Twelve - Mugun Mafarki


Koda Faash ya koma gida baiga motar Mahfooz ba, bai kawo komai ransa ba, shi a nasa tunanin kila ya tsaya wani wajen ne musamman wajen yan mata, tunda yanada su dayawa har saiya ture.

Da safe da zaije tada Mahfooz domin suje asuba shine ya lura da rashin sa cikin ɗakin. Gadonsa a shirye yake kamar ba'a kwanta ba. Anan dai ya duba bayi domin ya tabbatar da rashin Mahfooz.

Har makara ya kusan yi yana dube dube cikin gidan. Da yaje waje haka bai sake ganin motar Mahfooz ba. Anan ne yasha jinin jikinsa. Masjid ɗin yana kusa da gidansu, da sauri yaje domin har anyi sujjud na raka'an farko. Haka yayi sallah fargaba duk ransa. Tunda Mahfooz ya dawo gidan da zama bai taɓa zuwa wani wajen ba bai masa bayani ba.

Bayan ya kira wayan shi yaji a kashe, lokacin Sada da mutanen sa sun ɗauki wayan da motar baki ɗaya. Koda basu ga su Naseera ba zasu rage zafi da wannan tunda yanada tsada.

Faash gidan iyayen shi yaje domin ya sanar dasu cewa baiga Mahfooz ba, tunda har coach ya kira aka ce baya Abuja. Balle ma ga kayansa na kwallo cikin ɗaki. Gadan gadan aka soma neman inda Mahfooz yake amma babu labarin sa.

Shima Dr Abdallah ya kwana da baƙin cikin ɓacewar Naseera, Hajia Binti bata iya barci ba. Kwana tayi kan sallaya tana sallah tana kuka. Neman tsari take taya Naseera dashi a duk inda take.

Dr Abdallah yaje asibiti yana kallon dalilin dayasa bata shiga motar ta ba. Anan yaga taya ya sace daga dukkan alamu yin mata akayi. Tabbas yasan cewa ana nemanta da sharri, hankalin sa ya kwanta amma ba sosai ba. Yanzu kawai zai ajiye wayarsa a gefe ne domin idan sun kira sai ayi cinikin yadda za'a amshe ta.

Sanda Dr Chinedu yazo yaji zancen hankalin sa ya tashi. Saboda babu ARV ɗinta ba ƙaramin hatsari bane a tareda ita. Gashi shi kaɗai yasan da zancen, baiso kuma ya faɗa ma Dr Abdallah hankalin sa yayi mugun tashi. Saidai abinda ya sani koma menene ya kamata ubanta ya sani.

Lokacin Dr Abdallah yana wajen gate yana magana da yan sanda, anzo ana duba ta ina aka tafi da Naseera. Sannan ga kamfanin masu saka CCTV suna gefe an kira su. Suma zasu saka kowa ya hutu dan tsautsayin gaba.

Dr Chinedu yana gefe yana jira ya gama, bayan yan sandan sun tafi sai DR Abdallah ya juwo ya kalle shi.

"Lafiya dai Dr?"

Murmushi Dr Chinedu yayi sai yayi gyaran Murya, "Dama sanda bakada lafiya akwai wani yar matsala ne akan Naseera,"

Girgiza kai cikin takaici Dr Abdallah yayi saboda jiya Binti ke faɗa mashi, "Abu babu daɗin ji wallahi," saiya nuna hanyar asibiti alamar su shiga ciki, sunyi taku wajen goma sannan ya soma magana, "Wallahi sun cuce ne, jiya Hajia take faɗa min,"

Haɗiye miyau Dr Chinedu yayi, yanaso ya gaya masa ba wannan maganar ba. "Yi hakuri Dr amma bashi nake nufi ba, wannan sirri ne wanda daga ni sai Naseera muka sani,"

Anan Dr Abdallah yabar tafiya ya juya ya kalle shi, ganin tsoro yayi cikin ƙwayar idansa, anan shima jikinsa yayi mugun sanyi. Cikin ƙaramin murya Dr Abdallah yayi magana.

"Menene kuma?"

Numfasawa Dr Chinedu yayi, "Dr banso ɓoye maka ba. Naseera kamar yata ce. Yadda zan kare martaban Ada haka zan mata. Naso saika warke sai na gaya maka,"

"Karka damu... Menene?"

"Naseera tested positive..." sai yayi shiru.

Rufe ido Dr Abdallah yayi na wasu dakikai saiya buɗe, dukda ba'a karasa zancen ba yasan menene ake nufi. Naseera tanada cuta mai karya garkuwan jiki. Anan hankalinsa ya kuma tashi.

"Shine nake so nace maka Dr duk me suke nema ka basu domin she needs her ARV Koda yaushe," Dr Chinedu yace.

Dr Abdallah bai ce komai ba, wucewa yayi ya tafi office ɗinsa. Ya mance rabon daya shiga. Duk yayi kura da yanan gizo tunda babu wanda ke amfani dashi.

Anan ya zauna a couch dake wajen, 2 seater ne, saiya jingina bayansa. Ƙuna ransa yake masa. Yanada juriya ne amma daya fashe da kuka. Yanzu wai ƴarsa ɗaya wannan abubuwan suke faruwa da ita. Ita takeda cuta mai karya garkuwan jiki. Tausayin Naseera yakeyi, saboda ita kaɗai tasan me ke damunta. Shi dayake namiji kuma bashi bane da matsalar jibe yanda ransa ya ɓaci balle ita.

Ya lura ta fiye damuwa kwanaki duk ta faɗa, shi a zaton sa ciwon nan dayake yi yasa mata tunanin. Bai taɓa cewa ramarta daga matsalolinta bane. Yanzu komai na rayuwarta ya canza. Kuma saiya fara kuka da kanshi tunda shine ya aiketa ranar.

Ita kuma Naseera tana cikin gudu har ta kusan kaiwa bakin kofa taji an damƙeta gam an riƙe, ɗagowa tayi taga Mahfooz ne. Idansa ya canza yanayi babu alamar wasa cikinsa. Kici Kici suka soma sai kawai yayi zuciya, rabata da ƙasa yayi ya sakata a saman kafaɗarsa saiya tafi da ita.

"Ka sauke ni Mahfooz, wallahi zakayi dana sanin sani na... Idiot... Fool.."

Ko amsata baiyi ba, gaban rumbun da aka ce zasu shiga ya tsaya. Musa ya kalla yana matsar da hatsi tareda yayansa Bamanga. Ardo Bello dai yana kallon bariki iya bariki, kalle kalle ya soma yi domin yaga ko yara suna kallonsu ya kore su kada suga yan iska.

"Ku shiga," Bamanga yace masu.

Mahfooz bai ajiya ta ba sai cikin ɗakin, tazo zata sake gudu saiya tareta yana zare mata idanu.

"Banfa da mutunci, wallahi ki kiyaye ni. Koki natsu kona maki shegen duka tunda bakida hankali," yace mata babu wasa a fuskan shi. Anan taji tsoro saita murguɗa mashi baki ta shiga. Shima shigan yayi sai Musa ya soma saka hatsi domin ya kare su.

Suna ciki kusan minti goma sha biyar sai suka ji mutane sun shiga cikin gidan. Sada ne da mutanen sa suka isa. Kallon fuskan Naseera yayi yanaso yaga ko zatayi magana. Ya rasa gane taurin kai irin nata. Rayuwa yanada daɗi baisan meyasa takeso ta salwantar da nata ba. Idan ita bataso tayi tunanin abinda iyayenta zasuji idan sun rasa ta. Ita data tashi da gata tareda ma iyayenta kenan. Da ace itace ta tashi wajen Fauziyya tun tana karama zata kashe kanta kenan.

"Ina wuni Ardo,” Sada yace.

“muna neman mutane biyu da mace da namiji wanda na kawo su garin nan. Wannan karan bana san tashin hankali, a faɗa min inda suke. Duk wanda ya taimaka mani zansa a haƙo mashi ruwa na tuƙa tuƙa bai sai yaje rafi ba," sai Sada ya nuna mashi hoton borehole na tuƙa tuƙa.

" Ni bamuga kowa ba," Bamanga ne ya fara magana. Musa yana daga gefe yayi shiru. Baiso Sada ya gansa ya gane akwai rashin gaskiya tareda shi.

" Wallahi wannan karan babu harbi, sunada amfani sosai ne, kuma kada ku damu bazan kashe suba. Idan yan uwansu sun bani kuɗi na zan mayar dasu." Sada ya sake faɗi. Zagaye tsakar gida yakeyi yana dube dube da zungureriyan bindiga, sannan ya saka wani kwabɗeɗan tabaro tareda takalmin sojoji da rigar su.

Hannunsa ɗaya kuma sigari ne yana zuƙa tareda fesawa a karkace cikin kwarewa. Duka iyalan Ardo Bello suna kallon abinda ke faruwa. Tareda matan Musa da Bamanga duk ana kofar ɗaki.

"Bamuga komai ba muka ce," Ardo ya faɗa. Kallonsa Sada yayi yana nazari. Saiya shiga ɗaki ɗaki da kansa yana daga labule ya duba, da yakai gaban rumbun nan ya tsaya.

"Wannan ɗakin fah da kuka kulle?"

"Na hatsi ne" Musa yace tsoro fal ransa.

"Zoka buɗe,"

Masu ma Sada aiki ne suka je inda Musa yake suka janyo shi tunda sunga baida alamar tashi, "Muje mana, baka ji ne." sai suka nuna mashi bindiga.

Gaban Naseera ne ya cigaba da faɗi, tsoro yayita bin duk wani sansa na jikinta. Yanzu dataga mutuwa kusa da ita taji san zaman duniya cikin ranta. Koda HIV ko babu yafi mata zama wajen Sada. Allah kaɗai yasan me zasuyi mata idan sun ganta.

Kila harta sansa na jikinta zasu rinka yankewa suna aika ma Babanta domin su nuna basa wasa dashi. Mahfooz ne yayi amfani da hannun sa ya riko nata. Harta tsorata tasha su Sada ne suka damƙeta.

"Bazan taɓa rabuwa dake ba," yace ƙasa ƙasa wanda karantawa tayi ta leɓensa. Anan taji sanyi dukda tashin hankalin. Mahfooz makes it easy for her, akwai natsuwa datake samu wanda da chan bata samu. Harga Allah tasan yayi namijin kokari. Kokarin da bata taɓa tsammani ba a matsayin sa na mara imani.

An fara kokarin bude kofar Naseera ta sake matse hannun Mahfooz, rufe ido tayi tana hawaye.

"Irin famfon yan birni zakayi mana?" Fesindo ta faɗa. Matar Bamanga ne. Dafa kai Bamanga yayi saboda batada hankali ko kaɗan. Yanzu zata iya tonawa.

Harara Ardo ya bita dashi amma ko ta kula, ƙarasawa tayi taje inda Sada yake tana taunar cingam, "Muga hoton?"

Da sauri Sada ya nuna mata, "Kinga shi, wannan zanyi ma wanda ya nuna min inda baƙin suke,"

Anan Fesindo ta soma tunani, dama tun asuba take ƙorafi dole su Naseera su tafi. Ita bataga dalilin da za'a taimaka masu ba. Balle yan birni ba kirki garesu ba, tana zuwa gurin wata yar uwansu mara kirki. Kuma ita idan za'a yi masu tuƙa tuƙa gwara ta faɗi. Ta tsana zuwa rafi deban ruwa duk da baida nisa, ba kamar yadda tasha wahala gidan iyayen ta.

Kallon hoton tayi tana nazari, Bamanga bai isa yayi mata komai ba danta tona. Ai ba yan uwansu bane da zasu rufa masu asiri.

"Adda girkin ki yana ƙonewa," Charo matar Musa ta faɗa da sauri. Tanada tsohon ciki jikinta, saita karasa wajen tana nishi, "Adda ki wuce ki duba," saita amsa hoton hannunta na bore hole ɗin. Kallo tayi tana murmushi.

"Laa abin yan gayu,"

Miƙa ma Sada tayi, "Idan muka ji zamu faɗa maka, da kaina zan tayaka cigiya, bazamu bari wannan abin ya wuce gidan nan ba. Kaga na kusan haihuwa na tsani kuma zuwa rafi ɗiban ruwa,"

Murmushi Sada yayi, ya lura dabarar sa yayi kyau. Idan mutane suka ji wannan zasuyi saurin taimaka mashi. Yanzu gasa gida gida za'a yi wanda za'a yi mashi tuƙa tuƙa.

" Taminu muje gida na gaba, " Sada ya gayama wanda yake gaban rumbun zai buɗe. Anan suka bazama suka tafi. Banda ajiyar zuciya babu abinda Mahfooz da Naseera suke yi. Anan Naseera ta sake karaya, jibe yadda yan gidan Ardo suke yi a kansu bai kamata ta butulce suba. Idan sunce aure ne kawai abinda zaisa su taimaka masu, taji ta yarda. Nanda sati biyu duk ɗaya ne wajen Allah.

Kamar yadda Mahfooz yace, suna barin nan kowa ya kama hanyar sa. Dadda Matar Ardo na farko kuma Maman Musa ta soma magana, itama tana goyan bayan Fesindo, dama yar ƙanwarta ne auren zumunci akayi.

"Ardo jibe fah abin arzikin da zasuyi mana. Yan birni ai ba yan uwan mu bane," tace tana taɓe baki.

"Kul, karna ji kina faɗin haka. Ai yan birni mutane ne. Idan Musa akayi ma haka ko Bulu zakiji daɗi?" Ardo ya gargaɗe ta.

Lokacin su Mahfooz an fito hatsin dake hanya suna kokarin fitowa, Dadda da watsa masu harara sai ta wuce ɗaki, haushin yaronta Musa takeyi da munafukar matarsa Charo. Sam batasan meyasa aka haɗashi da ita ba. Fesindo wanda ba ita bace surukar ta tafiye mata sau dubu akan Charo.

"Kada kowa ya sake maimaita abinda ya faru yau, duk wanda ya sake tambaya sai kuce baku gani ba." Kallon Fesindo yayi wanda ta fito daga inda ake girki tana taunar cingam. Dama batada aiki sai tauna, abinda ke kaita cin kasuwa kenan. Zata siya pakitin cingam tazo tayita tauna.

Kowa watsewa yayi cikin tsakar gidan, sai aka bar Naseera da Mahfooz sai Ardo. Mahfooz ne ya soma magana, "Ardo mun gode da karamci, idan magariba yayi zamu tafi," yace a sanyaye saboda ya lura Naseera bazata taɓa amincewa da gaskiyar sa ba.

Da sauri ta kalle shi, "Tsaya... Na aminci." saita wuce ɗakin da aka basu tana hawaye. Bai bita ba kawai kallonta yakeyi, yasan ba ƙaramin daure zuciyar tayi ba. Amma ya ɗauki ma kansa alwashin cewa zai gyara komai. Sannu a hankali zai lallaba ta. Shiba mugu bane, kuma zai nuna mata.

Da Bamanga, Musa, Charo, Nenne sai Ardo akayi auren. Mahfooz shima ya hallara. Dadda da Fesindo basu fito ba. Dukda tsohon cikin jikin Charo bai hanata yin masu hidima ba. Itace ta ɗauki sabon kayanta na Atampha riga da zani wanda ta dinka da aurenta ta kaima Naseera. Ƙaramar yarinya ce sabida Naseera zata girme ta.

Nenne maman Bamanga taje ta tambaye Naseera sunan ta. Anan tace Naseera Abdallah Kwarbai. Shima a karo na farko da Mahfooz yaji sunanta. Ya riƙe yayita nanatawa cikin ransa.

Musa yana jin takaicin abinda mahaifiyarsa tayi, dama duk rigimar gidan itace take farawa. Tanada yara uku mata kafin shi duk sunyi aure yanzu. Shine babban ɗanta namiji. Yana kallon yadda Charo take hidima dasu Mahfooz, ko kokon safe ita takai masu kuma ga tsohon ciki da kyar take tafiya haihuwa yau ko gobe.

Charo a saman gado ta riske Naseera tana zaune, da ta ganta da sauri tayi Murmushi ta share hawayen ta. Ita kuma Charo sai tayi kamar bata lura ba.

"Adda ga wannan, na sauke maki ruwan zafi idan kin fito sai ki saka,"

Itama zaman tayi, Naseera amsa tayi amma batace komai ba. Shiru sukayi kowa da abinda yake ransa.

"Idan kin cire na jikin ki sai naje rafi na wanke maki, kinga kin samu na canzawa,"

Haka ta tashi ta wuce kewaye inda Charo takai mata ruwa, aikam yanada zafi sosai domin ta gasa duk wani sansa na jikinta. Koda ta dawo ɗaki Charo tana zaune tana jiran ta. Murmushi suka sakar ma juna. Ita Charo murna takeyi tayi kawa, kullum banda zagi babu abinda Fesindo da Dadda ke mata. Yanzu Naseera zata ɗebe mata kewa.

Hira sukayi kaɗan kaɗan har Naseera ta gane Charo tana zuwa birni tallan nono kafin tayi aure. Anan ne taji hausa sosai saboda nata yafi na sauran yan gidan fita.

Mahfooz yana wajen ɗakin Ardo tareda Musa ana zantawa, Musa yaji daɗi sosai da yaji cewa ɗan kwallo ne. Sau da dama Musa yana zuwa babban garin yaje gidan kallon ball idan anayi ya biya ya kalla. Shi ɗan Arsenal ne a cewarsa kuma ya roke Mahfooz akan ya rinka buga masu idan yaje Turai.

Dariya Mahfooz yayi saboda ba haka abin yake ba. A lokacin Bamanga ya tafi duba Shanaye a garke. Koda ya dawo saida ya dawo da nono wanda ya tatsa. Ya kawo masu Mahfooz ne tunda sune angwaye.

Da Musa da Bamanga baka taɓa jin tsakanin su dukda ba ɗaki ɗaya suke ba, iyayen su mata ne keyi. Koda yake Nanne batada matsala. Bamanga ne baban yaronta kuma ya girme Musa da shekara biyar. Yaran Bamanga uku da Fesindo amma idan tayi wani yarinta kamar gobe za'a haifeta. Charo tafita hankali nesa ba kusa ba.

Saida mangariba Mahfooz ya iya zuwa dakin, dama abinda yace zai rinka yi kenan. Zai fita da asuba bazai koma ba sai rana ta sauka. Ta haka ne Naseera zata samu taji sanyi cikin ranta.

Sanda ya shiga tana zaune tana saƙa mirjani, Charo ta soma koya mata wai domin ya ɗebe mata kowa. Bata gane abin da takeyi kawai tana kokawa dashi ne. Sallama yayi ya shiga. Saita amsa mashi chan ƙasa. Bata ɗago ba balle ta kalle shi.

Akan tabarma ya zauna, yana so yayi mata magana amma ya lura girar ta a harɗe yake. Itama tasan maganar yazo yi yasa tayi haka. Sun kwashi kusan minti talatin a haka saboda yanata kallon agogon hannunsa.

"Menene ?" yaji muryan ta amma kuma bata kalle shiba. Zaman shi gefenta takaici yake bata. Gwara ya faɗa bukatar sa ya matsa mata.

"Dama inaso na jaddada maki cewa ne karki damu. Babu abinda zai faru tsakanin mu...."

"Dama meya isa ya faru... You're delusional Mahfooz," ta katse shi. Har lokacin bata kalle shiba. Hankalin ta yana kan abinda takeyi. Ajiyar zuciya yayi saiya sake ƙasa da murya.

"Nasan cewa muba kamar sauran ma'aurata bane. Amma abinda nakeso ki sani kamar yadda miji zai kare martaban matarsa haka zan maki. Duk wanda zai cutar dake saiya fara da ni tukun....”

Daga mashi hannu tayi, a lokacin ta kalle shi a karo na farko.

“Rufe min baki Mallam! Sanda na tambayi taimakon ka ai cewa kayi baka sanni ba. Yanzu zaka zo min da gabli da ba'adin shirme. Daka taimaka min aida komai yana tafiya min daidai. Amma kasa sun cuce ni rayuwa na ya zama abin dariya.” kuka ne yaci karfin ta yasa tayi shiru. Anan ta rinka rera wa.

“Kiyi huƙuri Naseera,” yace. A karo na farko daya kira sunanta kenan.

“Ka cuce ni Mahfooz, daka san illan abinda kayi min daka taimaka min. Ban sanka ba, ban maka komai ba. Sai kace ba musulmi ba ka barni dasu,” saita cigaba da kuka.

“Aikin shedan ne kuma Kinyi kama da wata fau....”

Bai karasa ba ta taya shi, “Nayi kamada Fauziyya amma ai bani bace. Komai tayi maka idan ka haɗu da ita sai ka rama a kanta because she deserves it, ni ban haɗa komai da kaiba. Do you realise how stupid you sound, baka taimaka minba saboda nayi kamada wata da ban sani ba, " ta faɗa hawaye yana malalo mata. Da haɓan zanin ta rinka gogewa.

" Ka cuce ni," ta sake fadi. Ajiyar zuciya yayi, komai ɗaci yake masa kuma tabbas Naseera tayi gaskiya.

"Idan zaki yarda dani, toh ki yarda da cewa nafi ki jin ɗacin abinda nayi. Idan za'a juya agogo baya zan taimaka maki ko tunani bazan yi. Nima abinda nayi maki ya sakani cikin ruɗani. Kiyi haƙuri, ni bance ki yafe min saboda nasan da wuya. Amma inaso ki tausasa zuciyar ki akan batun,”

Charo ne tayi sallama, ta kawo masu tuwo da miyan karkashi. Sannan ta tafasa madarar ta kawo masu. Wasu plate ɗinta masu kyau ta saka masu ciki, ita kawai jinin ta ya haɗu dana Naseera.

Mahfooz ne ya ɗeba ma Naseera saiya ajiye mata gefenta. Harara ta bishi dashi saboda bata aike shiba. Madarar ya kafa kai yana sha, saidai ya kai kusan rabi ya ajiye. Dariya ya soma yana magana.

“Wai ni keda aure!” saiya tuntsire. Abin kamar a film. Jarida da Ardo ya siya wajen wata shida daya wuce ya soma dubawa. Ya fiye mashi zaman kadaici tunda Naseera bazata taɓa kula shiba. Dama shi bamai magana bane.

Wajen dare bayan sun gama cin abinci sunyi sallah, itace taje ta fitar da kwanonin. Anan kwararo ta soma daurewa da ruwan data gani. Saita kaima Charo ɗakinta. Anan tayi mamaki sosai ganin sa. Gadon rumfa gareta, sannan ansa labule mai kyau an rufe bango gaba ɗaya. Ga ledan ƙasa da ƙaramin tabur. Kamar ba kauye ba saboda ba aci bal bal gareta ba. Fitila ne zamani mai amfani da batir.

Mahfooz yana kwance saman tabarman, idonsa rufe sanda ta shiga. Kashe fitilar tayi domin bazata iya kwana da wuta ba. Ta yarda da Mahfooz bazai cuce ta cikin dare ba tunda yayi alkawari.

Anan ta mirgina ta soma barci, shikam yaso yace mata ta taimaka tabar mashi wutan amma yana tsoron karta soma masifa, ta cigaba da jin haushin sa. Sai kuma ya tuna dama baya barci. Kwanciya kawai yakeyi.

Amma abinka da gajiyar da sukayi ta fama dashi, sai barci ya ɗauke shi. Yana cikin yi chan tsakiyar dare ya soma mafarkin sa na fama. Sumbatu yakeyi cikin barci yana kiran zance kala kala wanda baida ma'ana. Naseera ce ta farka cikin tsoro. Da hasken wata dake haskaka ɗakin ta karasa inda aci bal bal yake, dama ashana yana gefe ta ajiye. Anan ta kunna.

Karkarwa taga Mahfooz yanayi yana zufa, gashi kuma kamar baya hayacinsa. Ita a matsayinta na likita abinda yake yi yana nuna Post traumatic stress disorder ne. Tabbas Mahfooz baida lafiya akwai mugun abu dake addabar sa.

Da sauri ta karasa inda yake, "Mahfooz," ta furta a tsorace tana taɓa shi. Shikam ranar da Fauziyya ta saka mashi guba yake mafarki akai. Anan cikin firgici yasha ta dawo zata sake ne, bai ɓata lokaci ba ya kaima wuyanta chapka. Nan ya maƙure Naseera gam zai kasheta. Ko ihu bata iya yiba saboda azaba, hawaye ne ta fara. Numfashinta ya soma daukewa sai idonta ya rufe.

Anan ya farka da sauri ya dawo hayacinsa. Jijigata ya somayi yana kuka.

"Naseera! Naseera!! Naseera!!!” yayita nanatawa yana hawaye. Amma bata jinsa balle ta amsa shi. Idanta ya ƙanƙane a rufe.

Wannan kenan!

#Naseera
#Mahfooz
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilicious
#FullyDimplated

Ainakatiti✨

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top