x39&40

AURE UKU

               (a hospital romance )

                  By chuchujay

                wattpad :@chuchujay

https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j

Join My whatsapp channel inda Zan baku noorurrahman kyauta.

Yes paid novel ne amma Zan baku shi a channel ɗina kyauta,

Just follow and share ❤

Episode 3⃣9⃣➡4⃣0⃣.

    Tunda akayi abun sameera kenan kwana biyar Nana batawa kowa magana ba duk da kuwa yarda kowa Ya damu da hakan,

Kowa yayi yarda zayyi da ita tace wani abu amma taƙi koda ehem ne iyakacinta taci abinci tayi bacci ,

Sameera kuwa washe gari iyayenta sukazo suka wuce da ita ,duk da kuwa Sunji haushi sosai amma hakan bai sa sunce komai ba saboda tsoro sukayi gaba da ɗiyarsu da tayi alwashi kala kala.

    Zaune imam Ya tarar da Ummu tana kamawa Afnan gashinta,

Zama yayi kan kujera ya gaida ummu Afnan kuma ta gaida sa Kafun yace "ummu intee kuwa takira ta sauka"?

    "Eh imam mijinta Ya kirani dai amma bamuyi waya ba,kasan halinta idan tayi tafiya duk kankartarta ,Babu jirgi Babu mota,"

Murmushi yayi yace "intee rigima,yauwa talking about rigima wadda ta ƙirƙiri rigima fa har yanzu shiru?"

Dariya Afnan ta saka tace "kai Hamma wato yar kakarmu ita ta ƙirƙiri rigima ma"Kafun yayi magana Affan Ya shigo bakinsa dauke da sallama biye dashi kuma KB,

Ɗan haɗe rai Paki yayi yace "Ai wallahi KB nasan dai dai gurin da zan saka ka a rayuwa ta,"

Shigowa ciki KB yayi yana yar karamar dariya ,zama yayi yana Mai gaida Ummu kafun yace "Ummu kinji dai Mai imam ke faɗi ko,shi baida uziri ne,idan naje asibiti na dawo ba yar karamar gajiya nake ji ba sai naga dare ko yamma kai kuma Kana ango dole ne na ɗaga maka kafa."

    Da fara'a Ummu tace "aikuwa dai amma kam baka kyauta ba kabir ,imam Ai baida wanda Ya fika ,yakamata ma ace yanzu zuwan ka na ba adadi ma kenan amma tun ranar da kuka kai shi daki 'fa."

    Yanzu mai idan ba zuwa duba Nana ba bazuwa zaiyyi ba,

Imam Ya fada yana Mai mayar da kunnesa bangaren Nana dan kamar maganarta yake ji,

Ille kuwa yana sake nutsuwa Ya jiyota tana Mai fadin"Habiba,Habiba na matsu ,Habiba ina da uziri ko sai nayi a wando ne a tafi dani a baki?

Dariya Afnan ta saka yayin da Ummu tayi saurin miƙewa jin Nana taƙi shiru.

Kallan Affan Afnan tayi tace"Nana rayuwa kanaji dai sir manja yasa ta tayi magana dole,"Dariya Affan yasa yana Mai cewa "Nana mu shagali,Hamma kazo mu Kamota mu kawota falo taga mutane idan ta gama.

    Shafa kai imam yayi yace"aikuwa ma 'dan tsokaneta ma muji daɗi kasan an kwana biyu ba'ayi ba.

    Bayan Nana ta gama uzirinta imam Ya shiga dakin,haɗe rai tayi data ganshi,

Zama yayi kusa da ita yaga ta wani sassandare kafa ita a dole bata warke ba alhalin malam hadi yace ciwan Ya warke,

Hannunta Ya kamo yasa cikin nata yace "amarya ta yaya jikin"?

    Shiru tayi masa batace komai ba sannan bata kallesa ba,

Murmushi yayi yace"Ya tauraruwata Mai haskaka rayuwata,Ya madarar zuciyata,Ya tsutsuwar rayuwa ta Mai sa zuciyata tashi kamar balbela ,Ya sanyin idaniya kibiyar dake soke dukkan kososhin dake daddane mun zuciyata,"

Shesheƙar kukanta yasa shi yin shiru,joyowa yayi sosai yana kallanta yace "Nana mal kuma Ya faru?"

Cikin shesheƙar kuka tace "ka tuna mun da Mai tagiya ne,sak irin kalamansa kenan da yake mun nake bashi tibani a lokacin shege matsiyaci sai ji nayi Ya auri haulatu ƙwata ,shegen ashe yana mun wannan kalaman ne kawai 'dan na bashi tubani,ranar saboda tsabagen baƙin ciki saida na rabar da tubanin nan duka amma na daku,

Allah kadai yasa Ya walakiri Ya mayar dashi sabida zuciyata da Ya karya dan naji ance Ya mutu.

    Dariya imam Ya saka yana Mai dafa ƙafarta bai sani ba wanda hakan yasaka kwallara wata iri ƙara da ta jawo mutanen falon reto zuwa sashen Nana,

Saurin tashi tsaye imam yayi yana faɗin Nana Mai Ya faru Mai aka maki,

Kafarta ta fara nunawa tace "wallahi Ya kashe ni imamu dukar mun kafa yayi sai dai tace ƙas,"

Da mamaki imam yake kallanta yace "ƙas 'fa kikace Nana ,sai kace karas,wallahi tab'awa kawai nayi,"

"Dan ubanka kenan sharri na maka,shin wai ina Umaimatu ne ni yau duka batazo ta gaida ni ba,"

    Dariya imam yayi yace "ashe ma ba ƙas ɗin yayi maki ba da kike tunanin matata sanann kar ki sake kiranta Umaimatu sunanta umaimah dan Allah,"Zama yayi yace yauwa Nana tunda kin gama azumin maganar dama ina san fada maki ne idan kina san sashen chan namu zamu bar Maki 'dan mu zamu koma sabon gidan mu ne gobe dan An ƙarasa share share,

Kallansa tayi tace "tunda mayyace ni Ai sai na je na zauna naci kaina ,munafiki dama ao kake ka tashi ɗin ,Allah ya kiyaye hanya ,Ai Apan ya kusa Aure sai mu tare dani dashi da matarsa a CChan.

    "Da sauri Affan yace 'hello old woman ke dawa zaku koma sashen chan ɗin?"Kalli nan kar na kiyi ƙokarin zamar mun damuwa 'dan wallahi ko Aure zanyi bazan zauna gidan nan ba ,ni da kika ganni ma abuja nayi saboda ke,

    Ai wallahi yaro ƙafata kafarka idan kuma kaga ƙarya nake to kace a'a,

"Dake ma zai tafi hajiya Nana ki kwatar da Hankalinki,KB Ya faɗa yana Mai ƙarasa shigowa inda take,washe baki tayi tace "kayi Alƙawari Kabiru,"

Kaɗa mata kai yayi yace Ai bama sai nayi ba,

Washe baki tayi kafin ta sake cewa"wai ina Umaimatu ne"?

Kallanta Paki yayi yace "ikon Allah,wai nikam kar ki cinye mun mata mana"

Nana zata sake magana umaimah tayi sallama dakin hannunta ɗauke da bowl Mai ɗan girma a rufe,washe baki Nana tayi tana ganin umaimah tace "kabiru matsa ta zauna ,sannu ɗiyata sannu da aiki,hannu ta miƙe tana san ƙarbar bowl d'in,babu musu umaimah ta miƙamata bowl ɗin tana faɗin hankali umaimah,"Aje kwanon tayi gabanta tana Mai bude wa ,take kuma murmishinta Ya dauke tace "Umaimatu wai so kike ki kasheni da farfesun Ahalin kifi?"

Daga tarwada sai karfa sai sukumbiya sai ragon ruwa,gobe kuma Inajin kada zaki saka akamo ki dafa mun,ina dalili to,nikam farfesun rago nake so yaji tafarnuwa da citta da masoro.

    Ta bayanta Affan Ya koma Ya ziro hannunsa a hankali yana Mai saka hannu cikin kwanon,bai aune ba yaji ta buga masa mirfin a hannu tana Mai fadin "kaji mun mayen yaro,"Dariya suka saka baki dayansu lokaci ɗaya kuma ta tsaya sakamakon Nana da ta haɗe rai tace "kowa Ya tashi ya bace mun zanci kifi harda ke kuma Umaimatu kar kiga ke kika kawo,

A tare suka fita suna dariyar mood swings ɗin nana Atleast yau ta gama azumin magana,ansha ruwa.

****

This is All i can give you guys for now,im having mad headache due to stress insha Allahu you'll get more gobe idan Allah Ya kaimu

Kuyi hakuri da typing error na page dinan cos ban editing ba.

Chuchujay ✍🏽

Tbc.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top