ta bakinta. Magana take so tayi hawaye yana fita idanta amma ta kasa, anan ta fita hayacinta tareda lumshe idanta.
Wannan kenan !
#Naseera
#Rumasau
#Mahfooz
#Tauraruwa
#MijinTauraruwa
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilicious
#FullyDimplated
Ainakatiti 💫
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top