Ten - Kallon Kallo

Yau ranar ki ce Zubaida Mohammad Nalado. Allah ya albarkace sabon shekarun ki, Amin summa amin. Haƙiƙa ke mace ce mai nagarta da ilimi. Allah ya kai haske kabarin Mommy, ya kuma bamu ikon koyi da kyawawan halayyar ta. HBD Habibtee, Allah's rahma Xobeaderh with the X❤️

***

Asibiti Naseera ta koma kai tsaye, dama tana duty, ta ɗauki uzuri ne domin ta amsa wayanta. Gabanta bai bar duka ba. Bata ƙaunar sake haɗuwa da Mahfooz. Bata fita daga parking lot ba, nan ta zauna cikin motan ta tana ajiyar zuciya da sauri.

Miyan bakinta ya ƙafe nan take, ƙishin ruwa ya soma addabar ta. Nan ta duba cikin motan ta amma babu ko ɗigon ruwa. Anan ta kafa kanta akan steering ta buɗe sabon babin kuka. Komai ya dawo mata fal, duk jeran abubuwan da suka rinka faruwa da ita ta soma tunawa.

Ita tana kyautata zaton akwai abinda ke damunta, ta rasa gane dalilin da jerin abubuwa suka rinka faruwa da ita kadai tilo daya bayan daya. Umma ta hanata wannan mugun batu, ta ɗauki kaddara a yanda yazo mata. Saidai mutum ajazi ne tunanin yana yawan gifto mashi.

Sai kuma ta tuna abinda Mahfooz yace, tabbas taji ya tambayeta ko ita yarinyar Fauziyya ce. Tunani ta fara shin wacece Fauziyya? Koda itace mahaifiyar ta kuma Mahfooz yasan ta. Batada amsar tambayar amma abinda tasani koma wacece Fauziyya yadda Mahfooz ya kafa mata karar tsana. Babu haufi ba mutuminiyar arziki bace.

Anan ta soma tunani kila yawan alhakin da Fauziyya take dauka ma mutane shine yake dawowa kanta saboda ita ce yarta. Ranta ya cigaba da ƙuna, bataso ta haɗu da Fauziyya koma wacece.

Saisaita kanta tayi ta fita daga motar ta, anan ta riske Musa ashe sunyi batan hanya. Tuntuni yana wajen yana jiran ta ance bata nan. Anan ta bashi kuɗin sa sai ta shiga cikin asibiti.

Office ɗinta ta wuce kai tsaye, sai ta buɗe safe ɗinta inda take ajiye ARV ɗinta. Dole ta mashi mugun buya saboda bataso kowa yasan abinda ke faruwa da ita. Anan ta ciro ta sha.

Yanzu haka rayuwar ta yake, koda yaushe cikin magani. Ta ɓoye wani roban a gida, sai wani kuma anan. Dr Chinedu yana mata bala'in kokari. Balle dama tasan duk abinda zata sani akan HIV. Ta taɓa shiga wani kungiya akan wayarwa mutane kai gameda cutan a baya.

Rumasa'u banda tauna ƙas ƙas ƙas bata yin komai, kallon hotunan Rahina takeyi na cikin wayan. Tanayi tana kushe munin Rahina cikin ranta. Sam batayi kamar da kalar ajebo ba. Dama itace takeda arzikin ta, tasan tabbas zai fi karɓan ta.

Shi kam taunar datake yi yana bala'in takura mashi, bayaso amma baiso yace mata ta bari kafin ta faɗa mashi babu daɗi. Yadda zuciyar shi ta lalace zai iya kalleta da mari.

Ya lura tun haɗuwar sa da Naseera a asibiti, bayada aiki sai yawan fushi da zuciya wanda da chan baisan kansa dashi ba. Naseera ta fito mashi da wani hali wanda baisan yanada ita ba. Tabbas yasan zasu sake haɗuwa. Ba anan bane rayuwar su zata kare. Abinda bai sani ba shine ta wani siga.

Natsuwar daya tsinta idanta yake kokarin kawar wa. Mai kamada Fauziyya saidai ta kawo mashi baƙin ciki ba alheri ba. Kuma ai bama karya bane, tun randa sukayi ido hudu insomnia mai tsanani ta kamashi. Yayi marabus da barci saidai ta sace shi na awa kaɗan.

Koda wuta ko babu wuta yanzu baya iya runtsa idonsa. Kawai kwanciya yakeyi saman gado saboda gaɓoɓinsa su huta. Abu ɗaya yake kawo mashi sauki, idan yana buga kwallo. Guje guje yana kawo mashi natsuwa tareda kwantar mashi da hankali.

Ya isa gaban gidan su Rumasa'u ya ajiyeta. Juyawa tayi tana mashi murmushi, ita a ranta bata yaga kuɗi yadda ya dace ba amma gobe rana ne, "My love zamu shiga ciki koh kaci lunch?" ta faɗa tana kallonsa, "My love nayi saving a matsayin sunan ka saboda kaine wanda nake so," ta sake faɗi.

Sosa ƙeya ya somayi da yaji ta kira sa da My Love, a lokacin ya tuna sunan daya saka mata. Akwai wata Rumasa'u wanda sukayi bautar ƙasa da ita cikin wayansa. Sai yayi saving sunan Kankana a matsayin "Rumasa'u Kaduna"

Wayancewa yayi sai yace, "Wallahi ana jirana, zamuyi dai waya anjima,"

Bata ce komai ba, ƙasa ta soma kallo. Ita kaɗai tasan abinda ke damunta. Kallon sa tayi babu wasa a fuskanta, "Halan gurin wancan tsohuwar mai tallan taban zaka?" ta tambaye shi amma ita Naseera take nufi. Kishin Naseera ya mamaye ta duk da bata san alakar suba. Ta lura yana ganinta ya daina walwala.

"Bangane ba?" ya tambayeta "Wa kike nufi?" ya ƙara.

Zare mashi ido tayi kamar ita ta haife shi, "Ina nufin korarriyan da muka gani a plaza, wanda ka dulmiya tunanin ta.... Mallam karka raina min wayo wancan tsohuwar mai tallan taban!!!" ta faɗa da murya mai ƙarfi.

Baice komai ba, kifa kansa yayi a steering yana ajiyar zuciya. Koba komai baya hauka sunga Naseera, gari banza saiya saɓa ma Rumasa'u. Amma masifan ta yau yayi mashi rana.

" Fitan min daga mota zan tafi, " yace mata ko kallonta baiyi ba. Kallonsa tayi tana sake baki.

"Ah lallai Korarriya ta shanye ka," tace tana girgiza kai.

Runtse ido yayi ya sake buɗe wa, baisan hayaniya baisan surutu amma zagin datake ma Naseera sam baya mashi daɗi. Ji yake kamar shi ake zagi. Anan ya kalle Rumasa'u, tunani ya soma cikin ransa. Baisan sanda yace yana santa ba datake zaƙewa.

Ya lura ta gama kamuwa da sanshi har zata fara hauka akansa. Tausayi ta bashi, saboda indai akan soyayya ne baisan komai ba. Kwaɓawa yakeyi. Yanmata suyita wahala saboda baisan yadda zai expressing emotions ɗinsa. Shi yanada zurfin ciki, kuma a soyayya ba'a haka.

"Sauka nace zan tafi,"

Rage murya tayi ta soma saisaita kanta, sai a lokacin ta lura da yadda tayi bai kalar masu mutunci ba. "My love kayi hakuri, bansan me ya shiga kaina ba. Wallahi kishin ka nake yi, bazan iya rabaka da kowa ba, kuma ganin wancan..." da zata sake faɗin mai tallan taba saita haɗiye maganar, "ganin wancan sai naji duk babu daɗi... Gashi ɗazu ka kira ni Zanira... My love ka rabu da duka yan matan ka, wallahi ni kaɗai na ishe ka,"

Ajiyar zuciya ya sake yi mai ƙarfi, "Jeki zamuyi magana,"

Kallonsa tayi tana mamakin wannan wani irin mutum ne, meyasa bazai mata bayani ba. Ya gaya mata koma menene, su fahimci juna kamar kowa dake soyayya. Korarta dake yi bazai taɓa faruwa ba. Tunda ta riga ta haɗu dashi babu abinda zai raba su saidai idan mutuwar su.

Fita tayi kamar guguwa bata sake cewa komai ba sannan ta buga murfin motan da karfi kamar zata balla mashi ƙofa, shima ya lura yayi mata tsauri. Bata cancanci korar daya mata ba. Amma kuma bazai iya jure zagin datake bin Naseera dashi ba. Basan Naseera yakeyi ba, it's not possible. Amma kuma baiji daɗin yadda Rumasa'u ta bita da zagi ba, wai har ce mata mai tallan taba.

Tunda yake bai taɓa jin an zage mutum haka ba, balle ace wai masu hannu da shuni tana haka. Mamaki yakeyi a ina Rumasa'u ta gwamatsu da yan tasha da har suka koya mata wannan kalma. Zai hukunta ta sabida shi bazai jure rashin mutunci ba.

Sanda ta shiga Rahina ta nemata ta gaji, baki ta saka hangangan dataga Rumasa'u da kayanta. Duk yafi tsada a wanda ta siya daga Dubai.

"Tsakani da Allah meyasa zaki saka min kaya baki tambaye niba,"

"Sorry, bari na ninke maki," ta faɗa cikin yanayin ko in kula. Bata ma kalle fuskan Rahina ba. Haushi ne ya kamata, wai danta saka kayanta take fushi. Yasa take yawan faɗin cewa Rahina ta gaji tsiya. Sam batada kirki. Sai meye danta saka kwara ɗaya a cikin kayanta? Tabbas batada tausayin talaka. Akan abin duniya shine take haɗa rai.

Anan Kankana ta cire kayan ta ninke, "Kinga ban yaga maki ba," ta faɗa cikin izgili. Zani ta ɗaura tunda batada towel zata shiga bayi tayi wanka. A duniya wanka cikin Jacuzzi yana birge ta. Sai tayi sama da awa tana zaune ciki.

Taso ɗaukar towel ɗin Rahina sai taga yadda ta haɗe rai. Harara ta watsa mata saita wuce bayi. Rahina batace komai ba. Takardan makaranta take dubawa abin ta. Kwata kwata bata jin daɗin zama da Rumasa'u. Duk ta takura mata. Gata da bala'in kazanta. Rannan bayan gida tayi batayi flushing ba. Gashi komai zubarwa takeyi bata ajiyewa inda ya kamata. Amma kuma tasan suna cikin matsanancin hali yanzu babu yadda zatace ta tafi.

Koda Rumasa'u ta fito Rahina ta kwanta akan gado zata rutsa, "Bulala! Bulala!! Bulala!!!" ta kwaɗa mata kira. A firgice Rahina ta farka saboda da karfin gaske ta kirata. Sai kace ba ɗaki ɗaya suke ba.

Da Kankana taga ta farka saita soma magana, "Na gyara IPhone ɗinki, kuma na saka sim ɗina. Zaki ara min kafin na siya nawa wayan tunda dai kinada wani," saita wuce wajen madubi ta soma shafa mai. Takaice ne yake dawainiya da Rahina. Bata masan ta inda zata fara ba. Tabbas Kankana ta soma wuce gona da iri.

Bayan Kankana ta gama shafa, lokacin Rahina ta soma barci kuma. Anan ta kunna waƙa tana babbaka rawa. Ba kalar da bata iyaba. Gashi duka tasan wakar tanayi tana rawa. Tsaki Rahina tayi saita bar ɗakin, ɗakin mamanta ta koma domin ta samu ta runsta.

Koda Mahfooz yaje gida ya soma shirya kayansa cikin jakarsa. Komai dayake bukata yayi ta sakawa a hankali idan ya tuna. Naseera ce take faɗo masa cikin ransa, shi kuma sai kawar da tunanin yakeyi. Haka kurum yaji yanaso ya ganta. Baida dalilin san ganinta, bazai ce ya tsane ta ba. Amma kuma bawai santa yake ba.

Kuma ya tabbata bata haɗa jini da Fauziyya ba, tunda daya santa. Anan kuma ya tuna Fauziyya batada kirki duk danginta suna tsoron zuwa inda take. A lokacin ya tuna da wata yar uwanta data taɓa taimakon sa yana ƙarami. Bazai iya tuna fuskan ta ba sosai amma yana tuna abin alheri daya shiga tsakanin su.

Fita yayi yaje training ɗin yamma, yana gudu amma tunani fal ransa. Sai mistake yakeyi har coach yayi mashi magana, absent minded ya zama kamar baya wajen. Idan yace ga taƙamanmen abinda yake tunani akai to yayi karya. Kawai dai yasan cewa hankalin sa baya jikinsa. Wani sukuku yake ji kamar bashida lafiya.

Da wuri yabar filin saboda Coach yayi masa magana ya dawo da hankalin sa wajen wasa har sau uku. Buɗe baki yayi zai watsa mashi zagi. Ya lura kamar mutane basuda imani. Basu ga shima baya cikin hayacinsa bane. Faash ne ya dafa shi.

"Man, what is wrong with you?" yace da harshen turanci.

Da kafaɗa Mahfooz ya amsa, alamar bai sani ba. Bugun bayansa Faash yayi a hankali, "Gwara ka tafi gida, you look like a mess,"

Harara Mahfooz yabi Faash dashi, saiya harara coach shima tareda jan tsaki saiya ɗauki jakarsa ya tafi duk zufa jikinsa. Kwata kwata baisan yadda yakeyi amma ya rasa yadda zaiyi. Faash ne ya tuƙasu domin suje.

Mahfooz bai damu da jira sa cikin mota ba, hanya ya nufa zai tafi a ƙafa. Gwaran mashi kila idan yayi tunani kaɗan a hanya zaiji sanya sanya. Zuciyar sa nauyi yake masa na rashin dalili kuma abin yafi baƙanta mashi rai.

Ya isa kwanar layinsu saiga Faash ya danno kai, horn ya mashi sai ya bude window domin yayi mashi magana, "Man, tafiya ba sallama ? Shigo," yace yana dariya.

Girgiza mashi kai yayi, Faash kuma saiya kafa mashi ido.

"Man, are you alright? Jibeka Kamar aljani duk sai zufa kake yi. Menene wai?" yace cikin kulawa.

"Karka damu dani... I am fine I think... In sha Allah,"

Faash bai sake cewa komai ba, Mahfooz ya riga ya soma tafiya ya barshi a wajen.

Sanda Mahfooz ya isa gida bayi ya wuce yayi wanka, baisan ruwan sanyi ko kaɗan. Koda zafi yana wanka da ruwan zafi. Amma wannan karan daya kunna shower ta wajen ruwan sanyi yasa. Wai duk domin yaji dama dama.

Zuciyar sa yana mashi wasiwasi, abinda yake gudu shi ke shirin faruwa dashi. Bai taɓa samun kansa cikin wannan yanayin ba. Yanayin da zai zama useless baida amfani. Sai yanzu ya lura da dalilin dayasa ya kasa barci. Ba komai illa wannan sabon shafin dake baƙunta sa.

A hankali yake mamayansa, ya shammace shi cikin dare. Yanzu gashi yazo yayi kane kane yana kokarin gina muhalli cikin rayuwarsa. Tabbas zuciya batada ƙashi, kuma ba'a kwaɓanta. Amma idan tace zatayi mashi abinda yake tsammani bata kyauta mashi ba.

Tayi mugun cutan sa. Ya kamata tayi tunani saboda abinda take so yafi karfin ta. Runtse ido yayi ransa yana mashi ɗaci. Shi dama dukansa akayi da itace zai fi jin daɗi akan raɗaɗin dayake ji cikin ransa. Akwai abubuwa da ke faruwa da bawa wanda baida ikon hanawa. Kamar yadda zuciyar sa take raya masa ga abinda takeso yanzu, idan kuma bata samu ba tabbas zatayi masa tijara.

Toh tijara na yaushe kuma, fafur ta hanashi barci. Murmushi yayi na takaici, "akwai ƙura," yace a fili. Jumper riga yasa da wando daya fito. Kalar navy blue ne, Shi Dama baya san kaya masu haske. Baisan yaje guri ayita kallan sa. Hular zanna bukar ya kafa a kansa. Yayi kyau ainun saidai rama kaɗan dayayi saboda yawan damuwa. Harta abinci jefi jefi yake ci.

Turaren Oud ya fashe jikinsa dashi, saiya ɗauki comb ya tsafe ƙaramin afro ɗinda ya tara tareda sajen fuskan sa. Haka gashin ya kwanta yayi lub lub abinsa.

Wani agogo na mata ya ɗauko ya saka a aljihun sa, duk inda zaije kamar tsafi saiya tafi da ita. Shi ke kawo mashi sukuni cikin ransa.

Masjid ya wuce domin yayi sallah magrib, anan ya zauna yana tilawa. Bai bari ba har saida yayi Isha. Yafi mashi zaman kadaici da zaiyi. Daga nan ya wuce gidan su Faash domin ya gaida iyayen sa. Mommy taji daɗin ganinsa sosai.

Tanada bala'in fara'a ga sanin ya kamata, itama ta lura da ramar dayayi. Haka tasa aka kawo mashi abinci kala kala gabansa domin yaci. Shidai baici ba kuma baice komai ba. Dama yazo neman albarkan iyaye ne domin gobe zai je Abuja a fara training.

"Son, lafiya dai koh?" tace masa. Tana kiransa son saboda ya sake jiki da ita. Murmushi yayi mata mai bayyana hakora.

"Yunwa zai kashe ku na lura. Nifa banga amfanin zaman ku a chan gidan ba" tace tana taɓe baki. Daidai lokacin Faash ya shigo.

"Mommy we're boys, that's why." sam Faash baya san yin hausa. Zaka mashi Hausa sau dubu ya mayar maka da turanci. Dama dama ya kanyi fillanci da babansa.

"Koko na rinka aiko maku da abinci ne? jibe Mahfooz duk ya faɗa"

Kallon Mahfooz Faash yayi saiya taɓe baki, "Mommy kila ya faɗa maki abinda ke damunsa amma nikam bansan me ke damunsa ba,"

"Son, faɗa min sunan ta mukai goro," ta faɗa tana murmushi.

Da sauri Mahfooz ya ɗago kai ya kalle Faash, ƙasa ƙasa yayi mashi magana, "Is it obvious?" wanda Mommy bata ji ba saboda wayanta ya soma ruri kuma ga TV yana aikinsa.

Kanne mashi ido Faash yayi, "No, amma yanzu na gane me ke damunka,"

Basu sake magana ba, sunci abinci sai suka tafi. Dama kowa da motansa. Faash ya tafi harkan sa wajen yan matan sa sai Mahfooz ya wuce gida. Ada tare zasu amma yau baida niyya yinma yarinya karya ko fara'a.

Gida ya koma, a falo ya zauna ya kunna TV. Sai a lokacin yaga channels sun ɗauke ashe subscription ya kare na dish. Wayansa ya ɗauko ya biya ta online, anan sai gashi sun soma dawowa. Super sport yasa yana kallo. Ana Highlight lokacin. Kallo yakeyi amma baya ganewa.

Wayarsa ya soma ruri, "Rumasa'u Kaduna" ya gani baro baro saman screen ɗin. Taɓe baki yayi. Zai amsata amma ba yauba. Wai ɗazu har tana zare mashi ido kamar akuyar data lashe gishiri. Kallon TV ya cigaba abinsa har wayan ya tsinke.

Nan yayi tsaki saiya ɗauki mukullin motarsa, tuƙawa yayi bai tsaya ko'ina ba sai Abdallah Specialist. Nan yayi parking gaban wurin kaɗan yana kallo. Baisan san me ya kawo shiba. Amma tabbas yasan nanne yakeso ya kasance.

Ya fito gaban motansa ya jingina, kallon gate ɗin yakeyi. Baya tsammanin zaiga abinda yakeso ya gani. Saidai nanne mafi kusanci da muradin sa.

Ita kuma yau ta ƙasa zuwa gida. Bataso taje tayita tunani. Gwara ta zauna tana yawo ɗaki ɗaki tana duba patients yafi mata. Da Dr Chinedu zai tafi gida ya miƙa mata roba biyu na ARV domin amfanin ta. Baiso ta takura kuma sannan koya ƙare mata. Gode masa tayi saboda tamkar uba yake wajenta.

Karfe tara saiga Dr Abdallah ya kira wayanta, murmushi tayi saboda Babanta shine abin alfaharin ta. Sallama tayi sanda ta kara a kunnen ta.

"Diyar Dr Abdallah, yau bazaki dawo bane. Kinsan kinada patient koh? dan ban gama warwarewa ba wallahi." yace cikin fara'a.

Murmushi mai haɗe da dariya tayi, tun yau sai yanzu ta dara ta samu nishaɗi. "Afuwan Baba gani nan,"

"Alhamdulillahi, dama Ummanki take kewar ki wai aikin nan yana takura mata. Amma bata san mu Dr's haka muke ba," yace yana dariya tareda kallon Hajia Binti dake gefensa.

"Okay, kace ma Umma nama tashi yanzu zan dawo,"

Bayan ta ajiye wayar labcoat ɗinta ta cire ta rataye a hanger. Saita saka ARV ɗin da Dr Chinedu ya bata cikin jakanta. Jakar kalar mai kama da school bag ne wanda ake goya wa. Saidai wannan yanada kwalliya da kuma duwatsu na gayu maƙale jikinsa.

Sannu a hankali take tafiya, dataje wajen motan ta sai taga tayi paci. Mamaki takeyi dan bata tuna ta taka ƙusa ba. Gashi dare yayi mutane basu nan sai kaɗan balle tace su canza mata taya na cikin boot ɗinta. Anan ta yanke shawara domin ta tafi a napep sai gobe ta gyara, dama motan yana mata wani ƙaramin ƙara sai makanike yazo ya tafi dashi.

Tafe take rataye da jakarta a baya, yana daga inda yake yana hanganta. Wani sanyi yaji wanda ya daɗe bai samu irinsa ba. Tabbas wannan ne abinda yake buƙata. Yana ganin yadda take kokarin tare napep amma basu tsayawa. Mamaki yakeyi yadda takai dare haka bata tafi ba. Dama baiyi tsammanin ganinta yanzu ba.

Haɗa ido sukayi suna kallon kallo. Ba zatace tsanar sa ke dawainiya da ita ba. Saboda ita anan aka cuce ta, batada riƙo duk girman laifin mutum. Hakanan da kanta zata yafe. Bata ce ta yafe ma Mahfooz ba, baza ma ta iya yafe mashi ba. Ya cuce ta fanni da bazata iya mancewa ba. Saninsa datayi bashida amfani cikin rayuwar ta.

Murmushi ya tsinci kansa yanayi, tabbas yaji daɗin ganinta koda batayi mashi magana ba. Koda ta tsane shi a rayuwarta. Tabbas yasan baida kunya idan ma yace zai nufeta da batunsa. Bama zata taɓa amincewa dashi ba bayan ya zalunce ta. Zuciyar sa ta soma tafasa tana mashi ɗaci. Anan ya sake ganin wautan sa. Sai kace mai ciwon hauka aida ya ceceta. Gashi yanzu ita kaɗai ce zata iya rayar dashi.

Wani baƙar mota ne tazo da sauri ta nufeta. Anan wani ya fito ya soma fincikar ta yana kokarin janta ciki. Itama damben ta soma yi. Mahfooz kamar wanda aka kafa a wajen bai iya yin komai ba. Kallon inda Mahfooz yake tayi, ita bata san me yakeyi a wajen ba. Tasan ya tsaneta. Tasan bazai taɓa taimaka mata ba. Kuma tabbas tasan bashida ɗigon imani amma bazata karaya ba.

"Ka taimake ni Mahfooz," ta faɗa tana kuka. Tana kallonsa yadda ya tsaya baiyi komai ba har yan kidnappers suka ingiza ta cikin motan suka wuce.

Wannan kenan!

#Naseera
#RumaSau
#Mahfooz
#DiyarDrAbdallah

Ainakatiti

Na lura baku sona yan wattpad ɗinnan, kodan voting dinnan bakuyi balle naci arzikin comment. Ba damuwa.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top