x43&44
AURE UKU
(a hospital romance )
By chuchujay
wattpad :@chuchujay
https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j
Join My whatsapp channel inda Zan baku noorurrahman kyauta.
Yes paid novel ne amma Zan baku shi a channel ɗina kyauta,
Just follow and share ❤
Episode4⃣3⃣➡4⃣4⃣
TWO MONTHS LATER.
Jin alamun ana mata tafiyan tsutsa a tafin kafarta kamar a mafarki yasaka ta buɗe idanunta a hankali tana tunanin ko Abdallah ne 'dan tasan hallayyarsa ce,
Tashi tayi zaune tana tunanin 'dan bazan dukan da Zatayi masa cos taga alamun bai daddara dukan da yasha a gurin ta ba da safe,
Cike da bala'in da take ji a yanzu tace "Abdallah you're trying me again ba,"
Ga mamakinta kuma sai taga ko ina na ɗakin dim sannan babu alamun mutum a gurin,ɗan tsaki tayi tana tunanin irin jarabar da Za tayi ga Paki idan Ya shigo gidan cos tun 10 ta kwanta da ta gaji da zaman jiransa ,maganar abinci kuwa yanzu tama daina jiransa ,muddin bai dawo da wuri ba zata saka abincinta ne taci ta rabu dashi,
Wayanta ta jawo taga 11:59pm,
Ƙwafa tayi tace "Baby you're dead ,kazo gidan nan ka sameni,bari ma na kulle ɗakina idan ka dawo Ai kana da ɗaki zamu haɗe da safe,"
Saukowa tayi a kan gadon tana Mai saka takalmin da ke bakin gadon ta nufi kofar 'dan kullawa ,tana saka key ta juya dan komawa taga ɗakin baki ɗaya Ya ɗauki haske ,tsaye yake bakin switch ɗin hannunsa ɗauke da balloons guda biyu,bin ɗakin tayi da kallo taga ko ina is well decorated da roses wanda hakan Ya bata amsar inda take jin kamshin rose,
Daga jikin bango an rubuta HAPPY 30 WIFFY da decorated shining Papers,
Hannu tasa ta rufe bakinta tana Mai jin wasu hawaye na zubo mata lokacin da yafara Takowa yana Mai faɗin"Happy birthday to you,Happy birthday to you,"
Takowa yayi gabanta da balloon ɗin a hannunsa wanda yake daure jikin wani box Mai kyau ,buɗe box ɗin yayi yaciro wata diamond chain siririya Ya zo daf da ita yana Mai faɗaɗa murmushin sa Ya maƙala mata a wuya,
Kafun tace wani abu Ya jawo wani envelope Ya miƙa mata yana Mai faɗin "Happy 30 wiffy,"
Washe baki kawai take kamar wata wawiya kafun ta buɗe envelope ɗin da zumuɗin dan ganin menene cikin ta,
Paper ne guda biyu ta ciro,a hankali tafara karanta na farkon ,property ownership ne na asibiti Mai suna UMAIMAH PRIVATE HOSPITAL,
Da mamaki take kallan paper kafin ta buɗe ta biyu Mai ɗauke da yarjewa na lasisin Buɗe asibitin,
Kallansa tayi tana Mai san saita kanta da kuma tabbatarwa da kanta abunda take zargi,realization ne Ya dake ta lokacin da ta tuna ya karbi Blue print na asibitin ta ,sannan duk lokacin da tayi masa maganar asibitin zaice mata ta bari tukunna wanda cikin yimasa biyayyah ta bari ɗin,
Rungumesa tayi tana Mai fashewa da kuka tace "Baby dont tell me this,"
Shafa kanta yayi yana Mai kissing saman kanta yace "yes wiffy asibitin ki Ya kammala da duk wani abu da kike buƙata a cikin sa abu kadan ne Ya rage ,im just Happy cos na samu na mamaki wannan birthday surprise ɗin da nake mutuwan san na miki,
Raba jikinta tayi da nasa tana Mai kallan cikin idanunsa kafin ta taba Chain ɗin dake wuyanta tace "Bansan wane Aikin lada ba nayi da yazama Allah ya mun kyautar ka,
Imagine wannan babban gift da ka bani wanda ban maka ko kwatankwacinsa ba da birthday ɗin ka ba
Mai zanyi idan babu kai?
Mai zanyi na saka maka na faranta maka?
Hannunsa yasaka ya shafa cikinta yace"wane Ya faɗa maki baki bani kyauta Mai muhimmanci ba,kyautar da kika bani tafi komai muhimmanci a rayuwata ,sannan yana ɗaya daga cikin kyauta mafi girma da aka Tab'a bani,
Aurena da kikayi umaimah kyautace da Allah yayi mun babban bayan kyautar rayuwa da lafiya,sannan mayar da yaranki nawa da kikayi shima gagaruwamar kyauta ce da kika mun,
Dan ɗukawa yayi yace sannan kuma gashi nan rabona a jikinki,
Mai kuma nake nema nikam a rayuwa bayan nayita kasancewa Mai yin kaunar ki da kuma yiwa ubangiji ɗumbin godia,
And yes kafun na manta abinda zaki mun daya ne yanzu da nazama broke Kina buɗe asibitinki Ya zaman nine employee na farko i want to work under you.
Sake rungumesa tayi tana Mai dariya cikin kuka tace "Allah Ya saka maka da Aljanna mafificiya sannan Ya bani ikon faranta maka ta ko ina mijina,"Sake rungumeta yayi yasa bakinsa dai dai kunenta yace "ɗan fara faranta mun tun a yanzu mana Masoyiya ,cos yunwar da nake ji a yanzu taki ce,"
Dan dukan kirjinsa tayi tace"nasan baka ci abinci bama ,bari naje na sake maka warming,"
Sake matseta yayi a jikin sa yace "ni bana wani Jin yunwa i told you naki nake ji feed me baby,
Smooches tafara bashi a wuyansa kafun kuma ta bari tana ɗan kallansa tace"hey ina goruba ta,"
Ɗan bude baki yayi yace *oopz yana mota kinga na manta ko?
Bari naje na ɗauko maki,
Ya juya zai fita ta kamosa tana Mai kashe masa ido ɗaya tace "'dan baba yanzu ba guriba yake so ba ganawa yake san yayi da daddyn sa so come here,
Licking lips ɗinsa yayi Ya ƙarasa gareta yana yin sama da ita.
*******
Cikin Abubuwan da suka faru a watan shine tashinsu daga gidan su Paki suka koma gidan da Paki Ya daɗe da tanfatsa mata wanda aka kashe maƙudan kuɗi akai da idan ka kalla zaka fara tunanin anya babu taimakon mahaifinsa?
Abun guda ɗayane wanda paki baya wasa da, duk kuɗin da yake samu gurin mahaifinsa kasancewar shi ba mutum ne Mai shashanci ba,
Baya shaye shaye sannan baya neman matan banza,kuɗin kuma da yake samu daily bukatunsa sun masa yawa cos yana da mahaifinsa for wanann sannan ga hamma osama ma Ya cigaba da b'atasa 'dan haka yayi tunani Mai kyau wajen saka kuɗaɗensa a kasuwa wanda ko mahaifinsa da yake jin abubuwan da Ya mallaka yayi mamaki sannan yayi alfahari dashi ,
Kuɗinsa na iyalinsa ne 'dan haka yayi ƙokarin fara gina masu mahalli,
Yasan cewa babu kuɗin da zai nunawa umaimah Ya burgeta ,amma 'yaci alwashin hanata kashema kanta da yaranta kuɗi muddin yana dasu cos Alhamdulilah yana da kuɗin,A cikin gidan ko wanne yaran da ɗakinsa ,hatta Nameer da bai zo ba lokacin da suka koma an gyara masa ɗakinsa da duk wani abu da zaya buƙata idan Ya dawo haka zalika gurin shatuh wadda Paki Ya ɗauka kamar ƙanwarsa ta jini ,
koda Nameer yazo yayi Tunanin bazai ƙarbesa ba duk da yasan da Auren amma ga mamakin kowa sai gani sukayi wani irin bond na shaƙuwa Ya hab'aka tsakaninsu ,
Shaƙuwa tsakanin sa da yaran baki daya bazakace wai na umaimah ne kaɗai ba,
Soyayya kuwa babu irin wadda Umaimah bata samu gurin Paki abun sai wanda ya gani duk da kuwa dama zaman Aure zo mu zauna zo mu sab'ane amma sabanin nasu Mai irguwane,
A lokacin da paki yasan umaimah na ɗauke da cikinsa kamar zai zuba ruwa a ƙasa yasha 'dan hatta Abbu baiyyi kunyar faɗawa ba 'dan a yanzu sun gama sanin akan umaimah Ya daina jin kunyar kowa,
Duk da cikin umaimah rigimammen cikine hakan bai taba sawa Ya sare da ita ba ko Ya nuna mata gazawa ba Illa ma wata sabuwar ƙauna da yake nuna mata da kulawa wanda a cikin asibiti ma har sun haƙura da gulmar,
Akwai ranar da ta tubure masa akan abincin baƙar mace take sanci ,kuma bana kasuwa ba a dangi take so,haka nan yayi tabi karshe sai da Ya samu abincin bakar mace wanda tana loma ɗaya tace bata ci,shi abun ma dariya yake basa .
*
Washe gari tana tashi da safe ta tashesa tana Mai shafa masa kwantaccen sajensa,yana farkawa ta ɗaga masa gira ɗaya tace"Good morning Baby ,"
Cikin sexy hoarsely voice ɗinsa na safe Ya shafo fuskanta yace "morning Baby Mai ɗan baba yake so,"
Murmushi tayi na salan rigima tace "to 'dan baba dai yau Ya tashi da wata sabuwa dan wai tuwan shinkafa yake san ci miyar kuka,sannan wai 'fa kasan wa yake so Ya tuƙa?"
Kaɗa mata kai yayi yana Mai kwanto da ita kan kirjinsa yana Mai shirya rigimarta yace "sai Ya fada da bakin maminsa".
Ɗan turo baki tayi tace "to wai dai na tsofaffi yake so kuma fa wai tsohuwarma Nana,"
Dagota yayi Ya zaunar da ita yace"wiffy Nana kuma?"
Haɗe rai tayi tana mai turo baki tace"bazan samu ba kenan ?"
Shikenan koƙarin sauka take a gadan idanun ta na kawo ruwa,Kamota yayi yace"oh come o'n mana matan Paki,Mai zai hana ki samu?"
Kawai dai kinsan rigimar Nana ne yanzu ina Nana ina tuka tuwu,?
Goge kwallar dake zubo mata tayi tace"Allah Hubby ni dazan iya cirema kaina da na cire,ji nake idan banci tuwan hannun Nana ba kamar zan mutu".
Saurin miƙewa yayi yace"bazama ki mutu ba ,yanzu brush kawai zanyi naje yau Nana taga ta kanta".
*
Koda Ya isa gidan baki ɗaya yagansu suna breakfast,
Zama yayi bayan Ya gaida iyayen sa inda kannensa suma suka gaidashi,
Kallan Nana yayi wadda tunda ta amsa gaisuwarasa bata sake cewa komai ba ta cigaba da cin abincinta dan tunda suka bar gidan take jin haushin su,
Kallanta yayi bayan Afnan tayi masa arranging plate yace"Masoyiya Mai yayi zafi Haka nan naga kinata faman haɗe rai".
Murguda baki tayi tace"share ni ɗan nan,bana san kinibibi da neman ayi ,"
Shafa kansa yayi yace mai yayi zafi lailata ta,?
Haɗe rai takuma tace ni majnuni yana kasa ,Sannan shikaɗai yake da damar kirana lailah,
Lailarka na gida wadda ciki Ya fitowa a fuska.
Sai da yabi shaho yabi muzuru kafun Ya faɗi abinda Ya kawosa,
Miƙewa Nana tayi tace"kutmarkata'in nan,ni zan tuƙa tuwo da miya?"
Muntari kana ji ko?
Ɗankwalinta dake kanta ta kunce taci ɗamara tace "to wallahi koni ko umaimatu,wato rainin har yakai nan ko?"
Dole kazo kana kaɗa wuya kamar jangwalagwada saboda zaka zageni,to wallahi ahir ɗinku sai 'in mata shegen dukan da zaisa ta haihu wata biyu baku shirya ba,bani da mutunci 'fa,nima kwalluwar kaina ce,
Taci na habiba mana ko muntari Ya tuka,amma dayake nice karkataciyar kuka Mai daɗin hawa dole a hauni,to a dakeni na tuƙa,
Dariyar da Afnan ke rikewace ta ƙwace ,
Kanta Nana ta koma tace "naci uwarki yanzunan shegiya Mai Kama da mujiya ,wuya kamar mariƙin lema ,to wallahi nafi dalma zafi,"
Tana ƙoƙarin wucewa dakinta imam yayi saurin zuwa Ya kamo kafafunta yace"wallahi Nana da kaina zan shiga kitchen ɗin na taya ki, nayi alƙawari,"
Da kyar da tsomawar bakin kowa na gurin Nana ta yarda ta shiga kitchen ɗin inda Ya bita yana tayata yana kunshe dariyarsa musamman datana tuƙa tuwan,diban albarka kuwa babu irin wadda Umaimah bata sha ba.
Lokacin da ya kaimata tuwan sai cewa tayi Ai ɗan baba Ya fasa ci,
Dariya Ya fashe da ita yana Mai hango reaction ɗin Nana idan tasan cewa umaimah bataci wannan tuwan da Nana tayiwa laƙani da tuwan Alaƙaƙai ba.
*****
Sauranku last page oo🥱🥰
Zanci tuwan Nana dan Allah.
Chuchujay ✍🏽
Tbc.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top