Twenty-eight - To Be Tainted

_Assalamu Alaikum Dimplicious Empire, barka da sallah da fatan na same ku lafiya? Allah ya maimaita mana cikin ƙoshin lafiya da walwala Amin. Wanda basuda da lafiya Allah ya basu, iyaye, kakanni da yan uwa da suka rigamu zuwa gidan gaskiya Allah ya jikan su, muma Allah ya kyautata karshen mu. Allah ya kare mu daga sharrin mahassada da kuma sharrin shedan, ya tsarkake mana zukatan mu daga aikin dana sani, Amin summa amin. A Ontario nayi sallah wajen Yaya Labib, kufa ? #FullyDimplated

Bayan sati biyu...

Salima bata fasa zuwa wajen Rumasa'u ba, duk lokacin data san Mahfooz baya nan saita lallaɓa taje. Bata nuna ma Rumasa'u cewa akwai komai ba, ko ta nuna mata tana jin haushin ta balle ta kawo komai cikin ranta ba. Zagon ƙasa take mata ita da Nurse Jamila, suna neman hanyar da zasu cusa Zubaida wajen Mahfooz harya aureta.

Boka ya riga ya buga ma Jamila ƙarya, yace mata Zubaida zatayi aure muddin sukayi abinda yake so. Cewa yayi yanada wani tsami daya shekara cikin wani ƙoƙo, kuma duk wanda yasha koda cokali ɗaya ne yana samun abinda yakeso. Amma da sharaɗi ɗaya, dole aje da Zubaida har Lokoja domin ya keɓe da ita shi kaɗai sannan ya shafa mata tsimin a duka sansan jikinta.

Abin duniya yayi ma Mahfooz cinkoso, komai ya cunkushe mashi. Bayada aiki sai yawan fushi da zafin nama. Rumasa'u ta gama ƙure haƙurin sa. Banda 'My Husband' datake ce masa idan ta gansa da safe, shima ba kullum ba babu abinda yake haɗashi da ita. Ya riga ya ɗaura ma kansa aƙidar rashin san kazanta, yasa duka aikin gidan shi yakeyi. Da safe idan yaje haɗa ma kansa shayi zai ga kitchen ɗin yayi kaca kaca, kuma duka daga kwamachalan indomie ko taliyan data dafa ne. Sai tayi amfani da tukwane uku. Saboda tanayi kana chatting ko tana kallon Reality show, Keeping Up with the Kardashians na 'E'

Haka zata babbake tukunya yayi baƙin kirin wanda saita canza sannan kuma ta sake maimaitawa. Tukwanen Naseera masu armashi wanda Hajia Binti ta siya cikin so da kauna, ƙananan ciki sune yan dubu arba'in. Amma Rumasa'u duk ta illantar dasu. Duk kayan kitchen ɗin ya halake, sannan kuma dan rashin hankali idan tazo zubar da abinci daga kwanan dataci, bata lura da cokula dake cikin kwanan haka take antayawa bola tayi gaba abinta. Gashi ta fasa flask ɗin ruwan zafi guda biyu. Kuma centre table ɗinta na tsakiyar falo yayi rotse.

Ta shagala tana kallon Kim Kardashian da kannenta a tsohon episode da suka je Greece suna ninƙaya cikin teku, abin ya bala'in burgeta. Tabbas wannan ne rayuwar daya dace da ita. Ba rayuwar datake ciki yanzu ba. Duk bayan kwana biyu Mahfooz yana ajiye mata dubu ɗaya akan dinning table domin tayi cefane idan taga dama. Subscription takeyi abinta babu abinda yasha mata kai. Tunda dai Salima itama tana sallamar ta idan taje. Garin kallon TV ne taji ƙauri indomie ɗinda take dafawa yana ƙonewa, saita tashi da sauri domin taje. Anan ta ingije centre table ya rotse.

Bayan nan, wata rana nepa sunata wasa da wuta ranar, daga su kawo low current sai su maida full current. Daga nan kuma sai su ɗauke su sake dawowa dashi. Ruma tana zaune akan three seater tareda ɗaurin kirji, ranar Salima bata jeba tayi tafiya. Mahfooz kuma tun safe wajen bakwai ya fice abinsa bama su haɗu ba. Bata tashi ta kashe kayan wutan taba. Kwan fitila na falo ya soma fashewa, tsaki tayi saboda ita kanta yana mata ciwo bazata iya motsa jikinta ba. Sai wayanta ya soma ruri. Sunan Inna ta gani dara dara amma tayi fari da idanu tareda taɓe baki.

“Nifa banida ko sisi,” ta faɗa a fili.

Ita kuma Inna tanaso taji lafiyar ta ne tareda sheda mata cewa Aliyu ya samu aiki a NBAIS dake rigacikun, sannan ran asabar za'a kai gaisuwan Fa'iza. Saurayinta wanda suke tare tun tana makaranta ya samu aiki a Federal Character Commission, shine take so Rumasa'u tazo ranar domin ayi da ita.

Amma haka wayan ya gama ruri bata ɗaga ba, tana kyautata zaton wani bukatar tasu ne ya tashi zasuyi mata maula, ita kuma ta daɗe da dawowa daga rakiyar talauci. Ta kasa gane dalilin dayasa suka ki rabuwa da ita kamar yadda ta share su. Wannan wani irin jaraba ne? Tayi ma kanta tambayar da babu mai bata amsar shi.

Tashi tayi ta tafi kitchen domin tasha ruwa, sai taji ƙauri ya baibaiye ko'ina. Mamaki tayi saboda yau ko kunna gas batayi ba balle ace ita ce. Anan taga gefen fridge yana hayaƙi wutan ya ƙona wayan. Tsaki tayi tareda balla ma fridge ɗin harara sosai saita wuce. Kuma jiya Mahfooz ya siya kaji biyu da catfish ya ajiye domin amfanin sa. Haka ta tafi tabar wajen tareda komawa cikin ɗaki ta soma danna wayanta.

Ranar Mahfooz bai koma gida ba sai sha ɗayan dare, Abuja yaje domin za ayi trials. Yana kokarin ya shiga kungiyar Manchester United dake Ingila. Tunda fridge ɗin sabo ne bai wani salance ba. Kashe gari haka ya sake fita amma aiki yaje wannan karan. Sun gama gina gadan da sukeyi za'a yi briefing ɗinsu akan sabon kwangilar da zasuyi ma Julius Berger. Kobi ta kitchen baiyi ba ya sake fita, haka duka kayan fridge ɗinnan suka soma bugawa, balle lokacin ana rana sosai ga zufa. Mahfooz bai lura da al'amuran gidan ba saida abin yayi kwana huɗu. Shima ranar yana jin cin ferfesun kifi ne zaiyi ma kansa. Anan wari ya koro shi daga buɗe fridge ɗin. Kamar an ajiye gawa duk ya soma tsutsa.

“Kankana! Kankana!!” ya kirata. Bata tanka ba sabida lokacin ta kwanta kenan kuma bazata iya tashi ba. Cikin takaici yaje ɗakin tareda buga ƙofa wanda saita ta firgita.

“Dalla Mallam meye haka?” tace a hasalce.

Shima bala'i yana cin sa ya amsa, “Dan rashin mutunci shine kika bar kitchen ya koma kamfanin tsutsotsi?” yana fadi duk tsigan jikinsa na tashi saboda kyama.

Da sauri yabar ta wajen yaje ɗakinsa ya shiga bayi, anan yayita kakarin amai. Bayan ya gama kakarin wanda babu abinda ya fito daga cikinsa, saiya wanke fuskan sa ya koma wajenta. Bai ganta cikin ɗaki ba saiya bita kitchen, lokacin ta leƙa itama ta gani ga mugun ɗoyi kamar sun ɓoye gawa. Da suka hada ido harara suka watsa ma juna.

“Shine kika bari ya lalace baki soya ba?”

“Karka dameni dan Allah, kaina yana ciwo kuma naga dai ba jaka ko baiwa ka ajiye ba. Tunda hannun ka ba haila yakeyi ba meyasa bakayi ba? Mts... Nonsense!” saita ratsa shi zata wuce. Janyota yayi ya riƙe gam. Zuciyar sa yana mashi mugun ƙuna. Ji yakeyi kamar ya nakaɗa mata duka dan takaici. Amma yasan duka bazai mashi maganin komai ba. Balle bayaso ya zama namiji mai dukan matarsa duk runtsi. Ita kuma saita fizge hannunta tana watsa mashi harara.

“Qwaro duk randa ka sake taɓani sai na shayar dakai madarar mamaki. Zaka san asalin waka aura.”
“Ni kike ma rashin kunya dan ina kyale ki?”
“Anyi ɗin me zakayi?”
“Wallahi ba laifin ki bane... Duk laifina ne. Karki damu.”
“Ai dama ni mena yi. Duk laifin kane,” sai tayi tsaki tareda wucewa, data kai wajen ɗakinta sai tayi magana, “Dan wahala kawai,” tace da karfin gaske tareda rufe ƙofa.

Hand gloves ya samo tareda dustbin bag. Saiya saka face mask saboda abin ya rage mashi ɗoyi cikin hanci. Sai kuma ya kunna humidifier wanda dama nashi ne, haka yayita gyara wajan yanata kakarin amai a sink har ya gama. Fridge ɗin bai bar wari ba. Amma ya wanke tas, warin ya riga yayi marinating da bangon. A hankali zai daina. Komai na ciki ya zubar ya fitar ƙofar gida wajen bola.

Sai yayi wanka ya wuce gidansu, ɗakin Mommy ya wuce kai tsaye. Idan ba gaidata yaje ba ko abinda ba'a rasa ba baya zuwa. Amma wannan karan nan ya wuce. Lokacin bata ɗakin tana kitchen tana duba abinda masu aiki sukeyi. Ranar Alhamis ne kuma Daddyn Faash yana azumi, gashi abokan sa uku zasuyi buɗe baki dashi.

Tuwan shinkafa da miyan taushe akayi, sai ferfesun bindin shanu dana kayan ciki. Sannan akayi ƙosai da kunun tsamiya dana gyada duka. Ga kuma kunun zaƙi da fruit salad a gefe. Sai chicken floss shima. Haka ya zauna a ƙasa yayi zugum yana tagumi. Duk ya fita hayacinsa. Banda gudu kamar jirgi zuciyar sa baya komai. Bai taɓa shiga tashin hankali da ruɗani irin na ranar ba.

Dirshan yake zaune jikin gado, hannunsa yana ninke a saman ƙirjinsa. Kansa yana kallon ceiling, duk sanyin dake tashi cikin ɗakin na AC bai hanashi jin zufa ba. Huda TV ke aiki a talabijin dake maƙale a bango. Duk maganar dake fita baya jin komai daga ciki. Dodon kunnen sa kamar an toshe mashi. Koda Mommy ta shiga ɗakin ta gansa tayi mugun mamaki. Mahfooz ya kasance mai zurfin ciki, duk abinka idan baiso ba bazaka ji abinda yake damunsa ba. Nisa tayi tareda ajiyar zuciya tana tausayin sa, dama hannunta riƙe yake da tray wanda akwai kankana, abarba, da ayaba. Sai taje gefen gado ta zauna.

“Son, menene?”

Baiji ba saboda yayi zurfi cikin tunani. Tafa hannayenta tayi wanda ya dawo dashi daga kogin tunani. Saiya wayance ya share gemunsa tareda sunkuyar da kai.

“Ina wuni Mommy?” yace ƙasa ƙasa.
“Ango kaine tafe, ya kake?”
“Lafiya lau Mommy.” daga nan bai sake cewa komai ba. Haka sukayi shiru.

Shan kayan marmarin ta somayi abinta, saida takai rabi ta tura mashi gabansa.

“Ungo,”

Da yaso yayi gardama amma ya karɓa, he needs the motherly love. Haka ya shanye tas wanda yayi mashi daɗi sosai.

“Ina jinka....” ta ce mashi.

Dagowa yayi ya kalleta, fuskansa tsantsan damuwa ke ciki. Duk ya faɗa ya rame. Ana kiransa ango ne amma duk a takure yake kamar anyi renditing ɗinsa. Ji yakeyi kamar an kamashi da ƙarfin tsiya an kulle a kurkuku sannan an jefar da mukullin cikin ƙasan teku. Daga nan kuma aka soma ɗanɗasa mashi azaba.

Dogon numfashi yaja amma baice komai ba, saiya fito da harshen sa ya lashe leɓansa. Kallon Mommy yayi sau ɗaya saiya mayar da idonsa kan tiles yana kallo. Har lokacin raɗadi yake ji cikin ransa. Itama Mommy ta lura abu ɗaya zai saka shi firgici da tashin hankali haka. Watau auren sa.

“Mahfoozz...”

“Mahfooz ɗina,” ta sake faɗi.

“Mahfooz ka sani cewa a rayuwa dukkan mu munada sirrin da bazamu iya faɗi ba, munada kuma nadamar da ke hanamu barci gashi bazamu iya faɗin ma kowa ba, da kuma burin da duk ya muka so bazamu iya cin masa ba,” ajiyar zuciya tayi saita cigaba da magana, “Sannan munada soyayyar da bazamu iya mantawa dashi ba. Mahfooz komai na duniya mai wucewa ne, duk yadda kake ganin rayuwar ka yayi baki bakada wani mafita, ina kyautata zaton akwai wanda zasu so dama ace naka matsalar shine nasu....”

“Anya Mommy!” ya katse ta cikin murya mai rawa.

“Kwarai da gaske Son. Akwai wanda matsalarka nafila ne a wajen su...”

“M-mommy, bazaki fahimci abinda yake faruwa dani ba. Bazaki gane duhun dake cikin rayuwata ba. Mommy it's so dark and twisted, Idan da zan juya hannun agogo baya. Zanyi wasu abubuwan daban... Mommy ni mai laifi ne... Nayi laifi babba. Na zalunce mutane....” sai yayi shiru. Tuna ranar daya fara ganin Naseera yayi, yadda ake janyeta cikin ɗaki kuma baiyi komai. Anan ya lura wannan abun ne gagarumin kuskuren daya tabka.

“Mommy bana san auren nan....” yace ƙasa ƙasa yana dabda zubar da hawaye.

Shiru Hajia Fati tayi batace komai ba, itama karin kanta batasan Rumasa'u. Amma wannan abin yafi karfinta. Bata sake magana ba saboda batasan abinda zatace ba domin yaji dama dama.

“Mommy nace bana san auren...”

“Mahfooz dan Allah ka rufa min asiri.” Ta katse shi cikin masifa, “Naji sanda ka faɗa da farko. Kada wani yaji ko Daddyn ku yace nike daure maku gindi kuna abinda kuke so.”

“Mommyyy!”

Hawaye ya soma gangaro mashi daga idanu, a inda yake yanzu yayi mugun karaya daga dokin ƙarfen daya hau. Idan ƙasa zata buɗe ta haɗiye shi a wannan lokacin zai bala'in gode mata. Komai ya cunkushe mashi kwakwalwar sa sai tafasa yakeyi. Da bayan hannunsa ya soma goge idansa, yana jin wani rami a rayuwarsa wanda ya rasa yanda zai cika shi.

“Mommy!” Faash ya shiga ɗakin kai tsaye.

Anan ya sandare daga ganin Mahfooz, rabon da su haɗu tun sanda yace zai aure Rumasa'u. Baisan meke damun Mahfooz ba amma ya bashi tausayi, saidai har yanzu yana fushi dashi.

“Bari na dawo anjima.” Faash yace sai ya juya.

Da sauri Mahfooz ya miƙe yana share sauran hawayen sa tareda binsa, "Man please wait mana.” Saiya dafa mashi kafaɗa.

Lokacin har Faisal yakai corridor yana sauri zaije wajen staircase. A miskilce ya juya saiya soma magana.

“Look I am busy,”
“Haba Faisal, kaifa dan uwana ne kuma kake min haka...”
“I am still busy,” saiya soma tafiya amma a hankali.
“Nasan nayi laifi, nayi abubuwa cikin fushi. Nayi jahilci banyi amfani da ilimi ba. Amma ai ba laifina bane duka,” saiya naushe iska.

Juyawa Faash yayi ya kalle shi, saiya koma inda yake, dafa mashi kafaɗa yayi saiya soma magana, “Man abinda nakeso ka gane shine, nobody cares about Wai Ko ka sake Naseera, she deserves it in a way – apparently –probably, I mean tasan tanada cuta bata gaya maka ba. That's fucked up man. I feel you ta wannan wajen... But auren Rumasa'u! Haba Mahfooz ! She's an Instagram Hoe and to think ka aureta ka kawo ta cikin family dinnan...wallahi bazan yafe maka ba.” saiya juya ya soma tafiya.

“And I hate it... Na tsana auren Faisal. Dan Allah ka taimaka min. It feels more like a rendition... I am tainted.” saiya soma hawaye.

Maganan Mahfooz ya tsayar dashi lokacin harya soma sauka daga bene. Haka ya waiga yana kallonsa. Tunani yayi na wasu dakikai saiya tafi abinsa ya barshi. Tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa yake duka.

Ranshi yayi mugun ɓaci ganin yadda Mahfooz ya sauya, tabbas duk abinda zai saka Mahfooz hawaye ba ƙaramin abu bane. Saidai bazai yafe mashi yanzu ba sai yayi mashi ƙaramin barazana. Shi kuma Mahfooz anan ya tsaya yanata tunani, daga nan ya soma safa da marwa a corridor ɗin. Hajia Fati ce tazo ta ganshi tsaye, kallonsa tayi tareda sakar masa ƙaramin murmushi saita sauka ta wuce kitchen. Chicken floss mai yawa tasa a farin roba ta bashi, lokacin ya sauko ƙasa zai fita.

“Ga wannan ba yawa,” ta miƙa mata.

Kallonta yayi da jajayen idansa wanda yasha hawaye, saiya miƙa hannunsa ya karɓa, batasan me zatayi mashi ba domin ya rage tunanin, “Kana bukatar kuɗi?” ta tambaye shi. Wannan ne kawai dabarar daya faɗo mata.

“Kai Mommy!” yace yana dariya. Itama dariyar ta somayi.

“Toh nasan ai yaran zamani ana zancen kuɗi kuke soma fara'a,”
“No please Mommy, bana bukata.” yace yana dariya ya fice.

Bai koma gida ba sai wajen goman dare, Rumasa'u ya gani a falo ta kunna waƙa tana babbaka rawa. MTV Base ke aiki an saka waƙar Olamide na Wonma. Bi takeyi kamar ita ta rera. Ga tukunya a gefenta wanda taci indomie bata kawar ba.

Ɗaki ya wuce kai tsaye, yana cire kayansa sai wayansa yayi ruri. Wannan number daya saba mashi saƙon an kwana lafiya yake kira. Gabansa ne ya soma faɗi, baisan koya dauka bane koya bari. Yana cikin tunani ne har wayan ya tsinke. Bayan kamar dakiku goma sai wayan ya sake ƙara. Jiki babu kwari ya ɗauka saiya kara a kunnen sa. Baice komai ba kawai yanata numfashi.

Itama Zubaida gabanta ne yake mugun faɗi, ta kasa magana tana tsoron kada ya wulakanta ta. Daya gaji da shirun saiya kashe wayan. Ita kuma zulumi fal cikin ranta. Gobe zata Lokoja tareda mamanta. Nurse Jamila tace tazo ta rakata bikin wata aminiyarta har Lokoja, bata so zuwa ba amma tace mata kota bita kota sha madarar mamaki.

Salima da Jamila sun haɗa baki akan zasu kai Zubaida Lokoja wajen boka ya shafa mata tsimi. Zasu kashe tsuntsu biyu da dutse ɗaya. Kowa zai samu abinda yakeso.

Kashe gari da asuban fari su Jamila suka wuce tasha suka hau motar Abuja, daga nan kuma suka kama hanyar Lokoja. Dayake Jamila malaman asibiti ne tasan maganin da zata bama Zubaida wanda zai gushe mata da hankali. Tabbas Zubaida bazata taɓa yarda da cewa wai sai anje wajen boka kafin tayi aure ba. Yarinya ce wanda takeda tsoron Allah cikin ranta. Tasan wannan babban shirka ne kuma bata fatan ta muta a matsayin mai shirka.

Boka Darbuzu yana zaune a wani ƙurmusun daji, sai an wuce confluence ɗin river Niger dana Benue. Ko tsimin sa daga daidai Y shape da kogin ya bada na haɗuwa yake ɗebo ruwan. Bayan sunyi chatan taxi da sunan zasu gidan ƙawar Jamila, sai ta siyan masu lacasera mai sanyi domin zafin rana. Ashe ta faki idon Zubaida ta watsa wasu muyagun ƙwayoyi. Lemun yanada sanyin gaske bata lura da canji wajen ɗanɗanon sa ba. Haka ta shanye tas. Banda murmushi Jamila bata binta dashi. Zubaida har tsarguwa tayi amma tayi shiru. Ana cikin tafiya zuwa wajen boka ta mirgina ta soma barci.

Kamar yadda Darbuzu yace zai keɓe da Zubaida haka yayi, anan yayi abinda yaga dama a jikinta domin zalunci. Saiya kuma shafa mata tsimin kamar yadda yayi alkawari. Sannan yace masu su tafi. Har lokacin Zubaida bata tashi ba balle tasan abinda yake faruwa. Haka Jamila ta cicibeta ta mayar Taxi dake jiransu ya kaisu hotel.

Zubaida bata farka ba sai ƙololon dare, nan gabanta yayita faɗuwa. Tana jin wani sauyi a jikinta. Da safe kuma sai Jamila ta soma ciwon ƙarya wai Diabetes ɗinta ya tashi gaskiya su koma gida. Sam abin bai bama Zubaida ma'ana ba. Zuwa Lokoja bafa zuwa Rigasa bane da za'a juya ba'a yi abinda aka je yiba. Tunda dai ba ciwon ajali bane yaci ace suje gidan biki aga fuskan su. Haka suka koma Kaduna kowa da abinda yake cikin ransa, Jamila tana tunanin soma tara kayan kitchen, ita kuma Zubaida tana neman yadda zata gayama Mahfooz abinda take ji.

***

Ontario, Canada.

Creed-Green Irish Tweed ke hannun Labib yana fesawa. Yau ranar Asabar ne kuma shine kaɗai ranar da baya zuwa aiki. Amma haka kurum yaji yanaso yaje asibiti domin yaga patients ɗinsa musamman ma Naseera.

Ranar Asabar yana kashewa ne tareda yin abubuwa daban daban kamar zuwa cinema, ko museum ko botanical garden. Wata sa'in yaje hiking ko kawai ya zauna a gida domin yayi karatu ko barci. Sam baya shiga harabar asibiti idan ba serious emergency ba, amma wani ƙaƙalen duba patients baya yi.

Faded jens wando yasa, sai farin t-shirt wanda aka rubuta 'Unbothered' akai sai baƙin leather jacket mai zip kaca kaca. Sannan kuma ya sake ɗaura grey coat a sama tunda ana mugun sanyi Canada. Kafansa brown boots ne suede. Sai ya saka bola hat tareda burberry muffler. Haka ya fita yana taƙama harya kai parking garage inda Convertible ɗinsa yake. Farin Aston Martin ne sai sheƙi yakeyi. For a Doctor, he's flashy.

A gaban asibiti ya tsaya shagon da suke siyan pastries ya siya abinda yafi so watau Crossaint da Milkshake. Saiya shiga cikin asibitin. Susan wanda take a matsayin receptionist ta soma ganinsa, ware ido tayi cikin mamaki tunda baya zuwa ranar Asabar.

“Looking good Dr Kakaki, any emergency?” Tace tana kyallara mashi ido tareda gyara mazaunin rigarta. A duniya tana mugun san Labib, saboda Labib ta soma san musulunci. Tunda da chan ita Islamphobic ce.

“Not really,” ya amsa cikin ko in kula.

Ba Susan kawai ba harta sauran ma'aikatan da suke wajen duk suna sanshi. Suyita mashi salo suna kinibibi idan sun ganshi. Amma ko sau ɗaya bai taɓa bin harkan gabansu ba.

Escalator ya hau saiya wuce ɗakin da Naseera take, ita kuma ta soma samun sauki sosai tana cin abinci tana komai. Ana lura da ita ne sabida juna biyu ga kuma HIV. Sanye take cikin jumpsuit na chiffon, saita ɗaura hoodie wanda aka rubuta, “To be tainted” akai.

Hular cheetah ke kanta tana kallon Spanish series Money heist. Tanayi tana zubga uban tsaki saboda dan wasan cikin Arturo yana bata takaici. Abinda yakeyi yayi daidai da wanda suka shafa mata kanjamau. Anan tayita binsa da ashar tana kwashe mashi albarka.

Kamshin turaren Labib ya riga ya zauna a kwakwalwar ta, koda wucewa yayi bai shigo ba tana jin kamshin. Yanada sanyi sosai wanda yasa yake birgeta kaɗan. Ko yanzu kamshin sa ya riga sallamar dayayi zuwa wajenta. Ya tura kofa sai yayi ma kansa iso ciki, ɗakin akwai room heater a kunne yafi waje wajen snow daya fito daga ciki. Ɗakin ta kashe wuta tanaso tayi kamar tana cinema ne, balle ita kaɗai ce Anty Jawahir taje gida ranar.

Kunna wuta Labib yayi tareda cire coat ɗinsa yasa a hanger, sai suka kalle juna wanda shine yayi mata murmushi. A sati fiye da biyun datayi cikin asibiti banda mutunci babu abinda yake haɗashi da ita. Tun sanda ya kusan kasheta cikin tiyata yake jinta cikin ransa. Ji yakeyi kamar akwai wani alaƙa tsakanin su. Kokuma wani alaƙa da zasu ƙulla nan gaba. Abin yadai cunkushe mashi ya kasa ganewa.

“I wasn't expecting you today.” Tace mashi da harshen turanci. Kwata kwata bata taɓa mashi hausa ba. Dama haka take idan bata saba da mutum ba bata mashi hausa.

Murmushi yayi saiya ƙarasa wajen table ya ajiye Crossaint ɗin hannunsa. Saiya janyo kujera ya zauna kusa da gadonta. Kallon kallo suka soma wanda itace ta kawar da fuskanta.

“Eh dama naje wani waje ne bayada nisa danan sai nace bari na biya... Ina Anty Jawahir?” ya tambayeta yana waige waige.

“She went home,” ta amsa.

Girgiza mata kai yayi, baisan me zaice ba kuma. Itace ta soma magana.

“When will I be discharged?”

Kallonta yayi, meyasa take kokarin a sallameta bayan bata gama warkewa ba. Amma kuma shima yasan zaman kadaici yana damunta. Danma tana kallo a laptop ne.

“Kinsan ke special patient ne, ana monitoring ɗinki. Dole sai Kinyi haƙuri aga komai yana tafiya daidai.”
“Okay,”
“Har yanzu kina jin amai ko kin daina?”
“I haven't felt that way since...”
“C'mon Naseera!” ya katseta. “Rabona da Nigeria shekara goma kenan, ganin ku ina yin hausa daku ba ƙaramin daɗi yake min ba. Nayi turanci har bakina ya soma ciwo, dan Allah ki saurara min.” ya marairaice mata.

Murmushi tayi bata sake magana ba, shine ya kuma ɗauko wani zancen. “Shekarun ki nawa?”

Kallon shi tayi kafin ta amsa, “Ashirin da hudu,”

“Allah sarki! da shekarar da ƙanwata zata kai kenan,” yace yana murmushi.
“Meya hanata?”

Shiru yayi sai fuskansa ya canza sosai, “Ta rasu ne, yasa nabar Nigeria.... And you remind me of her, itama taso zama Doctor, ” yace cikin takaici.

“Allah ya jikanta,” tace ƙasa ƙasa.
“Amin summa amin,” ya amsa. Saiya miƙe tsaye yaje wajen table ya ɗauko Crossaint. “Gashi abinda Falmata tafi so kenan kafin ta rasu,”

Amsa tayi suka soma ci tare, basu sake magana ba. Harya cinye uku, ita kuma ɗaya da rabi. Ita bata cika san zaƙi ba amma cikin yana sanyata kwadayi. Sai ta kunna film ɗin sunata kallo tare. Da aka gama episode ɗin saiya kalle ta.

“To be tainted,” yace tareda nuna rubutun kayanta. “Meye ma'anar abin?” saiya kurɓa Milkshake.

“Ni annoba ce – for real babu wasa,” tace tana ɗaga mashi kafaɗa. “I've been raped, positive with HIV, Divorced, and now pregnant.... Tell me a better résumé na masu annoba,” saita fara dariyar takaici. Shiru yayi tareda dana sanin tambayar. Mamaki yakeyi yadda take iya dariya da duk wannan abin. Sai kuma ya tuna babu yanda zatayi tunda ba canza wa zatayi ba.

Dr kana tunanin...”

“Labib Please, or YaLabib kamar yadda ake ce min a gidan mu... Ehen ina jinki.”

Jikinta yayi sanyi, ta lura Labib yana missing sister ɗinsa sosai. Amma ba ita bace, kuma bata jin daɗin shigo shigo ba zurfin dayake mata. Ta riga ta dawo daga rakiyar maza.






Wannan kenan!


#Naseera
#Mahfooz
#Tauraruwa
#MijinTauraruwa
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilicious
#FullyDimplated





Ainakatiti 💫

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top