3

*Damar Karshe*

*Neeshar*

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

Page 3

Bayan sati daya da maganar Malam Audu sai gashi ya fara zuwa zance ba kunya ba tsoron Allah, ana idar da sallar isha sai ga abba ya shigo gidan kamar yanda ya saba ko zama bai yi ba yace ma ummi ta tura Suhaima malam Audu na jiran ta kuma karta tsaya bata mishi lokaci cike da takaici ummi ta fice daga dakin, sallah ta samu suhaima nayi ta jira har ta ida ta gaya mata sakon Abba kuka ta fashe dashi ummi tace "hakuri zakiyi ki lallaba ki tafi karki barshi yana jiran ki" cikin sheshekar kuka tace "to ummi amma dan Allah ki kara yiwa abba magana" tace "Insha Allah" ko hijab bata canza ba ta fice fuska a kumbure, malam audu kuwa na ganin ta ya fara washe baki kamar wani sakarai har kasa ta duka tace "baba Ina wuni" dariya yayi yace "haba sahiba wane irin baba kuma tashi abunki" mikewa tsaye tayi ta rakube jikin bango kanta na kasa sai hawaye take zubarwa, goron dake bakin sa ya furzar kafin ya fara magana "nasan ba sai nayi miki dogon jawabi ba tunda shi malam Abbas ya riga da ya gabatar dani a gurin ki to abunda zance kawai Allah ya miki albarka da kika karbi wannan tayi nawa kuma kika yiwa mahaifin ki biyayya lallai kin cika 'ya ta gari da ko wane uba zaiyi alfahari da ita, kuma Ina so dan Allah ki saki jikin ki dani kar kiji komai ni mai son ki da Kaunar ki ne Allah ya nuna mana lokaci  musha biki dan bana so bikin ya jima" ita dai ba tace masa komai ba har ya gama soki burutsun shi ya tafi ta shige gida,wani zazzabi taji yana neman rufe ta da kyar tayi sallama cikin gidan saboda ummi tasan ta dawo ta shige daki. Bayan Abba ya kwanta ummi ta fito zuwa dakin Suhaima dan taji ya sukayi da malm Audu ko da ta shiga kuka ta samu tana yi  sai ta nema guri daga gefen katifa ta zauna nasiha ta mata mai ratsa jiki ta mata akan hakuri da daukar kaddara yanda tazo mata bayan nan kuma ta tambayeta yanda sukayi da malam Audu, bata boye mata ba ta gaya mata komai, jinjina lamarin malam Audu ummi tayi tana ganin kokarin sa na rainin wayo dashi ne ai bazai fara ma yar sa haka ba.
    Bayan fitar ummi Suhaima ta kwanta tana tunanin yanda rayuwar ta zata kasan ce tunda Abba ya fara mata maganar aure walwala da farin cikin ta suka ragu a cikin gida sai gashi kuma zuwan malam Audu gaba daya tayi bankwana da dariya ta koma kuka daya zame mata jiki yanzu, bawai bata da masoya ba aa Kawai dai halin samarin yanzu ne ba son tsakani da Allah bane a ransu duk wanda ya samu dama so yake ya taba jikin ka ita kuwa abunda ta tsana kenan, saurayin da tayi na karshe kuma sunyi alqawarin aure amma ya tafi service shi yasa ta daina kula samari duk da dama ita bawai ta cika kulasu bane, gashi abba bai san da zaman sa ba tunda ba'ayi magana da magabata ba. Da taga kukan ba abunda zai Kara mata sai ta mike ta cire hijab dinta ta linki  ta ajiye kawo wutar da akayi ne yasa ta ciro uniform dinta na islamiyya ta goge ta ajiye kafin ta saka charge din wayar ta ta kashe wuta ta kwanta.
     Washe gari da safe ta tashi tayi aikin gida kamar yanda ta saba, bayan ta gama ta daura ruwan zafin wanka dan bata son ruwan sanyi komai zafi kuwa, ummi data gama hadama abba breakfast kuwa ta kai mishi ba jimawa sai gashi ya fito cikin shiri zai fita, cikin isa da dakakkiyar muryar sa ya kwalama Suhaima dake shiryawa Kira, da sauri ta saka hijab dinta ta fita, fuska ba walwala yace "malam Audu yace baya so biki ya dade dan haka ki fara shirin barin gida bana tunanin bikin zai wuce wata 3" ba tace masa komai ba yace "ko baki ji bane" tace "to abba" daga haka yasa Kai ya fice daga gidan. Daki ta koma jiki a sanyaye ta cigaba da shirin islamiyyar ta bayan ta gama ta fito ta shiga dakin ummi ta mata sallama ta tafi.

✘Ø✘Ø(❁º◡º❁)

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top