prologue
_*♡BAKANDAMIYA*_
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_
BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
PROLOGUE:
Sau tari akance tsanar mutum shine abu mafi sauki da xuciya take saurin iyawa,kuma na yarda da hakan sosai,nafi minti sha biyar ina tuki going round the town for nothing, just thinking abt my horible past relationship da saurayi na khalid waxiri.
Tsana ce wanda bantaba tsammanin zan na jin shi araina ba,suddenly i almost hated the guy so so much musamman in ina tuna good times da lovely memories da mukayi sharing tare, bayan na gama tuna hakan kuma sai in tsinci kaina dayi ma zuciya ta tambayar toh meyasa ma muka rabu bayan mun dace da juna sosai?Kullum in nayi tunanin haka sai kuma inji na tsane shi,well,for sure..hakan yana nufin,.har yanzu ina mutuwar son shi kenan.
Tsakani na da khalid is a now a love-hate relationship but apparently nina ke jigila da nauyin tsanan araina,i knw im not an idiot, when he apologise to me many times akan abunda yayi min a last dinner and award nite na gama jami'ata deep down within my heart na fahimci cewa har yau khalid yana so na sosai sai dai ni bansan ko zan iya dawowa inso shi sosai kamar da can ba..
Wata na biyu kenan da rabuwa dashi,its alot more easier for me to cut him off sabida kammala makarantar da nayi so kullum ina gida abu na,sai dai har yau nakanji kewar soyayyar mu da khalid araina sosai,that tragic little bit of love nd feelings da kowacce ya mace takanji akan saurayin data rabu dashi,now what scare me more is Nasan duk sanda mukayi idanu biyu dashi i can surely fall for him again,as much as i hate him, ive loved him with all my heart,now zanso na tsakura muku labarin abunda khalid yamin ranar dinner da award nite.
My boyfriend khalid Aliyu waziri is a correct hausa fulani boy wanda daga kallon yanayin shi kawai u can tell he is from katugum zone,khalid ya iya
Daukar wanka da saka tsadaddun accesories,ga ego,ga buzz,ga nuna iyaye suna da uban kudi da connection harkan politicians da gwamnati da uwa uba sarauta,ga son hawa mota da kashe ma yan mata kudi,khalid's life style was so xtreme at this level sabida shi dan gidan shaharraren dan kasuwa kuma wazirin misau ne.
Khalid yana bala'in ji dakansa Wani bin nikaina yana yi min mulki da dagon kai,sumtimes i do wonder what if baban shi ne sarkin misau din dakan shi dame zai faru kenan?So,Despite his egocentric boastful lifestyle Soyayyar mu da shi bai taba samun wata matsala ba dan tun ina aji daya muka fara son junan mu amma bamu taba samun wani tangarda ba saida nazo kammala karatu na.
Lokacin dana zo level one a universityn Abubakr tafawa balewa bauchi khalid shikuma yana level 3 yana karanta petro_chemical engineering,to ni irin doguwa fara mayya ce din nan at first he choose me to match his personality a matsayin shi na babban yaro da ake jin su a fadin jamiar
Amma daga baya soyayya ce mai qarfi ta kullu a tsakanin mu,We have our normal ups nd downs amma
Abu daya ne bazan iya taba kushewa acikin halayar khalid ba,kuma shine wannan halin nashi na being a man of his words,kuma dama duk mutumin daya kasance mai magana daya a ko ina yake kimar sa kullum a karuwa take bazata taba raguwa ba.
So He earn alot of respect sabida wannan halyayyr nashi,in yace zaiyi abu to fa saiyayi in yace baxaiyi ba to bazai taba yi din ba,i was his only girl friend har ya kammala makarantar kuma i can swear i was so sure of it baitaba hadani da wata ba.
khalid ya gama nashi karatun lokacin ina kokarin shiga level 3 am a student of industrial design,so bayan ya tafi gida sai kowa yay zaton daga nan soyayyar mu zatayi sanyi amma to thy bigest suprise sabida ni khalid ya dawo zaman cikin makarnta 247 muna tare,daga nan aka cigaba da debar zazzafar soyayya
,my 300 nd 400lvel was a total blast sabida yadda khalid yake bala'in karramani,ya siya min wannan ya siya min wancan,har na manta ya ake siyan handout bare yin assigment,ko wani school tshirt in ya fito mai suna na za'a fara kawowa
Kuma zai tabbata ba'a hada design din nawa dana kowa ba,material din da akayi nawa kullum mai tsada ce,khalid yana daga min aji sosai,dadin karawa dama yana daya daga cikin manyan sponsors da oganisers din duk wani social event da akeyi na nishadi ko karramawa a makaranta,shiyasa duk wani award nite,dance nites,movie fair, dinner,get to gether duka dai bana missing,da ni dashi sau biyu ana bamu best couple ward and that means alot to me.
Kwasam Allah ya kawo ni 500 level shekarar da zan gama karatun nima.
Mukan yi maganan futuren mu tare amma khalid bai taba jan maganan har can can ba,rana daya kawai ya fara tahowa bakin hostel dinmu waje na da wata yarinya,she is almost my agemate yayi introducing dinta as "sister sa"nikuma yayi mata introducing dina as budurwanshi,yarinyar tana da cikar zati ko inanta a murmure yake sai dai bayan nan bata fini da komi ba
Yace min sunan ta Aysha waxiri,so i was quickly convince that yar uwanshin ne,daga baya daya nace da zuwa hira wajena tare ita sai abun ya bayyana min cewa ashe ita causin sister shi ba asalin
blood sister sa ba,i got that information frm her Id card data manta a inda muka zauna mukayi hira i also learn that she is a nurse,an rubuta sunan ta as Aysha ibrahim waxiri,
kenan akwai banbancin sunan uba tsakanin ta da khalid,so i tot the aysha waziri thing she is using in public might probably be a family tag badon a boye min komi akace min haka ba.
Wasa wasa Sabida yarinyar nan Trout my first semester a 500 level bangane kan khalid ba,toh kullum tare da ita suke zuwa waje na hira,she is alwys with us kamar handbag kuma duk abunda zamu fada sai dai mu fada agaban ta,in na matsu kuma sai dai na jira in gaya masa ta waya,then, ban dauki abun araina da wani fassara ba gaskiya,sabida nayi bala'in yarda da khalid kuma ina matukar kaunarshi har cikin raina, Haka dai nayi fama dasu har nazo naji kamar nafara Jin sudden feeling of irritation in naga fuskar yarinyar,ita dai bata cika surutu ba,but she is so attentive akan duk wani furucinshi da motsin shi,rana daya sai naji na fara jin kishin yadda take datse hirar mu sai tace yaya khalid dare yayi mutafi gida shikuma bazai kara 1 min ba sai yamin sallama su wuce,hakan yasha faruwa inajin haushi
Kawaye na sukayi caaa akaina sukace kawai ince masa ya dena zuwa da ita kurum, ko kuma ince masa ya rage zuwa da ita gaskiya ana shiga hakki na
Da kyar na iya furta ma khalid hakan baikuwa damu ba sai ya dena zuwa da ita kwata kwata,after then kwana biyu sai naga baizo waje na kwata kwata ba,sam abun baimin dadi ba sabida nasaba babu ranar da baya zuwa waje na arayuwar shi,it was so unsual of him,dayazo na tambayeshi ina ya shiga he gave me sum silly excuses yace min wai yana tare da aysha ne awajen aikinta just like that.
Naji babu dadi araina but i ignore it gods knws harda irin makahon son nan inayi ma khalid
2nd semster Na fara batun project dina,sai naga khalid bai taimaka min kamar yadda yasa ba again,kawai na share na masa uzuri atleast nasan ai yanamin din,but thing get woser evry day,a hkli ahnkli ya dena min komi musamman wayanda ya saba min wanda basai na tambayeshi ba,sai dai fa duk wayanan change of character nashi bai dame ni kamar abun da yake min na kullum in yazo hira waje na,yanayin 2 mint zaiyi waya da aysha daga nan sai yace min shi wajen ta zaije saiya tafi
Abun nan yay ta damuna araina,so Ana daf za a manna mana final year time table khalid ya yanke kafarshi,as usual he is alwys with aysha kawai exam tension da kishin da na dade ina dannewa sai ya fara fitowa fili.
Daga na fara mishi complain sai yayi ta ban hakuri yana jadadda min yar uwanshi ce fa,kuma worst part zamuyi magana yau gobe bashi zaisa inga canji ba,kawai sai naji na fara yin sanyi raina ya fara dagulewa da lamarin su,har nagama final exams khalid bai sani ba that really hurt me.
So i started acting cold with him dake yanzu ta waya muka fi gaisawa kullum cikin rarrashi na damin alkwarin zaizo zaizo amma abu kamar wasa ba khalid bai zo waje na ba,kuma gashi lokacin anata shirye shiryen final year dinner da award nite dinmu,khalid dina ne kuma sole sponsor na duk wani award din da za'a bayar a daren ranan,Bani kadai ba inaga kaf schll din mu ansaka ran yau dani dashi zamu karbi another best couple award with pride na barin ma makarantar tarihin soyayyarmu.
But to my biggest shock sai naga ko ranar final year rally an raba ma kowa customized tshirt da akayi ranar ni ban samu ba.
Na kira khalid inji ya akayi haka sai yacemin,ai ya siyamin nawa sai dai kafin ya kawomin aysha ta karba ta raba ma kawayen ta so nayi hakuri,tunda na datse wayar nake tambayar kaina shin aysha yar makarantar mu ne koko kawayen ta yan makaranr mu ne?that day my face was red with anger sai ban sake kiran shi ba.
Bayan kwana biyu daren award nite ya gabato,da naga bai kirani ba saina danne pride dina na neme shi,bugu daya ya dauka muka gaisa but bayan nan da kyar na same attention dinsa da alama yana wajen shiryen shiryen dinner ne kuma haka yazo bai neme ni har sai washe gari da safe
,Saina nuna masa banjin dadin new beharvirs din sa kwana biyu i went straight ahead to pour out my heart musamman akan tarayyar sa da aysha sai yace min inyi hakuri zaizo yau da yamma kawai ya same ni a bakin hostel muyi magana
So later that evening,hostel dinmu was filled up
Da yan matan going up and down kowacce tana shirin zuwa dinner wasu na make up wasu na gushing akan dinner outfits din mutane.
Komi nawa is ready amma sabida hanklina ba akwance yake ba sai babu wanda ta gane kaina
Ina idar da sallar magrib wayata tayi kara,my heart skip a beat dana ga khalid ne ke kira,babu shiri na kara a kunne yace min gashi nan a kofar hostel dinmu in fito.
Tsabar na matsu in ganshi muyi magana akan damuwar mu yau ko yar kwalliyar banyi masa ba kawai na karkade hijab din jikina na fita waje na same shi.
Muna fara magana A bugu daya Khalid ya fahimce kishin aysha nakeyi sosai,
Kawai Sai naga ya fara kame kame kamar yana so yace min ma kar inje dinner ne na hakura,but he was not clear,ni bansan meyasa yaketa lallabani yana ban hakuri ba,yasan dai bai isa yamin karyan cewa bazaije ba dan nima inche na hakura bazanje ba dan kowa yasan ba'ayin wannan hidimar sai dashi,Can dai na hade rai na datse dramar sa,sai na gaya masa cewa lallai fa tare dashi yau zamushiga hall din nan as romantic couples yadda muka saba,sai yace min eh to ya amince zaizo dakanshi ya dauke ni anjima a motarshi amma da abokan shi zaizo nace ok ba matsala.
I was bit relieve ina shiga daki na kira make up artist dina tazo aka cancanda min wani irin sasaanyar make up cat eyes din ya tsaru,ga wani uban contours da shimers evrything on ma face was on fleek nayi bala'in kyau,i was the talk of the nite tun ma bamu fita ba.
Na saka wata shegiyar flowing satin neck mai exagerrated bows at the neck kamar wacce za'a bani gramy award.
Time na cikawa saiga kirar khalid nayi ma girls din daki sallama na fita waje,sai naga khalid din shima agaban motar sa yana dan latsa wayar sa da alaman yabar mutane aciki ne ya tsaya awaje yana jiran fitowa ta.
A nitse nake tahowa anata kallo na tsabar kyaun danayi,so i was xpecting an extra odinary xclamation frm the love of my life sai naga ma kamar shi bata nan hanklin shi yake ba
Is asif bai ma kare min kallo ba,kawai naga yajani gefe wai xamuyi wata magana,xuciya na atake ya shiga bugawa nace khalid Lpya kuwa?sai bai boye min ba kai tsaye yace min
Su uku ne a motar sukazo da shi da best friend dinshi
Abba,da aysha.
Nace wata aysha?
Yace min sister sa aysha waziri,daga jin hakan sai ban kara furta masa komi ba na dauke kaina na hade raina sosai,atake Khalid ya riko hannu na cikin nashi ya marairace min fuska yanata kallo na da fuskar tausayi
Yace Im sorry babe dan Allah ki fahimce ni dama Wani alfarma nake nema awajenki dan Allah kiyimin wannan alfarman nasan zakiyi min baby na.
Sai naji wani irin tsoro daya furta hakan cos My heart was sinking with fear on it own batare danasan meyasa ba,kawai sai na daure nace masa ya fadi damuwar shi inji.
Nan yayi gyarar murya yace min
Yana so first of all in mun shiga motar na xauna a seat din baya tare da abokinshi Abba
Ban barshi ya idda maganan ba nace masa akan me?sai wa kenan ya zauna dashi a gaba
Sai yace min aysha ce take zaune awajen kuma baya so ya dagata.
Sannan dan Allah idan munje hall i shud please and please pretend to be with his friend Abba
Sabida shi zai shigo ne tare da aysha danya nuna ma jama'ar sa ayshan itama asanta.
"Hannun sa na ture da karfi,then ,
I said No...Da zazzafar sautin muryan fushi nace masa bazan yi masa hakan ba wannan ai rainin hankli ne.
Yace min not all,kawai alfarma yake nema after today ya rantse da Allah sai abunda nake so zai aikata game da aysha.
Naki sam amma haka ya lallabani muka shiga motar,shegiyar tana kime a gaba kusa dashi yau dai ko gaisawar fatan baki bamuyi ba she was pretending to be busy with her phone,Abba ne ya rinka yaba kyaun danayi while i was boiling inside.
Muna isa wajen evrthing was hot hot
Wayyyo haduwa iya haduwa,kamar yadda mukayi da khalid sai naga yaja hannun aysha nikuma na fara bin abba abaya muna shiga cikin mutane ana raha,Altho i was not my self.
Duk hanklina nakan su duk inda sukayi idanuna nakansu,
karku manta soyayyar mu was very popular so duk inda na tsaya sai antambaye ni shi
Duk da cewa ina tare da abokinshi abba amma Maza musamman baki dayawa sun taya ni amma haka naki na amince da kowa
Finally arand 11pm angama gulmace gulmace anci abinci anyi rawa award ya dau zafi,nidai babu walwala a fuskata cos i almost run out with tears dana ga har angama colecting nominess na wayanda zasu karbi award din amma babu sunana aciki,then aka zo bada award ma let say king of the night,Mc ya ce idan ya kira sunanshi then budurwanshi zata fito fili ta taya shi karba,kawai saiga khalid yayi xcusing dina waje.
He was bit nervous amma haka nan dai Yace min wai yasan wa shine za'a bada award din,so pls in an kira shi saman stage i shud pleaseeeeeeee let aysha be on that stage with him,cike da mamakinshi
Nace sabida me bayan kowa yasanmu tare?yace min kawai inyi hakuri kawayen aysha sunzo wajen ne kuma bayaso ya bata kunya in hau stage din tare dani
,inajin hakan kawai sai na fashe mashi da kuka,Murya na rawa rawa nace khalid baka taba walakanta ni kamar na yau ba meye na maka da zaki nimi ka walakanta ni?
Shiru yamin baice uffan ba yanata kallon yanayi na,
Im burning with jelousy and strange pain of betrayal.
Nace Rainin hankalin daka min kasa wata agaban mota ka hada ni da abokin ka inata bibiyar shi kamar budurwashi bai isheka ba sai kayi humiliating matsayi na awajenka sabida wasu?Yace min ai alfarma yake nema,yaune kawai,kawai in bazan yi masa in fada mashi.
Ganin duk wajen anata satan son gano halin da nake ciki yasa Nace
Masa yaje kawai yayi abunda yay niyya sai nayi sauri na goge fuskata na shige cikin hall na tsaya tare da abba bance komi ba.
And That was the moment i face the worst humiliation of my life.
Inda wajen ya dauka da shigowar khalid da aysha waziri,MC was bold enough to be calling her amaryan mu and all that flattery,ita kuma tana nanike agefen shi tana wani takun ta na barazana
Ina tsaye ne kawai amma gaba daya kafana shaking sukeyi dankansu
Mutane dayawa na zagaye dani anata raha amma banajin komi daga xantukan su,cos Daga gefe gefe inaji ana rade raden wai fa anyi baikon khalid da aysha waziri,wai ita zai aura.
Little did i knw that duk gayun dake wajen da tsirarrun yan matan sunsan da hakan,da alama nice kawai ban sani ba,Kyakkwar soyayyar su suka kwasa agaba na,the whole dinner cake na dinner dashi da ita suka yanka sukayi feeding juna anata hailing dinshi anacewa ango ango..
Lokacin har xuciya ya ficcike ni na fita waje na buya abayan motar wani bawan Allah inata kuka sosai basu lura ba,i was shocked and chocked frm evrtying that just happen,numfashi na ya fara sama sama yana barazanar daukewa.
Kawata kuma bunky na wato maryam yar sokoto ita tafara fitowa nemo ni danta fi kowa sanin yadda nasa khalid araina,ta same ni da kyar a mawuyacin yanayi,rarrashin duniyar nan tamin amma nakasa rarrashuwa i kept asking her out of confusion and pain inata cewa "meyake faruwa ayimin bayani,later later ta jani mukabar wajen saiga abba ya fito nema na shima,ya same mu awaje mun zauna akan wani chair tare da maryam tana kan bani baki,daga ganin yanayi na sai jikinshii Yayi sanyi.
Haka na rinka rokonshi ya fayyace min meke faruwa amma yaki sam saida maryam tayi diri ta fara masa barazanan zataje ta tambaye kawayen ayshan sai ya fara bamu labari altho atakaice yafada kunsan rufa ma juna asiri irin na maza
Yace min confirmed khalid yana soyayya da aysha,sai ya harhado karya dai bai cemin komi akan batun auren sun ba,yana ta babatu mene menenshi yana so lallai insa araina hakan ba wani abu bane,yace min ai aishan tasan ni girlfriend dinsa ce but she is ok with it kawai nima nayi hakuri,yace dama wai khalid yayi mata alkwari ne ita da kawayenta akan yau shi nasu ne su kadai shiyasa ma bansamu lokacinshi ba for sake of kar ya kunyatar da aysha agaban kawayen ta yasa duk yayi hakan.
Aikuwa Muna cikin maganan sai kuwa gasu nan sun fito su hudu,ayshan ita daya a gefen daman shi sai kawayen ta su uku agefen shi na hagu sun jeru
Khalid ya ganmu sarai but He wanted to pretend kamar bai ganmu ba sai da Abbah ya daga masa hannu sannan ya tsaya,bai dai karaso ba daga wajen yace masa wai sauri yakeyi zai kaisu gida kawai sai gobe zasu hadu,thats how ya dauke kansa,nd he left with them kamar bai taba ganin wata mai irin kamata a duniya ba
Daga nan dai I dont
Actually knw what happen to me,sai washe gari karfe 11na safiya dana farka na ganni kwance a school clinic an dauramin drip duk yan matan dakinmu ne akaina anzomin jaje.
And i also forget to tell you one thing which is My name
i am JADWA ABUBAKAR MARAFA.
*💫BAKANDAMIYA*
BY
SURAYYAHMS
*Assalamu Alaikum fanmily we are suprisingly Back ooo🥺*
Wasunku suna sane da cewa littafan kungiyar mu ce guda biyar zasu fito a wannan lokacin saidai unfornately hakan baxaiyu ba sabida wasu matsalan da aka dan samu,to cut the crap short my own story.
*BAKANDAMIYA*
Dana fara rubushi nace bari kawai in karasa muku so zai fito Shikadan shi
A COMPLETED COPY ACIKIN WATAN FEBRUARY DIN NAN INSHA ALLAH😍 SO GAME BUKATAR KARANTA COMPLETE SAI YA SAKA HIMMA WAJEN YIN BOOKING DINSHI DAGA YANXU AND DONT FORGET UR PAYMENT IS GONNA BE CODED OOO,FIRST COME FIRST SERVE THING😎UR DATE OF PAYMENT WILL VALIDATE UR ODER OF DELIVERY.
FARASHIN SA MAI RAHUSA ne
@1000 NAIRA
TA ACCT ONLY @ 0152983148
MOHD SULE SURAYYA GTB
THEN SEND UR EVIDENCE TO 09132352275
For proper delivery RECORD ND INSHA ALLAH NO DELIVERY WILL EXCEED WATAN FEBUARY
BUT INKA SAN U WILL BOOK IT AND THEN PRESSURE ME TO RELEASE IT TO U BEFORE TIME THEN LETS NOT START THE DRAMA NOW OO.
GA MARASA HALIN SIYAN COMPLETED COPY U CAN ALSO START PAYING UR FEES AT CHEAP SUM OF 500 NAIRA DOMIN A SAKI A GROUP DIN DA ZA ANA MUKU POSTING DINSHI AKAI AKAI KUMA A GAMA MUKU SHI A ADADIN KWANA ASHIRIN DA BIYAR.
FOR GROUP U PAY
500 VIA 0152983148
MOHD SULE SURAYYA GTB
OR MTN PIN TO 08060712446
THEN SCREENSHOT UR PAYMENT TO
08036651119
Or
08067224865
REMEMBER URE JUST BOOKING OO
💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top