Thirteen- Permanent Stalker

Please don't forget to vote, comment and share with your friends.

Kwakwalwarsa tafasa yakeyi, komai ya cunkushe mashi. Banda jijiga Naseera baya komai. Tunanin yadda zaiyi masu Ardo bayanin abinda ya faru yakeyi. Kokuma abinda zai ce ma Dr Abdallah. Tabbas daga yau rayuwar sa zata canza.

Ruwa dake cikin buta a gefe ya gani, da sauri ya ɗauko ya soma watsa mata. Bata farka ba har lokacin. Aikam gaba ɗaya ya sheƙa mata shi. Nan ta soma jan numfashi tareda tari. Riko ta yayi da sauri saiya tallaba ta jikinsa. Bakinsa yana rawa ya soma magana.

"Naseera..."

Kallonsa ita kuma takeyi tarin ya tsagaita. Tana kokarin tuna abinda ya faru.

"Wallahi na sha..." sai yayi shiru baice Fauziyya ba. Tabbas yasan Naseera ta gaji da jin sunan Fauziyya a bakinsa.

"Nagode da kika farka, kiyi haƙuri in sha Allah bazan ƙara ba," yace tsoro ƙarara cikin idansa. Har lokacin jikinsa bai bar yin rawa na tashin hankali ba.

Ita bata amsa ba, binsa da kallo takeyi tana nazari. Jibe yanda ya susuce. Yayi kaca kaca kamar dambu. Sai kuma ta soma ɓanɓare kanta daga jikinsa. Batasan wani abu dazai haɗata dashi kwata kwata.

Shima ya lura saiya janye daga gareta, har lokacin bata bar kallonsa na al'ajabi ba. Anan sai taga cewa wata kila matsalar dake damunsa zai fi nata ta wani fanni. Domin duk tashin hankalin da take fuskanta idan ta kwanta barci baya hanata. Saidai idan ta tashi saita ɗaura daga inda ta tsaya.

Zuwa tayi wajen fitila zata sake kashewa tunda batasan silar shigan sa wannan yanayin ba kenan. Da sauri ya dakatar da ita.

"Kada ki kashe dan Allah," ya faɗa a tsorace. Binsa da kallo ta sake yi tana nazarin yanayin daya shiga. Kamar yaro ƙaramin ya koma.

Shimfidarta ta koma saita kwanta, barci da wuta a wajen yana takura mata. Amma ta tsinci kanta cikin kogin tausayin sa. Tabbas shima yanada nashi abin ruɗani. Anan ta tsinci kanta tana son sanin labarin sa. Ƙila idan taji nasa zataji dama dama akan abinda ke faruwa a nata.

Amma kuma data tuna cewa shine sanadin shigan ta nata matsalar. Sai kuma ta daina tausayin sa. Anan tayi mashi fatan Allah ya kawo mashi ruɗani ninkin ba ninkin. Kamar yadda bai koma barci ba haka itama bata koma ba. Itace ma taketa juye juye, shikam matashi yayi da hannunsa saiya kafa ma ceiling ido yayita kallo.

Baisan wanne yafi bashi takaici ba, rashin barcin sa koko shaƙe mutane idan sunzo kusa dashi. Kaico da lamarinsa yakeyi. Baisan ma ta inda zai fara ba domin yaji dama dama. Ya saba ganin turawa a film suna zuwa wajen therapist domin su samo masu mafita.

Amma baya ganin zai iya zuwa ofishin wata ya zauna yayita bayyana mata sirrin sa. Wani abu da sirri yanzu sai a fara maka kallo ana tausaya maka. Shi abinda ya tsana kenan. Gwara ka zage shi dakaji tausayin sa. Shi a ganinsa daga tausayi sai raini.

Dataga barcin ba mai zuwa bane saita fita tayi alwala, ya fiye mata zama tana tunane tunane, balle kuma datayi magana da Mahfooz gwara ayi mata duka da itace.

Anan tayita jero salloli, iyayenta taketa ma addu'a Idan tayi sujjada. Tabbas tasan suna cikin ruɗani musamman ummanta.

Da zakara yayi chara sai Ardo Bello ya fito, a lokacin shima Mahfooz ya fita. A wajensa yayi sallah. Bai koma ɗakin ba domin kwata kwata baya san yadda Naseera take tamke gira tamau. Abin yana bala'in ƙona mashi rai kamar zaiyi hauka amma yake dannewa.

Bayan kwana shida...

Haka rayuwa ya cigaba da kasance masu, basa shiga harkan juna kwata kwata. Abin yana bala'in ma Naseera daɗi kawai dai ita bata ganin gudun kwanakin ne. Idan taga Mahfooz toh daga nesa ne idan tazo wucewa. Shikam duk me tayi idansa yana kanta.

Tana kwance a ɗaki tana hutawa, lokacin hantsi ya fito. Sai taji an shiga ɗakin, duk daukarta Charo ne amma dataji ba'a yi sallama ba saita fara tunanin kila Mahfooz ne. Anan ta rufe idonta dama bata fuskantar ƙofa.

Buga katifar taji an somayi da kafa, a hankali sai kuma da ƙarfi.

"Keh ! Ki tashi kije ki ɗebo mana ruwa a rafi," taji muryan Fesindo ya dira kunnen ta. Anan ta waiwayo domin ta tabbatar da cewa eh abinda taji gaskiya ne. Kallon rainin wayo Fesindo ta bita dashi, sai tayi ƙarar cingam ƙas ƙas ƙas.

"Na'am," Naseera tace mata mamaki bayyane a fuskanta.

"Eh nace ki tashi ki tafi kije ki ɗebo ruwa a rafi. Tun safe Charo tana wani juya idanu taƙi aikin komai. Kema kin wani kwanta kun barni da aiki zai kasheni. Halan auren ku nake yi?" ta ce tana zabga mata harara tareda jijiga.

Naseera bata gane dalilin dayasa Fesindo ta ɗaura mata karar tsana ba, kullum saita takale ta da faɗa tana mata rashin mutunci. Amma na yau waita tafi taje rafi bayan tasan cewa duka garin na neman sune domin su gayama Sada. Takaici ne ya mamaye Naseera, jikinta duk yayi sanyi. Batada lokacin da zatayi sa'in sa da Fesindo. Gwara taje Sada ya ganta, ba ita kaɗai ba harta Fesindo zata yabama aya zakinsa sabida tayi mashi ƙarya rannan ai.

Wuceta tayi domin taje ta ɗebo ruwan, a wajen ɗakin Charo taga wani bokiti ta ɗauka. Bamanga yasha kewaye zata amma dayaga ta nufa hanyar kofa saiya dakatar da ita.

"Likita ina zaki haka?"

Anan ta soma inda inda bataso ta gaya mashi abinda yake faruwa, Fesindo matarsa ce kuma bata so ta shiga tsakanin su. A lokacin Fesindo ta fito tsakar gida tana tauna, kallonta Bamanga yayi takaici ya soma ɗawainiya dashi.

"Ke kika ce taje rafi?"

"Eh ni ce, ai ba jaka suka ajiye ba da wancan," saita nuna ɗakin Charo. "sun wani shige ɗaka sun bar mara aikin yi tana masu aiki, toh wannan ta fito yanzu kuma zanje na finciko Charo tazo tayi min surfe," tace cikin yanayin ko in kula.

Mahfooz yana daga gefe yana ji, abin bai mashi daɗi ba. Yaso yace ma Bamanga zaije ya ɗebo amma kuma duka daga shi har Naseera basu kamaci su fita ba. Saidai idan aikin gida ne shi ba matsalar sa bane. Fauziyya tayi mashi tarbiya mai kyau ta fannin nan.

Ko yanzu bayan Asuba tunda baya komai, shi ke samun tsintsiya ya share tsakar gidan tas ya ƙona datti. Ita kuma Naseera duk abinda ta kama zatayi sai Charo tayi maza ta karɓe tace ita baƙuwa ce ya kamata a karramata. Har tana zolaya ta akan cewa idan taje birni wajenta itama zama zatayi bata komai.

"So kike Sada ya ganta?" Bamanga yace mata.

"Toh ni ina ruwana! Ai ba yar uwata bace." Fesindo tace tana hararar su duka.

"Meyasa bakida tausayi ne, idan kinaso ta taya ki da wani aiki ba sai ki sakata girki ba, meyasa zaki ce ta fita cikin gidan nan?"

"Wallahi bazan ci abincin yar birni ba. Suda suke dafawa yayi ɗanye salan ya lalata min ciki na tsinke da zawo.... Bazai yiwu ba,"

Kallon Naseera tayi fuska babu wasa, saita nuna mata yatsa ta fara ruwan bala'i, "Wallahi idan baki ɗebo ruwan nan ba bazan baki abinci ba yau. Kinji na gaya maki," saita wuce ta barsu.

Idan ran Naseera yayi dubu toh ya ɓaci, ji tayi kamar ƙasa ta buɗe domin ta haɗiye ta. Kunya duk ya mamaye ta, ga duka yan gidan an fito ana kallon yadda Fesindo take cin mata mutunci. Muryan Nenne taji tana magana," Ita Charo meya sameta?"

Da Naseera takeyi amma ita bata san amsar da zata bata ba, tasan dai sun haɗu lokacin karin kumallo. Anan ta nufa hanyar ɗakin. Sallama tayi bata amsa ba. Sai ta waiwaya ta soma dube dube a wajen kewaye. Anan taga kofar wajen a bude alamar babu kowa ciki.

Ajiye bokitin hannunta tayi a waje saita shiga cikin ɗakin, akan gado ta riske Charo tana numfashi da kyar. Da sauri Naseera ta ƙarasa wajen.

"Charo !!!" ta kira sunanta. Ita kuma wanda idanta yayi ƙanana bata amsa ba. Kawai dai tana jinta ne kaɗan kaɗan. Saidai tayi kokarin ta kama hannun Naseera gam ta riƙe.

"Tun yaushe kike haka, meke damun ki ?" Naseera ta sake tambaya. A lokacin Charo tayi kokarin fara magana.

"Ina Mijina yake ki kira min shi." anan Naseera ta fita da sauri.

"Ina Musa yake, Charo batada lafiya," ta faɗa a tsakar gida. Nenne ne ta bita suka shiga. Sai lokacin Naseera ta lura Charo haihuwa zatayi.

"Inaga haihuwa ne yazo," tace ma Nanne. Ita kuma dakai ta amsata. Anan suka je inda Charo take sai suka zaunar da ita. Ruwa ta buƙata tanaso tasha. Randar dake ɗakinta mai kyau kuma gashi yana sanyi Naseera ta ɗebo mata ruwa daga cikinsa, dama ga kofin silba gefen wajen. Anan Charo ta shanye.

"Sannu kinji!" Nanne tace.

"Tun yaushe kika fara jin haka?" Naseera ta tambayeta.

" Tun shekarar jiya," ta amsa da kyar. Mamakin karfin halinta sukayi su biyu. Nanne ta fita domin ta gayama Ardo abinda ake ciki. Harta fita tana zura takalmi sai Naseera ta tsaida ita.

"Asibiti za'a kaita yanzu?" tace cikin damuwa.

Murmushi Nenne tayi saboda kamar Naseera bata lura nan kauye bane. Babu abin hawan da zasu hau suje da ita. Idan akayi gigin fita da ita zata iya haifan yaron a titi.

"A'a anan zata haifa abin ta. Yanzu zanje na gayama Ardo, akwai wata wanda take taimakon mata su haihu. Sana'arta ne, harda ƙaramin shago na magani takeda shi,"

Tunani Naseera ta fara, bata taɓa aiki a irin nan wajen ba tunda take. Ko a UK inda tayi karatu komai na asibiti na gani na faɗa an ajiye masu. Saidai kuma Charo kamar kanwa take a wajenta. Zatayi komai domin taga ta taimaka mata.

Bamanga ne yazo da bokitin ruwa guda biyu, anan yaga sunyi carko carko.

"Inna lafiya?"

"Dama za'a kira Hadiza mai magani ne, Charo tana nakuɗa,"

"A'a ni zanyi." Naseera ta katse su da sauri.

Anan suka soma kallonta, ita Fesindo wanda ita tun kafin taje ta tada Naseera ta lura nakuɗa Charo keyi. Dama daga ɗakinta ta fito kuma tana ganin yanayinta amma tayi banza da ita. Yaran Fesindo uku duka mata. Yanzu tana bala'in kishi da Charo kada ta haifa namiji ya samu garken shanu.

"Nenne karfa ku yarda da ita. Waya tabbatar tanada ilimi. Wallahi na taɓa zuwa asibiti kuma wannan dai batayi kamada kalar da za'a kira likita ba,"

"Dan Allah idan bakida abin da zakayi ki wuce ɗakin ki," suka ji muryan Ardo. Kowa yayi mamaki saboda idan ana ƙananan magana haka baya saka baki. Saidai yayita binsu da mugayen kallo. Kamar guguwa ta wuce ɗakinta ta barsu a wajen.

"Likita kika ce zaki iya?" Ardo ya tambayeta. Dakai ta amsa mashi. Daga Nenne har Bamanga sunji daɗi. Dama sunfi so tayi, domin ko ranar sun zanta cikin ɗaki sunata fatan Charo ta haihu lokacin Naseera tana nan saboda zata samu kulawa yanda ya dace.

Shi Musa ranar yana bayan gari yaje kiwo tun asuba ya fita yasa baisan wainar da ake toyawa ba. Ardo ya miƙa ma Bamanga kuɗi domin ya siyo kayan da Naseera zatayi amfani dashi. Shi da kansa ya miƙa mata biro da takarda wanda yake tanadin su.

Anan ta rubuta kuma ta karanta mashi, Hadiza dama ba'a garin ta tashi ba. Taje aikatau birni tana yarinya har tayi aure a chan. Toh taje ɗan 'san kowa' wanda ake yi na sanin makamin aikin nursing kaɗan kaɗan.

Cikin minti talatin ya dawo mata da abinda ta bukata, wasu ba irin suna ɗaya bane amma kuma amfanin su ɗaya. Da haihuwa yazo ma Charo bata wahala chan ba. Da Naseera da taimakon Nenne ta haifa yaronta namiji.

Baƙin ciki mara mitsaltuwa ya kama Fesindo da taji abinda Charo ta haifa. Itama Dadda sai lokacin taje ɗakin. Tana fizge fizge tana haɗa rai. Koda ta ɗauki yaron sai ta gansa sak kamar Musa sanda yake yaro. Anan sanshi ya soma shigan mata rai wanda dole ta sake fuskanta.

Itama ta sake jikinta domin ayi aiki da ita, da kanta taje rafi ta ɗebo ruwa ta saka ma Charo a garwa domin tayi wanka. Kuma bayan an goge ɗakin ta bishi da kalanzir domin ƙarnin ya tafi.

Mahfooz banda alfahari da Naseera baya komai. Anan santa ya sake shigan mashi rai. Dukda ba kallon inda yake takeyi ba, ganinta kusa dashi a haka ya fiye mashi zaman Kaduna idan sun koma. Saiya fara tunanin dama suyi zaman su anan. Yana ganin sannu a hankali zai iya shawo kanta akan ta yafe mashi. Kuma idan tayi haka zai iya koya mata yadda zata so shi.

Sanda Musa ya dawo shine yayi mashi huɗuba tareda saka mashi suna Bello Adama. Bayan Isha Naseera ta kaima Charo abincin dare, tuwo ne sai kuma katan kofin shayi. Ita tace ma Musa yaje ya siyo kayan shayi sai kuma biredi domin zai fi gina mata jiki.

Charo bata wani ɗauki yaron ba saboda kunyar ɗan fari. Naseera ce ta ɗauki yaron tana wasa dashi, lokacin Nenne tayi mashi wankar dare. Yan uwan Charo basuda labari saboda sunada nisa da inda suke balle kuma basuda karfi sosai da zata koma wajen su jego.

Yaron yanada bala'in girma ga kyan gaske. Naseera tana riƙe dashi hannunsa yana sagale a nata. Murmushi kawai takeyi tana gode ma ni'imar Allah. Saidai kuma ita batayi tsammanin zata iya samun yaron kanta ba. Bayan fitar ta daga nan garin zata kama gabanta saboda dole Mahfooz ya saketa.

Kuma ita tayi alwashin bazata taɓa aure ba balle kuma batun rabo ya gifta. Anan idanta ya ciko da kwallo saboda tana bala'in san yara. Balle yanda Ummanta batada yara dayawa ita tace idan Allah yaso zata haifa dayawa domin zuriar Dr Abdallah ya ruɓanya.

Hawaye ne ya soma gangaro mata daga idanu, da sauri ta fara sharewa kafin Charo ta ganta. Abinda bata sani ba shine Charo ta daɗe tana kallonta kuma taga yadda take zubadar da hawaye.

"Adda kema kina san yara koh?" tace mata.

Kallonta tayi ta gefe taga eh da gaske ta ganta tana kuka kuma da ita takeyi. "Uhm" ta amsa dashi.

"Ai tunda kinada aure ki saka rai kema zaki samu naki. Saidai na lura Adda kamar bakison Baffa Mahfooz. Meya maki ?"

Naseera wannan karan kuka ta fashe dashi, har hawaye yana zuba a fuskan Bello Adama. Charo bata hanata ba, Saboda itama sarkin kukan ce. Kuka yana kawo mata natsuwa sosai. Tana wani jin sanyi sanyi cikin ranta nauyin datake ji cikin ranta yana rage wa.

Tsoro fal cikin ran Naseera, bata san ko zata iya yarda da Charo ba da sirrin ta amma kuma tasan bazata cutar da ita ba.

"Banida lafiya..." Naseera tace. Muryan Dr Chinedu taji cikin dodon kunnen ta sanda yake sake jaddada mata zatayi aure kuma zata haihu muddin ta bi dokokin da aka gindaya mata. Wannan ai karatun da sukayi ne a jami'a kuma sarai ta sani. Amma dan Adam yanada rauni, kuma nata shine tsoro. Ko ɗazu datake taya Charo wajen haihuwa safan hannu guda biyu biyu take sawa bata so tsautsayi ya gifta.

"Banida Lafiya Charo... Ciwona babba ne," saita fashe da kuka. Kallonta Charo tayi tana mamakin meya haɗata da Mahfooz. Menene dalilin tsanar Mahfooz domin ciwon.

"Ina ruwan Baffa Mahfooz? Shiya saka maki?" Charo ta watsa mata tambayoyi.

Tunani Naseera ta soma, ba Mahfooz bane ya shafa mata. Ta wani fanni tana yanayi da Mahfooz. Batada maraba dashi. Ya cutar da ita bisa dalilin cewa tana kamada wanda ta cutar dashi a baya. Itama tafi tsanar Mahfooz akan wanda suka cutar da ita. A fuska yanzu idan ta gansu bazata gane suba, amma kam ta ɗaura karar tsana akan Mahfooz.

"Bashi bane... Amma da zai iya taimaka mani kuma baiyi ba"

"Adda komai mai wucewa ne, duniyar guda nawa ne. Nasan cewa ya baki haƙuri. Ki yafe masa. Allah ma mun yi mashi laifi ya yafe mana balle mutum." Charo tace, anan ta ɗauki shayinta tanata ƙyanƙyanma. Saita gutsara burodi tana ci. Taji daɗin sa sosai saboda yanada bala'in zafi. Naseera banda nazari bata komai. Muryan Charo taji a kunnen ta tana mata magana.

"Kuma ni na tabbata Baffa Mahfooz yana bala'in sanki. Bayada wani abu bayan kallon ki. Duk inda kika gifta idonsa yana biye dake."

Naseera shiru tayi tana kallon Charo cikin wasi wasi, cikin mamaki take nazarin abinda taji. Ita dai duk tunanin ta tasan cewa Mahfooz yanaso kawai yaga ta yafe mashi ne. Amma kuma wai zancen soyayya bata taɓa kawowa ranta ba.

"Bazai yiwu ba, Mahfooz ya tsane ni. Ni nake gaya maki wannan! Na fi ki saninsa." Naseera tace cikin takaici.

"Ina so ki lura da yanda yake maki, baya nuna akwai kiyayya tsakanin shi dake face soyayya. Adda nayi samari kala kala kafin nayi aure kuma ina gaya maki wannan soyayya ce,"

Naseera bata sake cewa komai ba, haka suka zauna shiru cikin ɗakin har Charo ta gama cin abinci. Anan ta kwashe kwanonin ta fita dasu, daga nan ta wuce ɗakinta. Abin al'ajabi kawai take ji a cikin ranta. Wai ace Mahfooz ke santa. Abin da kamar wuya gurguwa da auren nesa.

Mahfooz ta riska cikin ɗakin zaune akan tabarman sa, yana haɗa ido da ita saiya sakar mata wani lallausar murmushi. Bata mayar masa ba, amma bata harare shi ba kamar yadda ta saba.

Shimfidar ta taje ta zauna, zaune take zuciyarta fal da damuwa. Bata ji daɗin sanin abinda take zargi akan Mahfooz ba. Tabbas wannan al'amari na Mahfooz bazai taɓa faruwa ba. Batayi tsammanin akwai wanda zai amince da ita ba da cutar ta mai karya garkuwan jiki. Musamman Mahfooz wanda yake matashi. Yanada kuɗi yanada kyau kuma ta tabbatar yana da yan matan da suke binsa.

Me zaiyi da ita? Taketa tambayar kanta. Sai kuma wani rai ya raya mata da cewa tausayin ta kawai yakeyi babu wani abu daya wuce wannan. Amma kuma saita tsinci kanta da son taji labarin sa. Tanaso tasan dalilin dayasa yake firgita. Tunda yana tausayin ta shima tana so tasan wani abu game dashi. Balle suna zaune cikin ɗaki ɗaya ya kamata su san wani abu game da juna.

Nisa tayi saita kalle shi, "Waye Fauziyya?" ta tsinci kanta da furtawa. Shima yayi mamaki sosai saboda bai taɓa tsammanin zata bukaci taji wani abu game dashi ba. Saidai shi bayada niyyar faɗa ma kowa komai gameda rayuwar sa na baya. Ya riga ya birne wannan labari chan ƙasan zuciyar sa kuma baya so ya ɗauko wannan babin balle wani kuma yaji.

"Hmmm......" Mahfooz yayi ajiyar zuciya. Kallonta yakeyi, yanaso yaga dalilin sauyin data shiga, ko kiptawa ba yayi yana kallonta. Sai kuma ya Shafa kansa yana tsafe gashin sa da yatsun sa. Gefe da gefe yayi da kai yana kokarin ya samu lafazi tattausa wanda zai gaya mata wannan bukatar bazai iya cika mata ba.

Har lokacin bai ce komai ba, bata karaya ba saboda tasan cewa sirri yanada nauyi. Kamar ita ne yanzu a tambayeta dalilin dayasa bata so tayi aure.

"Kawai inaso nasan meyasa baka barci ne," saita sakar mashi murmushi alamar ya yarda da ita, "Ka bani tsoro ranar chan, harna mance na tsane ka naje na taimaka maka. Idan haka rayuwar ka yake ya kamata kaje a duba ka, kaje gurin kwararru domin su gane ta inda zasu magance matsalar..."

"Karki damu Naseera, ba wani abin tashin hankali bane." ya katse ta. Kwanciyarsa na kallon sararin samaniya yayi abinsa. Sai ya rufe ido, ba barci yakeyi ba. Bazai ma iya ba bayan wannan guntun maganar da sukayi da ita. Tun da yake da ita sai yau ta taɓa mashi magana cikin natsuwa tareda murya mai taushi. Anan ya shiga kogin santa tareda begenta, sai dai kuma baiyi tsammanin zai iya faɗa mata abinda takeso taji ba. Yasan daga nan zata soma tausayin shi kuma shiba abin tausayi bane. Kamar yadda shiba maraya bane ya ɗauki iyayen Faash a matsayin nashi.

"Bayan duk rashin mutuncin da kayi min, bayan canza min rayuwa daga fari zuwa baƙi. Rannan har kusan kasheni kayi. Ya kamata yanzu ka fanshe kanka da wannan," sai tayi nisa tareda tari kaɗan domin ta gyara muryanta. Kallonsa tayi wanda shi baisan tanayi ba.

"Mahfooz ka faɗa min wacece Fauziyya, kila baka san ko nasan ta ba," tace da murya ƙarami.

Gyara kwanciyar sa yayi saiya kalle ta, murmushi ya sakar mata wanda yake bayyana hakora. "Nace maki baki santa ba, kuma wallahi bana fatan ki santa. Ke harta maƙiyana banaso su santa balle ke...."

Anan maganar ta sargafe a bakinsa tayi mashi nauyin faɗi, baisan da wani yanayi zata karɓe batunsa ba. Baiso kuma ya firgita ta ko kaɗan. Ita kuma gabanta ne ya faɗi, harga Allah tana kyautata zaton ta gane hanyar daya nufa. Ta gode ma Allah da bai ƙarasa zancen ba. Domin idan ya furta mata abinda Charo take zargi komai zaije chaɓe masu. Koda bai furta mata ba idan da gaske ne komai zai canza.

Rayuwarta zai shiga sabon fasali, kuma rabuwar ta dashi zai zama abu mai bala'in wuya. Ta lura Mahfooz yanada naci da kafiya. Idan yasa ranshi a abu toh saiya cinma birinsa. Kuma abin yana burgeta a mutum, ita abu kaɗan zata karaya ta cire hope. Saidai ita ba abinda zai iya mallaka bane, ko sanda take da lafiya balle yanzu ta zama haka. Bazata iya yarda ta cutar dashi ba. Dauriya gareshi amma ta lura lalurar sa yafi nata yawa. Rayuwarsu yanada kusanci sosai fiye da yanda mutum ke tsammani.

Kamar yadda ta sanadiyar Mahaifiyarta Fauziyya ya shiga ruɗani, haka ita ma saboda shi komai ya jagule masa. Ta wani fanni bata ganin laifin sa, dama ance alhaki kwikwiyo ne. Gashi na Fauziyya ya risketa. Ta rasa bakin da zata gaya mashi cewa ita ba yarinyar Dr Abdallah bane kuma wannan Fauziyya data buwaye shi itace mahaifiyar ta, tabbas fansan daya dauka yazo daidai. Amma kuma saita tsorata, yadda ya iya kallon yan iskan nan suna ingiza ta cikin ɗakin su tasan haka zai rikiɗa ya mata rashin mutunci.

"Bakasan duka dangina ba, ta ina zaka gane ban santa ba," tace masa cikin barkwanci. Shi a karo na farko kenan daya ganta cikin yanayin nan kusa dashi. Ya tsinci kansa cikin nishaɗi. Murna yakeyi cikin ransa kamar anyi mashi albishir da kujerar Makka.

"A'a Naseera babu wani abu daya alakan ta ku sai yanayin fuska," ya ƙarasa chan ƙasan muryan sa. Saiya tashi ya zauna ya dubeta. Itama kallon nasa takeyi. Akwai tazara tsakanin su, ji yayi kamar yaje dab da ita domin ya zauna.

"Babu abinda kike dashi irin nata, kinada tausayi kinada natsuwa ga kuma hankali. Fauziyya idan aka ce a gidan magajiya aka haifeta bazan musa ba," ya kara fadi yana dariyar ƙeta.

"Amma ai bashi bane zaisa ace ban santa ba kokuma ban haɗa komai da ita ba," ta faɗa. Tanaso ta kawo masa batun cewa zai iya yiwuwa tasan Fauziyya, kuma tanaso ta karance yanayin da zai shiga.

"Hmmm" yayi ajiyar zuciya.

"Fauziyya..... Anty Fauziyya tana Kano, kuma idan kun haɗa abu da zan sani sabida a wajenta na tashi,"

Yanzu taji mahaifiyarta a Kano take, tanaso ta sake jin wani abu game da ita wanda zai taimaka mata domin ta neme ta.

"Amma..." ta soma Magana saiya tsayar da ita da hannunsa. Maganar Fauziyya takaici yake bashi sosai fiye da yadda take tsammani. Tunda yabar Kano banda Naseera baiyi maganar da kowa ba.

"Dan Allah ki rabani da maganar ta, wallahi bana so," ya nema alfarma wajen ta.

"Bawai na tambaya da nufin gulma bane...."

"Koma menene," ya sake tsayar da ita. "Naseera baki santa ba, kuma bana so ki santa, bana san maƙiyana suyi gamo da ita balle ke da nake so..." maganar ta kupce mashi daga baki. Hannu yasa saman leɓensa amma yasan taji shi. Anan ya sunkuyar da kansa saiya sake dagawa.

"Naseera ina sanki, so na haƙiƙa wanda bakya zato. Bansan ko saboda na cutar dake bane, kokuma kawai nawa kaddarar kenan. Amma ki sani na daɗe da faɗawa kogin sanki," dariyar takaici ya soma yi, tunda yake sai yau ya taɓa faɗa ma mace yana santa na haƙiƙa babu lauje. Ita kuma Naseera gabanta duka uku uku yakeyi. Ta kasa kallonsa. Wasa takeyi da yatsunta saboda duk ta tsargu. Ya riga ya cuce ta ɗaya gaya mata. Wannan abu ne mai wuyan samu duk da shi baya gani.

"Karki damu, nasan matsayi na wajenki sarai. Kuma bana buƙatar ki amsa batu na. Amma gwara na gaya maki saboda ko zan samu natsuwa cikin raina. Zan daina jin raɗadin danake ji, kuma kila zan samu na soma barci."

"Ba Fauziyya kawai take hanani barci ba, Naseera tunda na ganki banyi barcin kirki ba. Kin shiga cikin rayuwata ta yanda bana tsammani. Akwai wahala bazan musa ba, amma kuma gwara wahalar sau dubu."

Tashi yayi yaje dab da ita ya tsuguna, magana yayi cikin raɗa babu wasa, idansan ya sauke akan nata. Tanajin hucin numfashin sa a jikinta, "Naseera kece muradin zuciyata, kuma bazaki fitar dani daga rayuwar ki haka kawai ba. Duk yadda zaki ɗauki wannan maganar keya shafa, amma bazan taɓa kyale kiba. Ki sani daga yau cewa ni Mahfooz Abubakar Gwaiba is a permanent stalker in your life."

Saiya koma tabarman sa ya kwanta tareda rufe ido. Murna fal ransa, gaya mata dayayi har zuciyar sa ta soma mashi sanyi.

Wannan kenan!

#Naseera
#Mahfooz
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilicious
#FullyDimplated


Ainakatiti 💫






Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top