Episode 9

https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK

AURE UKU

    (a hospital romance)

            By

    Chuchujay.

EPISODE 9⃣

  Washe gari bata shiga Asibitin ba saboda weekend ne kuma musamman saturday ,sunday ne takan shiga , Tana tsaka da bacci taji ana ja mata ƙafa,

"Yi tayi kamar bata san anayi ba ,"Cigaba da jan ƙafar yasata farkawa ,

Dariya nadiya tasa tace "hamma nameer i won dole ka bani Tab din ka na sati nayi game,"Ɗan bata rai yayi yace"mami why do You wake up We bet ne 'fa.

"Tashi tace tace "akan me kuka yi betting ɗin tell mami"

"Haurowa gadan da take Nadiya tayi tana Mai washe hakora tace "mami betting mukayi nace masa yau saturday mami na bacci amma nasan idan naja miki kafa zaki tashi ,shine hamma nameer yace Ai bazaki tashi ba Cos kina da gajiyan weekday ,amma idan kin tashi yasa mun tab ɗin sa na sati ɗaya".

"Ƴar karamar dariya umaimah tayi Kafun ta kalli nameer dake faman haɗe rai zai bawa nadiya Tab ɗin sa tace"okay ku saurare ni,"Anything betting is haram,ko menene shi koda da wasa ne,a musulunci babu kyau 'dan Haka Banda Wasan betting,

"Idan nameer zai baki tab ɗin sa aro ne to Ya baki amma ba wai ɗan Kin cinyesa a bet ba ,okay".

"Kaɗa kai sukayi a tare inda Nameer  yace dama mami banyi niya ba"cos duk ranar da na arama nadiya Tab ɗina sai ta cinye chaji tas take dawo mun dashi .

"Mami nima Tab ina san na kalli johnny johnny hamma Nameer kuma baya bani,

"Dariya Umaimah tasa ga maganar da Abdallah wanda yake shigowa da gudu shatu na binsa a baya yayi".

"Ɗannowa yayi kan gadon yana Mai hawa jikinta yayin da ta rungumesa ,"

Zama shatu tayi bakin gadon tace"Adda ina kwana ?"Kin tashi kenan.

"Murmushi tayi tace "wallahi shatu sun tashe ni zan ce ma ,ina fatan baku jira ni ba kun karya ."

"Kaɗa kai tayi tace "ai Adda kema kin san rigimar Abdallah da rashin haƙurin sa ga yunwa ba zai bar mu shan ruwa ba musamman ace mun kai sha ɗaya ."

"'Ɗan buɗe ido tayi tace "har sha daya ,kace na sha bacci,".

"Mami mene plan ɗin yau ko za mu Roly park ne it have been a While,nameer Ya faɗa yana Mai Marairaice murya..

A tare suka haɗa baki wajen faɗin"roly park,suna chanting tare,".

Zata yi magana taga wayanta na ringing da baƙuwar Number,

Ɗauka tayi ta kara a kunnenta tana Mai faɗin hello a yayin da yaran nata suka cigaba da faɗin Roly park ,Roly park,.

Daga ɗaya bangaren taji an kashe wayan 'dan Haka tace naji roly park kuje Auntyn ku ta shirya ku bari na yi wanka na ci abinci,

"Ihu suka fara cike da murna ,kana suka fita nadiya na faɗin Yau zan ridding real horse".

"Kallan shatu umaimah tayi bayan fitar nameer da nadiya tace"Auntyn  yara shiryawa zakiyi muje fa".

"Murmushi tayi tace "Adda kuje dai ku dawo kinsan ni ba ma'abociyar san fita bace,ina nan gida ina jiran ku,ga wankin su Abdallah chan ma nasa cikin washing machine ga gugan su kinsan ni da aiki muna haɗe amma wani zuwan zan biku.

"Kallan ta Umaimah tayi cike da kulawa tace "shatu nasan halin ki fa kilan ki zauna kina aikin tunanin da kika saba ,in dai Aikine idan mun dawo ni da kaina zan taya ki".

"Faɗaɗa murmushin nata tayi tace "Allah Adda kar ki damu ,ba wani tunani da zan tsaya dama akwai wani series film da nake kalo ,ina gama aiki zan cigaba har ku dawo,"

"Shikenan tunda kince Haka ,shafa kan Abdallah da yayi makale a jikinta tayi tace "malam Abdallah maza tashi kaje Aunty ta saka maka sweater a saman rigan nan Cos da sanyi,".

******

"Kai tsaye Roly park suka je ,park ne wanda aka tanada domin yara dan kuwa duk wani abu da yaro zaiso na dan Wasa akwai a gurin .

"Kallo ɗaya zaka yiwa su nameer kasan suna cikin farin ciki,"Motan wasan dake ta juyawa da yara nadiya tayi da gudu tana cewa"mami this".

"Murmushi umaimah tayi tace "okay lets go ,da gudun su sukaje gurin ,inda ita kuma taje siyan coin.

"Sun jima a wurin motan ,dan coins ma sai da ta b'ata a lissafin siya,.

Bayan sun bar gurin suka nufi gurin doku nan Wasa,

"Nameer ne yace"mami ina nadiya tayi"?

"Da mamaki ta juyo tace "nadiya ? Ina tayi"?

Cikin lokaci ƙankani hankalin umaimah Ya tashi da ta fahimci Nadiya bata biyosu ba tun daga baya,

Daukar Abdallah tayi ta riƙe hannun Nameer tana Mai san assuring kanta a gun suka barta ,tace"Nameer nasan tana chan gurin Cars ɗin chan ,muje zamu ganta"

Kula da ɗan ruɗewar da tayi nameer yayi yace "mami nasan ma tana chan nadiya kuma da san mota ,ko sch mukaje sai mun shiga aji zaki ganta ta shigo,"

"Wata kwallane ya zubowa umaimah lokacin da sukaje gurin motar bata ga nadiya ba ,"Gogewa tayi tana Mai tambayar mutumin da suka siya coin a gurinsa ko ya ganta.

"Kafun Ya bata amsa ta tsinci muryar nadiya tana mai faɗin"mami!!"

Da saurinta ta juya,turus tayi ganin nadiyan da Paki ?

Da gudu nadiya ta zo gurinta tana faɗin "mami  meet My new friend ,"

"Wani kallan banza ta bata Kafun tace "ina kikaje when kin san i warned You ba sau ɗaya ba akan strangers kina so na fara dukanki ko?".

" A yarda tayi maganan da harshness Ya tabbatarwa da Paki tayi fushine dan koda ta joyu sai da ya tsinci tashin hankalin da take shirrin boyewa, ".

Boye nadiya yayi a bayan sa yace"calm down mummy And ni Ai kinsan ba stranger bane".

And i saw this beautiful sweetheart buying her mothers favourite icecream.

"Cikin fushi umaimah tace And taya kasan nice maman nata"?

Smirking yayi yace "well i guess boyewar bata da amfani ,i was stalking you and nasan fuskarta a hoto sannan na kiraki earlier naji suna ihun kuje Roly park And nayi missing ɗinki sosai na rana ɗaya kawai ,cos na saba da saka ki a idanuna muddin idan kuma ban ganki ina shiga damuwa shi yasa da na samu dama na dama."

Haɗe rai Nameer yayi yace"mr man who Are YOu?".

Murmushi paki yayi ganin yarda nameer Ya haɗe ransa ,tsugunnawa yayi dai dai tsayin Nameer Yace "ni sunana Imam paki Sannan ni Abokin aikin mamanka ne Kaifa.

"Sake cin mur Nameer yayi yace"Nameer Habib And im My mom's protector and i don't find You to my liking a bit ".

"Dan buɗe baki paki yayi jin yarda angry young man ɗin ke nuna masa kuri kuri baya sansa,"Shafa kansa yayi yace "well dear Nameer i cant help it amma na tabbatar zaka so kazama frnd ɗina idan ka zauna dani"

"Ni bana na so Ya zama frnd ɗin ka cos handsome uncle nawa ne ni kaɗai ,nadiya ta faɗa tana jin haushin yarda Nameer yake cewa baya san Paki ".

Murmushi paki yayi Ya tashi kana yace "well beautiful princess its okay since ni dake team ne ,and im sure little Prince is on Our sida too ya ƙarasa maganar yana Mai miƙawa abdallah hannu akan yazo ,"

"Ganin Ya miƙo hannu yasa umaimah sakar masa shi ,"

Murmushi yayi yace "mamin mu wannan katan saurayin kike ɗauka?"

"Da blank kallo ta kallesa tace "Paki zaka iya tafiya cos time ɗina ne yau da kids ɗina idan abune da Ya shafi aiki Ya kawo ka ka bari mu hadu ranar monday amma yanzu is My Family time".

"Shafa gefen gashin sa yayi yace"nima Ai Family ne ko beautiful princess. "

"Da tsalle Nadiya tace yes mami dan Allah ki bar uncle handsome mana i like him".

"Tsintar kanta tayi da kaɗa idanun ta tace "what ever".

"Murmushi yayi yace "After you Queen,"Murmushin da batayi tsammani bane ya kwace mata,wanda Ya sauka a idanun Paki.

"Yarda nadiya da Abdallah suka Sake Suna Wasa dashi abun har mamaki yake bata musamman yarda Pakin Ya biye musu kamar yaro, "

"Amma Nameer kuwa babu abun da yake sai Aukin haɗe rai karma ace yarda yaga maminsa ta ɗan saki jiki da Paki har tana dariya idan sukayi abun dariya".

Bayan sun gama wasan su ne Abdallah Ya fara faɗin "mami Food ,"

"Food Abdallah ko ,nima kagan ni na fara jin yunwa ,juyowa yayi Ya kalli umaimah Ya turo baki yarda Abdallah yayi yace "mami food".

"Dariya tasa tace "don't do that paki you look childish ,tsayawa Kallan dariyar da take yayi yana Mai sake admiring ɗinta ,jinsa yake kamar Ya mallaketa ,jinsu Nameer yake kamar shine Ya haife su,yaushe wannan bunrin nashi na Auren umaimah zai cika?

Yaushe zata bashi dama Ya nuna mata soyayyar da bata taba gani ba a gurin ko wanne ɗa namiji?"

"Snapping fingers ɗinta tayi a fuskansa tace" paki magana nake like forever tunanin mai kake?"

"Shafa kansa yayi yace "naki"

"Kaɗa kanta tayi tana Mai jin kumatunta na ja duk da ba yau Ya fara maganar yana tunanin nata ba amma a yau sai taji kunyar abun da Ya faɗa".

"Restaurant suka shiga dan cin abinci,Family table suka zauna,kallo ɗaya zaka masu kaga sun burgeka Cos baza kace wai ba Family bane  ".

"Bayan sunyi order suna zaune suna jiran order ɗinsu waiter ɗin yazo da mini cake a tray,"Aje wa yayi yana murmushi.

"Kallan sa umaimah tayi tace "i dont remember ordering cake,ko da wanda yayi a cikin ku ,ta maida tambayar garesu"

"Professionally waiter ɗin Ya tsaya yace"this a little gift from our restaurant wanda mukan bawa lucky family And yau kune first lucky Family ɗin mu a Customers so thats your gift And ma'am i must say ,your Family is lovable ".

"Faɗaɗa murmushi Paki yayi kafin yace "thank you."

On behalf of My Family And I.

"Shiru umaimah tayi bata iya cewa komai ba"sai da waiter ɗin Ya tafi Nameer ya kalli Paki cikin bacin rai yace "you're not My daddy,".

Riƙe hannunsa umaimah tayi tace "Nameer?"Ina manners ɗinka?

"Its okay cewa paki Kafun yace "nameer its okay ,who knows i might be one amma yanzu ina san ka zama frnd ɗina ne."

"Daurewa nameer yayi 'dan shi paki bai masa ba musamman yarda yaga yana yiwa maminsa."

"Ranar sosai umaimah ta sake wa paki,wanda shima Ya saki jikin sa yana jin kamar ya samu karbuwa gurinta,"

"Bakin park ɗin suka rabu wanda duk nacin paki bata bari Ya bisu ba,"

Mabi Phone store ta nufa ,Tab uku ta siya da system daya,

Na nadiya daya na Muhammad ɗaya sai nameer ɗaya inda ta ce suna zuwa gida zai bata nashi tshon ,system kuwa ta siya wa shatu ne,

Da dare bayan ta gama hira da daddy ta sa yara bacci ta dawo ta kwanta,

Tunani ne kala kala suke mata zarya  zuciya wanda galibi kan imam yake wanda yawan sa yafi karkata akan sawa alaƙar su da bata fara ba birki 'dan kuwa bata ganin future tsakanin su ,abune wanda ba zai taba iyuwa ba dan haka tun kafin ta bashi wrong signals Ya kamata komene ke san cooking tsakanin su Ya tsaya nan.

"Saukin sa ,saukin ta saboda ta sani alaƙar soyayya babu zancenta tsakaninta da Imam,dan bashi da wata riba sai faɗuwa, "

da haka bacci b'arawo ta kamata.



CHUCHUJAY ✍🏽

TBC.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top