One - Kankana
Bismillahi rahmanin rahim,
“Mutuwa hutu ce a gareni," ta ayyana a ranta yayin da zufa ya karyo mata a wuya, bayan ta da sauran ilahirin jikinta.
A farad daya labarinka zai juya, daga fari zuwa baƙi. Tabbas ta saba jin yadda rayuwar mutane ke canza wa amma bata taɓa cin karo dashi ba sai yau.
"Daga ina zan ɗaura?” ta sake ayyanawa, sai dai kuma babu wanda zai bata amsar tambayar ta.
So da dama zaka kwanta cikin walwala amma ka tashi komai ya tarwatse maka. Duka abinda kake tunanin shine gaskiya sai kaga akasin haka. Wanda ka yarda dasu sai su kasance sune masu cutar dakai. Rayuwar da kake zama da makashin ka amma ta sigar mutunci. Tabbas a yanzu ta yarda da maganar da bahaushe yace, "mugu bai da kama."
Ance rashin sani yafi dare duhu, amma da wani sanin gwara zama cikin tandun kwalli. Saboda yanzu rayuwarta ya canza fasali.
Haɗiye miyau tayi mai mugun zafi, idan kana kusa da ita zaka iya jin ƙarar sa. Sannan ga wani matsanancin ciwon kai da ke addabar ta, tashin hankali tareda rudani data shiga kwanakin nan shine sila.
Fuskan ta a tamke yake babu annuri ko kaɗan, girar sama da ƙasa a harɗe. Goshin ta kuma yayi layi layi. Idanta kuma ba kalar daka saba gani bane, ruwan toka ne ƙwayar sannan kuma yana sheƙi. Budurwa ce ajin farko mai kimanin shekaru ashirin da hudu a duniya.
Tanada bala'in juriya da dakewa, duk abinka da ita, bazaka ga wani gazawa a al-amuranta ba. Ko yaya matsala yake damun ta bazaka gansa a fuskanta ba. Hawaye kam idan tace tunda take bata taɓa kuka ba bazaka musa ba. Shi kansa ma murmushi za'a iya dirga sau nawa takeyi a rana.
Hakan bawai yana nufin da chan ta shiga wani ruɗani bane, a'a ita haka halittan ta yake. Akwai juriya da dakewa.
Matse ƙaramin towel ɗinda ke hannun ta tayi, sai ta sake shafa mashi a saman goshi. Bata iya haɗa ido dashi saboda ɗacin dake ji cikin ranta. Yana bala'in bata tausayi. Ita bata kuka, a yau tayi kishi da wanda suke iya kuka tareda nuna damuwan su ƙarara. Tabbas kuka rahama ne a tareda ɗan adam. Kukan zuciya wanda yafi na bayyane ciwo shi takeyi. Shi kam murmushi yakeyi tareda binta da addu'a cikin ransa.
Dattijo ne mai kimanin shekaru sittin da biyu, fuskan shi akwai furfura wajen girar sa da kuma gemun sa. Hannun sa yake kokarin motsi dashi inda ta miƙa nata tareda magana cikin sauri.
"Baba! Ina ke maka ciwo?"
Murmushi yayi sai yace, "Ba inda ke min ciwo Naseera, ki daina damuwa."
Daci kawai zuciyar ta ke mata, ga gudun dayake yi kamar jirgi. Tabbas BP dinta ya hau a yanda take jin kanta. Ita kaɗai tasan abinda ke mata ciwo. Saboda Zuciyar ta yana mata barazanar fashewa, ga kuma tausayin mahaifinta daya luluɓeta kamar bargo. Haƙiƙa an zalunce shi.
"Ki tashi ki tafi ya isa haka kafin supervisors su fara neman ki. Kada ace zaki nuna preferential treatment saboda ni Babanki ne."
"I want to be here," ta faɗa a sanyaye tareda ƙara saka towel cikin ruwa ta sake matsewa. Wannan karan wajen wuyan sa tabi tana gogewa. "Baba, bana so na rasa...."
Bata karasa magana ba sai ƙofa ya bude, "Assalamu Alaikum," aka ce yayin da wata dattijuwa ta shiga. Hannun ta cike yake da coolers.
Amsa sallamar Naseera tayi a dikilce saita miƙe tsaye tareda gyara mazaunin rigarta, "Baba toh bari na tafi zan dawo anjima... " shima bata kalle matar ba tayi maganar. Baza'a ce mugun kallo ta watsa ma matan ba amma Ƙaninsa ne.
"Allah ya maki albarka," saiya kalle matar data shigo, "Binti kice yarki ta daina damuwa. Zan warke in sha Allah."
Hajia Binti ta kalle Naseera fuskanta cike da annuri, "Yar Siri Siri, Naseeran Babanta naga tana jin gari, ciwon nan yasa ta sai kumbure kumbure takeyi, ita a dole Daddy's girl." Hajia Binti ta faɗa fuskanta babu damuwa.
A dikilce Naseera ta murmusa saita dauki jakarta tareda wani envelope ta fita bata sake cewa komai ba. Tana rufe kofar a bayan ta saida ta tsaya ta gyara kallabin ta saboda duk ya sukurkuce. Ajiyar zuciya ta sake yi saita tafi office dinta, Resident Doctor ce amma kasancewa asibitin Babanta ne Dr Abdallah dole saida aka bata nata office din.
Zama tayi akan kujerar ta, saita ɗauko takardar tana sake kallo. Ta kasa gasgata abinda yake bayyanawa. Ba karo na farko ba kenan tana sake tura sample lab, zai Kai kusan sau 6 amma duka haka results ɗin ne.
Tafasa kwakwalwarta ya cigaba da yi, anan ta soma ganin dishi dishi, duk ilahirin jikinta yayi mugun sanyi. Bakin ta ɗaci yakeyi kamar taci danyen shuwaka.
Buga kofa aka yi tareda shiga, "Dr, ana neman ki a male ward yanzu," wata Nurse ta faɗa a ladabce. Da kai Naseera ta amsa, saita kalle Beeper dinta, anan ta lura an daɗe ana mata magana batama lura ba. Envelope din hannun ta takai cikin safe ɗin office ɗinta ta kulle. Saita saka lab coat ɗinta tareda fita.
Hajia Binti ta lura da mugayen kallon da Naseera ke binta dashi kwana biyu. Amma duk abin ka bazaka ji cikin Naseera ba, kamar kwalta take saidai ka wuce amma ba'a bambaranta. Zurfin cikin ta ya bala'in ɓaci. A duniya kuma Hajia Binti ba abinda take so kamar Naseera. Kasancewar sun shekaru bila adadin bayan aure kafin suka sameta.
Gatan duniya sun nuna mata, yasa yadda ta canza mata kwana biyun nan ya bala'in ɗaga mata hankali.
Saidai abinda ta sani shine duk abinda ruwan zafi ya dafa, idan aka yi haƙuri ruwan sanyi zai dafa shi.
****
"Ƙas Ƙas Ƙas" ɗin taunar cingam ke tashi tareda waƙar Hamisu Breaker tana bi, baiti baiti babu wanda bata sani ba kamar ita ta rubuta waƙar. Tanayi tana fesa kwalliya. Idan wani ya gani zaiyi tunanin biki zata. Amma kwalliya kawai takeyi na nishaɗi saboda zata gidan kawarta anjima domin ta samu tayi hoto wanda zata watsa Instagram. Yau Laraba kuma rana ne na hashtag din WCW watau Woman Crush Wednesday.
Madubala wanda aka fi sani da saurauniyar kyau ta cige ta satin daya gabata, hotuna tayi masu kyau, gashi samari sunata yabon ta. Tabbas tasan wasu sun bita private domin su bata kuɗi. Kuma abin ba ƙaramin ɓata mata rai yayi ba. Dama itace abokiyar hamaiyarta a duniya. Basu taɓa haɗuwa ba, kuma ba garin su ɗaya ba, asali ma basa following juna amma suna kishin juna sosai.
Kofa aka tura yayin da aka shiga, a wulakance ta kalle wanda ta shigo, ba kowa bane illa ƙanwarta Fa'iza.
"Ruma jiya naje ajin ku amma ance babu wata mai irin sunan, babu irin kwatancen da banyi ba harta hoton ki babu wanda ya gane ki. Kaɗan kuma sun gane fuskan daga Instagram ne," ta faɗa fuskanta babu yabo babu fallasa.
Ninke kayan saman gadon ta soma yi ba tareda ta kalle Ruma Sa'u ba. Ita kam gabanta ne ya soma faɗi amma ta ƙware a bariki.
"Meaning?" Ruma tace a dikilce tareda watsa mata harara da dara daran idanta.
"Eh yana nufin ko karya kike baki samu admission ba, ko an kore ki, ko kuma ba'a department din kike ba."
"Toh FBI, da wannan lokacin da kika ɓata wajen bin diddigi da kin bincika meyasa kike da masifan muni daya fi miki... Matsalata da talaka bakin ciki da hassada. Ina ruwan ki da rayuwa ta??? " sannan saita ja dogon tsaki.
Murmushi Fa'iza tayi, idan da sabo tsab ta saba. Da kuma zagi yana aibu daya yi mata wani abu. Amma bazai yiwu yanda iyayen su ke kokarin ganin sun basu rayuwa mai inganci ba a rinka zalinta su.
"Kuma idan kin ga dama ki haɗa min annamimanci wajen su Inna, wallahi saina maƙure maki wuya, ki koma kina zare ido kamar akuyar data lashe gishiri." Ruma ta sake cewa.
Tas Fa'iza ta gama Ninke kayan saita dauki khaki dinta na nysc ta fita tabbas Ruma zata aikata. Yau sunada CDS- community development service. Ruma Sa'u kuwa ko a jikinta, bayan ta gama kwalliya saita saka hijab dinta sannan ta dauki wani katon jaka ta fice.
A tsakar gida ta riske mahaifiyarta tanata fama da itace, laifin ta ne ruwa ya dake shi saboda ance ta rufe da leda ita kuma ta mance.
"Inna ni zan tafi makaranta, munada tutorials sai mangariba zan dawo."
Murmushi Inna tayi tareda ta fitowa daga inda aka keɓe a matsayin kitchen. Idanta sai ruwa yakeyi saboda hayaƙi. Da haɓan zaninta ta goge kana tayi magana, “Ba zaki karya ba, koda koko ne kisha mana?”
“Inna kenan! Zaƙi da mai na biyo birni.” ta faɗa tana murmushi.
“Shikenan Ruma Allah ya bada sa'a, dan Allah a maida hankali,"
"Amin" tace sai ta nufa zaure.
Bata sha wuyan samun napep ba, anan ta dauka suka wuce GRA. Gidan wata tsohuwar aminiyar ta Rahina zata je. Koda yake bafa ƙawarta bace, cin zalin yarinyar takeyi sanda suke ƙanana. 'Ruma Annoba' ake mata laƙani dashi, saboda ta buwayi yaran mutane.
Kullum Inna sai taje ban haƙuri maƙota, Ruma Allah yayi mata jin haushin mutanen da acewarta basuda kyau. Idan bakada kyau kullum saita takale ka da faɗa tayi maka dukan tashi kasha gishiri. Ajin su ɗaya lokacin a islamiya da Rahina, kuma ta wahala matuƙa sai daga bisani babanta ya fito takarar chairman kuma yaci. Anan ya siya gida a GRA suka koma. Yanzu shekaru uku kenan basu haɗu da Rahina ba. Saidai kwanan nan ta ganta a Instagram ta bala'in gogewa.
Ruma Sa'u tayi mugun mamaki saboda Rahina kamar an haƙota a rami take. A sanin data mata duk kyan kaya baya mata kyau, a tsuke take kamar bulala. Shiyasa Ruma ta laƙa mata suna Rahina Bulala, wanda sunar ya bita lungu lungu daga baya kuma sai aka koma ce mata Lala tunda wancan yayi tsawon faɗi.
Lala ta wuce tunanin mai karatu yanzu saboda ko turanci da hanci take faɗin wasu kalamai, ga wani kamala da natsuwa wanda arziki ke sanyawa. Uwa uba har umara taje da dubai duka tayi hotuna a chan tayi posting.
Ruma da kanta tayi mata friend request a Instagram sannan ta karɓi number dinta. Yanzu zata je tayi mata yini, ita da biyu zata saboda ta samu ta watsa hotuna gidan yan gayu.
Tunanin abinda da Faiza tace ya faɗo mata. Anan taja dogon tsaki tareda tsine ma Faiza da la'anta ta. Ruma tayi jamb sau 4 duk bata samu abin kirki ba, daga baya idan an bata kudin jamb jambaki da Hoda take siya, ranar jarabawar ta fita gantalin ta saita dawo tace, "Inna an kuma, nifa bada boko zanyi arziki ba"
Faiza kanwarta ce, amma yanzu haka tana bautar ƙasa a banki. Ganin yadda ake takura ma Ruma Sa'u akan inda zata sai tayi karya tace ta samu admission. Yanzu haka a karyar ta har anyi shekaru 2 tana aji biyu a jami'a.
Kowa yayi mata murna sanda admission ɗin ya fito harta yayanta shine ya biya mata kudin makaranta. Duka kudin ta kwasa ta siya ankon kawaye da kayan kwalliya. Kullum ta buga hijabi tace taje lectures ko tutorials amma tana kan titi tana gantali kala kala da bin kawaye musamman wanda aka haɗu dasu social media. Idan kuma ƙawar yar jam'i ce, wata sa'in har lectures Ruma tana rakata daga nan a wuce gantali.
Bukokuwa kuwa ba'a kirga yawan wanda taje, bata sati biyu bataje biki ba. Wata sa'in a wani bikin take haɗuwa da amaryar da za'a yi bikinta sati mai zuwa. Ba'a wuce hotuna biyar a Instagram na ƴan mata wanda suka yi cinkoso na kamu watau group pictures baka hangeta ba.
"Kankana uwar ruwa, Kankana abin sanyaya rai. Kowa yana marmarinki saboda bakida abin da za'a zubar, kwallon ki da ɓawon ki duka magani ne. Koda kuɗin mutum saida rabon sa. Matar manya, ganin ki yafi zuwa Dubai," Lala ta soma mata kirari yayin da suka rungume juna.
"Rahina Bulala ashe zaki iya gogewa" Ruma tace cikin izgili, Lala ranta ya sosu amma tayi fuska. Janyo mata hannu tayi suka shiga cikin gidan. Anan Ruma Sa'u ta saki baki, gidan ya ƙawatu. Domin yafi na sauran ƙawayenta na social media haɗuwa.
"Ya kamata da Lala zan ƙulla aminta bada yan group din One Love❤️ ba” ta ayyana cikin ranta. One Love ya shahara a WhatsApp, asali Big Boys and Girls ke ciki, ajebo masu kayan alatu da duniya. Amma yanzu ta ɗauki alwashin zata koresu duka domin ance zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai. Ƙulla alaka da Lala zai sa itama ta goge tayi arziki wata rana. Tabbas Lala alheri ne a rayuwar ta.
Ƙarewa ɗakin Rahina tayi tsab tana yabawa, pink ne komai cikinsa. Gashi ƙal ƙal dashi komai yana inda ya dace. Sanyin AC yana ratsata ga Samosa wanda yaji kayan haɗi tana watsawa bakinta, nan take haushin mahaifinta ya ɗiran mata. Wai ya rasa duk sana'ar duniya da zaiyi sai malunta. Shima ɗin wai malamin firamari. Baida mota baida sutura, duk kayansa ya koɗe.
Sai dai a haka yakai yaransa biyu jami'a. Aliyu yayan Ruma Sa'u sai kanwarta Fa'iza. Aliyu ya haɗa karatu da aikin typing, printing da photocopy. Ita kuma Fa'iza tana ƙananan ɗinki kamar su huluna, hijabi da sauran su tana siyarwa. A haka suke rufa ma kansu asiri.
Canza kaya Ruma Sa'u tayi a gidan su Rahina, saita dauki iPhone ɗinta taje farfajiyan gidan tana hotuna, anan taga mai aikin gidan saita miƙa mata wayar domin ta dauke ta. Riga ce off shoulder wanda ya bala'in matse ta, sai pencil skirt. Duka sansan jikinta a bayyane, gashi tanada diri mai kyau. Daurin ture kaga tsiya tayi inda yayi masifan mata kyau.
Anan ta saka a Instagram ɗinta. Sunan da take amfani dashi shine "Kankana" kuma kafin kace kwabo maza harda mata sunata yabon ta.
'Kankana uwar ruwa'
'Kankana mai sanyaya rai'
'Ajebo dan Allah kizo ki aure ni'
'Hurul ayn ɗin duniya. Bakida matsala babban yarinya'
Sai kuma wanda sukayi ta ajiye account number ɗinsu suna mata maula.
Ita kam ba abinda ya dameta ba kenan, jira takeyi wani babban yaro a Instagram mai suna Qwaro yayi liking hoton. Ta ɗauki alwashin zata ƙulla alaka dashi tunda shima ɗan masu dashi ne.
Ko'ina akwai yarensa, yasa daga kudi sai kyau kaɗai ne yaren da Ruma take ganewa.
Wannan kenan!
#DiyarDrAbdallah
#YarSiriSiri
#Kankana
#OneLove
Kyan tafiya dawowa, duk wanda ya bar gida tabbas zai barsa. Barkan mu jama'a. Gani na sake dawowa da wannan labarin nawa mai suna Diyar Dr Abdallah. Ku bini sannu a hankali domin muga yadda zata kasance. Nagode.
Ainakatiti⚡
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top