Seven - Mahfooz II


Wannan shafin na sadaukar dashi ne Zuwa ga Zanira our able Admin na TASKAR AINAU DIMPLES thank you for your input. Allah ya bar mana ke Amin.

Hankalin Fauziyya fari tas sanda ta koma gida. Ta amso kayanta taji daɗi. Zuwa tayi durowa domin ta ajiye su inda suke. Anan tasha madarar mamaki, lokacin ta lura cewa Alhaji Sani ya haɗa da Atampha dasu Leshi. Cizan yatsa ta soma yi. Baƙin cikin yazo mata sabo fil, har wani ɗaci takeji.

Ita har tafi so yaran Auta su saka kaya mai tsada akan ita ta saka. Abin yayi mata mugun ciwo. Anan ta soma ganin dishi dishi. Jiri ya soma ɗibanta saboda tsabaragen baƙin ciki. Nan take ƙafanta ya kasa ɗaukanta. Haka tayita baya baya harta kai kan gado ta zauna tana numfashi sama sama.

Anan ta tuna tana bala'in jin yunwa, ko karyawa batayi ba ta wuce kaduna saboda bala'i yana cinta. A hanya ne tasha roban ruwa sai kuma biredi, sai kuma ta wajen hunkuyi taga Gauda ta siya taci.

"Bilki ! Bilki!! Bilki!!!" tayita kwaɗa ma Bilkisu kira domin tazo ta kawo mata abinci kafin yunwa ya kasheta. Bilkisu kuma ta tafi kasuwa cefane bata nan. Yagana ne ɗayan mai aikinta wanda tafi manyanta tazo da sauri.

"Salamu Alaikum Hajia, Bilki taje siyo cefane." tace a ladabce tareda ɗukawa. Da kyar Fauziyya ta iya kallonta saboda yanda duk wani kasala ya sauko mata farad ɗaya.

"Kawo min abinci maza... Kuma ki kawo min kayan shayi," tace. Har Yagana ta kai kofa sai Fauziyya ta sake magana, "Idan kin dawo kizo kije chemist kice masu su baki maganin zazzabi," da kai Yagana ta amsa sai ta tafi.

Fauziyya tana jin zazzabi jikinta, kuma tasan  bakomai bane illa takaicin Auta.

"Ina Auta ina ɗaura super?" ta tambaye kanta a fili. "Duk laifin Alhaji ne, kuma zan nuna masa fushi na ƙarara idan ya dawo."

Tashin hankali sosai ta shiga, domin jikinta har ɓari yakeyi. Ga zufa sai keto mata yakeyi. Wani yaga yanayin data shiga farad ɗaya zaiyi tunanin an aiko mata da saƙon mutuwa ne. Koda kuwa Auta ce ta rasu bazata shiga ruɗani haka ba. Yanda jikinta yake mata kamar naƙuɗa yana shirin kamata a cikin wata bakwai.

Taso ta sake komawa Kaduna ta kwaso kayan, Auta bata cancanci saka suturar ba. Ina ma laifi Atampha wanke kuɗin ka. Balle yadda taga ɗakin Auta a sukurkuce kamar dambu. Ko ledan ɗakinta ya farfarke. Sannan labulen ta tun wanda tayi aure dashi ne. Balle dama ba wani aminci gareshi ba.

Duk dangi ana ganin yadda Fauziyya keda wadata ita zata fitar da Auta kunya sanda ta tashi aure. Amma kam ta basu kunya. Maman su lokacin tanada rai amma ta tsufa sosai. Gashi ciwon ƙafa ya sakata a gaba. Mika'il ƙanin Fauziyya yayan Auta yace gwara a maida maman Kano domin zata fi samun kulawa.

Fafur Fauziyya taƙi yarda wai itama ta gaji ciwon ƙafan, tanaji da kanta bazata iya hidimar maman suba. Haka babu daɗi ya ɗauke Maman a inda ta zauna dashi harta rasu.

Civil servant ne wanda ba'a rasa mashi transfer gari gari, yanzu haka yabar arewa. A lokacin bikin autan ba yanda Maman Fauziyya batayi aike ba domin ta bada gudunmawa. Abin yayi ma Fauziyya ciwo, a ganinta ai raini ne. Wai ace ana ta binta kamar bashi. Itama ai tanada hidimar gabanta amma anki mata uzuri.

Abinda ke haɗa ta da talaka kenan, watau rashin haƙuri. Shi baida shi yayita saka maka ido a naka. Idan ka hanashi yaji haushin ka. Amma ita idan magana ne ko ra'ayi na talaka bata ɗauka. Baida amfani a rayuwarta.

Alhaji Sani ya tura maƙudan kuɗi saboda ayi ma Auta hidima, da kuma Atampha na fitar biki da kuma gara, duka Fauziyya ta cinye ta hana, da kyar ta iya basu dubu shida lokacin, wai ayi haƙuri baida yawa harkoki sunyi mata yawa. Mamanta saida hawaye ya zubu mata. Da ace tana haihuwa a asibiti ko wajen anguwan zoma toh tasan tabbas Fauziyya ba nata ba.

Amma haihuwar Fauziyya yazo mata da sauki, saida tayi sallar asr tukun ta fara nakuɗa. Kafin magrib ta haifeta. Anan ne ta kwaɗa ma sauran matan gidan kira su suzo suga jaririya. Mamakin inda Fauziyya ta gada baƙin hali takeyi saboda wannan ba daga ita bane.

Yagana ta kawo ma Fauziyya abinci, ita dama ƙa'idar sai taci kaza guda ɗaya nan take. Tanada bala'in ci kamar rumbu. Sai kuma ta haɗa kofin shayi. A jug take haɗawa saboda kofi yayi mata kaɗan. Saita juye gwangwanin madara ɗaya da rabi.

Shima likita yace ta rage kokuma wannan cikin dake jikinta zai zama ajalin ta. Amma bata wani rage ba. Yau taci gobe ta bari, sannan kuma daga gwangwani biyu zuwa ɗaya da rabi.

Gyatsa ta kwarara bayan ta gama ci, sai anan komai ya soma tafiya mata daidai. Da ta dauki alwashin cewa zata Kaduna gobe domin ta amso kayanta. Sai ta tuna hatsarin data gani har guda uku hanya. Suma da kyar suka sha saboda wani triller ya dumfaresu. Shima cikin tsoro ta fara kiran "Annabi" tana rabka ihu.

Girgiza kai ta rinka yi na cikin takaici tsaboda Auta ta sha ta misilla. Amma gobe rana ne, tabbas zasu haɗu wata rana ko a wani sha'ani na ƴan uwa. Anan zata yaga mata rigar mutunci. Musamman idan taga Auta sanye da Super ɗin. Zata gayama kowa kayanta ne tazo har Kano ta sace.

Rayuwar Mahfooz cikin yan kwanakin nan ya zama abin kwatance saboda rashin Alhaji Sani. Fauziyya ta nuna masa cewa gwara kiɗa da karatu. Da farko ta hanashi zuwa boko. Amma saita lura cewa hutu take bashi. Daga nan idan Driver zai kaisu sai tace ya dakata zata aike shi. Bayan minti biyar saita ce ya kama hanya.

Haka a ƙafa zai tafi, idan yakai makaranta a hukunta shi saboda latti. Dawowa babu yadda zatayi dole direba ya ɗauko su duka.

Randa Alhaji Sani ya dawo haka tasa Mahfooz yayi wanka ya saka kaya mai kyau. Batasan Alhaji ya lura da wani abu. Ita tana jin daɗin gallaza ma Mahfooz takeyi, abin ba ƙaramin nishaɗi yake bata ba. Musamman yadda Mahfooz ke susucewa idan ya ganta.

Kaya masu kyau Alhaji Sani ya siyan ma Fauziyya na haihuwa. Ita kanta tafi sansu fiye da wanda ta ɗauka a Kwari. Designers ne komai. Sannan ya siyan ma sauran yaransa da Mahfooz kaya suma daidai gwargwado.

Da yaje ɗakinsa saiya sha mamakin ganin kayan daya bama Auta a durowa. Kiran Fauziyya yayi yana kallonta domin tayi mashi bayani. Inda inda ta rinka yi tana borin kunya. Anan ya soma mata masifa akan abinda tayi.

"Yar uwar ki kika bi har Kaduna akan abinda kika fi karfi? Kinada Imani kuwa?"

Harara ta soma watsa mashi, "Toh ka kafurta ni akan Auta. Kasani ni ce matar ka. Kuma ni ce hakkina  yake kanka ba Auta ba,"

"Ki rinka jin tsoron Allah Fauziyya, kisan cewa zumunci ba abin wasa bane. Shawara nake baki."

Fita tayi tabarsa wajen, takaicin duniya sai dawainiya dashi yakeyi. Gashi yanzu yana bala'in kunyar Auta. Da wani ido zai kalleta bayan wannan mugun ƙaranci da tazorci.

Washe gari bayan Asuba ya kwashe kayan daya siya daga China tas ya saka a bayan motansa. Saiya kira direba suka wuce Kaduna. Zai je ya bata haƙuri sannan kuma ya mayar mata da kayan da suka fi da. Shi a rayuwarsa baya so yaga ana wulakanta talaka.

Da an wulakanta shi shima ai bazai zama abinda ya zama ba. Amma yaci sa'a da mutanen arziki marasa ƙyashi. Suka koya mashi sana'a sannan kuma daga baya suka bashi rancen jari har ya biyasu.

Talauci kaddara ne, kuma Allah ne mai azurtawa. Shi yake bama wanda yake so ya kuma hana wanda ya so. Mai kuɗi ba sallah yafi talaka iyawa ba da Allah ya bashi arziki, talaka kuma ba laifi yayi ba ya tsinci kansa a haka. Kowa da nashi jarabawan. Talaka akan talaucin sa, mai kuɗi da kuma arzikin sa.

Wajen tara na safe suka isa. Lokacin mijin Auta ya tafi aiki. Dama malamin makaranta ne. Iso Alhaji Sani yasa akayi mashi da Auta, tayi mamakin ganinsa a gidan su. Da fara'a ta ce su shiga cikin falon. Daya ga yadda falon yake duk sai yaji babu daɗi.

Inda kara Auta kamar ƴarsa ce, kaɗan ne bazai haife ta ba. Saboda baiyi auren wuri ba.

"Ina mijin naki?" Alhaji Sani yace.

A ladabce ta amsa mashi, lokacin tana ajiye mashi kofin ruwa a randa wanda ta ɗebo, "Ya tafi aiki,"

"Allah sarki, na same ku lafiya? Dama naso na gansa ne."

"Aikam sai sha biyun rana yake dawowa idan an tashi,"

Duba rolex ɗinda ke hannunsa yayi, sai yaga karfe tara da minti arba'in da biyar, anan ya ɗaga kai ya kalleta. "Ina ne makaranta bari naje inaso muyi wata magana."

"LEA Badarawa ne, akan Titi yake. Idan kaje zaka gansa," tace mashi.

Shanye ruwan yayi tas, bai nuna yana kyamar suba. Saiya fita ya tafi wajen motansa. Anan shida direba suka fito da kayan suka kai mata. Bata ce komai illa hawayen murna. Alhaji Sani mutum ne. Fatan alheri take ta binsa dashi.

Da yaje inda mijin Auta yake nan suka gaisa, nan ya tambaye shi inda mai gidansu yake. Shi ce masa yayi yanaso ya biya masu haya akan gaba kada azo a tozarta su. Mallam bai kawo komai ransa ba, ya bada tsaron ajinsa suka tafi.

Mai gidan wani dattijo ne, duka hayan dayake bayarwa nasu Auta shine ƙarami duk ya bige yayi manyan flat. Wannan ne kwanta fege ya rage. Ɗayan kwatan shima ya siyar.

Wanda suke haya a gidan tareda su Auta watan su Uku kenan da tashi saboda sunyi gidan kansu. Alhaji Sani yace mai gidan yayi mashi cinikin gidan domin zai siya. Dama hayar su Auta dan cikin cokali ne. Anan ya faɗa kuɗi sai Alhaji Sani yace ya rage.

Haka suka sasanta, da aka zo rubuta sunan gida sai yace a saka sunan Malam. Har ƙasa Mallam yayi yana godiya. Gani yakeyi kamar a mafarki. Wai yau shine yakeda gidan kansa.

Su ukun suka duguma banki inda Alhaji Sani yayi mashi transfer tunda lokacin babu wayar hannu. Saiya bashi dubu ashirin domin yayi filasta da kuma fenti kafin Auta ta haihu.

Kuma yace idan sunada matsala kota wasika ne su aika mashi. Da yardan Allah idan bai fi karfinsa ba zaiyi masu.

Alhaji Sani ba anan ya tsaya ba, Zaria ya wuce wajen danginsa dake Gidan Gwaiba. Nan yayita masu sha tara da arziki. Dama basa zuwa gidansa saboda Fauziyya.

Kowa yazo da matsalolinsa haka yayita kokarin daidai gwargwado yana biyan masu. Masu neman admission a soja ko jami'a suma ya amsa takardun su. Addu'a ya sha bila adadin sannan ya tafi.

Koda ya koma gidan kwashe kayansa tas yayi ya koma ɗakin Amina. Ya daina ma Fauziyya magana ya daina cin abincin ta. Saidai ya shiga yaga yaransa harda Mahfooz, anan yaga yanata ramewa. Yayi mashi tambayar duniya sai yace babu komai.

Haka rayuwa ya cigaba da kasance ma Fauziyya a gidan ta. Abu ɗaya tasan zai faru da zata karkato hankali Alhaji Sani wajenta. Idan ta haifan mashi ɗa namiji dole ya sauya.

A kwana a tashi...

Fauziyya ta haɗa kayanta tas zata bikin kawarta a Abuja, ta gayama Alhaji Sani amma ko tanka ta baiyi ba. Ya dai bata dubu ashirin gudunmawa. Shima Zanira ya bama envelope. Shifa yana san matarsa sosai, kawai halinta ne yake cin masa tuwo a ƙwarya. Idan tayi abu kamar mai rafanai. Yana so dan nisanta tada yayi yasa ta gane ta canza su cigaba da zaman su.

Fauziyya tana chan biki tana shagali sai nakuda yazo mata. Anan aka kaita asibiti inda ta haifa yaronta namiji. Murna bayan mitsaltuwa wajen Alhaji Sani, bayan yara shida Fauziyya ɗinsa abin begensa ta haifan mashi yaro namiji.

Gagarumin liyafa yayi ma abokan sa na kantin kwari. Sannan kuma yaron yaci suna Al-amin amintacce.

Haka rayuwa ya cigaba da tafiya gidan Alhaji Sani, Mahfooz dai babu abinda ya canza wajensa. Koda baije makaranta ba Zanira ta kan zo ta koya masa tunda ajinsu ɗaya. Abin yana masa daɗi. A haka suka zana common entrance na shiga secondary school.

Mahfooz bai wani ci sosai ba, pass ya samu. Zanira ce ta zama zakaran gwajin dafi har aka bata kyauta. Fauziyya yanzu kusan kowane al-amuranta yana kan yaronta. Bata san abinda zai takura mashi.

Da Al-amin zata mallake duka gadon Alhaji randa mutuwa zatayi gaba dashi. Bata farga ba saiga Mahfooz yana secondary. A lokacin Alhaji ya gama ginin sa har Mahfooz ya samu ɗakin sa yana zaune ciki.

Lokacin Mahfooz yana ss1 shekara sha biyar, Fauziyya taje ɗauko birth certificate ɗin Al-amin a cikin document ɗin Alhaji Sani. Anan taga takardun shagon sa, sai taga ya siyan ma Mahfooz shago daya wanda sunan shi ke ciki.

Mayarwa tayi kamar komai bai faru ba, abinda ta sani shine zaman Mahfooz ya ƙare a gidan. Taso ta cutar da Mahfooz ta fannin gobara amma kuma ta tuna cewa Al-amin shima anan yake kwana. Gashi kuma Zanira in dai Mahfooz baya kasuwa yana gida toh tana tareda shi.

Shi bamai magana bane, zaka iya ɗirga sau nawa ya furta abu a rana. Ko hirar su da Zanira itace take yawan faɗa. Shi dai murmushi kawai yakeyi yana "Uhm" ko "A'a".

Shekara ɗaya da rabi ya bata, amma sun shaku kamar yan biyu. Zanira itace kaɗai cikin yaran da Fauziyya takeda shi wanda yake so suma suke sanshi. Duk sauran halinsu ɗaya da Fauziyya. Basa ko ga maciji. Balle yanzu Alhaji Sani ya lura da kiyayan Mahfooz wajen Fauziyya.

Guba Fauziyya tasamu, inda aka ce mata idan tayi mashi allura dashi shikenan shida duniya sunyi bankwana. Murna fal ranta saboda zata fidda shi gidanta. Ta daɗe tana begen ranar barin Mahfooz. Dabarar bai faɗo mata bane tuntuni data yarda kwallon mangwaro ta huta da quda.

Abu biyu ne yanzu matsalar ta, ta inda zata bashi ba'a ganeta ba sannan kuma lokacin da yaranta basa nan. Dabara ya faɗo mata lokacin, dama Al-amin ya buƙaci yanaso yaje ya kwana gidan kawarta Hajia Zainab matar kwamishina. Jikanta Muhsin ajinsu ɗaya da Al-amin.

Anan Fauziyya ta yardan mashi akan yaje. Sauran yanzu ta raba Mahfooz da Zanira. Ita kuma tana yar shekara sha uku da rabi. Amma tasan me take so. San datake mashi bana yan uwantaka bane. Ganinsa takeyi a matsayin ɗa namiji wanda take gani nan gaba zata iya aure.

"We shouldn't be talking about this," Mahfooz yace yana kurban shayin data kawo mashi.

"Meyasa, idan bakaso nane kayi min bayani. Idan akwai wanda kake so ne shima ka faɗa. Amma bazan bar maganar nan ba."

Ƙaramin dariya yayi yana kallonta, idan yace bai taɓa tunanin ta ba ya yaudara kansa. Amma kuma yasan ko zai mutu Fauziyya bazata taɓa yarda ya aura yarta ba. Yasa yaja mutuncin sa.

" Toh naji, kinsan menene so? "

" Eh"

"shine mene?"

"Shine san dan uwanka fiye da yanda kake san kanka. Shine saka wanda kake so a addu'a. Idan wanda kake so yana murmushi zakaji dadi, idan wani abu yana damunsa kaima zaka shiga damuwa...."

Hannu ya ɗaga mata domin tayi mashi shiru, ya gaji sosai saboda sunyi chemistry practical za'a fara jarabawa.

"Okay, yar novel... Zamuyi magana gobe... Barci zanyi."

Tashi tayi ta kwashe kwanonin saida ta kai bakin kofa saita juya ta soma kallon sa. Shima tsarguwa yayi ainun.

"Lafiya dai koh?" yace mata. Kaɗa kafaɗa tayi saita fara magana, zakaga tsoro a idanta. "Mahfooz promise me zakayi tunanin abinda nace, kasan cewa nida kai are meant to be. An halicce ni domin ka, I am suppose to take care of you, musamman yanda rayuwar ka yake." hawaye ne ya ciko mata ido fal.

Murmushi yayi, amma bai ce komai ba, jira yayi ta gama share hawayen da suka soma zuban mata. "Ki tafi ɗaki Zanira kafin dake dani mu daku." A tare suka tuntsire da Dariya. Saboda sarai Fauziyya tazo taji abinda suke faɗi har Zanira zata daku.

Sanda Zanira ta shida ɗaki Fauziyya tana kallonta. Murna takeyi daga yau zata rabata da Mahfooz. Shiryawa tayi taje sasan kamar zata wajen Alhaji. Lokacin sha daya ne na dare har Mahfooz ya soma barci.

Ji yayi an shiga ɗakin, duk zaton sa yana ganin cewa Al-amin ne. Bai waiwaya ba bai kuma bude ido ba. Guban na cikin sirinji Fauziyya tasa, batayi wata wata ba ta danna mashi ta jiki. Da karfin tsiya ya juya tareda kai mata hannu wuya ya shaƙe gam. Ita kuma tana kokawan matse alluran cikin jikinsa.

Zafi mara mitsaltuwa yaji nan take kamar ya samu shan inna. Sai ya sake mata wuya hawaye yana malalo mashi. Babu abinda zai iya motsi dashi, yaso yayi mata magana yace ga duniya taje taci amma ya kasa.

Tun yana kallonta har hankalinsa ya gushe ya rufe idansa. Abin yayi ma Fauziyya daɗi, yanzu taga tsiyan shagon da zai mallaka. Dama bataso ta saka mashi a abinci kafin Zanira tayi mistake taci.

Fita tayi tabar sasan baki ɗaya ranar a nata sashen ta kwana. Zanira ce tana barci saita firgita. Haka kurum taji gabanta yana faɗi. Tanaso taga Mahfooz taga yaya yake. Tasan ta barshi lafiya amma tanaso ta sake dubawa.

Hijab ɗinta ne tasa ta nufi sashen su, kofar ɗakinsa a bude ma yake, "Mahfooz ka tashi karatu ne?" ta fada yayinda take shiga.

Abin mamaki ta gani kamar baya motsi. Da sauri ta karasa ta soma jijiga shi. "Please Mahfooz wake up for me," ta faɗa tana kuka saita saka kunnen ta akan ƙirjinsa. Babu bugu ko ɗaya. Nan ta duba pulse ɗin sa na wuya amma babu alamar rai.

Ihu ta rinka kwararawa tana neman agaji, Alhaji ya fito a razane. Anan ya soma duba Mahfooz suka ga baya numfashi.

Tambayan Zanira yayi yanda akayi, shine ta Labarta mashi yadda ta bar Mahfooz lafiya amma tayi mugun mafarki. Anan tazo dubawa ta ganshi a haka.

Amina Itama tazo wajen, sai bayan awa ɗaya saiga Fauziyya. Murna fal ranta amma bata nuna ba. Alhaji Sani har hawaye yayi akan mutuwar. Amina itama kukan takeyi.

Abin tausayi itace Zanira, Gefensa ta zauna tana kuka. "Mahfooz meyasa ka tafi ka barni sanda nafi buƙatar ka. Yanzu ya kake so nayi rayuwa bayan na riga na saba da input ɗinka. Shikenan ka tafi da farin ciki na. Bazan ƙara dariya ba ko yin abinda zai sakani farin ciki.... I refuse to be happy without you..." sai ta fashe da kuka.

Da kyar aka bambamreta daga jikinsa. Haka tayita kuka har safiya inda akayi masa wanka aka sanya masa likkafani tareda masa sallah gawa.

An daura sa akan makara an kai sa makwabcin sa, an tura sa a rami saiya farka. Ashe dogon suma yayi. Yana wasu irritation jikinsa sai ya siya wani anti biotic yanata sha. Sanadin dayasa poison bai kashe shiba. Saiya saka mashi dogon suma.

Shi kuma sanadin daya sa baya kaunar duhu kenan, kafansa ya soma motsi dashi. Anan wanda yake rufe shi da itace ya firgita. Sai kuma Mahfooz ya fara tari kaɗan kaɗan. Nan mutane suke dunguma suka kai masa agaji. Anan suka fito dashi za'a kaishi gida.

Nan zance ya bazu Mahfooz ya dawo daga lahira. Shine wasu suka soma kiran sa Qwaro, wasu kuma suna ce masa Makara. Zanira tana ɗaki tana kuka aka zo mata da zancen Mahfooz ya farka ashe dogon suma ne.

Bakin cikin mara mitsaltuwa wajen Fauziyya, anan Zanira ta ruga da gudu domin taje ta gani. Itama Fauziyya binta tayi domin ta hanata zuwa. Shi kam Mahfooz ya dafa Alhaji Sani da wani abokin sa, da kafansa yake takawa. An bashi ruwa yana sha saidai jikinsa yana mashi bala'in ciwo. Ga kuma fuskan Fauziyya karara dayake tunawa.

Yanzu baisan irin zaman da zasu yi ba, yasan dai cewa dole ta sake maimaitawa. Anan ya yanke shawarar gwara ya tafi boarding kowa ma ya huta. Sunyo kwanar layinsu, itama Zanira tanata sauri zata wajensa.

Fauziyya kam ashar take mata tana cewa karta bishi, ita kam ko'a jikinta. Bata ganin gabanta wani mota yazo wucewa irin yaran nan sangartattu ne aikam yayi ciki da Zanira. Nan ta wuntsula sannan ya take ta. Duk abinda akeyi a idon Mahfooz da Fauziyya.

Nan ya kwarara ihu ya zube ƙasa. Fauziyya ɗinma ihun ta saka. Zanira kam bata ƙara minti ɗaya ba Allah ya ɗauke ranta.

Wannan kenan!

#DiyarDrAbdallah

Ainakatiti ✨

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top