Three - Ummata
Abdallah Specialist aka kai Naseera, nan aka wuce da ita emergency ward. Uncle Sadiq baisan an kwantar da Dr Abdallah ba.
Shi ƙanin Dr ne kuma yana PhD a Spain. Yau ya dawo saboda yabar matarsa da cikin yaronsu na biyu. Ya fita ya siya abu ne saiya kaɗe Naseera.
Bai kawo komai ransa ba ya kira Number ɗin Dr Abdallah, shi kuma a lokacin yana sallah bai dauka ba. Anan ya kira wayan Hajia Binti wanda take gida. Ta fito daga bayi kenan tana shimfiɗa sallaya sai wayarta ya soma ruri. Harda bazata ɗauka ba saboda lokacin sallah ne, sai wani zuciyar yace ta dauka tunda bata fara ba.
Data ga sunar Sadiq nan take ta sake fuska tana murmushi. Sallama tayi mashi shima saiya amsa. Anan yake mata bayanin tazo asibiti da Dr saboda ga abinda ya faru. Nan take ta zura hijabinta ta nufa ɗaki domin ta ɗauko ma Naseera kayan da zata saka saita nufa asibitin. Tunani kala kala kawai takeyi.
Likitocin sun duba Naseera sannan sun dauki samples a jikinta wanda zai taimaka ayi arresting wanda sukayi laifin. Sannan suka umurceta akan tayi wanka tareda magani.
Koda ta shiga bayi ta kunna famfo zama tayi akan seat ta buɗe sabon babin kuka. Ta kasa gasgata abinda ya faru da ita. Daga haduwar ta da yan daba, sai kuma Mahfooz. Eh Mahfooz yanzu ta sake tuna abinda yayi.
Tabbas ta sheda wasu babu alheri a sanin su, da ace bata taɓa ganin sa yafi mata akan wai yasan ta ya kuma san inda ta fito amma yayi ƙememe. Mamakin irin halinsa takeyi. Ba ƙaramin mugu azzalumi bane na bugun jarida.
Anan tayi kuka kashi kashi, na farko ga abinda yake wakana na cewa ba DR Abdallah bane mahaifinta. Na biyu ta ina zata ɗaura rayuwarta daga nan. Wa'annan mutanen sun cuce ta.
"Naseera kina bayin ne?” Umma ta tambayeta. Shima kukan Naseera ta sake fashewa dashi. A yanzu lallai ta gane ma'anar maganar da tayi da Babanta ɗazu akan bama mutane uzuri. Yanzu ta fahimci ƙila zai iya yiwuwa mugaye suka ma Umma fyade har ta ɗauki cikinta.
Tasan Ummanta kuma tasan halinta, tasan cewa tanada tsoron Allah. Fasikanci ba abu bane wanda zata aikata. Nan take duk wani makami data ɗauka akan Hajia Binti ta sauke. Tasauyinta takeyi matuƙa. Abinda yayi ma Naseera daɗi shine tasan cycle ɗinta kuma yau yana cikin ranakun da bazata iya ɗaukar ciki ba. Balle kuma anyi flushing mata system ɗinta.
Koda ta fito da Hajia Binti ta fara haɗa ido da, kwalla fal idanta. Tana tausaya ma yarta da sabon abinda zata shiga. Flash backs zai rinka damunta duk sanda ta runsta ido. Taimaka mata tayi domin ta saka kaya sai suka zauna su biyu shiru. Babu wanda yace komai.
Uncle Sadiq ne ya dawo tareda wani abokin sa, ASP Musa. Anan aka soma tambayar ta abubuwan daya faru. Nan ta faɗa masu komai harta abinda Mahfooz yayi. Bata dai nuna ta san shi a ido ba. Cewa tayi wani ya gani amma bai hana ba.
Umma ta tsine ma Mahfooz sosai, mamaki takeyi ace wai mutum bai da ɗigon imani a zuciyar sa. Tausaya ma iyayen sa takeyi saboda sunyi asarar haihuwa.
Shi kuma gida ya koma baije chemist ɗinba. Tanata faɗo mashi a rai yarda take hawaye tana kiran sunan shi. Abin ya so ya ɗan bashi tausayi amma yayita kawar da tunanin.
"She deserves it," wani zuciyar ta ayyana mashi. "All is fair in love and war," ya sake tunawa. Duk laifin tane ya kasa taimaka mata. Yana rage wani duhun dake cikin ransa. Yana rama abinda aka yi mashi yana yaro koda basu bane. Shifa baya cira ran cewa Naseera batada alaka da makiyan sa.
Bazai illanta ta da kansa ba, amma idan yaga tana ƙone wa kuma akwai kofin ruwa gefen sa, toh tabbas zai shanye ne.
Hawa kan gadonsa yayi yanabin shafukan kwallo, sai a lokacin ya tuna Ruma Sa'u. Anan ya koma explore yasan bazata rasa yawo ba. Nan yaga wani page na fresh ajebutters sun yi posting ɗinta. Cikin ikon Allah kuwa sunyi tagging ɗinta.
Koda ya shiga handle ɗinta gani yayi tana following ɗinsa. "Ta zo cikin sauƙi" yace a fili. Nan ya gyara kishingiɗan sa ya soma liking hotunan ta guda uku.
Ita kuma ihu ta soma yi da taga notification daga Instagram Qwaro yayi liking har hotuna uku. Ruwan da aka yi ɗazu yasa Inna bata ƙarasa masu sanwar suba. Tunda basu da kitchen langa langa aka maƙala kuma anyi iska mai ƙarfi yayi fatali dashi.
Yanzu ne Inna take kokarin tuƙa masu tuwan dawa. Ita duk rintsi ita takema Mallam abinci idan tana nan. Basu da arziki amma soyayyar su abin sha'awa ne. Kullum suna kokarin kyautata ma juna tareda rufawa kansu asiri.
Ihun da Kankana tayi saida ya firgita Inna. Anan tukunyar ya kusan ɓarewa, garin sauri domin ta gyara sai muciya mai haɗe da tuwo ya faɗo daga tukunyar ya ƙona mata ƙafa.
Zafi mara mitsaltuwa taji ba kaɗan ba, amma ta danne ta cigaba da aikinta. Dama ta riga ta gama miyan karkashi. Ta zuba ma kowa a kwano, takai masu ɗaki. Fa'iza tana raɓe cikin bargo ta rufa saboda tanada Pneumonia.
"Inna bazan ci ba wallahi. Farin ciki nake yi kamar an min albishir da kujerar Makka" ta faɗa tareda ɗaukar kwanan tuwo ta nufa zaure dashi. Cikin ikon Allah almajiri yazo bara ta juye masa ta dawo ɗaki.
Abin yayima Inna ciwo amma dannewa kawai tayi. Ita kuma Ruma Sa'u mayafi ta ɗauko saita wuce teburin mai shayi. Anan aka soya mata indomie da kwai sannan ta siyan naman ɗari biyar.
Inda sabo yan gidan sun saba, idan ta kawo tarkacen ta ita kaɗai take ci. Sau ɗaya tayi ma Inna tayin shawarma, sai kuma sausage ɗin ciki ya tada mata zuciya. Ba ƙaramin daɗi Ruma taji ba. Tun daga nan idan tazo da abu sai tace, "Inna fah mutumin ne bari na yanko maki." anan Inna zata ce Allah ya amfana ta bar shi.
Fa'iza ta kusan cinye tuwanta sanda Ruma Sa'u ta dawo. Dama basa magana sosai sai jefi jefi, balle ace wai hira ta haɗa su. Anan Ruma ta saka Indomie da tsire tayita ƙyanƙyanma. Tanaci tana habaici.
"Jama'a Iya kudinka iya shagalinka, iya talaucinka iya munafincinka, iya fatararka iya sa'idonka, gwargwadon gulmarka gwargwadon yanda za'a ragargaza buhun ubanka,” tayi ta faɗi cikin sigar waƙa.
Har lokacin Qwaro bai mata dm ba, ita a nata tunanin bayan yayi liking hotuna uku yaci ace magana yayi mata. Anan ta cire girman kai domin ita tayi mashi magana. Dama ance girman kai rawanin tsiya.
'aw fr' tace masa. Yana kwance zai kashe datansa kenan domin ya soma kallo. Tsohon film mai suna Merlin yake so ya sake kallo. Saƙon ta shine ya dakatar da shi.
Yana ganin saƙo ya soma murmushi amma yadda ta rubuta abu kamar yar tasha yayi mugun bashi haushi. Dama 'How far' ta rubuta gabaɗaya spelling ɗin dayafi. Baya san masu rage yadda ake faɗin kalamai. Asalima idan ka rubuta abu haka kamar su 'Ykk, lfy, 10x' da sauran su toh kai zaka bama kanka amsa amma ba Mahfooz ba.
Ya so ya shareta, amma kuma ita ɗin mai kyau ce. Gata yar masu hannu da shuni. Talaka shi keda matsalar rubutu amma ba ita ba.
'Hello Mai kyau! How are you?'
Ya tura mata, anan ita kuma ta soma ihu. Mallam ne yazo har ɗakin yana gargaɗinta. Kada ta mayar masu da gida bariki. Gwara ta kiyaye tayi masu shiru zasu kwanta.
Salon rubutun Qwaro ya burgeta, saidai duk abinka da Kankana baza tayi typing daidai ba. Bawai salo yasa take haka ba, a'a tsakani da Allah bata ma iya spelling ba. Daga kalmar Hausa harna Bature. Yasa Koda yaushe tayita yankewa koda inda bai kamata bane.
Haka suka kwana suna chatting, domin sun karɓa Number ɗin juna sun canza manhaja zuwa WhatsApp. Kuma ta tura masa hotunan ta sosai. Ya yaba da kyanta kuma yayi mata alkawarin zai zo cikin satin gidan su domin su gaisa. Murna mara mitsaltuwa tayi, Qwaro zai kawo mata ziyara. Gidan su Rahina Bulala zata kai shi. Sannan kuma ta ajiye shi a falon babansu. Tasan ba ƙaramin girma zata ƙara ma kanta ba.
Shi kam cikin dare yana barci ya farka a firgice. Mafarki ya soma yi. Ga gumi yana karyo masa ta ko'ina. Abin daya bashi mamaki shine wai fah ga hasken lantarki. Amma duk da haka bai hana shi ziyarar rayuwarsa na da ba. Rayuwar datake kawo masa firgici da ruɗani. Rayuwar ƙasƙanci da rashin gata.
Hankalinsa duk a tashe, yana mamakin sabon yanayin nan da yake, yanda yaga rana haka yaga dare. Yana zaune ido a bushe kamar jemage ya kasa rufewa.
Washe gari....
Buga ƙofa ake yi tareda Sallama. Yau ba Mallam Salisu zaiyi conducting assembly ba yasa bai fita da wuri ba. Tashi yayi yabar kokon dayake sha domin yaga waye.
Anan ya riske yan sanda guda biyu. Sun miƙa masa hannu tareda tambaya ko anan ne gidan da wata Ruma Sa'u take zaune. Ya shaida masu cewa ƴarsa ce, sai suka ce mashi ya kirata su wuce office saboda tayi gagarumin laifi.
Dukda ya tambaye su me tayi amma suka ce idan anje office za'a ji komai. A tsakar gida Inna take tambayar sa ko lafiya. Anan yake cewa yan sanda ne suke neman Ruma Sa'u.
Ita kuma Ruma Sa'u ta gama goge kayan da zata saka anjima. Saita miƙe taje wajen Jakarta domin tabama Fa'iza admission letter ɗinta. Fa'iza na cikin dubawa sai ta lura da mistake wajen matric. Tabbas wannan takardar bogi ne, amma ta dake kawai tayi murmushi.
"Congratulations sister, dama bana zargin ki. Allah ya sanya alheri." saita miƙe tsaye ta rungume ta. Za'a iya cewa wannan ne karo na farko da suke runguman juna. Kwata kwata basa jituwa, kamar yaran kaji suke kullum cikin faɗa.
Saboda Ruma bata abinda ya dace, ita kuma Fa'iza sai tayi mata gyara. Farkon mugun faɗan su shine sanda Fa'iza takai ƙarar ta bata sallah. A yanda ta lura Ruma Sa'u ta kusan kwana uku batayi sallah ba kila ma yafi haka. Shine ta kai ƙarar ta wajen su Inna. Abin yayi ma Kankana ciwo inda tayi mata duka cikin dare.
Ita kuma yau Ruma Sa'u har cikin ranta taji daɗi. A karo na farko ta damfara mutane kuma ba'a kamata ba. Zatayi magana kenan sai suka ji abinda Malam yace. Anan cikinta ya ɗuri ruwa. Nan take ta fizge takardan ta yaga tas ta tura baki ta fara ci kamar akuya tana kuka tareda dana sanin abinda tayi.
"Bazani gidan yari ba," ta soma fadi hawaye yana zuban mata a idanu. Duk a tunanin ta identity theft ne aka zo kamata dashi.
Malam ya ɗaga labule ya soma magana, "ki saka kaya kizo muje police station hukuma sunce kin masu laifi."
Tareda Fa'iza suka shirya sai suka fita, anan suka je zaure inda yan sanda suke. Magana Ruma ta soma yi tana hawaye, "Officer Al-quran banyi komai ba," saita fashe da kuka. Suma Inna da Fa'iza shi suke yi.
Yan sandan basu ce komai illan umartan Ruma Sa'u ta shiga mota a tafi station. Idan kuma taƙi yi cikin mutunci zasu fizgota su saka mata ankwa. Nan hankalinta yayi mugun tashi. Haka ta wuce, yan layinsu kap sun fito sai kallo sukeyi. Abin yayi bala'in bama Mallam takaici amma saiya tuna laifin ƴarsa ce.
Aliyu ya goya Mallam a machine ɗinsa tunda shi Mallam baida shi. Su kuma su Inna zasu bi su a napep. Police station ɗin Kawo aka kaita.
Koda suka isa sai Ruma Sa'u taga Bello abokin ta na group ɗin one love, sannan kuma ga Sakina da Halima duka suma an ɗauko su. Cikinta ya kaɗa sosai ta cigaba da kuka. Saboda yau social media zai kaita ya baro.
Anan akayi masu bayanin cewa Bello ya shahara a ɗauko wayan sata yana siyarwa. Kuma wayan hannun Ruma Sa'u na sata ne. Ya siyar ma Sakina da IPhone 11 a dubu ɗari da tamanin. Shi ne ana tracking ɗinta har ta bada sunan Bello. Anan shi kuma yace harda su Ruma ya siyar masu dashi.
Wata officer ce tazo ta yanke Ruma Sa'u da mari, anan ta soma kilarta sai duka takeyi kamar zata kashe ta. Tanayi tana kwaɗa mata gargadi sai kuma ta ingiza ƙewarta zuwa cell tareda sauran ƙawayenta wanda suma sun jibgo.
An tura Fa'iza da wata yar sanda gida domin su ɗauko wayan aka karɓe. Sai kuma aka ce dole su bada dubu ɗari ayi bailing Ruma Sa'u. Gashi an fizge mata mayafi da kallabi da takalmi ana tozarta ta. Ko su bada kuɗin kokuma ta zauna a wajen. Kuma idan ta wuce sati ɗaya prison za'a kaita direct.
Tashin hankali Mallam yake gani. Duk unguwar ana ganin mutuncinsa. Bayan Malunta dayake a firamare. Shine ladanin masallacin layinsu. Yanzu wai ace ƴar cikinsa ita ce wannan. Saiya tuna ɗan kuka ke jawo ma uwarsa jifa.
Naseera taji daɗin jikinta sosai fiye da yadda take ji a da. Tun wajen shida Uncle Sadiq da matarsa Jawahir suka je, sun kai masu abinci cikin cooler. Tun jiya Hajia Binti tayi mashi bayanin halin da brother ɗinsa yake. Dama Naseera zata bada bone marrow ɗinta wannan satin amma kuma ga abinda ya faru.
Baiyi wata wata ba yace a gwada sample ɗinsa, tunda Dr Abdallah ɗan uwansa ne. Kada a takura ma Naseera, yanzu abubuwa sunyi mata yawa. Idan an dace saiya bada nashi. Har hawaye Umma tayi tana gode masa.
Karfe takwas sun dunguma hanyar Police station, Naseera tace ta yafe, saboda maganar ma karin kanta tashin hankali yake sakata. Anan Uncle Sadiq yace ko tayi bayani kokuma su je da motocin yan sanda duka matasan layin a kame su.
Haka ta hakura suka tafi, VIP treatment aka bama Naseera, tana office ɗin DPO suna zaune. Asp Musa shima ya hallara. Anan ta sake zayyana masu abinda ya faru daki daki daga fitar ta asibiti har haɗuwar su da Uncle Sadiq.
Wata officer tana ciki itace zatayi documenting. Aikam nan taje waje ta bama sauran abokan aikinta labarin yarinyar da tazo da iyayenta wai anyi mata fyaɗe. Dama officer ɗin ba musulma bace. Anan sukayi ta sababi wai waye ba'a raping.
Daya daga cikin su tace da zata samu number wanda yayi raping ɗinta data ƙulla a laƙa dashi itama taje ya kwana da ita. Saboda yadda Naseera ta jigata ya nuna shi asalin namiji ne. Anan suka bushe da dariya suna ce mata batada dama. Wata kuma tace ƙila ma dumping ɗinta saurayinta yayi shine tazo ta ƙala mashi sharri saboda tanada kudi.
Nan yan sandan su uku sukayi ta tsine ma Naseera saboda yanzu zata karo masu aiki. Duk abinda ya shiga ta hanyar DPO sai anyi shi babu mistake. Su kuma sunfi so suzo suci gyada ko masara. Idan an kawo case kanada kuɗi su sake ka koda babu gaskiya a tareda kai.
DPO ya tura yan sanda layin da Naseera tayi masu bayani akai domin aje a taho da wanda sukayi mata aika aikan.
Su Mallam su kuma suna gefe suna tattauna yanda zasu samo dubu ɗari yanzu. Sam bazai bar ƴarsa ta zauna a wannan azzalumin wajen ba. Sai ya yanke shawarar zai saida gidan sa, kokuma ya bada jingina. Kwatar fegi ni amma yasan baza'a rasa masu soba.
Aliyu ne yace fafur baza'a siyar ba, gwara shi ya sayar da machine ɗinsa a samu kudin. Machine ɗin ba sabuwa bace amma tana mashi amfani. A wajen abokinsa ya siya. Yanzu haka duk dare yana fita achaɓa bayan ya tashi daga shago. Dole ya hakura su fito da Ruma Sa'u.
Fita yayi cikin awa ɗaya ya dawo da kuɗin hannun sa, anan aka bada kuɗin bailing. Ruma an miƙa mata kallabin ta tana sakawa kenan sai ga Naseera ta fito tazo bakin kanta signing wani form. Nan yan sandan biyu suka soma zunɗen ta. Daya daga ciki ta kasa shiru ta soma mata magana.
"ke ce akayi raping jiya ko?"
Da kai ta amsata. Saita cigaba da rubutun ta. Buden bakin Ruma Sa'u saita soma magana, "Raping kuma sai kace karamar yarinya." saita fashe da dariya. Suma yan sandan dariyar suke yi.
"Amma anyi yar gari," Officer ta faɗa tana dariya tareda nuna Ruma.
"mostly mata munada matsala, soyayya dole ne? Yace baya sanki sai kiyi mashi sharri? Kinada sheda cewa an maki fyade," saita kalle yan sandan, "Officer wallahi kuna kokari. Idan ina aiki anan za'a yi artabu dani. Yarinya ta gama iskancinta wai tace an mata fyade."
Nan aka babbake da dariya a wajen, har maza officers suma suna yi, wani yace, "wai wai mata kuna sha'anin ku."
Su Inna suna waje suna jiran tafito yasa basu san tsiyan da take tafkawa ba. Hawaye kawai Naseera takeyi ba tace komai ba. Ita kaɗai tasan abinda ke damunta.
Su Umma da Uncle Sadiq ne suka fito, ance anga biyu daga samarin. Ita Naseera tace bataso ta sake ganin su. Semen ɗinsu da suka bari jikinta an ɗauko sample za'a DNA test. Da wannan ya isa su daɗe a gidan yari.
A farfajiyar police station ɗin suka tarar dasu Inna. Su kuma suna rakuɓe a gefen motan su suna jiran Kankana ta fito. Gaban Inna ne ya soma faɗi da taga Naseera. Yarinyar tana yanayi da danginta. Wani abu kawai taji ya tsaya mata a rai. Da kyar ta iya bude baki tayi magana, "Sannun ku," tace masu.
Ba Naseera ba harta Ummanta suka kalle Inna a tare. Suna mamakin yanayin matar. Harta muryanta tsab baida bambanci dana Naseera. Shi kuma Uncle Sadiq wayansa ya soma ruri, number ne daga Spain suka kira sa. Anan hankalinsa ya komai maimakon su Inna.
"Holla ! Ki pasa? (Hello! Menene?)," ya faɗa da yaren Spain. Yana wayan har ya shiga mota, suma suka shiga suka wuce, su kuma su Inna suka nufa hanyar gate a kafa domin suje su hau motar haya.
Wannan kenan!
#Naseera
#RumaSau
#Mahfooz
#DiyarDrAbdallah
Ainakatiti 🌠
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top