Seventeen

Ina wanda suka ce bazasu ƙara karanta ABDULQADIR ba? Kada Allah ya bako ikon yi. Sai meye idan baku karanta ba? Koko kuna tunanin cewa dan baku karanta ba zai cire mata wani abu daga cikin ruhinta? Koko kuna tunanin karatun ku shine iskar datake shaƙa kullum kuma rashin karatun ku zai ɗauke mata numfashi. Tun kafin a haifa mai sabulu balbela da farinta take. Dan rashin mutunci batayi maku komai ba sai ku bita private kuna zagin ta domin batayi update ba, wasu hakiman harda kiranta a waya suna zagi. Sannun ku Quraishawa dole ayi yadda kuke so. Her life revolves around you ai. Ita bazata yi ciwo ba, bazata je nema ba, bazata yi wasu hidama ba. Kawai zata zauna tayita feso maku da labari 24/7 idan kuma batayi ba sai ku soma tsine mata da makusanta ta. Ke idan kinada sabgar gabanki zaki ajiye karatu kije kiyi har wata sa'in fiye da sati guda, idan kin dawo kizo group kina cewa a tura maki wasu episodes saboda sanda aka tura you were busy ko bakida Lafiya. Amma writer bata isa tace tanada uzuri ba. Kuma the post she made on Wattpad SHE IS NOT SORRY. Wanda bazai iya jira ba sai yayi marabus da takardar yaje chan ya nema wanda aka gama ya karanta. Sannan kuma wasu na alakanta ta da wasu kungiya ana cewa bai kamata Lubna tayi update ɗin ba saboda ansan yan kungiyar basa haka, ana tunanin tanada hankali blah blah blah. Well bata cikin kowane kungiya, so apparently idan zaki zageta ki fito baro baro ki zageta as Lubna Sufyan. Da masu kuma cewa she's a writer bai kamata tayi post ɗin ba, zama da mutane saida haƙuri. You people are very selfish and heartless, watau writer ce kawai zatayi haƙuri. Ke da kike karatu ba zakiyi haƙuri ba? Kema ai alaƙa da mutane kike yi, so why won't you apply your theory on yourself? Wallahi Allah saiya saka mata, da masu zaginta, da masu mata sharri Allah saiya saka mata. Kunga shurun nan datayi maku kuna tunanin kun zaga banza? Wallahi zaku gani a gaba. Baku san uzurin ta ba, baku san ko tanada lafiya ba. Amma ku kawai a maku update, na tabbata ko gawarta kuka gani zaku riƙe kuce saiya karasa maku labari.

And please wanda zasu ce dama Ainau batada mutunci we expected more from her, don't worry I don't even care, never have and never will. So kwantar da hankalin ku. Kuma Lubna bazata yi rubutu ba sai randa ta samu ikon yi, mu makusanta ta munsan zafinta. And those clout chasers su cigaba da amfani da sunanta Allah ya basu sa'a. Wanda yaji haushin abinda nace ya hau dutsen kufena ya faɗo. Mind you, come at me and I'll drag your ancestors through hot coal and steel.

***

Haka Inna tayita kallon Rumasa'u tana mamaki, ai talauci ba hauka bane. Idan bata kunyar hulɗa dasu bai kamata ta ce sun mutu ba. Sai tayi marabus dasu kamar yadda tayi tun asali.

“Inna wallahi ba abinda kike tsammani bane,” tace idanta fal da hawaye. Itama ko ba'a faɗa mata ba tasan bata kyauta ba. Amma idan batayi haka ba Latisha bazata gane ita ba babban yarinya bace kuma zata yanke ta'ammali da ita. Inna bata ce komai ba, dama mayafi zata ɗauka domin ta kai markade, haka taje ta dawo.

Kallon Rumasa'u takeyi, irin kallon ƙurilla. Bata ce mata komai ba amma Rumasa'u ta gwammace datayi mata maganar data saba. Shirun yana takura mata, gaba daya ilahirin jikinta yayi sanyi duk bata jin daɗin.

Data fita zata je banɗaki, sai Inna tayi maza ta share hawayen dayake malalo mata. Tunda Rumasa'u take bata taɓa damuwa da abinda take saka iyayenta ba. Babu ruwanta, ita dai su biya mata buƙuta. Amma ta lura soyayyar ta yana cikin ran Inna. Koda take gidansu Rahina wata rana suna dawowa daga gantali tareda yan kungiyar One Love, sai taga Inna a layin. Tasan kuma tazo taji lafiyar ta ne, dayake direban yayi mankas. Saura kaɗan ya kwashe Inna da mota. Da kyar tasha daga kaidin sa.

“Ke tsohuwa dalla matsa,” ya daka mata tsawa mai firgitarwa. Yanda ta firgice abin dariya ne. Haka su Kankana suka bushe da dariya. Bata nuna masu cewa mahaifiyar ta bane kafin su raina mata wayo. Balle kayan jikinta ya koɗe duk yasha omo.

Ita Inna Nafisa tunani takeyi akan Rumasa'u, halinta sak yana kamada na yar uwanta Fauziyya. Kamar an tsaga kara. Mugun halinsu na kyaman talaka iri ɗaya, da Rumasa'u da Fauziyya batasan waye yake da dama daman zama ba.

Gwara Fauziyya tanada abin hannunta, ita kuma Rumasa'u bata dashi kuma bata ajiye ba. Yasa take bala'in tausayin ta cikin yaranta. Tana tsoron duk inda taje za'a koreta. Saboda mugun halinta yafi hasken rana bayyana. Gashi tun ba'a je ko ina ba har Rahina ta koreta. Yanzu idan ta aure tayi haka za'a dawo mata da ita kafin wata daya kenan.

Mallam kuma bayan assembly gidansu Rahina yaje, cikin fara'a Rahina ta tarbe shi harda karin kumallo ta kawo mashi. Ana zaune a falo ga Baban Rahina da mamanta sai Rahina tana gefe.

Kunyar duniya ke dawainiya dashi, mutanen da suka taimaka masa shine Rumasa'u ta tozarta. Ko baiji komai ba yasan ita ce da laifi. Aiba a banza yara ke ce mata Rumasa'u annoba ba. Nisa yayi yana ajiyar zuciya, saiya soma magana cikin ƙaramin murya.

“Dan Allah Chairman kayi haƙuri, ni ba butulu bane. Kuma bazan ciza yatsan dayake ciyar dani ba. Duk abinda Rumasa'u tayi na ɗauki laifin, kuyi haƙuri saboda nasan tayi babban kuskure ne.”

“Yanzun nan Maman su take min bayani,” Chairman ya amsa. Kallon Rahina Mallam yayi wanda ta kasa haɗa ido dashi.

“Ni wallahi ban ma san meya faru ba, kawai naga ta dawo ne, Menene ya faru?” ya kalle Rahina domin ta gaya mashi.

Anan ta zauna ta fayyace mashi komai, gumi ya soma saboda takaici. Rumasa'u kwata kwata batada mutunci, ya rasa meke damunta. Ya za'a yi tana zaune gidan mutane tayi ma yarsu duka? A ina aka taɓa haka? Ko a garin mahaukata yasan ba zasuyi haka ba.

Haƙuri ya shiga bama Rahina inda Chairman ya dakatar dashi, nan yace ai ƙawaye suna faɗa kuma a shirya. Sai yayi ma Rahina faɗa akan korarta datayi. Nan ya gargaɗeta akan ba'a haka. Alamomin munafiki ne, idan yayi alkawari ya saba. Tunda tace ma Rumasa'u zata zauna da ita bai kamata ta koreta ba duk fadan su.

Mallam yace zai bada kuɗin wayan da dubu darin, shima Chairman ya hana. Anan Mallam yayi godiya ya tafi. Yace kuma gobe zai tasa ƙeyar Rumasa'u suzo su basu haƙuri. Shima ance ya barshi amma yace sai yayi. Har gate Chairman ya raka shi, dama suna abota kaɗan sanda suke layinsu idan sun haɗu masallaci.

Wajen yamma Latisha tayita saka hotuna kala kala na ƴan gayu ana bidiri. Duk Rumasa'u taji babu daɗi, yanzu da da ita za'a je. Anan suna cikin zantawa sai Latisha ta tambaye Kankana yanzu ya zatayi da batun kuɗi. Tunda kawunta azzalumi ya kwace mata gadon ta. Ajiyar zuciya Rumasa'u tayi, bata san me zata ce ba domin ita dama yanzu Latisha zatayi mata hidima. Itace zatayi mata uwa zatayi mata uba. Tare zasu rinka facaka da kuɗin Daddy.

Latisha tace mata zata bata wani sarƙan gwal idan ta dawo daga Maldives inda baby shower ɗin yake wakana. Saboda ita sam bata san gwal, sai yayita wal wal yana ƙyalli ga ɗaukar ido. Tafi san su crystals da Ruby. Balle kuma sarƙan yanada bala'in nauyi. Idan ta saka kuma zata duƙa ƙasa. Rinjaya yakeyi kamar zai finciko ta ya zubar saboda girman sa da nauyi.

Kamar yadda Latisha take tsammani, haka Rumasa'u tayita jin daɗi tana cewa tana bala'in san gwal saboda shine cikar mace. Canza maganar Latisha tayi zuwa wani daban. Saida tayi gyaran murya tareda karkata baki.

“Besty, idan kinaso zan iya samo maki hanyar da zaki bi domin ki samu naki,”

Mamaki Rumasa'u tayi sosai, ita dai batayi karatu ba balle Latisha ta samo mata aiki a daya daga cikin kamfani dubun da Daddyn ta ya mallaka, cikin garin Kaduna da Nigeria baki ɗaya. Jikinta yayi sanyi, kawai bata ji daɗin maganar ba. Balle dama ita bataso ta nema na kanta. Tafi so aje a samo a bata.

“A ina kenan?" tace a sanyaye tareda haɗiye miyau mai zafi.

“Noo Besty, karki ɗaga hankalin ki,” tace cikin shagwaba, “Ba wani abu bane da zai fi karfin ki, kawai dai ki saka a ranki zakiyi komai domin ki samu kuɗin ki,” ta jaddada mata.

“Komai kuma?” Kankana tace tsoro fal ranta. Dariya Latisha cikin izgili, “Toh ai nothing good comes easy, nema ne ai, kuma dole yanada challenges ɗinsa, balle wannan yi wa kai ne,”

“Amma ai akwai abinda bai dace ba,” Tunda Rumasa'u take bata taɓa faɗin abin arziki ba sai yanzu. Mamaki takeyi anya Latisha abinda take gaya mata gaskiya ne. Koko dai yar yankan kai ne, saboda sune suke ƙeƙeshe ido suyita tsiya. Gabanta sai faɗi yakeyi, idan ka matsa kusa da kirjinta ta zaka ji bugun sa zaiyi kusan toshe maka kunne.

“Karki damu Besty, kinada kyau sosai basai an faɗa ba. Toh wannan kawai jari ne mai tsoka. Nasan wasu mutane za zan hadaki dasu, idan kika kwantar da hankali kikayi masu biyayya zasu samu duniya sosai...”

“Wani irin mutane?” Kankana ta tsaida ta.

Ajiyar zuciya Latisha tayi, data haɗu da Kankana tana tunanin ta waye ta san bariki. Ashe ma baƙuwa ce a harkan. Duk tsammanin ta tana tunani bazata sha wahala akan Kankana ba, domin jiya ta sakata a status duk hajiyoyin datake harka dasu suka soma nuna maitan su a fili wai suna san Rumasa'u. A ina Latisha ta samo yar shila. Kuma sukayi mata alƙawari zasu bata tukwici idan ta haɗasu da ita.

“Akwai wasu matan manya haka, sunada kirki sosai. Basuda maƙo komai kike so zasuyi maki. Kawai suna so ku ƙulla abota ne, kingane ai?”

Rumasa'u bata gane kalar abotar ba, kawai tace dai eh ne saboda a haɗa su. Indai abota ne irin wanda takeyi da Rahina da sauran ƙawayenta ai tana maraba dashi. Kawai ƙawance da matan manya suyita mata bidiri da kuɗi. Ai shine addu'an da takeyi tun tana karama, Allah ya bata arziki tana kan gadon ta.

Anan aka haɗata da Hajia Salima, tsohuwar kwamishina ce yanzu kuma babban mai bama gwamna shawara akan kiwon lafiya. Suna gaisawa sai tace ma Rumasa'u ta aika mata da account number ɗinta, da sauri tayi tana rawar jiki. Aikam nan take alert ɗin dubu ɗari ya shiga wayanta. Cewa tayi idan batada passport taje tayi, nanda sati biyu zata ɗauki hutu domin suje dubai su biyu su sha iska. Kuma tace zata rinƙa samun haka idan zatayi mata biyayya sosai.

Wannan kenan!

#Naseera
#Rumasa'u
#Mahfooz
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilicious
#FullyDimplated

Ainakatiti ✨

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top