Eleven - Farin Wasa
Assalamu Alaikum Dimplicious Empire, please endeavour to like before you start reading. Also don't forget to comment on your favourite paragraphs. Lastly my youtube channel link is in my bio, please kindly subscribe. Love yall fisabillahi ❤️
***
Komai dib ya ɗauke ma Mahfooz. Gabansa ne ya cigaba da faɗi. Tashin hankali mara mitsaltuwa ya shiga. Cikin ƙanƙanin lokaci komai ya cunkushe mashi. Da sauri ya shiga motarsa yabi hanyar da suka tafi. Dama idan gudu ne a mota sai kace fast and furious.
Cikin ikon Allah ya hange su daga nesa, aikam yayita tsare dasu. Barin Kaduna sukayi suka nufa hanyar Buruku mattarar kidnappers. Addu'a kawai yakeyi kada su ilanta Naseera. Saboda idan wani abu ya faru da ita bazai yafe ma kansa ba.
Ita kuma sun rufe mata ido da wani riga, tayi kokarin tashi suka zabga mata mari tareda nuna mata wani zungureriyan bindiga. Anan ta ja mutuncin kanta ta natsu. Kawai dai kuka takeyi ƙasa ƙasa tareda neman agaji. Tsanar Mahfooz ya dirar mata sosai.
Anya bayada bakin uwa kuwa a kansa? Tunda take bata taɓa ganin azzalumi irinsa ba. Abin nasa ba'a magana. Tabbas tasan yaji sanda ta sake neman taimakon sa amma shine yayi mata mirsisi. Ɗabi'un sa kamar na hatsabibin boka babu ko ɗigon imani.
Addu'a takeyi akan Allah ya kawo mata taimako saboda idan na mutum ne zata wahala. Allah kaɗai ne gatan ta kuma tana fata kada ya kyaleta a cikin wannan halin. A haka tayita kuka mai tsuma rai.
Masu garkuwa da mutane sunfi sati uku suna lura da al'amuran Naseera. Yanzu dama sana'ar da tafi ci kenan. An raina yan fashi da makami saboda basu samun wani kuɗi. Amma indai kana garkuwa da mutane ana tsoron ka. Sanna yafi kawo kuɗi mai yawan gaske. Miliyan ɗari suke so su ƙwaƙula wajen Dr Abdallah. Koda baida ita sun san yanada abokai manya da zasu bashi. Balle kuma Naseera ƴarsa ce tilo. Koda birnin sin ne zaije ya nema wannan kuɗin kokuma su illanta mashi ƴarsa tilo.
Sunata zurara gudu shima yana binsu, basuyi tunanin cewa akwai wanda ke binsu ba. Balle dama ga ɗan tazara tsakanin su, shine yake hangen su kaɗan kaɗan.
"I am not a coward Dr, zan taimaka maki," yake jaddada ma kansa cikin mota. Ƙara gudun motan sa yi saboda suna tsare mashi. Bai kira kowa agaji ba, baida wani dabara. Kuma shiba soja bane amma yasan yanaso ya taimaka mata. Yana so shima ya kasance a inda take koda shima zasu kama shine.
Lungu da saƙo suke bi da ita, kwata kwata baisan inda suka shiga ba. Wani kurmusun jeji ne zakayi mamakin yadda mutane suke raye a wajen. Shidai kawai yana binsu bai karaya ba.
Daya karaso kusa da motan masu garkuwa da mutane, bai jira komai ba ya dake su ta baya domin yaja masu hatsari. Nan motan masu garkuwan ya soma tangal tangal. Haka ya sake zuwa da karfin tsiya ya dake bayan kuma. Saiga shi sunyi daji sun dake itace.
Wannan karan saboda karfin daya dake motan saida shima ya fita hankalin sa na wasu dakikai. Anan ya fita da gudu ya je inda motar yayi hatsari. Duk sun zube suna jan numfashi. Janyota ya soma sai zatayi ƙara ta tada sauran. Da sauri ya saka mata hannu a baki.
"Shhhh.... Ni ne."
Batasan waye ba tunda har lokacin tana tareda tsumma a fuskan ta. Amma koma waye ta tsinci kanta a cikin natsuwa. Data fito harda jakanta wanda ke rataye bayanta har lokacin, kwance mata ɗaurin hannunta yayi sai ya cire tsumman fuska. Anan ta buɗe ido taga Mahfooz ne. Bata ɓata lokaci ba ta yanke shi da mari.
Saita juya ta soma tafiya tana hawaye, anan shi kuma ya cabke ta amma tana turjewa. Bata so ta ganshi kuma bata san ya taimaka mata. Daya janyota ta sake amfani da ɗayan hannunta tayi ta mare shi. Zuciya yayi sosai cikin bacin rai, saiya riko duka hannayenta yana zare mata idanu.
"Calm down Dr... Gashi nazo ai... Nazo saboda ke ne,"
Bata kai ga amsa shiba sai ga masu garkuwa sun soma farkawa. Harbin bindiga suka bi su Naseera dashi. Anan Mahfooz ya finciko hannunta suka fantsama daji. Gudu suke yi babu kakkautawa. Yayi mamakin yadda ta sake jiki tana rambaɗa gudu.
Suna jin ƙarar bindiga daga bayan ana harbi domin a tsorata su. Masu garkuwan basu taɓa samun babban kamu ba kamar Naseera kuma bazasu haƙura ba sai sun damƙeta. Ran Ogansu ne yayi bala'in ɓaci akan abinda Mahfooz yayi kuma sukace zasu koya mashi darasi. Tabbas idan suka kama shi zasu yanke mashi ƙafa ɗaya daga gobe bazai sake nuna jarumta a hurumin da bana saba.
Su kuma su Dr Abdallah sunata jiran Naseera basu ganta ba. Wayanta yana hannunta sanda masu garkuwa suka damƙeta saiya faɗa kwalbatin dake gefe wajen, yasa ba'a samunta. Anan Hajia Binti ta soma tada hankali. An kira a asibiti aka tambaya inda Naseera take amma ba'a ganta ba. Gashi kuma motan ta yana parking lot.
Mai gadi yanata Gyangyaɗi sanda suka tafi da Naseera, baima san abinda ake ciki ba. Kuka Hajia ta soma saboda jikinta yaƙi kwanciya. Ita tana tsoron kada Naseera ta sake faɗawa hannun wanda zasu cuce ta.
Haka Dr Abdallah ya tashi yasa direba ya kaishi asibiti, raban sa da asibiti tun randa aka sallame shi a matsayin mai jinya. Basuda camera a asibitin balle aga meya faru. Amma tabbas masu zama a réception sunce sunyi Sallama da Naseera inda ta basu ɗari biyar su sha ruwa dashi.
Hajia Binti sai kirar wayan Doctor takeyi tanaso tasan me ake ciki, shikam kasa ɗauka yayi. Baiso yace mata baisan inda ƴarsa ta shiga ba.
Abokinsa wanda sukayi Barewa College dake Zaria tare ya kira. Shi police ne kuma yanzu ya zama babba a wajen. Dr Abdallah ya labarta mashi komai. Anan yace su bari gobe kila ta tsaya wani wajen ne. A ƙa'ida sai mutum yayi awa arba'in da hudu kafin ayi declaring ɗinsa ya ɓace.
Abin duniya yayi ma Dr Abdallah cinkoso, tun bayaso ya saka tunanin yana kawar wa har ya yarda da cewa eh fah Naseera ta ɓace. Gari yanzu ya ɓaci garkuwa da mutane ake yi ta kowane fanni. Balle yasan cewa yanada arzikin da zai sa mutane suso cutar dashi.
Gwiwa a sanyaye ya koma gida, tun da Hajia Binti taji ƙarar gate ta fita da sauri. Ganinsa shi kaɗai babu Naseera ya sake firgita ta.
"Na shiga uku ni jikar Habiba." ta faɗa tareda fashewa da kuka. Sosai takeyi babu kakkautawa.
"Kila ta tsaya wani wajen ne?" yace dakyar saboda shima tashin hankalin yake ciki.
"Wallahi wani abu ya sameta ne. Ai ba yanzu ta soma shiga cikin haka ba,"
Kallon ta Dr Abdallah yayi yana nazari, "Ban gane ba?" yace tareda kafata mata ido kur. Har lokacin basu bar parking lot ba.
"Babu komai," saita juya da sauri ta shiga ciki. Bai ce komai ba yabi bayanta suka shiga. Kitchen ta wuce tana kuka. Bataso ta gayama Dr abinda ya faru da Naseera, kafin zuciyar sa ya buga ta rasa shi gashi babu Naseera da zata ɗanji sanyi.
Tsaye yake a bayanta yana kallonta, kokarin gane ma'anar maganar datayi ɗazu yakeyi. Shi a nashi sanin Naseera bata taɓa shiga wani mugun tashin hankali ba. Amma kuma kila sanda yake ciwo abu ya faru basu sanar dashi ba.
Anan ne tunanin yazo masa, tabbas abu zai faru kuma ayi mashi ƙememe.
"Binti," yace cikin ƙaramin murya.
Bata tanka ba, illa jan majina tana kokarin saisaita kanta. Hannunta tasa tana share hawayen da suke zuban mata kamar famfo.
"Binti," ya sake maimaitawa, "Maman Naseera," ya kuma faɗa. Anan kuma ta barke da sabon kuka. Kawai tunani takeyi kada masu garkuwa da mutane ne. Makon daya gabata sun shiga sun ɗauki wani Alhaji a layin. Batasan ya zatayi da rashin Naseera ba, sun bala'in shakuwa. Tasan duka al'amuran ta. Naseera bamai shige shige bane yasa tasan bataje gidan kawaye ba.
Sai Naseera tayi shekara 2 batayi baƙuwa ba a matsayin ƙawa. Yasa yanzu duk ta rude. Dr Abdallah ne ya ƙarasa inda take tsaye. Riƙeta yayi yana dukan mata baya a hankali alamar tayi shiru, saida yaga ta tsagaita saiya soma magana.
"Menene ya faru da Naseera sanda bana nan?"
Taso tayi mashi karya, amma ta kasa. A iya zamanta dashi babu maganar karya. Ita dai bata gayama shi abu to zancen bai taso bane. Ko wannan tana jin nauyi cikin ranta. Anan ta Labarta meya faru randa ya aike Naseera gidan Nurse Jamila kai mata Insulin.
Idan ranshi yayi dubu toh ya ɓaci, amma da yaji Sadiq ƙaninsa yana nan yayi handling case sai yaji dama dama. Koba komai yanada wanda zasu riƙe iyalan sa idan baya nan.
Suna cikin gudu su kuma chan sai suka ga titi, koda yake kawai dai buɗarɗen hanya ne domin babu kwalta ko fasali game da hanyar, sannan daga titin sai sabuwar daji. Sun san tabbas masu garkuwa zasu yi tunanin sun sake fantsama cikin sabon dajin ne. Sai suka ruga gefe sukayi yamma. Anan suka cigaba da gudu fiye da awa daya. Daga ita har shi babu abinda suke cewa. Hannunsu yana maƙale da na juna ya riƙeta gam baisan abinda zai taɓata.
Suna haka ne har wajen ɗaya na dare sai gashi sun riske wani Rugar Fulani. Ba Naseera kawai harta shi yaji daɗin ganin wannan. Anan suka sake saurin gudun su. Yanzu basa jin harbi saboda tuni sun sha bambam da ɓarayin.
Gidan farko suka kwankwasa, bugu ɗaya sukayi wani matashi ya fito da saurin gaske tareda sandar sa. Lokaci ne na tsaro ba'a barci mai nauyi kafin a shammace ka. Abin mamaki ya riske shi, saboda ganin su, mace da namiji.
"Noi," yace masu da harshen fillanci.
"Ka taimake mu dan Allah," tace saita fashe da kuka tana nishi sama sama. Batada lokacin fara mashi bayanin bata jin fillanci. Mahfooz shidai yana ji kaɗan ƙaɗan amma baya mayarwa. Zaman shi da Faash dole da karfin tsiya yake tsinta.
Matashin kallon su yaketa yi yana nazarin su."barayi suke bin mu nida matata, ka taimaka mu dan Allah,"
Wani yar taji cikin ranta. Taso tace mashi ita ba matar sa bane, sai kuma wani zuciya ya raya mata idan ta kuskura tayi wannan magana zasu koreta. Su Fulani sunada al'ada kuma tarayyan mace da namiji baya cikinta.
"Toh ku shiga nan da sauri," ya umurce su tareda nuna masu inda ya fito. Naseera ta fara shiga sai matashin ya sake magana, "Ina fatan babu wanda yaga kunyi nan. Bana naso na jayo ma Ardo matsala wallahi,"
"A'a bamu bari sungan muba wallahi," Mahfooz yace. Da kai matashin ya amsa su. Shima zakaga tsoro fal ransa. Wannan ba hurumin sa ba, an riga an hanasu kawo ɗauki ma wanda suke neman. Fatan shi kawai ba yan kungiyar Sada bane. Saboda idan yasan sun fantsama daji ruga bayan ruga zai ta bi yana neman su.
Kuma wanda ya kawo ɗauki ya harbe mashi ƙafa, wata uku daya wuce saida Sada ya harbe wani abokin sa akan wannan taimako daya bama baƙi.
Anan wannan matashi ya janye tabarma dake jingine akan bango, shimfiɗa wa yayi a ƙasa saiya zauna. Yau shine da tsaron rugar, dama duka matasa an rabama kowa ranar da zaiyi tsaro. Tun ranar da Sada yayi wannan harbi, sai suka ɗauki alwashin zasu zauna bakin wajen duk wanda yazo walau a miƙa shi wajen Sada kokuma a ce yaje wani wajen.
Fitilar aci balbal yake ci akan wani ƙaramar tebur. Ɗakin ƙarami ne amma ba sosai ba. Katifa ce wanda tayi laushi sosai tama kusan mutuwa shimfiɗe a ƙasa. Ƙasan kuma tabarma ne ya malale. Naseera ta gama kallon ɗakin tana tunanin yadda zata kwana da shi ciki.
Shi kuma binta yakeyi da kallo, ɗakin shiru babu abinda ke tashi banda numfashin su suna ajiyar zuciya. Shine ya soma magana, "Babu waya cikin jakarki?"
Yi tayi kamar batasan da ita yake magana ba, saida takai kusan minti uku. Ita bata zauna ba, kuma bata buɗe jakar ba. Daga bisani ta doka tsaki ta hau kan katifar. Jakarta ta soma leƙewa bataso yaga ARV ɗinta balle ya raina ta yana kiranta mai aids.
Duba jakar tayi bataga wayan ba, anan ta tuna yana hannun ta kuma babu mamaki ta zubar dashi. Bata bashi amsa ba. Shima ta wannan fanni ya gane ma kansa. Dafa kansa yayi ya soma safa da marwa. Shi yabar nasa cikin motarsa. Gashi kwata kwata baisan inda yake ba, baisan yadda suka isa ba balle yayi ma matashin daya taimake su kwatance.
Kafa kanta tayi akan gwiwar ta saita soma kuka, tausayin yadda iyayenta zasuyi idan sunji labarin takeyi. Ido kamar garwashi ta ɗago kanta. Kallon Mahfooz takeyi cikin ido, shi ma yana kallonta ɗin. Bai zauna ba har yanzu, yana jingine da bango ya saka hannayen sa cikin aljihun wandonsa.
Hawaye ne yake malalo ma Naseera a idanu, shima saida ya tausaya mata. Yasan cewa tana cikin tsaka mai wuya. Amma abinda ya sani yanzu shine ita da shi suna tare. Kuma abinda ya shafe ta ya shafe shi.
Baisan me zai iya cewa domin ta daina kuka ba, bayasan kuka a rayuwarsa, balle yanzu ganinta tanayi ga sautin shi yana ji. Ji yake kamar ana narka mashi ruwan batir. Runtse ido yayi ya cigaba da ajiyar zuciya, saiya buɗe yaga har yanzu ɗin bata bar kallon sa ba.
Kallo take masa irin na tsana, kallo take masa na mun saka ƙafar wando daya dakai. Muryanta wanda ya dishe tayi amfani dashi, "amma kasan niba matarka bace koh? Danaga auren ka gwara naga ranar mutuwa na," kuka ne ya sake kupce mata data tuna tanada HIV, ita tana ganin ko yanzu a haka a mace take. Gawa ne kawai tana jirar ranar da za'a birne ta.
Takawa yayi yaje inda take ya durƙusa, saiya soma magana da hankali." Bawai na kiraki matana bane saboda na raina ki ba. A'a saboda shi kaɗai zaisa wanda basu sammu ba su taimaka mana. Aure yanada wani natsuwa... Shiya saka,"
Bata kula shiba, shiya sani. Amma abinda ta sani shine ita ba matarsa bace. Miƙewa yayi ya janyo wani tabarma cikin ɗakin. Anan ya shimfiɗa saiya kwanta. Kallon ceiling yayi yana tunane tunane, fatan shi kawai Naseera taga wannan abin dayayi, sannan koda murmushi dashi zatayi idan sun bar wajen nan gobe da safe.
Daga ita har shi babu wanda ya iya runtsawa. Kawai sai juye juye suke yi, wajen ukun dare sai wannan matashin ya kwankwaso ƙofa ƙasa ƙasa, Mahfooz ne yace ya shigo.
"Ku tashi na kaiku gidan mu yanzu, kafin azo a ganku anan ku shiga matsala kuja min matsala nima,"
"Bangane ?" Mahfooz ya tambaye shi a mamaki ƙarara fuskan shi.
Anan matashin ya labarta masu wani Gagarumin dan ta'adda Sada yayi ma kowa kashedi. Kada su shiga harkan sa shima bazai shiga nasu ba. Idan wanda yayi garkuwa dasu suka gudu duk wanda ya gani ya dawo dasu zai basu lada, wanda kuma ya taimaka masu zai wulakanta shi tareda hukunci.
Anan sukayi shiru suna nazarin abinda yace, matashin ne ya soma magana don tsagaita shirun, "Yasa nace kuzo muje gidan mu tun yanzu kafin wani ya ganku ya gayama Sada, za'a bashi kyauta ni kuma hukunci ya hau kaina. Saidai zai iya yiwuwa kila harda
yan uwana zaiyi ma haka,"
Buhu ya miƙa ma Naseera domin ta rufe kanta, yanayin shiganta yayi kamada dana yan birne. Kafin suna tafiya wani ya tashi fitsari cikin dare ya hangeta.
Sannun a hankali suka ƙarasa inda wannan matashi yake, gidansu an kewaye shi da kofar langa langa kafin ka shiga. Bugawa yayi sau uku.
"Waye?" aka ce daga ciki da fillanci, muryan wani dattijo ne.
"Musa ne."
"Musa, me ka dawo yi nan bayan yau kana tsaro?"
"Fitsari zanyi na koma,"
Ya faɗa haka kafin wani yana sauraro daga ɗaki. Dattijon ya fito yana magana. Anan ya buɗe ƙofar sai yagan su. Kallon su yayi tas, saiya matsa masu suka shiga. Wani ɗaki ya kaisu yace su jira shi.
"Musa bana ce ka daina shiga harkan mutane ba?"
"Ardo wallahi tausayi suka bani, miji da mata ne yasa na taimaka masu,"
"Ni wallahi bana san haka, Sada yace idan aka shiga harkan sa akwai matsala. Yanzu ya kake so muyi dasu saboda bazasu iya tafiya ba sai ranar kasuwa?"
Anan Ardo yayi dogon nazari sai suka je ɗakin da su Naseera suke, murmushi yayi masu bayan yayi sallama. Daga Mahfooz har Naseera sun samu natsuwa fiye da.
Nuni yayi masu da tabarma akan su zauna, sai shida Musa suka zauna akan wani. Gyaran murya yayi saiya soma magana.
"Sunana Ardo Bello, kuma wannan yarona ne Musa. Su waye ku?"
Mahfooz ne yayi magana, "Sunana Mahfooz kuma wannan matata ce, Dr.....Dr....Likita ce," nan ya soma in'ina sabida baisan sunan Naseera ba.
Sai yayi gyaran murya ya soma tarin karya, ta lura dashi amma tayi mashi fuska. Ita bata damu ba ta tona domin ta tozarta shi.
"Matata ce wannan, kuma nazo daukarta daga aiki shine kafin na karasa sai ɓarayi suka ɗauketa. Shine fah nabi bayansu har muka isa nan garin."
Murmushi Ardo yayi kafin yace, "ba dai nan garin ba. Kun tsaya inda kuka tsaya saboda nan garin mota baida hanya balle ku shiga, gashi kuma bamuda wutan lantarki. Wayan hannu kuma sai anje chan babban gari yake shiga," saiya soma hamma. Zakara ne yayi chara suna sauraro.
"Yanzu abinda nakeso kuji shine dakai da matarka zaka zauna cikin nan gidan sai bayan sati biyu tukun?"
"Sati biyu!!!" Naseera tace tareda zare ido. Wanda shine abu na farko data ce tun shigarta gidan.
"Eh, saboda bazamu bari ku fita ba sai ranar da ake cin kasuwa. Kuma mu nan gari sati biyu-biyu muke ci, kuma jiya aka ci. Yanzu sai kunyi sati biyu tukun idan kowa ya fito zaici kasuwa sai kuyi shiga kamar yan fatauci mu fitar daku... Bama san matsalar Sada wallahi,"
"Yanzu babu wani hanyar fita daga nan sai munyi sati biyu?" Mahfooz yace.
"Babu fah," Musa ya amsa. "Wallahi idan Sada yaji labarin cewa na taimaka maku, bani ba har Ardo zai iya kashewa. Yanada manya manyan bindigogi kamar na sojoji,"
Ardo mikewa tsaye yayi, sai Musa ya tashi shima. Kallon su Mahfooz yayi, "Mahfooz da Likita asuba ya kusa, ni bari na tafi. Anan ɗakin zaku zauna har ku tafi. Idan gari ya waye zan maku iso da sauran iyalai na," saiya kalle Musa, "Yi maza ka koma bakin aikin ka kafin a gane wani abu."
Mahfooz ne ya bi bayansu yace yanaso yayi alwala, anan yayi ya koma ɗakin. Naseera ko kallonsa batayi ba tana zaune tana tunanin irin zaman da zatayi dashi harna sati biyu kamar arna.
Har wajen azahar suna ɗakin, an kawo masu abinci kaɗan suka ci suka ajiye, ta faki idon Mahfooz daya fita sallah saita ɗauko ARV ɗinta domin tasha. Fuskan Naseera babu annuri banda bin Mahfooz da harara bata yin komai. Ardo Bello ya lura da ita tun dare haka takeyi. Anan ya soma tunanin da kyar idan matar Mahfooz ne.
Kada ya zamanto cewa Mahfooz ɗin yafi Sada annamimanci zai kuma illanta Naseera ce. Anan ya yanke shawarar zai masu magana.
Lokacin Naseera taje kewaye domin ta kama ruwa, sanda ta dawo taga Mahfooz da Ardo zaune a gaban ɗakin akan tabarma. Sai ya umurce ta domin ta zauna. Chan gefe ta rabuka bataso tayi kusa da Mahfooz. Ardo ya sake lura da wannan.
Kallon su yayi da kyau kana fuska tamau babu wasa, "Wannan matar ka ne ka faɗa min tsakanin ka da Allah?"
Duka su biyun sun tsorata. Basuyi tunanin sunyi abinda zai kawo masu zargi ba. Kallon Naseera Ardo yayi, "Mijin ki ne wannan? Ki faɗa min zan taimaka maki,"
"Ba mijina bane," saita fashe da kuka. Mahfooz ya dafa kansa cikin takaici. Yanzu zaiyi wuyar su cigaba da basu muhalli. Babu wanda zai yarda mace da namiji da ba muharraman juna ba su zauna ɗaki ɗaya kamar kafurai. Akwai aikin sheda da zai iya giptawa.
"Gaskiya zaman ku babu aure inuwa daya cikin gidana bazai yiwu ba," Ardo yace a sanyaye. Mahfooz dai baice komai ba. Naseera har lokacin kuka takeyi.
"Ai babu damuwa, zamuyi yadda kace. Gani, gata yanzu sai a daura mana aure."
" An taɓa ɗaura ma mace aure babu waliyi ne?" tace a fusace.
"Ba ga Musa ba," ya amsata.
"Forget it, I'll never marry you," tace tana kuka. Abin yayi mata wani iri. Ana zaune ƙalau za'a ɗaura mata aure. Ita ta riga ta ɗauki alwashin bazata taɓa aure ba. Bazata zauna tana tsoron kada wata rana ta shafa ma mijinta ba. Duk da tasan idan tana shan magani tana kiyaye dokoki bazata shafa mashi ba. Amma akwai wannan tsoro dake bibiyanta.
"Ko ayi maku aure kokuma idan dare yayi ku tafi Allah yasa ku dace. Amma wannan ne taimakon da zan iya maku... Dan Allah ku fahimce ni." Saiya miƙe tsaye, "Ina zuwa," yace saiya tafi.
Naseera ta fara shiga ɗaki, kuka wanda shi ya zame mata jiki yanzu ta soma. Bazata iya auren Mahfooz ba kwata kwata, batada ɗigon sansa ko ɗaya cikin ranta. Kallonsa yana sakata shiga kogin damuwa. Kuma koda a yau bata jin haushin sa akan cin zalin daya mata. Bazata iya zama dashi tanada HIV ba, tabbas zata zalunce shi, kuma daya san tanada HIV bazai yarda a barsu ɗaki ɗaya ba.
"Bafa zan aureka ba!" ta jaddada mashi tana nuna mashi yatsu.
Shima yasan bai kyauta mata ba, shima yana nadamar abinda yayi mata. Shima yasan ya zalunce ta. Amma idan ta lura shine ma ya kamata ya aure ta bayan yan iskan chan sunyi mata abinda sukayi. Laifin sa ne kuma shine zai zauna da ita ba tareda tsangwama ba.
Tafiya yayi yaje dab da ita ya tsaya, magana yakeyi ƙasa ƙasa cikin natsuwa, "Kowane ɗan adam ajizi ne, babu wanda bai wuce yin laifi ba. Nima nayi kuskuren da bazan taɓa yafe ma kaina ba. Dr, dana tsaida su, koda basu saurare niba I should have tried," anan saita barke da kuka harda durkusawa. Shima abinda yayi kenan ya ɗurkusa saiya tallaba mata gemu domin ta kalle sa.
" Bance ki yafe min ba, I don't deserve it. Amma abu ɗaya nake so kiyi min. Duk abinda kika ga ya dace kiyi domin ki rayu. Idan kika rayu shine kwanciyar hankali na. Idan kika rayu I'll find peace. Idan mun fita abu na farko da zanyi shine na sake ki kowa ya kama gabansa, I promise, "
Miƙewa tsaye yayi saiya naushi iska, safa da marwa ya soma hannunsa yana kan ƙugun sa. Baisan yadda zasuyi sati biyu a rugar nan ba, gashi zaman doya da manjan da suke yi zai ƙaru ne musamman idan akwai aurensa a kanta. Saidai a shirye yake ya ɗauki duk wani cin fuska da zatayi mashi. Kome zatayi mashi idan zata rayu bai dame shiba. Ita ce murudin zuciyar sa, kuma yafi samun natsuwa kusa da ita.
Musa ne ya shigo gidan da sauri yana neman su Mahfooz domin su ɓoye, a cewarsa Sada yana bi gida gida domin yana kyautata zaton kayan sana'an sa nan suka nufa kuma za'a bashi abinsa.
Rumbun hatsi Musa ya soma gyarawa domin su shiga. Naseera tana kallo tana tunani. Menene take fighting zaman cikin duniya din nan? Ta lura ita annoba ce kwanakin nan. Alhakin Fauziyya yanata binta duk inda taje. Matse kwalla ta sake yi, kaico da halin data shiga tayi. Tabbas uwar da bata sani ba ta cuce ta. Tashin hankali ya cigaba da ɗawainiya da ita. Anan ta yanke ma kanta cewa gwara ta tsaida wannan wahalar kowa ma hutu. Daga Babanta, Ummanta, Ardo Bello harta Mahfooz zata kawo masu karshen wahalar su yanzu.
Ita ɗin dai ne! komai dake faruwa yanzu saboda ita ne Naseera! Kowa yana kokarin yaga ta rayu bayan ba'a san ita matacciya bace. Da hannunta tasa ta share hawayen ta. Rugawa tayi zata fita domin taje ta samu Sada, idan bai ganta a cikin gidan su Ardo ba zai kyale su.
Kuma gwara ta tafi koda Sada zai kasheta ne data aura Mahfooz.
Wannan kenan!
#Naseera
#Mahfooz
#DiyarDrAbdallah
#Dimpilious
#FullyDimplated
Ainakatiti✨
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top