episode 7

AURE UKU

(a hospital romance)

      By.

  Chuchujay

EPISODE 7⃣

Umaimah!

Na'am Daddy .

Gyaran murya yayi yana mai gyara zaman sa yace "umaimah naji komai da yake faruwa ,sannan ina Mai baki Haƙuri ga dukkan abunda ya faru wanda a yanzu Ya zama past ɗin da baza'a kuma maimaitawa ba nan gaba na miki Alƙawari,

Yanzu ki ɗauko su Abdallah kizo mu koma gida zamu zauna a yi magana wadda na tabbatar miki babu makamancin Abunda Ya faru da zai kuma faruwa indai nine Mai gidan Bulama sannan marin da Ali Ya miki har haƙuri zai baki .

Shiru tayi kafun tace"ni Daddy bana so Ya bani haƙuri kawai ina san Ya kiyaye Ko da Wasa kar Ya kuma marina, 'dan Allah Daddy idan ya kuma shari'ace zata rabani dashi, tunda dai su basu ɗauke ni yar uwar su ba,tun kuruciya ina sane  da dukkan abunda suke min daga su har hajiya,yaya Abubakar ne kawai yake nuna ni tashi ce".

Sannan ni Daddy ba zan koma gida ba, ba tare da na samu Mai kulamun dasu nadiya ba tunda Family na duk Albarkars u babu Mai sansu.

Dafa ta yayi yace "umaiman daddy idan kina faɗan Haka har da Daddy fa".

Ɗan karamun murmushi tayi tace"ni banda Kai Daddy dan nasan da ace kai mace ne zaka kula mun da yarana kamar Kai ka haifesu,"

Yanzu ma Dada tace zamu tafi da shatu ƴar baffa dikko ƙanin baffa da mijinta Ya rasu babu abunda take gida ni ko biyan ta ne zan nayi duk da tace bata so,

Hankalina zai fi kwanciya idan tana tare dasu,sannan ba wai nace Aunty sadiya bata mun ba, Daddy itama Ga ɗawainiyar yaranta ga na su nadiya abun yana mata yawa,

Dama kuma Nameer jiya yace mun yana san zai rubuta exam ɗin NTIS (Nigerian Turkish international school)na Abuja yayi jss to sss a chan wanda dama nima na dade Ina so.

Murmushi daddy Ya faɗaɗa yace kinga shikenan sai suje tare da Ibrahim(ibi) ya samu ɗan uwa,

kicin kicin tayi da ranta tace"Daddy nifa ba wai bana san Alaƙar su nameer ne da jikokin ka na gun su yaya usman ba kawai ni dai gwanda nameer yaje Abuja ɗin in yaso su suje na nan Adamawa ɗin. "

Tabbas abunda zaisa umaimah ta nemi su ibi suyi nisa da nameer ba ƙaramun abu bane duba da yarda take nunawa yaran kauna ,

Shafa kanta yayi yace shikenan yarda kike so Haka za'ayi, yanzu dai kije gurin baffa ki kira su nameer ɗin mu koma gida tunda ai nasan Ko yanzu kikace shatun tazo zata zo Ai baza a tsaya ma dasu Nadiya karatu ba ,ga Abdallah ma za'ayi enrolling ɗinsa ya kamata kuma ace da kaina naje na saka shi.

Bata san cigaba da musu da Daddyn nata 'dan Haka tace "to daddy".

Sallama sukayi da Dada da baffa yayin da suka ɗauki shatu wadda a kalla umaimah zata bata shekaru huɗu da haihuwa ,

Taron gaggawa daddy ya kira a daren ranar wanda dukkan sun tabbatar da sun hallarta har da matan su kafin Ya buga musu zazzafan warning ɗin da Ya tabbatar suma zasu wa ƴaransu dan bazai lamunta ba su b'ata masa gida da negativity ba.

Sanin Halinsa yasaka ko wannensu shiga taitayi.

Washe gari da sassafe ta wuce asibiti inda daddy kamar yarda Ya faɗa Ya dauki Abdallah da kansa ya kaishi makarantar su Nadiyan domin saka shi.

Tana zaune a office kamar kullum bayan Farouk Ya gama shigar mata da duk abunda take bukata ciki har da coffee ,bata nemi wani cookies ba 'dan yau da irish and egg sauce ɗin da shatu tawa su nadiya ta taho ,

A hankali take kurban coffee ɗin a yayin da hankalin ta guda yake kan system ɗinta tana studying wani method na surgery,

Kulan irish ɗin ta buɗe ta faraci a hankali bayan tayi bismillah,

Knocking taji a bakin door ɗinta,

Sai da akayi a karo na biyu Kafun ta bawa Mai kwankwasawar izinin ya shigo ,

Da sallama a bakin sa ya shigo wanda jin muryarsa kaɗai sai da yasata kwarewa ,

Da saurinsa Ya tako yana faɗin Ya salam kinyi missing ɗina har haka kenan,

Bottle Water ɗin dake gefen Kulan Ya ɗauko ya balle mirfin Ya miƙa mata ,babu musu ta ƙarba ta kafa bakin Gorar a bakinta .

Sai da taji dai dai Kafun ta aje ruwan,kallan sa tayi tana Mai haɗe ranta tace "lapia"?

Murmushi yayi yace "lapia ,da fari dai ina san saka Ki a ido nane domin a yanzu kallan ki shine yake kosar dani naji bana jin ko wacce irin yunwa,"

"Na biyu kuma idan kin manta ni ban manta ba kince ni dake zamuyi magana dan Haka yau da zumuɗina nazo Asibitin nan Cos i cant wait to hear duk wani abu da zai fito a bakin ki koda zagi nane domin ni akan ki mahaukacin masoyine,

Ya ƙarasa yana Mai saka irish ɗin da Ya ɗauka a bakinsa a yayin da idanunsa ke cikin nata kamar zai fasa kwayar idanunta.

"Wata iri ƙaramar dariya tayi Kafun tace "imam paki Ina san ka maida hankalinka kasani ni ba tsarar ka bace.."

Tsk yayi da baƙinsa Kafun Ya karkaɗa dan yatsansa cikin rashin amincewa kafin yace"point of correction ni yayanki ne da wata ɗaya".

Serious face tasa tace "lallai zamu samu matsala da kai a asibitin nan saboda i wont tolerate this,"

"Wani murmushin Ya kuma yace "nifa ba wai ina nemanki da hanyar banza bane umaimah Auren ki zanyi ".

Nunasa tayi da ɗan yatsanta tace "DR Bulama,ba muyi kusancin da zaka kirani umaimah ba ,dafe goshinta tayi cikin rashin sanin Abunda zatace masa ta furta"get out ".

"Yunƙurawa yayi kan table har sai da ya Kai saitin fuskarta Kafun yayi wani irin arnen murmushi ganin yarda Ya zaro idanu yace "Stop thinking silly ,im not going to kiss you Ina so naji ne idan da gaske kike san datse Alaƙar da na kulla mana ,amma ga mamakina sai naji zuciyarki tana luguɗe da sauri da sauri tana kiran Imam Paki,wanda Haka Ya tabbatar mun baki tsaneni ba".

"Wata irin kunyace ta kamata musamman da Ya zaman zuciyar ta sai da tayi skipping beat.

Murmushi yayi yace "abincinki zai huce zuwa anjima Zan dawo na sake duba lafiyarki dan yanzu aiki nane."

Tashin sa keda wuya farouk Ya kwankwasa kofa,

dama ta bashi Ya shigo,

Kallan paki dake tsaye yayi Kafun Ya Kalle ta yace "Doctor kinyi baƙo and yana ta creating scene akan dole sai Ya ganki duk da bai da Appointment dake sannan baiyyi kama da mara lapia ba amma yace a faɗa miki Baban nameer ne "

"Cikin wata irin faɗuwar gaba tace"Habib?"Mai yake yi anan?

Ɗan kallanta Paki yayi yaga take yanayinta Ya chanza jinn ance baban nameer ,abu ɗaya Ya sani wanda shine wannan Habib ɗin ba baƙon maraba bane,

"Baya san mata katsalandan musamman a yanzu da yake san gina Alaƙa da ita wadda yasan zaiyyi nasara,

Juyawa yayi zai fita bayan tace da nurse farouk yace ya shigo.

"Imam paki?"

Tsaye yayi chak jin ta ambaci sunansa Kafun kuma Ya juyo yana Mai fuskantarta yace "na'am Abar alfaharina".

Kamar bataji abunda yace yayin Amsawa ba tace zauna .

Na'am?

Ya tambaya kamar baiji Mai tace ba,

Ɗaga masa gira guda ɗaya tayi tace "ba kana san soyayya dani ba"?

Zama yayi kamar anyiwa yaro kyautar sweet yace "nace a turo ne?"

Tsintar kanta tayi da yin ƙaramar dariya duba da yarda Ya faɗi maganar kafun tace"zan biya maka buƙatarka ne ta yanzu kacal ,bayan nan kuma ka fita hanyata ,just take it kamar im using you for now ".

Shafa kwantaccen sajensa yayi Yace "im here use me like a tissue amma ki sani idan na ɗanɗana sai an ƙaramun,.."

Tana koƙarin magana Habib ya turo kofar ya shigo,

Dago Kai tayi ta kallesa ,

Ya chanza sosai kamar ba shi ba,girma Ya ƙara bayyana a tattare dashi Haka zalika kasumba da Ya tara wadda a da bashi da ita,

Sallama yayi yana mai washe mata haƙora,

Haɗe rai tayi ,jan kujera yayi Ya zauna yana Mai faɗin"umaimah ina wuni".

"Wata ƴar dariya ce ta kwace mata jin gaisuwar da yayi mata Kafun tace "Ina fatan kayi wunin ka lafia habib sannan ina fatan abunda ya kawoka Mai amfani ne".

"Da saurinsa yace "Wallahi Mai amfani ne umaimah ,Kallan Paki yayi wanda tun da Ya shigo yake Kallansa ,"

Mai da Kallan yayi kan umaimah yace"wannan Ya ɗan bamu Guri mana"

Kallan paki tayi kafun ta kallesa tace "duk maganar da zakayi kayita a gabansa saboda tsakanina dashi babu wani boye boye saboda MIJIN da zan Aura ne,take gaban paki Ya yanke Ya faɗi jin abunda ta faɗa wanda yazo masa a ba zato babu tsammani,amma a wani bangaren kuma sai yaji dama daga zuciyarta maganar ke fita ,amma Shin wanene Wannan ɗin? "

Shine tambayarsa.

"Wata ƙaramar dariya yayi ya kalli Paki yace "haba umaimah ,wannan yaran kema Ai kinsan ba sa'an Aurenki bane Daga gani da kyar idan baki girmesa ba ,kodan kinga kina da kyan jiki?"

Ajiyar zuciya tayi tace"Habib idan maganar kyan jikina kazo yi nima nasan yana da kyau ,zaka iya tashi ka tafi dan Ina da abun da yafi saurarenka amfani,"

Sniffing yayi yace "kalli nan umaimah ni nasan wasa ma kikeyi,dan Allah umaimah a bar maganar Wasa tunda kuma kince nayi gabansa zanyi yasan matsayin sa,

"nazo ne akan Auren mu ,'dan Allah umaimah,nasan saki uku Ya shiga tsakanina dake amma Ai kinyi Aure har biyu wanda Addini a yanzu Ya ƙara hallarta mun ke,ki taimaka ki bani dama na rufa maki asiri Ko dan Nameer dake gurinki,"

"Nayi imani da Allah yaran nan yana buƙatar uba,Mai zai hana kizo mu sasanta kan mu?"Nasani daddy idan yaji daga gareki zai amince ,

"Umaimah look I'm a changed man wallahi duk abunda kika sanni dashi yanzu na bari."

"Lokacin imam ya fahimci wanene Habib,duk da bai san menene ya raba su ba amma tabbas yasan abunda Ya raba su babu daɗi sannan daga jin furucin Habib bawai Ya dawo bane dan Ya tuba ,Ya dawo ne dan wani boyayyen burin sa"

"Har a lokacin hankalin umaimah a kwance ,Kallan sa kawai take tana observing ɗinsa Kafun tace"Na yarda baka da kunya Habib, "

"Yanzu da kazo ka ganni anan kana nufin asirina a tone kaganshi?"

Ko na taba ce maka ka kawo taimako wa Nameer mai shekara sha daya yanzu?

Kai kana tunanin idan ni kaɗai da kai muka rage a duniya zan sake zaman aure da kai?

"Bana san sunan Nameer yasake fita a bakin ka saboda idan baka manta ba a yanzu baka da wata alaƙa dashi,"

Kalli nan'

Ta nuna masa paki ,

Kallan pakin yayi kafun tace"ka kallesa da kyau nasan ka hango qualities ɗin da baka dashi,"

Ka kallesa da kyau,He's handsome,charismatic ,hot and breathtaking,ba sai na maka wani bayani ba kasan ta ko ina Ya fika ,to ka faɗa mun Habib ina dashi Mai zanyi da kai?

Ka kalli kanka a mudubi kafin daƙikiyar kwakwalwarka ta baka shawarar zuwa inda nake?

"Ajiyar zuciya tayi har a lokacin baza kace maganar daga bakinta take fitowa ba Kafun tace "ka tashi ka fita sannan zan manta da wannan maganar Ko dan darajar Nameer da Ya shiga tsakaninmu. "

"Cike da bala'i yace"kaji mun ƴar iska 'fa ,ni zaki ma lalata har kina nuna mun wani kwartan yaro dake saka miki tayin igiyarsa da ba tayi kwari ba ,kuna kunshe a office kuna alfasha kice wai ya fini?"

"Dan na zo maki da sauki kenan,Ko kina tunanin ban san karuwancin da kike da likitocin dake asibitin nan ba ?"

To Ko wanne baya na yake sabida ni na fara farƙe ki na fara sanar dake menene wahala da zaƙin sex,ina fatan baki manta ba a yarda na ƙarbi budurcinki a wulaƙance a daren da a ka kawo ki gida na.

Ina nan a Habib ɗin da kika sani kuma wallahi sai an ban ɗana tunda bake kika yiwa kanki ciki ba kika haifesa reproduction ne daga sperm ɗin.

"Karshe ma Kin Auri ɗan kungiyar asiri masu tsafi da mutane gwara ni giya kawai nake sha banyi abunda za'a rataye ni har mutuwa ba,"Wama Ya sani shi wannan ɗin wanne kalar lalatace ne....

"Kai karshen zancensa yana dai dai da ƙaimasa naushi da paki wanda keta tafarfasa yayi a baki yana faman huci."







CHUCHUJAY ✍🏽

TBC

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top