finale
AURE UKU
(a hospital romance )
By chuchujay
wattpad :@chuchujay
https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j
Join My whatsapp channel inda Zan baku noorurrahman kyauta.
Yes paid novel ne amma Zan baku shi a channel ɗina kyauta,
Just follow and share ❤
FINAL EPISODE.
Jeka ka dawo Imam paki yake a bakin theatre room na Queen cleopatra Hospital dake ƙasar misra yana Mai shafa fuskar sa a hankali,
Kallo ɗaya zakayi masa kasan cewa yana cikin tashin hankali wanda ba'a sawa rana.
Dafa sa Ummu tayi tana Mai faɗin"Imam kazo muje ka zauna dan Allah tun ɗazu kake abu daya komai zai zama dai dai da ikon Allah ,Addu'ar mu bazata faɗi kasa nan ba Za'ayi aikin nan lafiya,"
Hannunsa ta kamo ta zaunar dashi kafun ta buɗe ruwan gora ta miƙa masa ,
Babu musu Ya ƙarba ya daga a bakinsa Ya sha Mai isarsa kafun Ya sauke ya kalli Ummu cike da damuwa yace"Ummu sun jima 'fa har yanzu shiru,"
Ganin yarda Ya ke cikin mutuƙar damuwa ne yasata fara bashi baki a hankali tana kwantar masa da hankali.
Ji yake kamar Ya tashi Ya shiga ,tsinewa rashin samun licence ɗin sa yayi cos da ace yana da shi da babu wanda Ya isa Ya hanasa ko tsayawa ne yayi akan matarsa ,
Dalilin zuwan su misra umaimah ta takura akan ita Chan take san haihuwa tun tana da sauran wata ɗaya ta haihu,
Bai yi mata musu ba ya yarda da zuwan nata duk da bai samu sun wuce tare ba saboda kammala medInternship ɗin sa wanda dole dole yasa shi tsayawa ganin yarda ta nace akan Ya tsaya ɗin she will be okay musamman hindu na tare da ita sannan ga Afnan Ya haɗasu tare.
Satin ta biyu a garin Ya kammala abunda zaiyyi Ya bita .
Kallo ɗaya zakayi mata kasan cewa wannan ciki ba abu ɗaya ke cikinsa ba ,ille kuwa scanning ɗin farko aka ce musu Twins ne wanda murna gurin Paki ba'a saka mata rana,siyayya kuwa da yayi kamar bashi da mafaɗi ,
Ciwo sosai ta fara da yaje tana Mai yan ƙananun naƙuda dan haka Ya tatarata suka koma asibitin su hindu baki ɗaya wanda suke ta kulawa da ita kamar su maida ta ciki,abunka da larabawa,
Yarda take nakudar ja da ja yasa da aka dubata suka tabbatar masu bazata iya haihuwa da kanta ba dan babies ɗin sunyi girma da yawa sannan ciresu shine kawai zai tsallakar da uwa da yaran,
Babu musu Paki yasa hannu inda suka tsaya a washe gari zasuyi aikin dan haka yakira Ummu Ya tada mata hankali dole tayo takakkiya ta taho.
Suna wannan zaman jiran tsammanin Hindu ta fito tana Mai washe baki tace"Ummu,Imam Congratulations,"
da saurinsa Ya tako inda take yana Mai faɗin"Hindu matana fa?"
Murmushi tayi tace "ka kwantar da hankalin ka baban uku ,matar ka da yaran ka suna cikin koshin lafiya,"
Washe baki yayi yana Mai faɗin"Alhamdulillah ,Allah na gode maka,zan iya ganinsu?"
Shiru yayi lokaci guda kuma yana san tuna abunda tace cike da mamaki yace "yara nawa ma kikace?"
Sake faɗaɗa fara'arta tayi tace "yara uku ,kai da umaimah kun samu triplet .
Da saurinsa Ya koma ga ummu yana Mai hawayen murna yace "Ummu Kina ji ko,
Wai yara uku 'fa,
Shafa gefen fuskarsa ummu tayi tace "naji imam,Allah Ya baka kyautar da ba kowa yake bawa ba,
Alamu tayi ma da Hindu akan tazo,babu musu ta tako gareta,rungumeta tayi tace "ki zabi duk kasar da kike san zuwa honey moon nan da sati uku idan an ɗaura maki Aure da Ahmad ,ko Mai da kika sani zaku buƙata is on me na kwanakin da zakuyi ,shine tuƙuicina ,
Sake rungume ummu Hindu tayi tana mata godia kafun paki yace "na baki kyautar kujerun hajji guda biyar ,kiyi yarda kikeso dasu now tell me ina matana da yarana ina san ganinsu, .
Murmushi tayi tace "an shiga dasu ɗakin hutu ta back door amma zaku iya shiga amma 'fa bata farfaɗo ba,"
Kafun ta kuma cewa wani abu Ya nufi ɗakin da suke,
Kwance take idanun ta a rufe tana bacci yayin da hannunta ke ɗauke da drip,
Kamar Mai sanɗa haka Ya ƙarasa gareta Ya zauna a kujeran dake bakin gadon ya shafa gefen fuskanta a hankali kafin ya sumbaci goshinta Ya furta "Thank you Wiffy,Allah na gode maka daka bawa matata damar kaiwa wannan stage ɗin,wasu hawaye ne suka fara zubo masa a kuncinsa yana Mai jin tsananin santa a cikin ransa yana masa yawo,"
Goge hawayen yayi da sauri jin Ummu da Hindu sun shigo tana Mai faɗin"Amma Hindu inace yan biyu ne cikin ta".
"Eh ummu girman da sukayi sosai guda uku ne guda ɗayane Ya boye a gefen kafar ɗaya wanda ba'a gani ba,amma ni nafi mayar dashi da ikon Allah wanda babu wanda Ya isa yayi masa shishigi akan sanin maine a ciki,dama yana bamu dama ne muga abunda yaga dama ,yanzun ma hakan ya faru,cos Snr Dr ɗin ma da yayi Aikin bakiga yarda yake mamaki ba ,
Gasu nan mata biyu namiji ɗaya ,".
Sai a wannan lokacinne Imam Ya isa ga yaran nasa ummu na miƙa masa yana masu addua yayin da idanunsa ke ɗauke da hawayen murna wanda shi kaɗai yasan yanayin da yake ji,
Suna fa?
Ummu ta tambaye sa bayan Ya aje su,
Murmushi yayi yana Mai riƙe da macen dake mutuƙar Kama da umaimah yace"Ummu bamu yanke shawarar suna ba cos mun bari sai munga abunda muka samu ,and kingani yanzu muna ma tunanin biyu amma uku nema sannan wannan damar na bawa umaimah Ummu matsayin ƙyautarta ,ita zata zabi sunan da take so"
Murmushi ummu tayi tana Mai jin dadin yarda Paki Ya samu kyauna da kwanciyar hankali a tattare da umaimah.
Koda labari Ya isa nigeria ba ƙaramun murna suka shiga ba da samun wannan gagarumar kyautar a dangi karma ace kakanin dake bangaren iyayen yaran,
Hajiya Nana kuwa kamar ta jiƙa kasa ta zuba a ƙasa tasha dan murna 'dan rigima ta tayar akan sai taje misra amma Abbu Ya tausheta akan suna sallamarsu zasu dawo ,dole ta haƙura.
Koda umaimah ta farfaɗo kamar imam zai cinyeta saboda murna da nuna mata tsantsar godiya da kaunarsa,
Tsokana kam yashata gun Hindu wadda ko a jikinsa dan idanunsa sun riga da sun rufe.
Bayan sati guda suka koma nigeria wanda suka tarar ana jiransu da gagarumar tarba,
Iyalan na Bulama da Paki kowa ka tab'a da alherin da zai maka saboda tsantsar farin cikin da suke ciki,
Kyautar yara uku a lokaci ɗaya Ai abun ka motsa aljihune duk maƙonka.
Ranar da aka ware domin raɗa ma yaran suna yara sukaci suna ,FAWHA,FAWZA sai namijinsu FAWZAN,
Taro ne akayi na zo a gani 'dan duk wanda Ya hallarta sai ya tabbata da anyi haihuwar yaran gata,Su Nadiya kuwa ji ake kamar an masu kyautar Aljanna .
A lokacin da ta fara Nursing yaran Asibitinta wanda ta chanza masa suna zuwa UMAIMAM PRIVATE HOSPITAL ta damƙa a hannun Paki wanda yaƙi karban position ɗin da take san bashi na founder ,Ya faɗan mata dream ɗinta ne shi nasa yana tare da ita ne kuma yana tayata bin dream ɗinta da bata dukkan support ɗin da Ya kamata Ya bata.
Duk da haihuwan yaranta uku hakan bai taba chanza soyayyar da yake wa su Nameer ba aransa iyakaci ma ƙara jinsu da yayi a jikinsa yana mai jin babu yashi, uban yara Shida at 30 years,its a real blessing.
**********
BAYAN SHEKARA DAYA.
Zaune suke baki ɗayansu kan Carpet domin yin dinner,
Umaimah ,Nadiya,Abdallah,Shatuh,Nameer,Fawza,Fawha,Fauzan,(yara yan shekara ɗaya) waɗanda ke faman wasa kamar ba abinci za'aci ba yayin da shatuh ke faman tayasu suna dariya,
duba agogon bango umaimah tayi taga har ƙarfe 8:30 amma babu Paki babu alamun sa.
Kallan yarda Abdallah ke faman hamma yasata murmusawa tace"Kids its time for dinner let eat,"
Ajiyar zuciya Nameer yayi yace "Mami zamuci abinci babu PAPA?
Kinsan fa abincin nan yafi daɗin ci idan yana nan Call him again ,mu jirasa Kaɗan,
Dan tsuke baki Nadiya tayi tace"Nima dai Mami kinsan bana koshi idan babu Papa sannan tare muke ci nidashi shine ma dalilin da yasa mukayi abandoning dining table ba,"
Dariya suka saka a tare ganin yarda aka jera abincin a ƙasa,
Murmushi tayi tace "okay kids ku kalla nan ,Papa nasan dole abune Ya rikesa so lets eat sai ku haɗu a breakfast ,okay kunga akwai School gobe sannan kai Nameer kasan gobe zaka koma ba".
Dan haɗe rai yayi Kaɗan yace and mami ni bazan koma ba idan Papa bai Kaini da kansa ba,
"Naji zai kaika okay ,yanzu maza muci abinci,Auntynsu oya kibar su Fawzan kinsan fa su wasansu baya ƙarewa,tasowa tayi inda fawzan da Fawza suka taso da tafiyansu da bai nuna ba yayin da fawha ke binsu da rararrafe cos tsoro yaƙi barinta ta miƙe."
Bayan sun gama Cin abinci suka dawo falo suka zauna danyin kallo,
A hankali takan duba agogo sannan takan kirasa a waya amma bata samunsa,
Wurin tara yaran kowa Ya wuce ɗakinsa yayin da ta zauna ɗan taya shatuh feeding Yan uku,
Bayan ta gama ta taimaka mata ta ɗaukosu 'dan zuwa ƙwantar dasu gadajensu dake dake cikin ɗakinta cos bata raba ɗaki dasu ba tukunna,
Sallama shatuh tayi mata ta wuce dan kwanciya ,da kallo umaimah ta bita tana Mai jin kewarta tun kan ta tafi cos a yanzu ta kawo miji wanda ba'a gama tsayar da magana ba tukunna amma tana san asa rana amma sai ta kammala karatunta a yanzu da yarage shekaru biyu.
Sake kimtsawa tayi tana Mai jiransa bayan ta gama jera masa abincinsa a table ɗin dake ɗakin,
Tana zaman tsumayinsa taji alamun buɗe kofansa ,ajiyar zuciya tayi tana jiran shigowar sa,
A hankali ya buɗe kofar Ya shigo,murmushi tayi ta tashi a kan gado tace "Baby naganka and ba bacci nake ba so kadaina wannan sanɗar,"
Ƙarasawa tayi garesa yana Mai bata puppy eyes idanunsa ɗauke da gajiya,
Rungumesa tayi tace"ba sai kayi magana ba fuskan kama Ya nuna mun a gajiya kake,
Ɗagata sama yayi yace "amma banyi gajiyan da zan iya ɗaga abar ƙaunata sama ba ,sannan na nuna mata nayi kewarta kamar menene,
Dariya tasa a yayin da Ya sauketa yana Mai riƙe waist ɗinta sosai yace "nayi kewan ki sarauniyata ,hutunki yayi Ya ƙare ki dawo kusa dani ina sakaki a ido koda zanyi dukka aikin wahalan ne,just come for me"
Murmushi tayi tana Mai shafa gefen fuskarsa tace "kar ka damu abun ƙauna ,yanzu dai muje nayi maka wanka kaci abinci,After that nayi maka tausan da zai tafi da dukkan gajiyar da ka kwaso,kasan magic d'in hannuna ba,"
Kamo hannun yayi yana Mai licking finger ɗinta yace "they are delicious and sexy,amma matana is the must sexiest,
Murmushi tayi tace "yara shida na kawo so calm down "
Jawota jikinsa yayi yace "baki san sake zaman sexy kikayi ba ko?
Zan nuna maki,
Kafun tace wani abu Ya dauketa suka faɗa bathroom,
Bayan ta basa abinci Ya ƙoshi Ya koma yana Mai sake yiwa yaransa addua kafin Ya ɗauketa suka haura gado yana Mai faɗin"duty time".
Chakulkuli yafara mata tana dariya kafin Ya koma gefenta Ya kwanta yace kafin na fara baki wahala dai Ya AHALINA .
Murmushi tayi tace AHALINKA dai sun gaji da jiranka sunci abinci sunyi bacci and babban cikin AHALINKA yace na tuna maka gobe zaka kaisa makaranta,
Murmushi yayi yace "Nameer ɗin Papa,bazan taba manta abunda Ya shafesa Mai muhimmanci ba,"Kinsan mene,idan inaa kallanku ko jinake kamar nafi kowa sa'a,youngest father of six,can you imagine?
Mirginowa tayi kansa tace idan Mungana maganar AHALINKA,bari na kula da ɗaya kuma jagaban cikin AHALINA mijina abun alfaharina,
Kafun yace wani abu tafara bashi passionate kiss ɗin da yake kashesa.
Da haka chuchu ta fito tana Mai jin wannan AHALIN suna mutuƙar burgeta,
Shin kuma wannan AHALIN sun burgeku?
Idan eh to kuzo ku Kama hannuna domin kaiku cikin wannan tawaga ta AHALIN umaimah da Paki domin jin abunda zai kunsa nan gaba.
ALHAMDULILLAH anan Ink ɗina Ya ƙare inda nake neman sako wani domin wasa shi dan kawo maku cigaban AURE UKU(HUDU)na alheri da wani salan na daban.
Allah Ya yafe mun kurkuren dake ciki,sannan Allah Ya bamu ikon amfani da ilmin cikinsa idan akwai.
Idan da wanda kuma rubutun Ya batawa yayi mun afuwa sab'abine.
Sai mun haɗu a AHALINA 2 in AURE UKU series.
Ina ƙaunarku masoya sosai da sosai nagode da kwarin gwiwarku.❤
Nice taku a kullum .
AMINA JAMIL ADAM(chuchujay)✍🏽
Ma'assalam.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top