Chapter 38

"Kallon jikinsa yaci gaba dayi cikin mamaki yana sake kallon mom da sadiq zaune cikin mamaki yace mom a ina nake nan?mom me kikeyi da wannan azzalumin kuma macuci?da sauri sadiq ya karasa inda deen yake tsaye ya kai hannu zai rikeshi a zafafe deen ya kalleshi yace don't touch me......sannan ya sake kallon mom yace mom menene yake faruwa?mom meyasa na ganni a haka?mom menene yake faruwa?jariri a gidan nan?when and how?

"Jikin mom sanyaye ta kalleshi tace deen kaje kayi wanka ka samu hutu tukunna zanyi maka bayani,,,,apartment dinsa ya wuce yana cigaba da kallon jikinsa....jikin babban mirror din dake kusa da closet dinsa ya tsaya yana cigaba da kallon fuskarsa cikin tashin hankali.....is that me?ya fada muryarsa a sanyaye sannan yayi saurin cire shirt din jikinsa da singlet faffadan hadadden kirjinsa ya bayyana sannan yaci gaba da kallon ciwukan da suke jikinsa,gashi yayi baqi ya rame

"Shower gel yai saurin zubawa cikin bathtub ya shiga ciki sannan yaci gaba da wanke jikinsa kamar wanda yake wanke wani datti,,,yayi spending kusan 1 hour cikin bathtub din sannan ya fito ya nufi dressing mirror yaci gaba da kallon jikinsa cikin tsananin mamaki yake tambayar kansa what's wrong with me?

"Lotion kadan ya shafawa jikinsa sannan ya bude closet ya dauki blue jersey ya saka ya feshe jikinsa da perfume,yana styling hair dinsa sadiq ya turo dakin ya shigo jikinsa a sanyaye,,,cikin zafin nama deen ya kalli sadiq yace get out....sake turo door din yayi ya rufe yaci gaba da kallon deen idonsa na shirin zubar da hawaye

"Sake kallon sadiq yayi a karo na 2 yace i said get out,bana son sake kallonka a gurina just get out please,zubewa yai a kasa idonsa na kallon deen yace i am sorry tiger.....sorry for your self ya fada a zafafe ya bude kofa ya fita ya bar sadiq tsugunne a kasa......be tarar da kowa ba a parlour hakan ya sashi karasawa apartment din mom,a kitchen ya tarar da mom ta gama hada kunun gyada da jug a hannunta ta fito....murmushi tayi tace deen har an fito

"Kallonta kawai yake yi kamar wani dolo...komai na gidan ya sanja gaba daya rayuwar gidan ganinta yake wata sabuwa.....kamar me shirin kuka deen ya kalli mom da jajayen idonsa yace mom just tell me meyake faruwa?mom menene ya faru dani?mom gaba daya jikina ciwo ne meya faru danine?

"Dad ne ya sauko daga upstairs din apartment dinsa ya samu guri ya zauna,itama mom da sadiq duk suka zauna kusa dashi jikinsu a sanyaye sannan dad ya fara yiwa deen bayani

"Innalillahi wa inna ilaihir raj'un..hauka?that's impossible hakan bazai taba yiwuba deen ya mike tsaye da sauri yana ci gaba da kallon jikinsa,,,da kyar dad yasa deen ya koma ya zauna sannan yaci gaba dayi masa bayanin komai....sosai deen yake kuka kamar karamin yaro....ajiyar zuciya dad yayi shima jikinsa sanyaye yace ba kuka zaka yiba deen komai daka gani ya faru dakai mukaddarine daga Allah wannan itace kalar taka kaddarar kuma kar kaga haka ta faru dakai kayi tunanin cewa wai Allah bayasonkane ko kuma kayi masa wani lefine...dukkanin wani dan adam daka gani a duniyar nan kowa yana da tashi kaddarar don haka ka dauki taka hannu bibbiyu

"Dad nina jawa kaina,dad komai ya faru dani nina jawa kaina kuma na tabbata akwai wani hukunci anan gaba....deen ya fada cikin kuka

"A firgice mom ta kalli deen tace haba deen kasan me kake cewa kuwa?kana da hankali kuwa?

"Daga kansa yayi yace ina da hankali mom kuma nasan me nake fada,babu wata karya da zata sake fitowa daga bakina,sannan ya maida kallonsa gurin dad yace ni macucine ni mayaudarine kuma ni mazinacine kuma mashayine,dad na lalata rayuwar yara dayawa saboda ban taba daukan wata mace da mahimmanciba,dad kowa a gurina wulakantacce ne mara daraja.....nayiwa yara sama da dari fyade nasan ta dalilina wasu suna chan a wulakance ina ganin duk wannan abubuwan da suka faru dani alhakin sauran......saukar marin da yaji a kumatunsa ne ya dakatar dashi daga maganar da yakeyi ya dafe cheek dinsa,dad ne ya sake kai masa marina 2 a fusace wannan karon mom tai saurin rike hannunsa tace haba alhaji har ka yarda da maganar da deen ke fada karka manta fa hauka yayi be dade da samun sauki ba baka tunanin duk cikin ciwon nasa ne

"Babu wani ciwo dama na dade ina zargin deen tun a gadon asibiti hankalina ya kasa kwanciya da deen,ashe dama yaron banza ne kai bansaniba?ashe dama baka da tarbiya kuma baka tsoron Allah?deen ka yaudareni kuma ka bata sunan zuri'ar gidan nan bazan taba yafe maka ba Allah ya...........da sauri sadiq ya tsuguna gaban dad idonsa cike da hawaye yace dad wallahi duk abinda kaga ya faru nine sila,nine na batawa deen rayuwarsa duk abinda deen yayi nine nan na sashi don haka babu wanda ya dace kayiwa Allah ya isa seni dad,deen bashi da wani lefi nine nan na sashi saboda yardar da yayi dani
Na rokeka don Allah ka yafewa deen ko ze fara ganin haske a rayuwarsa,sosai sadiq,deen da mom ke zube a gaban dad suna rokon yafiyarsa....ransa a bace ya saka takalmansa ya fice ya barsu zube a kasa,da sauri mom ta mike ta bishi

"Cikin kuka sadiq yayi hugging din deen sukaci gaba da kuka,sadiq naci gaba da rokon deen gafara

"Sai da akayi kwana 5 tukunna aka shawo kan dad din deen ya yafe masa,gaba daya zaune suke a palour junior deen na hannun deen yana wasa dashi

su kuma su mom da sadiq suna watching movie....knocking door aka fara a hankali sadiq ya bude kofar don ganin waye ke bubbuga kofa haka.....police officers ne fiye da shida kowanne hannunsa dauke da bindiga sai wani babban mutum guda 1 da wata budurwa....daya daga cikin police dinne ya nuna I.D card dinsa sannan ya kalli yarinyar da take tsaye yace mata yana ina?hannunta na rawa ta nuna deen daya saki baki yana kallonsu.....ransu a bace suka nufo deen da ankwa a hannunsa suka ce "you are under arrest"

"What?how dare you?ku suwaye da zaku zo ku tafi da yarona?me yayi muku?mom ce tsaye tana huci take yi musu tambayoyi......ajiyar zuciya daya daga cikin police din yai yace ranki ya dade wannan yaron ana zarginsa da yin kisan kai on 27th may 2018,sannan yayiwa wannan yarinyar sumayya yar gidan Alhaji ba wargi fyade on 18th july 2018

"Innalillahi wa inna ilaihir raj'un,,,haba officer kisa fa kace,taya deen zai kashe mutum da hannunsa?

"Yanzu ba lokacin bayani bane ba idan munje court duk se kuyi bayani domin ranar da akayi kisan kan muna da tabbacin deen ne ya dauki yarinyar kuma ba'a wuce awa 2 da daukanta ba muka tsinci gawar yarinyar ajiye.....

"Karya kukeyi wallahi karya kukeyi tsinannu,babu inda kuka isa ku tafi dashi....dad ne ya karaso fuskarsa dauke da murmushi ya mikawa police officers din hannu suka gaisa sannan ya kalli mom din deen yace haba hajiya ya kike abu kaman wata jahila,taya zaki tsaya gaban hukuma kina sa'insa dasu akan abinda baki da tabbaci dashi,sannan ya kalli officers din dake tsaye yace zaku iya tafiya dashi

"Haba alhaji taya zaka barsu su fita dashi kanaji fa cewa suke wai yayi kisan kai,wannan ai zubar da mutuncine,karka manta fa we are rich kowa yasan family din modibbo yanda mukayi suna a duniya taya zaka bar yaronka tilo ya wulakanta a idon jama'a

"Murmushi dad yayi yace shine ya fara wulakanta kansa don haka ni ban isa inja da shari'ar Allah ba.....yana gama fadar haka ya fita daga gidan idonsa na zubar da hawaye....wannan shine karo na farko da mom ta taba ganin hawaye a idon dad din deen

If you are little confused with this chapter,just go and read the first chapter of this book i mean chapter 1.

Thank you for reading my story!
Lots of love
From maman hanan❤

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top