x35&36
AURE UKU
(a hospital romance )
By chuchujay
wattpad :@chuchujay
https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j
Join My whatsapp channel inda Zan baku noorurrahman kyauta.
Yes paid novel ne amma Zan baku shi a channel ɗina kyauta,
Just follow and share ❤.
Episode 3⃣5⃣➡3⃣6⃣
BAYAN ƊAYA.
Tun ranar da umaimah ta bawa Paki labarin ta yake bata wata irin tarairaya kamar zai maida ta ciki 'dan gani yake babu irin soyayyar da zai nunawa umaimah ya isa,sannan yayi mata alƙwarin bawa yaranta kulawa irin wadda mahaifi zai basu,
Yaso ta dawo dasu nan amma tace masa a'a Ya bari tukunna sai sun gama da saga ɗin Nana cos tasan yanzu idan tace zata dawo da yaranta nan gurin to zaman bazai daɗi ba 'dan ko cikin satin ba karamin gwagwa suka sha ba.
Hutun sati biyu ta ɗauka wanda yanzu sati guda taci a ciki,duk da takurar Nana amma zata bada labarin ta Mai daɗi indoor tsakaninta da mijinta .
Kamar kullum yau ma wuraren 7 imam ya fita dan ko breakfast bai tsaya yi ba ,abinda Ya tsiri mata kwana biyu kenan sannan yaƙi faɗa mata inda yake zuwa 'dan tasan ba asibiti bane tunda tare hutunsu yake ,
Kiranta da yayi yace mata yana nan dawowa sannan yana mutukar jin yunwa yasata barin duk wani abu da take ta shiga kitchen 'dan sarrafa masa abinci,
Shigarta kitchen ke da wuya sameera ta shigo kitchen ɗin cikin wata irin karairaya jikinta sanye da rigar bacci Mai santsi iya gwiwa yayin da kirjinta ba bra kanta kuma babu ɗankwali,
Wata irin miƙa tayi tana Mai yin hamma kafin ta taka bayan umaimah tana Mai buɗe fridge dan ɗaukan fresh milk,
Ta process ɗin ta bangaji umaimah wadda ke wanke nama a cikin sink,
Tunda ta shigo kallo ɗaya umaimah tayi mata ta ɗauke ido dan tasan bala'i take nema sannan ta lura kullum safiya yanzu ta ɗauki sarar fito mata falo da Kananun kaya duk da kuwa bata samun Paki wanda tasan danshi ake yi,
Juyowa umaimah tayi tana Mai kallan sameerah wadda ke shan fresh milk ɗin 'in a seductive way,ƙaramar dariya umaimah tayi tace "ina fatan ba kina haka bane dan ki burgeni cos ni da kika gani nan i do no homo,sannan koda ace ina da lust akan mata bazan taba jin wani desire akan ki ba,ni kenan ballantana namiji,cos ba wai body shaming ba baki da wanann ƙirar,ki kalle ki koda sau ɗaya ne a mudubi,you're beautifuly ugly ga kina stinking irin na masu bleaching Mai arhar nan cos nasan baza ki iya affording Mai worth hundreds ba,ina ga kuma masoyina mijina Mai jiyar dani daɗin da babu Mai baki ,kisa a ranki indai wai bada tsubbu ba babu abunda imam zaiyyi dake ,ki sa a wannan daƙiƙin kanki ɗin ,Nana kawai tana deceiving ɗinki ne amma kina abu kamar babu kwakwalwa akanki,ki kalleni da kyau Ni nafi ƙarfin zaman kishi dake cos you're not My lane ,you're not my spec ,not to brag amma im a senior surgeon while ke you're just An intern wadda bama tasan abunda take ba ,ki kalleni da kyau banyi kama da tsaranki ba,ta Ko ina na fiki So why the race?
Fuck off!
Juyawa tayi ta cigaba da wanke namanta,
Fincikota sameerah tayi ,ta ɗaga hannu zata kwaɗa mata mari,riƙe hannun umaimah tayi ta kai mata nata yatsu biyar ɗin a fuska ,
Bango ta kaita ta maƙure tace"gwanda ki gudu kafun Nasaki ki gudu cos bani da kyau idan ka shiga gonata,ki kiyayeni sannan ki kiyayi mijina,"
Cikin maƙurar Sameera tace "ni da imam yanzu zanen soyayyar mu ma yafara saboda nasanshi Kafun ke ,and Ya soni Kafun kizo da asirinki Ki janye masa hankali,sannan da kike magana ta jikina ,da wannan jikin Zanzo na kwacesa na kaishi gado ki bani nan da kwana bakwai sai na kwanta da mijinki".
Sake maƙureta umaimah tayi tana Mai wani irin murmushin gefen baki tace "threat?"
Okay im in,ki kaisa gado ɗin nan da kwana bakwai ni kuma na miki Alƙawari Kafun kwana bakwai ɗin sai na fitar dake a gidan nan,kilan ma baki sani ba Yau shine baccin ki na karshe a gidan nan,Allah kaɗai Ya sani,amma ina so kisa a ranki Kafun ki kaisa gado zan kaiki waje,
Tana kai karshen zancen ta kama wuyan fingilalliyar rigarta ta fara janta har saida ta sadata da ɗakin Nana wanda tana shiga ta watsa ta,
A zabure Nana ta miƙe tana Mai rafta salati,
Lapia menene hakan?
Sameera Ya akayi?
Kuka sameera ta fashe dashi tace "ni Nana idan bazaki saka imam Ya Aureni ba na haƙura na tafi,baƙiji irin wulaƙancin da matar nan ta mun ba wai har da cewa Kafun kwana biyar sai ta koreni dake daga gidan nan baki ɗaya har da ce miki wai tsohuwar kilaki,Allah kaɗai yasan irin barikin da kikayi Kafun Aure "
Da zafin nama Nana ta mike tana na faɗin"nice karuwa?"
Ni kike faɗawa karuwa?
Har kina faɗin zaki koreni daga gidan ɗana muntari,
Ni zaki kora daga gidan muntari?
Hannu Nana tasa ta ɗauke Umaimah da mari wadda ta dafe kumatun ta tana Mai jin saukar hawaye yana zubo mata ,sake ɗaga hannu Nana tayi ta sharara mata wani marin amma still umaimah bata hana ba sai ma cire hannunta da tayi daga kumatun ta matsa kusa da Nana tace "Nana ki kuma marina ,Nana ki mareni bazan hanaki ba,kisa abu ki zane ni idan har nafaɗa maki gaskiyar abunda Ya faru baki gamsu ba,"
Zubewa tayi a ƙasa dai dai kafar Nana tana mai rikewa tace "Nana Bansan Mai zan maki ki soni ba,ni da kika ganni Babu abunda nake nema da zuria'r nan sai alheri,ban san Mai yasa kike nuna mun wannan asalin kiyayyar ba,wallahi Nana da zuciya daya nake zaune daku,Kin sani da ace da baƙar aniya nake zaune daku da bazan taba bari ku zauna anan lafiya ba,har akawo wata ƙatuwar banza wadda take da ido akan mijina amma na danne .
Kinsan Mai tace ne Nana wanda yasa na kamo ta na kawo ta nan, har marin ta nayi saboda irin zafi 'da girman maganar da ta faɗa.
Nana wannan yarinyar da kika gani"micijin sari ka noƙece,cewa fa tayi wai amfani take da ke 'dan cimma burinta saboda ta kula ke tsohuwar banza ce da kike amfani da farin cikin iyalinki 'dan ki cima burin ki,wai ke tsohuwa ce Mai san zuciya,sannan muguwace ke ,bakiji yarda nake jin ɗacin maganar ba a yanzu da nake maimaitawa,".
Cike da kiɗimewa sameera ta kalli Nana tana Mai kaɗa kanta bakinta yana rawa tace"wallahi Nana karya take ,ke umaimah kiji tsoran Allah ki faɗi gaskiya,"
Kallanta umaimah tayi tana mai rusa wani kukan tace "nasan Nana saboda abubuwan da suka shiga tsakanina dake bazaki yarda da magana ta ba da ta Sameera zaki yarda saboda itace tagaban goshin ki,"Amma Nana wanda ka tsana yakan faɗi gaskiya ka share sai daga baya abun yayi maka illa.
Kinsan Mai ma tace ne Nana?
Kuka ta kuma sawa tace tunda nake ban tab'a jin kazamin furuci ba irin wanda tayi,
Da sauri da ƙaguwa Nana tace"ki daina mun shegen kukan nan ki faɗa mun Mai tace ,Ya rage nawa idan na yarda idan ban yarda ba,"
Cikin kukan da umaimah bata san tana dashi ba tace"Nana cewa 'fa tayi wai sai ta kai Abbu gado sannan sai ta tarwatsa dukkan farin cikin gidan nan,sannan wai ke zata fara kaiwa ƙwararo sai abincin da zakici Ya gagare ki ,sai kinyi bara ,sai ta mayar dake almajirar da za'a ƙyara "
Duk da abunda ke tsakanina dake sai da naji zuciyata tayi nauyi 'dan ke ɗin kakar imam ce kuma mahaifiyar Abbu Shine dalilin da yasa nace sai nasa tabar gidan nan.
Cikin ƙidimewa sameera tace "wallahi Nana imam nace".
Tafa hannu umaimah tayi tana Mai sake fashewa da kuka tace" kinji ko Nana gaskiyar maganata ko?
Kinji ko Nana,inda maganar imam ta fito anan cewa tayi wai idan ba Abbu ba imam,wai sai ta b'ata masa suna ta sa a waje ma sai Ya saukar da kansa .
Kaɗa kai sameerah ta fara tana tare kukan dake san zubo mata ganin yarda Nana ke gabato ta,
Alamu ta fara da hannu tace "wallahi Nana sharri take min."
Mari Nana ta ɗauke ta dashi har sai da ta kifa,
Nunata Nana tayi da yatsa tace"na rufa maki asiri ,ina san naga na Aura miki jikana amma da abunda zaki saka mu kenan ko?"Dama Ai ance tsintaciyar mage bata mage,dama ɗan adam haka yake ka sakashi inuwa ya kaika rana ,ni zaki tozarta,?
Muntari tsararki ne?
Yo ko ba muntari ba shi imamu ɗin kyayi masa haka?
Inace tun yarinta kuke tare Shine yanzu da sheɗancinki zaki tarwatsa shi,
Dama Apnan ta faɗa ke shaiɗaniyace amma soyayarki ta rufe mani ido na gagara ganin abunda ya kamata na gani,
Nan haka nasa baiwar Allah ɗinnan a gaba da fitina na kasa ganin kirkinta 'dan da ace tayi niya yarda kika tunzurani na shigo musu ranar daren Aurensu da ta cire mun ƙoda da hanji,amma haka nan ma koda nayi fitsarin tsoro zani ta bani amma duka bani gani saboda ke,
Wato ni gani sakariyar tsohuwa,
To ki kalli idona da kyau,kar nake gane karya da gaskiya ,a wannan karan kuwa ƴar nan ce Mai gaskiya,
Bari kiga karshen kai mun ɗa da jika gado.
Ƙaton hijabin sameera da tasa kan couch ta jawo ta miƙa mata tace "maza saka yau zamanki gidan muntari Ya ƙare ,fam fam fam An gama,"
Kuka wiwi sameera take tana Mai cewa"Nana wallahi shiga tsakanin mu akayi,wallahi karya take mun".
Cike da masifa Nana tace "ɗiyar nan Ai Angama tunda da bakinki kin faɗi bangare cikin gaskiyar,yau ba gobe ba sai kinbar gidan nan,dama bani na aje ki ba,to yau kinyi isfaya,gidan nan koda kuɗin tsohonki sai kin barshi Allah,
Bari ma kiga naje na nemo madoki kigane da gaske nake,
Fita Nana tayi tana Mai ruwan balai".
Tashi umaimah tayi tana Mai goge hawayenta tace "Ya kika ga kafcen nawa?"
Ɗaga mata gira tayi tace "na daɗe da sanin da na shiga film zan tashe saboda iya kafce na
Tick tock tick tock,
Awa nawa ma yanzu da furucin ki amma har zaki bar gidan abun ƙaunar ki?
Ƙaramun murmushi tayi tana Mai dafa sameera dake faman sharb'ar kuka tace"ke yarinya ce,kina da ƙuruciya yakama ace kinje chan domin zuwa ki samu naki farin cikin amma baki tsaya a guri ɗaya ba kamar danko kina neman abinda ba naki ba,
Sannan ki kirani da duk Abunda zaki kirani,Allah ma ya gani nayi faɗane akan wadda kesan tarwatsa mun Aure,
Kina tunanin idan na faɗin gaskiya Nana zata saurareni?
Kema kinsan A'a shiyasa na buga maki nawa chaskalen yayin da ke kuma cikin sakarci kika yaye ma kanki hijabi."
Hankaɗe hannunta sameera tayi tace"sai na zame maki damuwa a rayuwa,wannan abunda kikayi mun sai Ya zama silar tarwatsewarki."
Kamar an jefo Nana wadda tasha wahala Kafun ta samu muciya ta tsinkayi maganar Sameerah,
Kwala mata muciyar tayi a kafafunta tace "aw baki daddara ba sai kin zamar mata damuwa ko?
Bari ni nafara zamar maki damuwa,
Fizgarta Nana tayi tana Mai faɗin kalli Chan umaimatu wanchan akwatin Mai ruwan miyar kuka koriya shar ɗin nan Shine nata,tattaro mata kayanta ki duƙunƙune kisaka mata a ciki 'dan ubanta.
Babu musu umaimah ta fara haɗa kayan sameerah tabi bayansu dashi,
Har harabar gidan Nana ta bita tana Mai jan ta kamar akuya,sai da tafitar da ita harabar gidan ta juya tana Mai faɗin umaimatu kawo mata tsinyarta harda tarho ɗinta..
Nana na rufe baki sameera tayi mata wata irin muguwar Hankaɗa ta faɗi kasa ta haye kan ruwan cikinta ta fara nausar mata baki wanda karaf a idanun Imam wanda Ya gabato gurin tare da Affan,
Da gudu suka karasa gurin yayin da Sameera tasa hannu ta shaƙe wuyan Nana ta ƙarfi tana Mai faɗin"bari na kasheki tukunna tsohuwar banza,'dan nasan idan na kashe ki zuriarki ma zasuyi alfahari dani ,"Fincike ta imam yayi Ya ɗauke ta da wani irin zazzafan mari wanda yasata tuntsirawa tayi gurin Affan wanda shima Ya ɗauketa da wani mari Mai Zafin gaske,da gudu umaimah tayi kan Nana wadda take kwance jini da majina .
Chuchujay✍🏽
Tbc.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top